Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 46

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*46*

Inna tana zaune a falon kasa tare da aminiyarta Hajiya luba da Kuma anty Balqis wacce yanzu Koda yaushe suna tare a waya ko a gida, suna tattaunawa kan zancen auren hajjo ne ita inna tafison hajjo ta kammala karatun inda anty Balqis kuwa ke nuna mata ayi bikin ta karasa a d’akin mijinta, bugun kofa sukaji shine yaja hankulansu saboda bugun da karfi Ake Babu kakkautawa anty Balqis tace ” Amina waye Kuma haka ?” Wallahi anty bansani ba bari na duba ” hajiya luba tayi saurin cewa ” A’a ki Duba Kuma, kina Jin irin wannan bugun Anya na lafiya ne kidai leka kafin ki Bude ” inna ta Bude eyelet ta leka ware Ido tayi ganin zee a gaba tabbas ta shaidata matar Aman ce tare da wasu mata sunkai 6 kowacce ta tura dankwali gaban goshi da ganinsu Babu alheri a tattare dasu, juyowa tayi wajensu anty Balqis ” wallahi matar yaron nan ne tazo da kawayenta da alama rashin mutunci ya kawo ” “tirkash! Yau Ake yinta Bude kofa Amina idan sunsaba rashin mutunci ana barinsu yau zan koya musu hankali idan suka shigo kada wacce ta kulasu don Allah ”

Babu gardama inna ta Bude kofa kamar Jira suke nan suka fada falon suna bin gidan da kallon up and down kowacce tana tauna chewing gum anty Balqis ta dauki wayarta tana dannawa inna ta koma bisa kujera ta zaune , hajiya luba ta tabe baki tana binsu da kallon d’aya bayan d’aya, zee ta nuna inna da yatsa ” ashe duk Jan kunnen da mukazo mukayi ban shiga kunnenki ba koh, har kika bari akazo Neman auren toh shikenan Ina so ki sani cewa duk abunda yasamu y’arki ki kuka da kanki domin kuwa a yau din nan zan dauki mummunan mataki akan ta , ba gidan mijina takeson shiga ba shikenan ayi mugani ” Babu wacce ta tanka musu inna ta cire waya ta kira driver tace ” ka turomin security suzo su fitar min da wasu tsageru sun shigomin gida Babu sallama ” daga haka ta kashe wayar , wata daga cikinsu tayi dariya harda guda tace ” ashe mun Isa kenan tunda ke bazaki iya fitar damu ba sai kinhada da security aikin banza lallai toh y’ar taki Bata shirya zama da kishiya ba ” zee kuwa sarkin tsoro Jin an ambaci security yasa tace “kuzo muje ta Jira abunda zai biyo baya ”

Sun juya zasu tafi kenan aka kwankwasa kofa inna ta tashi ta Bude wasu securities ne su uku kana ganin fuskarsu Babu annuri masu gadin estate din ne Amma suna da uniform nan zee da kawayenta kowacce tasa Kai ta fice daga gidan inna tayiwa securities din godiya tare da cewa ” next time banason ganin wadan nan matan ” ayi hakuri hajiya kuskure aka samu wancan tace mana su Yan uwanki ne Amma kiyi hakuri” shikenan a dai kula da masu shigowa daga yanzu ”
“Okay ma ” nan suka juya suka tafi, hajiya luba ta Kalli anty Balqis tace ” Amma da kin bari mun Basu amsa wallahi, ya za’ayi mubari yaran da muka Haifa zasu cigaba da zuwa suna ci mana fuska irin haka gaskiya banji dadin wannan lamarin ba da kin bari naci uwar shegu ”
Murmushi anty Balqis tayi ta kunna wayarta recording ashe takeyi duk abubuwan da suka fada ta nada komai tace ” Kun fahimci me nake nufi ko a muku bayani ”

“Bangane ba me Kuma zakiyi da muryarsu ”
“Yanzu nan ba sai anjima ba , wucewa zanyi civil defence headquarters zan shigar da kara a dauki mataki akan wannan matar duk abunda yafaru da hajjo itace Sila ” gyada Kai sukayi cikin gamsuwa anty Balqis ta dauki veil nata tana kallon inna tace” a Ina kika ajiyemin makullin motata ”
“Yana sama bara na dauko Miki ” hajiya luba tayi dariya tace ” aiki da masu ilimi kenan Kai jama’a…wato kaji tsoron Allah kaji tsoron sharrin dan Boko ” dariya anty Balqis tayi tace ” ai Wanda ya fika ilimi ya fika da komai a rayuwa, walau irin addini ko na zamani ko ilimin zaman duniya ”
“Wannan haka yake yau nagani na shaida Allah ya Bada sa’a ” inna ta miko mata car keys din tana cewa ” nasan Halin ya ysuf ne da tare zamu tafi Dake wallahi Amma next time zamuje Kuma Yaya ysuf na dawowa zan Kara tunzura shi lallai lallai ya dauki mataki Akai, ba yarinyar tana jida cewa ita y’ar masu kudi ba yau ko uban waye ubanta a garin nan sai ta Gane kurenta ” daga haka ta fita daga gidan.

