Ni da Patient Dina Book 2 Page 37
Haka tanzarzar yabace yabarta batare dawani taimako ba , fitowa Mansoor yayi daga bedroom dinshi rikeda shisha pot idonshi ne yasauka akan mommy dake kwance tana fitar da numfashin wahala arazane yanufeta yana ” mommy meya sameki haka? Waye yamiki wannan abu?” Ahankali ta iya cemai yakaita dakinta ciccibarta yayi yakaita yana mata sannu.
_____ tana zaune agaban mirror tayi light make up tana sanye da dakakkiyar lace me tsada dinkin dogon riga fitted gown wuyanta yasha sarka da dan kunne na gold tayi kyau sosai takafa dauri , Allah Allah takeyi tagama shiryawa taje ta gaida su abba dan rana harya dan fito karfe 10:30 gama shiryawan tayi tadau gyale tasa da takalmi hill tana tafiya kamar wata me tsoron taka kasa shigowa falo tayi tanajan kofan bedroom dinta jin muryan aneesa tayi se zuba surutu takeyi mamakine yakamata wai ita wannan bata da aikinyi se makalewa mutane, karasowa falon tayi taganta tana zaune atare da Mr azaad jikinsu amanne yakwantar da kanshi ajikin kujeran dasuke zaune idonshi alumshe kamar wani me bacci dan gaba daya surutun aneesa ya isheshi, cike da neman magana taje kusa dasu tatsaya akansu tana rike kugu ” ke kam aneesa wace irin mayyace mara zuciya ban rabaki da mijina ba? Kinzo da sassafe zaki hanashi hutawa to baki isaba ki tattara kibarmin part ko kuma inyi maganinki ” tana magana ta jijjiga jiki kamar dagaske in anbarta da aneesa din iya dukanta zatayi . Slowly yabude idonshi akan kyakyawar fuskanta shide yagaji da lamarin fanan ciwon kai takesashi dan yalura bajin magana takeyi ba inya biye mata ze iya karyata abanza a wofi.
Sake shigewa jikin azaad aneesa tayi tana fadin ” to badole inzo ba keda kwata_kwata bakya bashi kulawa baki masan yanda zakiyi da miji ba so he needs me by his side ! Kinga ni zan mishi abinda bazaki iyaba tunda haryanzu baki gama girma ba” dan zare ido fanan tayi tama rasa mezata fada mata wanda ranta zeyi mugun baci, samun kanta tayi dafadin ” aneesa shiyafada miki haka ? To bari kiji jiya kwana mukayi bamuyi bacci ba gabaki daya yanzu haka agajiye nake kawai karfin hali nayi zanfita gaba daya yasa jikina se ciwo yakeyi abinki da yarinya nasan dakece goggiyar yar duniya nasan Koda wasa bazakiji kingaji ba to nina tafi se anjumanku ! Honey sugar bye” tana fadin haka kuwa tayi waje batare da jira amsar da aneesa zata miyar mata ba.
Mr azaad kam he’s totally out of words lamarin fanan goge mishi hadda takeyi yarinya karama da zaro manyan maganganu kwafa yayi yana fadin ” zaki dawo kisameni” ya shige bedroom dinshi yabar aneesa afalon ta cika tayi bam kamar zata fashe.
Ahankali take taka staircase din gaba dayansu sun hallara afalon daga gani abu me mahimmanci suke tattaunawa, tsugunawa tayi tagaida abba da ummi,anty Zainab dasu anty Amina gaba dayansu seda tabisu tana gaidasu, suka amsa da murmushi akan fuskansu areef ne yace ” Ina kwana anty ? ” Hararan wasa tawurga mishi tana ” Allah ya areef banaso kabari ” zeenat ma tace ” anty fanan ina kwana” banza tayi da ita, dariya sukayi duka , anty shayida tace ” yauwa kingama maganarki akeyi segaki nan ” murmushi tayi tace ” to anty gani ” fawwaz ne yace ” daman maganar bikinku akeyi kinga kwata_kwata baayi komai ba, so nan da 1 week ko 2 weeks zaayi event din bikin dinner ne da kamu se walima ” shuru tayi tana tunanin itada zasu rabu da Mr azaad meye kuma na wani shagalin biki, tana jinsu se tsara yanda bikin ze kasance sukeyi.
Abba ne yace ” Fatima gobe dukanmu zamuyi tafiya zamu tafi dubai yiwa kakansu zeenat yajiki kwana biyu bayida lafiya bazamu dade ba munso tafiya dake amma kinga ke bakida visa inmun dawo zaku tafi tare da mijinki daga yanzu zuwa lokacin komai dinki zezama ready” cike da kunya tace ” to Abba Allah yakaimu” Suna haka se gashi yasauko cikin shirinshi nazuwa office yasha kyau suffarshi ta larabawa yakara fitowa, sakai yayi zefita abba yace ” azaad zo nan” dawuwa yayi yazauna kusada abban .
__” yauwa namanta banfada maka ba next week inmun dawo in sha Allah zaayi event din aurenka ” kaff dinsu zuba mishi ido sukayi dan sonjin mezece.
Yau tunda yatashi bayajin yin wata dogon magana ciki_ciki yace ” auren waye din ake magana?” Ganin yamanna musu haukane yasa ummi cewa ” son auran kai da fanan mana kuma bawai shawaranka muke nema ba! Ah ah munriga da munzartar seka fara shiri zaka iya tafiya” mikewa yayi besake ce musu komai ba dan shibawai ya iya musu bane kuma yasan insukayi magana ba canzawa zasuyi ba.
