Ni da Patient Dina Book 2 Page 36
Mommy wallahi sena kasheta inbahaka ba hankalina baze taba kwanciya ba ” cewar aneesa dake magana tana kuka tsaki mommy tayi tace ” yanzu ke ko kunya bakiji ba kanwar bayanki zaki tsaya kina mata kuka baki kamata ba kin manta jakin duka ! Wallahi shame on you” sake fashewa tayi da kuka tazo tafada mata instead of sunemi solution tahau ta da fada lura da hakan ne yasa mommy takwantar da murya ” is okay my angel karki damu yau yau din nan zandau mataki setayi danasanin abinda ta aikata miki karki kara shiga part din se gobe kinji ko angel din dadi” sake fuska tayi tana murmushi seyanzu hankalinta yakwanta jin mommy tace zatadau mataki akanta.
Har seda time din sallah yayi ta farka taje tayi sallah har time din tana tuna bakaken maganganun da Mr azaad yamata haka tazura dogon hijab dinta tayi falon ummi samun zeenat tayi afalo tana shan rufaida yogurt zama tayi tana karban roban yogurt din tafara sha sake baki zeenat tayi dan batasan da shigowarta ba tace ” ikon Allah anty fanan yaushe kika shigo ” tana Shan yogurt din tace mata ” sanda kike kwadayi mana” dariya zeenat tayi tace” to naji ya kike ya program munganku a tv alhamdulillah komai yatafi successful yanda akeso” ” hmmm kede bari kawai nikadai nasan irin farin cikin danake ciki ” hira sukeyi har anty Amina tafito tasamesu kallon fuskan fanan tayi taga alamar tayi kuka kiranta tayi wajanta fanan taje tazauna waigawa tayi ga zeenat tace ” to anty kwadayis kidan bamu waje zamuyi magana ” tashi tayi tayi dakinta maida kallonta tayi kan fanan sannan tace ” my fanan meke damunki wani abu azaad yamiki ” dasauri ta girgiza mata kai alamar ah ah ta fahimmci tanason boye mata ne yasa tace ” karkimin kallon sirka kidaukeni amatsayin antynki firdausi duk wata damuwarki karki boyemin dakuma tsakaninki da azaad semu samo solutions kinji” sosai hankalinta yakwanta dan dama tarasa wazata fadawa damuwarta , bata labarin tun daga dawuwarsu da shaketa da aneesa tayi har izuwa abinda Mr azaad yamata dakuma maganganu daya fada mata. Jinjina kai tayi dan tasan zaa rina kuma bakomai yasa yakula aneesa ba sedon taji haushi amma yanzu dole tadaura fanan akan hanya dazata gyarawa azaad zama dakuma ita kanta aneesa datakeson takurawa rayuwarsu.
____” kinaji abinda kikayi yau kinmin dede domin inkika sake kika kyale aneesa tsaf zata renaki sannan inason kinunawa azaad ke ba yarinya bace kamar yanda yafada shida kanshi zedawo yana baki hakuri da lallabaki ! Tunda harya ce miki kwaila yayi mukuma zamuyi iya kokarinmu dan muyi proving dinshi wrong ” zare ido tayi tana kallon anty Amina kamar amafarki ” yanzu Mr azaad dinne zewani lallaba mutum har yabada hakuri tabb ” sosai anty Amina ta dinga bata shawarwari tayanda zatajawo hankalin Mr azaad duk da fanan tanajin kunyan wasu Abubuwa amma haka tanutsu tana sauraran anty Amina dan tadau aniyar nunawa Mr azaad ita ba yarinya bace. Farin ciki anty Amina tayi ganin fanan tadauki shawararta dakuma wayon data mata yayi tasiri dan ita tayi hakan ne da tasamu su dede ta kansu dan tasan yanda Mr azaad baya son fanan, haka itama fanan bata sanshi auren kawai Allah yayi de zaayi shine .
