Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 43-44

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*43&44*

 

 

………sai wajen k’arfe biyar y’an Adamawa suka iso KD”tun kafin su ida isowa suka kira Amaan suka fad’i inda suke da nufin Aje Ataho dasu”cikin d’oki ta fito rik’e da mayafinta da nufin ta sami sadeeq a parking lot su wuce tare” sbd Ammi ta kirashi yafito da mota”saidai tana fitowa sukayi clashing da shariff yadawo”d’an murmushi ta masa tana fad’in hamma kadawo?”Ina zuwa?shine Abinda yafad’a yanata kallonta be Amsa tambayar tataba”sunkuyar da kanta k’asa tayi sbd idan yana mata irin wannan kallon daburcewa takeyi….idan bazaki fad’amun ba kije mana”yafad’a yana k’ok’arin rab’ata ya wuce”sufa mommy ne suka iso shine zanbi yaya sadeeq mutaho dasu….tun kafin ta rufe baki yayi saurin katseta da babu inda zakije ki zauna ki jirasu mana”wayyo hamma! kaga basusan shiba, kuma zasu iya zaton koda wata matsala idan ba’a zo dani ba”ta fad’a tana sakin kukan shagwab’a”wani iri yaji Ajikinsa”zaki bini muje?”uhmm”tozo muje”batayi mgn ba ta d’ago kanta “ya matso ya rik’e mayafin nata”da kallo kawai ta bishi”yafa mata yayi saman kafad’arta”kafin yaja karan hancinta yana fad’in saura idan kinga su mommy ki manta da hammanki”yak’are maganar suna jerawa suka nufi k’ofa”kai hamma taya zan manta dakai?”Ai kasan bazan iyaba ko?”nasan ko zumud’in ganin family naki yasaka hakan”yak’are maganar suna isowa parking lot “sadeeq na tsaye gefen motarsa dama Agajiye yake dawowarsa Asibiti kenan Ammi ta kirashi tace suje”shariff ya kallesa yana fad’in kabarshi kaje ka huta bara muje kawai”dato ya Amsa ya wuce”su kuma suka nufi wajen had’ad’d’iyar motarsa “Amaan ta saka shagwab’a wai saiya bud’e mata k’ofar da kansa”Allah ya gyaramun ke da shagwab’a Amaan shariff “yafad’a yana bud’e mata k’ofar”ta saki murmushi ta shiga”shi kuwa sanarwa driver yayi ya zauna shi kad’ai zai fita”bayan ya shigo ya kalleta Ina muka nufa?”sunafa tasha hamma”okay”yafad’a yana tashin motar ya kunnah wa’azi “malamin nayin nasiha game da matan Auren dake k’in yadda da mazajensu babu wani dalili”sosai Amaan taji kunya”shi kuwa uban gayyar driving nasa yakeyi Anutse yana saurare”dama kuma sbd yabata kunya yasaka wa’azin”ni Allah hamma ka maida mana karatun Alkur’ani mana”shiru yamata yak’i mgn “kaji?”uhmm?nace ka maida mana karatun Alkur’ani “shi wannan wa’azin meyasa bakyason jinsa ne?”nidai Allah saika canza….ganin yadda take zuba masa shagwab’a yasaka yacanza bbu shiri yana dojewa kawai”bayan ya canza motar ta d’auki shiru ,kallo d’aya zaka yiwa Amaan kasan cikin farin ciki take”sbd zataga family nata”ba wata fira sukeyi ba”ita hankalinta na wajen waya tana danne danne shi kuma yana driving d’in yana satar kallonta…..suna shigowa cikin tashar ta hango babbar motar daddynta”wayyo hamma gasu can”tafad’a cikin zumud’i tana yarfe hannunta guda “d’aure fuska yayi ya juyo ya kalleta”ta sunkuyyar dakai da sauri”saida yagama shan k’amshinsa kafin yace”kinsan Allah kika kama wasu guje guje ko ihu saina b’ata miki rai”kayi hak’uri hamma” pls gasu can”bece komai ba yayi parking suka fito Atare….hamma yusuf ya kalli Nasir yana fad’in wow! ko waye waccan guy d’in da suke tare?”naga kamar nasan shima”da sauri Nasir yabud’e k’ofar motar suka fito”tun daga nesa yatsare Amaan da shariff da Ido”wanda kallo d’aya zaka yiwa Amaan ka tabbatar tana cikin zaman jin dad’i”sbd yadda tak’ara y’ar k’iba da haske had’e da shek’i “uwa uba kuma irin suturan dake jikinta da motar da suka fito ya Isa yanuna wa mutum ba daga k’aramin hannu ta fito ba”kasancewar su 7 ne