8:00pm tana zaune afalo tana kallon series din India atashan zee word me suna the promise, jikinta nasanye da guntun wando jeans boom short da wata yar ficikar riga iya cibiya batasa bra ba rabin dukiyar fulaninta awaje wandon yadámeta tam tayi donot da gashinta sosai tayi kyau kamar wata bakar balarabiya, duk da kana nan kayane amma haka taji sundame ta haka tadaure taci gaba da kallon.
___ bashi yashigo gida ba har 9:00 part dinshi yanufa hannu yakai kan handle din ze murda yaji kamar karan tv shiga yayi yahangeta tana zaune tana kallo se shan fruit takeyi batama san da shigowanshi ba, zama yayi akan kujeran dake facing dinta se anan ne taganshi ” barka da dawuwa Mr azaad” bece mata kalaba yacire socks din kafarshi yafincike necktie din , tunda tagaidashi be amsa ba bata kara kallon inda yake ba .
” Ke tashi kikawo min tea ” tashi tayi tashiga kitchen tahada mishi tea tadawo falo bata sameshi ba yasa tawuce bedroom dinshi nanma baya ciki ajiyewa tayi akan center table tana kokarin juyawa taga yafito daga toilet yana daure da towel akugunshi, runtse idonta tayi gam dan tunda take bata taba kallon namiji ahaka ba , karasowa wajanta yayi yasa dukka hannunshi yatallafo fuskanta
Murya anarke yace ” miyasa kike rufe idonki bayan kina gaban mijinkine ! Ohhh namanta ashe yanzu lokacin dazaki bani kyakyawar kulawa ne oyah Start” gabanta ne taji yana duka da karfi tuna abinda tamusu da safe shine yanzu yake dauko mata maganar, dasauri tajuya da niyar tafiya fincikota yayi tafado akan faffadar kirjinshi dayake dauke da kwantaccen gashi jikinshi gashi ajike da ruwan dayayi wanka gashin kanshi se diga yakeyi mannata yayi da jikinshi hannunshi daya narike da waist dinta.
Wani kalan kunyarshine yarufeta tarasa yazatayi tabar dakin. Ganin haryanzu taki bude idanunta ne yasashi sake matseta ajikinshi ba shiri tabude ido,
Kallon fuskanshi tayi taga kalan kallon dayake mata nan take tasunkuyar dakai kasa dan bazata juri kallon kwayar idonshi ba , sa hannu yayi ya dauketa kamar yar baby besauketa a ko inaba sekan bed dinshi . kokarin tashi takeyi yasa hannu yamaida ita yamata rumfa kwanciya yayi ajikinta yasake mata nauyinshi duka nan take tafara nishin wahala dan jitayi kamar wanda aka dorawa buhun cement ajiki tureshi takeyi amma ko motsawa beyiba zatayi magana yadaura yatsanshi a libs dinta ” shhhh don’t say a word ! Kikace jiya bamuyi bacci ba saboda kinbani hakkina? Tom bari inbaki yanzu tunda haka kikeso , aibansan kinaso ba da tun ranar da aka kawoki gidan nan nabaki ” fanan ido yarena fata inbanda danasani babu abinda takeyi nan take hawaye yafara wanke mata fuska dan talura Mr azaad babu wasa alamarinshi. Slowly yafara zame mata rigan jikinta harya kawoshi zuwa cikinta sa hannunta duka biyu tayi tarufe kirjinta tana kuka ” please Mr azaad don’t do this to me” dede kunnenta yafurta ” I will! abinda kikeso kenan tunda har kika iyayin shela na gajiyar dake bari ayi na gaskiyan karki damu it won’t be hurt” daduk karfinta take dukan kirjinshi tana kuka da rokonshi daya kyaleta bazata karaba.
Hade bakinsu yayi waje daya yafara bata hot kiss harda na mugunta na cizon libs dinta da karfi sosai take kuka tana tureshi amma ko motsawa bayayi seda yatabbatar da ta mugun galabaita kafin yadakata yadago yakalleta yana wannan killer smile din nashi dayake kara mishi kyau, shafa libs dinta yakeyi da yayi jajir yadan kumbura dan bakar wahalar dayasha yace ” tom yanzu saura inbaki hakkinki ko?” Hawaye na gangarowa daga idonta tace ” kayiwa Allah daya halicceka Mr azaad kayi hakuri kabarni” watsa mata harara yayi yace ” stupid girl bakince ke mara kunya ba naso yau inga karshen inda rashin kunyan zetsaya yarinya tunbaki tafasa ba kina kokarin konewa harkinsan kicewa wata mijinki ya gajiyar dake saboda taji haushi ko? ” Girgiza kai tayi alamar ah ah matse libs din yayi seda tayi kara” ni kurmane dazaki girgizamin kai kokuma ke kurma ce? common open your mouth and talk joo” cikin muryan kuka tace ” ah ah ” kwafa yayi ” I warned you several times amma naga kamar kwata_kwata taurin kanki yahanaki saurarata to muzuba nidake agidan nan kedajin dadi kuma se randa narubuta miki sakinki as from today you’re my maid duk wani aikace_aikacen part din nan ke zaki dingayi inkuma ba hakaba ” ya kyasta yatsunshi afuskanta, yatashi daga jikinta kifa kanta tayi akan pillow tana kuka daga baya ta tashi tashige bedroom dinta ahaka tacigaba da kuka daga baya bacci yasaceta.