Duk sunyi sallah isha suna zaune akan dinning zasuyi dinner kowa ya hallara harta Mr azaad yafito serving dinsu akayi suka faracin abinci kwarewa fanan tayi tana yar tari kadan_kadan suna mata sannu abu kamar wasa tari yayi karfi hartana biga kanta da table din gaba daya rudewa sukayi suna mata sannu anty Amina da ummi suna bubbuga bayanta. Nan take kuma tarin yatsaya suka bata ruwa tasha idonta yayi ja dan wahala , rike wuyanshi yayi dayaji kamar anshake shi jin shakewan yayi yawane yasa yamike rike da wuyanshi yana kakari kamar wanda zemutu tashi sukayi arude suna nufo wajanshi sosai aka shakeshi amma su basa kallon kowa se rike wuyanshi dayayi babu yanda basuyi ba dan su cire hannunshi akan wuyanshi amma sun kasa. lokaci daya jikinta yayi wani irin kaduwa akayi walkiya da karfi farin haske yarufe ko ina tashin hankali baasa mata rana gaba daya yau sunga abinda basu taba gani ba hasken seda yakai 5mint kafin yawashe duk sundukufa akan Mr azaad dake kakarin mutuwa se adduah sukeyi mishi ga farin hasken daya tsorata su mikewa azaad yayi yazauna yana sake wuyanshi jin ansakeshi , Karan sarkan kafa sukaji duk taku daya idan tayi se yayi kara juyawa sukayi domin ganin ta idan karan kefitowa tozali idonsu yayi da SARAUNIYAR nasminaya cikin shiga ta jarumar sarauniya dakuma sadaukiya wacce ta amsa sunan ta jaruma farin wando ne me fadi kamar wandu nan Pakistan kafan wando kamar ansa mishi roba se riganshi me hannun vest tsayinshi har kusada guiwanta farin kayane sol anmishi kwalliya da zinari domin kayan da sarki da sarauniya suke sawa ma daban ne asaman kayan kuma ga irin rigunan nan kamar nakarfe da akesawa idan zaa fita yaki bayanta nadauke da kwari da baka dasuke cikin gidansu akillace suna jiran kota kwana. se kugunta dake dauke da wukane dogo na sarauta awajan , kunnent,wuyanta duk suna sanye da sarka da dankunne harta dantsen hannunta nadauke da wasu irin saraquna , kafanta tana sanye da sarkokin kafa na zinari dawo da kallona na iya izuwa fuskanta da kanta gashinta nagani yakara tsayi amma bawani sosai ba yayi curly anzubasu agefen wuyanta nadama dana hagu sauran kuma suna gadon bayanta anmusu kwalliya da sarkan kai ( head band chain) ga crown akanta me matukar kyau fuskanta kamar wacce akayiwa kwalliya ( umm to aidole ma aga fuskar sarauniyar aljanu da kwalliya ) dan karamin bakin nan yasha dark maroon janbaki idonta na sheki sosai .
Fuskanta ahade kamar hadari gaba daya ta tashi daga fanan din dasuka sani se takoma ainihin sarauniya babu abinda takeyi daya wuce yalki saboda gwala gwalan dake jikinta gaba daya gakuma daddadar kamshin dake fitowa ajikinta wani irin masifar kyau takara . Suman tsaye sukayi suna kallonta tunani suka farayi kode yaune ranar komawarta masarauta gaba daya sukaji tayi musu gwarjini jikinsu yayi sanyi, tafiya tafara kamar wacce take lankwasa jiki da gangan takaraso wajansu ko kallon direction din dasuke batayiba tasa hannu tashake iska tunani suka farayi meye to tashake dansu basu ga komai ba. Cikin wata murya me zaki da amo tayi magana tana karkata kanta gefe kamar wata robot ” ki bayyana kanki ” seda falon ya amsa da muryanta aikuwa tana gama fadin haka wata halitta tabayyana cikin bakaken kaya mara kyaun gani seda sukaja baya banda azaad.
Dagata tayi suka fara tafiya a sararin iska acikin falo seda suka kusa roof din falon suka bace batt.
Sunshiga cikin damuwa yanzu shikenan bazasu sake ganin fanan bah kenan zeenat se kuka takeyi, iyayenta zasuji zafin tafiyanta batare da sunyi bankwana ba, Mr azaad ne yace ” Amma ai waadin tafiyanta beyi ba bekamata ace tunyanzu harta tafi ba ” abbane yace ” Kuma hakane waadin tafiyanta beyi ba taya zaayi ta tafi yanzu kila abinda yafaru harin da aka kawone yasa jaaazana bayyana ajikinta da sauri ” jimami suke tayi har sha Daya nadare basu kwantaba wani security ne yashigo falon da gudu haryana kokarin faduwa zuba mishi ido sukayi suna kokarin tambaynshi lafiya yayi saurin fadin ” ranka yadade naje zanrufe kofan garden ne naga mutum akwance awajan jin haka yasa Mr azaad fita da sauri yafice yanufi gadin din suma suka rufa mishi baya tundaga nesa daya hango hijabin jikinta tana kwance plat bata motsi yaganeta sa hannunshi yayi yadagota kamar yar babyn roba yayi ciki da ita ahanya yahadu dasu ummi duk sunfito sunbi bayanshi ganinshi dauke da itane yasa suma suka koma ciki haurawa yayi da ita part dinsu dakatawa sukayi afalon suna alhamdulillah sannan abba yacewa kowa yaje yakwanta se gobe haka kowa jiki amace suka tafi.
Direct bedroom dinshi yayi da ita yakwantar da ita akan bed hannu yasa yacire mata dogon hijab din jikinta da kayanta yarufeta da blanket yashiga bedroom dinta yabude wardrobe yadauko sleeping dress white color me guntun wando yadawo yasa mata kallon kirjinta dake cike da dukiyar fulani yayi nan take yaruntse ido yanajin haushin kanshi naganin dayayi mata yagyara mata kwanciya, yayi toilet bayan kamar 15mint yafito yayi wanka yasa sleeping dress dinshi yahau bed din dan nesa da ita kadan yaje yakwanta yana rufe jikinshi da blanket yayi musu adduah yakashe wutan dakin yabar bedside lamp.