suka zo”daddy,mommy,hamma yusuf,yaya Nasir,sai kawu bellow da y’arsa madeenah babbar k’awar Amaan”Ajere suka iso gabansu duk suna tsaye”fuskar shariff bbu yabo babu fallasa”Madeena tayi ihu tazo ta rungume Amaan suna sakin kukan farin ciki”yayinda shariff yaduk’a yana gaida dattijan biyu”wato daddy da kawu bellow”kafin ya gaida mommy dayaga kamannin Amaan Asaman fuskarta”hamman Amaan! cewar hamma yusuf yana murmushi yabashi hannu sukayi musabuha”shariff yace”kasan new name nata?”Eh mana ta bani labari”d’an murmushin gefen baki yasaki yusuf Aransa yace”lallai ba k’aramin mutum bane k’amshinsa ma na dabanne”ya Ayyana Aransa yana kallon Nasir dayaga beyima shariff magana ba yanata kallon Amaan dataje ta rungume mahaifiyarta”wanda shariff na lura dashi”haka nan yaji yaron be masa, sbd yasan yarone wajensa bazai wuce age mate d’in sadeeq nashi ba”hakan yasa ya d’auke kansa ya tsaya gefen su daddy suna mgn”daga bisani duk kowa ya shige mota”sanin halin mutumin nata besan surutu yasaka bata ja madeenah A motar ba tace ta shiga tasu daddy”ita kuma tabi shariff “motar su Amaan ce daga gaba sai tasu daddy Abaya suna binsu”shariff duk yabi ya d’aure fuska Amaan batama luraba sbd farin cikin datake ciki”tun kafin su iso Ammi ta shirya musu liyafa ta musammun Atsakkiyar carpet Aka shirya musu komai”tunda suka doso Anguwar family d’in Amaan suka tabbar shariff ba k’aramin mutum bane”sbd sunsan Anguwar Bata talakawa bace “basu gama mamaki ba saida suka doso gidan sukaga securities bakin get sun bud’e musu get”dakewa kawai sukayi basuyi k’auyanciba”Amma sun tabbatar shariff yana daga cikin masu Arzik’in garin”sbd ganin katafaren gidan nasu Anguwa guda….lolx”bayan duk sun fito”shariff yakira Ammi gasunan zasu shigo”Atare dasu daddy sukayi gaba”yayinda Amaan ke tare da mommy da madeenah Abayansu suka wuce ciki da sallama”Ammi na zaune kan kujerah da hijabi Ajikinta tasha shiga ta Alfarma “ta mik’e tsaye ta tarbesu da sakin fuska had’e da maraba”tun Anan suka fahimci Amaan ta had’u da mutanan Arzik’i”kowa zama yayi suka gaisa”mommy da daddy suka gabatar da kawu bellow Amatsayin yayan mommy”sannan suka dinga zuba musu godiya da Addu’ar gamawa da duniya lafiya”had’e da sakama shariff Albarka”Ammi tace”babu komai kuci Abinci ku huta mlm zaizo yakoma yi muku bayani sbd Ad’auki matakin daya dace “Nasir dai na zaune yana tab’e baki Aransa yana mamakin meyasa salma bazata tanka shiba?”koda da sunan gaisuwa ne”ya lura sai mannema wannan me girman kan takeyi(shariff)”babu wata kunya ya kalleta yace”salma bazaki gaisheniba ko kuwa girman kai kika koya ne?”gaba d’aya duk suka bishi da kallo”dama mommy bataso Akazo dashi ba”tab’e baki Amaan tayi tace”ba mamakin girman kai d’in na koya”wani kuma be iya mgn ba komai yazo masa furtawa yakeyi”tsabar b’acin rai shariff barin parlourn yayi”Amaan na lura dashi”Ammi ta mik’e tsaye tana fad’in Amaan pls suci Abinci sai Akaisu masauki su huta ko?”dato Amaan ta Amsa Ammi tabar parlourn “daddy yaja tsaki yana kallon Nasir yace ka iya bakinka wlh”dama kunya ka biyomu ka bamu ne kome?”k’in mgn yayi fuskarsa bbu walwala…..bayan sunci sun k’oshi mazan suka tafi sallar magrib a masallaci”bisa jagorancin sadeeq”wanda tunda yaga madeenah yarasa natsuwarsa lokaci guda yaji yarinyar ta kwanta masa Arai”sai bayan sallar isha’i suka dawo”sadeeq yakai daddy da kawu bellow sashen bak’i”kafin yaja hamma yusuf sashensa”Nasir kuwa shima d’aki Aka bashi”mommy da madeenah ma haka”Amaan na lik’e dasu sunata fira”sai wajen k’arfe 8:30 mlm da mus’ab suka iso”kafin Akira kowa”sharif na zaune gefen mus’ab Acikin parlourn