____ cikin dare tafarka da zazzabi jikinta rau zafi cikin bacci yaji kamar sheshekar kuka tashi yayi zedubata yagansu manne da juna yana rungume da ita ajikinshi kokarin raba jikinsu yakeyi tasake rikeshi tana ” uhmm uhmm sanyi nakeji karka tashi” tafada ashagwabe kallon fuskanta yayi da hasken dake gefen bed din idonta arufe ga hawayen datakeyi gashin idonta sunyi zara_zara seturo baki takeyi duk abinda take fada acikin baccine da zafin zazzabi kallon cute face dinta yayi yasamu cikin dabara yatashi toilet yaje yadibo ruwa a bowl medan fadi yafito da karamar towel ahannunshi zama yayi akan bed din yatallafo ta jikinshi so yakeyi yadan goge mata jikinta da ruwan sanyi saboda zafin da jikinta gashi dole seya cire yacire mata riga amma yana tunanin karta tashi tayi tunanin wani abu tazo ta renashi he has no choice hakan yayi yacire rigan yafara goge mata jikinta da towel din jin hannunshi na gogan kirjinta ne yasa yahakura yamaida mata rigan yakwantar da ita locker dayake ajiye magunguna shi yabude yadauko mata magani tashinta yayi , kallon fuskanshi tayi tace ” miye! miye ? katasheni nikam bacci zanyi ” sa mata magani yayi ahannunta yace tasha bata fuska tayi ganin kwayan magani fashewa dakuka tayi nikam ” bazan shaba ” tafada tana make kafada ganin inya biye mata dagasken bazata shadin ba, yasa yawatsa kwayoyin maganin cikin glass cup suka jiga dan kwantar da ita yyi ajikinshi yasa hannu yamatse bakinta yadùra mata kakarin amai takeyi yahade bakinsu waje daya seda yatabbatar aman ya koma kafin yakwantar da ita shima yakwanta manne da ita ajikinshi
Karfe 5 dede tafarka jinta ajikinshi yasa tayi saurin tashi sosai abin yadaure mata kai metakeyi ajikin Mr azaad akuma dakinshi duk abinda yafaru adaren jiya ta manta kallon jikinta tayi taga kayan datake sanye dasu waro ido waje tayi data tuna ai ita dogon riga ne da hijab ajikinta taya akayi suka dawo kayan bacci kuma gata a dakin Mr azaad zuciyarta ce tace ” waye kike tunani zeyi haka Mr azaad ne mana” cikin sauri takalleshi bacci yakeyi abinshi hankali kwance sadaf _ sadaf ta tashi tabar dakin tashiga nata dakin wanka takesonyi dan kwata_kwata batajin jikinta da karfi.
To bari muleka bangaren mommy.
Awurge a tsakiyar falonta nahangota acikin mawuyacin hali se numfashi takeyi dakyar kamar zata mutu kayan jikinta duk ya yayyage ga jikinta nafitar da jini kamar wata al majira. Abinda yafaru shine bayan tayiwa aneesa alkawarin gamawa da babin fanan atime din dasuke dinner taje da niyar kasheta tayi iyayinta ana haka taji anbuga ta da kasa kallon wacce tamata hakan tayi taga ashe khairatyyy ce ganin mission dinta na kashe fanan beyi bane yasa takoma kan azaad kokadan khairat batayi yunkurin hanata ba domin ita umarnin kula da sarauniya kawai jakadiya tabata. Ganin zaayi kisane yasa wani bangaren jaaazana yamotsa shisa fanan ta bayyana a ainihinta ta sarauniya domin takareshi cike da jindadi ganin sarauniya tabayyana khairaty ta duka kasa cikin girmamawa, lokacin da sarauniya ta rike mommy suka bace sararin samaniya takaita tamata mugun duka kokarin ramawa mommy tayi amma ina ko kadan karfinta beze iya da sarauniya ba haka tanaji tana gani taji mata mugun raunika ajiki sannan tasaketa tafado kasa dakyar mommy ta iya lallabawa takoma gida.
___ wasu irin sambatu tayi nan take tanzarzar yabayyana yana wannan dan iskan dariya nashi mara dadinji kafin yafara magana ” hafsat nadade da fada miki da ki nisanta kanki da ita gashi yanzu kinjawa kanki ina matsayin shugabanki amma kikasa bin umarni na wannan shine hukuncnki babu abinda zanmiki kije kiyi jinyar jikinki taurin kai yanzu yamiki rana ai” ya karashe maganar yana dariya me karfin gaske kafin yabace bat.
Masha Allah masoyana inata ganin ruwan comments da adduah ina godiya sosai Allah yabar kauna love you Lodi lodi
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
⚕️⚕️ NIDA PATIENT DINA
Story & written by
MRS ISHAM