fuskarsa Ad’aure yak’i kallon inda Amaan take”Nasir da gayya ya zauna gefen Amaan d’in yana mata mgn k’asa k’asa “mus’ab na lura da yanayin da shariff yashiga”yadinga dariya Azuciyarsa “sbd yasan kishine kawai ke damunsa”yanaso yamasa zancen shin son Amaan yakeyi?”saidai halinsa daya sani yasaka yabarsa”idan tayi tsami zaizo masa da maganar…bayan sun gama gaisawa mlm yamusu bayanin komai”daddy ya sauke numfashi yana sanar musu Abinda yafaru Acan da irin kalaman zabba’u da Abinda yafaru da ita”….mlm ya numfasa kafin yace”to hak’ik’anin gaskiya itace silar komai”fatanmu Allah ya shiryi masu irin hali nata”yasaka Abinda yafaru da ita yazama iznah ga y’an baya”babu tantama sihirin yakoma kanta”sauk’in abun An farga An rik’eta bata tafi ba”saidai idan Akayi mata taimako zai k’arye ko Anemi bokan da yayi Aikin ya karya”idan har zamu gane kuma mu yadda da hukuncin Allah Tofa zuwa wajen mlm ko boka bazai Amfanemu dako maiba sai rasa Imani”domin duk Abinda Allah yatsara bbu mahaluk’in daya Isa ya canza hakan”wannan gaskiya ne mlm muna godiya da jajircewa da taimakonka”Allah yabaku ladar baki d’aya”cewar kwu bello duk suka Amsa da Ameen “bayan sunyi sallama shariff yabisu suka fita”koda suka tafi ta k’ofar baya yabi yanufi sashensa”tun Amaan na saka idon ganin yadawo harta dena”gaba d’aya sai taji babu dad’i”tarasa wane irin murd’add’en mutum ne hammanta?”tayi iya tunanin ta hango laifin data masa Amma bata gani ba”tanaso ta kirashi Amma tunanin be tab’a kiran taba daga jiya zuwa yau yasaka ta fasa”madeenah na lura da ita kamar tanada damuwa tabarta dai sai zuwa safe”dan Amaan cewa tayi wajen Amminta zata kwana…..washe gari tunda safe Amaan da madeenah dasu jummai suka had’a break fast”Ammi na tare da mommy sunata firansu irinta manya”mommy Anan tasan mahaifinsu shariff yarasu…suna zaune d’in shariff ya shigo ya gaidasu”yana lura mahaifiyar Amaan najin nauyinsa”kasancewar dama ya gaidasu daddy a masjeed bayan sun fito saiya wuce sashensa kawai……bayan sun idar da komai suka wuce suka shirya”ba k’aramin kyau Amaan tayiba saidai ganin duk safiyar bata saka shariff a idon taba taji damuwa”kowa sashen dayake Aka kaimasa Abin kari”su mommy ne kawai suka karya Amain parlour “Amaan dai takasa zama ta karya Ammi na lura da ita”kan idonta taga ta shirya komai na break fast saman wani babban tray ta d’auka ta nufi upstarts”Ahankali ta turo k’ofar ta shigo da sallama”shariff na zaune kan 2 seeter”yasha zazzafan wanka”yana jin sallamarta zuciyarsa ta tsananta bugawa”ita kuwa Ahankali ta Ajiye tray d’in saman center table ta zauna gefensa” k’amshin turaren ta me sanyi yadaki hancinsa ya lumshe kyawawan idanuwansa”sassauta murya tayi tana fad’in wai hamma meyasa kaketa fushi kak’i walwala tun jiya??”kasan ko Abaya da bana A hayyacina Ina damuwa idan kana fushi dani balle yanzun”kafad’amun laifin mena maka zan dena wlh! ta fad’a cikin shagwab’a kamar zata fad’o masa Ajikinsa “ya kawar da kansa fuska bbu walwala da k’yar yace” wanene wannan yaron me red d’in t shirt? shine Abinda yafad’a yana maida idanuwansa ya kulle”k’irjinsa na wani irin bugawa”yayinda kasala da mutuwar jiki suka dirar masa lokaci guda sakamakon shagwab’ar da Amaan keta masa….idan bazaki iya fad’in waye shiba tashi ki koma inda kika fito?”yafad’a still idonsa Arufe sbd yaga tak’i yin mgn”Amaan kuwa Aranta tace”na fika miskilanci hamma”baka sanniba sadda nake Agida shiyasa….bakiji mena ceba ne? yafad’a yana bud’e idanuwansa da har sun fara canza kala”tabbas taso taje tabarsa saidai irin hallacin data tuna yamata Arayuwa yasaka bazata iyaba”dama Ina wasa ne dake?? yak’are maganar yana zaro mata manyan idanuwansa “ta b’ata fuska tana fad’in Ada wannan fad’an da tsawar taka ke tasiri kaina hamma”yanzun bana jin irin wannan tsoron naka”saidai Ina tsoron fushinka da bacin ranka”wanda kake tambaya yaya nasir ne”kuma ni yanzun na tsanesa ko?”dama duk dan sbd shine yasaka kaketa fushi ko Abinci baka ciba nima na kasa ci sbd kanata fushi….ta k’are maganar tana shure shuren k’afafuwa”yabita da kallo kamar tv”ganin zata mik’e tsaye tabar masa parlourn yasaka yayi saurin rik’e gefen rigarta yana fad’in kinsan dai natsani irin haka ko Amaan?”niba sunana Amaan ba”d’an murmushi yasaki yanata kallonta yace”sunanki kenan kuma ko Acan Adamawa da haka zasu dinga kiranki yarinya”tasaki kukan shagwab’a tana zama gefensa”fad’amun ya sunanki?”yafad’a yana matso da kansa gab da fuskarta har tana jin hucin numfashinsa” yanayin yadda yayi mgn saida taji gaba d’aya jikinta ya mutu murus….oya fad’amun sunanki”tana dariya ta rufe idonta tace”sunana *Amaan shariff* tafad’a tana b’oye fuskarta Atsakkiyar cinyoyinta tana dariya”shima murmushi ne shimfid’e saman kyakykyawar fuskarsa yana jin farin ciki da nishadi “nauyin da zuciyarsa ta masa yana jin ta rage”meye haka?”oya d’ago fuskarki ki fad’amun Ainahin sunana”batayi musuba ta d’ago suka had’a Ido”hararar wasa ta masa tana kauda kai”shi kuma yayi k’asa da murya yana fad’in me kuma nayi kike hararata Amaan?”k’in mgn tayi tana kallon warmers d’in Abinciccikan dake saman center table ta matso da center table d’in gabanta tafara zuba masa Abincin”shi kuma yana satar kallon ta”Aransa yana k’ara girmama ikon ubangiji”daya Azama Amaan wannan lalura yakuma yaye mata….Hamma bissimillah”ni bara naje nakomyin wanka” nasan yanzun kacemun k’azama”na k’oshi! Atake Amaan ta had’e rai tana fad’in shikenan nagode”sbd kema baki ciba”ki zauna muci mana”Amma hamma kar Ammi taga na jima ko?kodai kina gudun kici Abinci dani ko?”ah ah wlh ba haka bane”bece komai ba ya d’auki plate d’in doya da k’wai da farfesun kayan ciki ya sakko k’asa yasaka musu spoon”itama sakkowa k’asan tayi ta zaunah”saidai ya fahimci ta kasa sakewa”yana kallonta yace”dama ni ba k’onkine ko? dazaki k’i sakin jikinki dani?”idanfa kinyi hak’uri Amaan tafiya zakiyi gobe kibarmu da kewarki ko?”ai zamu dinga waya da Ammi da Abdallah da yaya sadeeq”nifa bandani?”ya tambaya yana langab’e mata kansa kamar wani k’aramin yaro yana kallonta”murmushi yasub’uce mata tace”hamma nah ! kai Ai any time muna tare ta waya saidai idan ko Aiki kakeyi ko?”hakane “na d’auka Ai zaki manta danine?”nina Isa nayi hakan”ta fad’a suna fara yin break fast d’in “sai janta da firar dabaiyi zaton ya iyaba yakeyi har suka cinye Abincin tas”ta zuba masa ruwa”yasha yabata sauran ta shanye”Ahankali tace”bara naje”ni baza’a ce nayi wankan ba?”to hamma naga duka befi Awa guda naganka ka canza kayaba”nasan kuma wanka kayi ko?”hakane”to yanzun zanje nayi wankan”bafa yau zaku wuceba sai gobe mun gama mgn da daddy”to shikenan hamma”ta fad’a tana kwashe kayan da suka yi break fast d’in”na taso na rakaki?”uhmm! beyi mgn ba yamik’e tsaye suka jera suna mgn suna murmushi suka sakko k’asan”gaba d’aya mutanan dake cikin parlourn suka bisu da kallo”nasir yatab’e baki yana jin dasun koma gida zaiyi mgn abashi kud’in gaisuwarsa yafasa Auren”wayasan ma data bishi upstairs d’in me suka Aikata?”k’ilanma da bata hayyacinta yabata mata rayuwa”sbd bbu lafiyayyan namijin dazaiyi Arba da ita tana cikin wannan yanayin yabarta”sam bazai Auri sauran wani ba dama sbd kyawunta yake sonta….✍️

 

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button