Aman ne tare da hajjo a can waterfalls suna kallon masu wasa da ruwa kowannensu Yana rike da pineapple drink da straw cikin cup din, Aman ya juya Yana kallon kyakkyawar fuskarta yace ” kinsan Allah ranar da aka daura mana aure the next day zan daukeki mu gudu zuwa Qatar ” murmushi tayi Wanda ya Kara mata kyau ta lumshe idanu cikin nata salon Jan hankali ta sake budesu a hankali ba tare da ta kallesa ba tace ” uhmm.. really toh meyasa ”
“Saboda na tanadae mana da abubuwa dayawa Kuma idan Muna nan garin visitors bazasu bari mu…” Wayarsa ce tayi ringing ya duba Ammi ke kiransa kamar bazai d’aga ba har ya kusa katsewa ya d’aga “hello Ammi… daga can yayi shiru sai Kuma ya lumshe Ido yace ” God…wai me zee takeson ta zamane … No Ammi there must be a reason for that…No is not that am …, ta kashe wayar ya furzar da iska ya Maida wayar cikin aljihu ya tsaya jimm..

“Any problem Bae ” ciza lips nasa yayi kafin yace
” My wife.. civil defence corps sunyi inviting nata tana can ” haba dai toh me Kuma tayi ”
Shiru yai ya sunkuyar da Kai ” ur mom…I mean inna lodged a complain against her ” ware Ido tayi tana kallonsa ” inna! Wat… da gaske u min innata ” ” yeah of course Amma am sure laifintane bari naje ”
“Zan bika Bae ”
“No please my mom is there also banason Wani abu ya sake faruwa , I’ll call you, muje na saukeki sai na wuce ” cike da mamaki hajjo take bin bayansa toh Amma meyasa inna zatayi haka.

A can civil defence headquarters zee ce zaune tana faman rutsa kuka duk abunda aka fada ta karyata aka kira inna isowarta baifi minti 10 ba Aman ya shigo , nan aka tambayi inna ta fara narrating tun farkon zuwan da sukayi tare da Ammi da Kuma zuwan nata na yau da abubuwan da ta fada , Aman ya sunkuyar da Kai cike takaici Yana Mai Jin kunyar abunda ya aikata anty Balqis ta hada rai tamkar Bata taba ganin Ammi ba nan ko babbar aminiyar ta ce , Ammi kuwa mamaki take meya hada hajiya Balqis da inna . Sai da zee ta gama karyata duk abunda aka fada anty Balqis ta cire waya ta Mikawa mutumin tace ” yallabai ga shaidata ” hantar cikinta ne ya kada Aman ko bacin rai ya masa yawa ya juya ya fice daga ofishin ya tsaya waje Yana sauke ajiyar zuciya a jere Yana cin Wani daci cikin zuciyarsa , a takaice sulhu aka nema inda aka nuna cewa kishine kawai na mata aka ba inna hakuri sannan aka tsorata zee kan kalaman da ta furta na threat sannan tayi signing cewa bazata cutar da hajjo ba Kuma duk abunda ya faru zasu riketa responsible, Ammi dai jikinta yayi sanyi bayan sun fito ta Kalli aminiyar tata suka gaisa sama sama inna tayi gaba tana jiran anty Balqis Ammi tana son tambayarta me dangan takarsu da inna Bata samu fuska ba haka sukayi sallama kowa ya kama gabansa. Cikin motane take cewa inna ” kinsan wannan aminiyata ce fah sosai ashe daman Aman ne yake son Hajjo ”
“Haba..ai Bata da mutunci ko kadan aminiyar taki Bata kaunar talaka ” murmushi tayi ” hmm..ai ni zan Baki wannan labarin tunda nafi shekara goma tare da ita , mijinta abokin mijinane sosai a nan muka shaku, yanzu nasan zulumi na cinta sai ta kirani ta tambaya me dangantakarmu ” haka dai suka cigaba da hira har suka iso gida. Hajjo tana falo ta musu sannu da zuwa bayan sun zauna take tambaya meya faru nan inna ta sanar da ita komai ta jinjina Kai, lallai lamarin zee sai gaba gaba yake anty Balqis tace ” don ubanta aure dole a matso dashi nan kusa , nan da wata d’aya za’ayi bikin bari Yaya ya dawo idan zai Basu amsa ya fada musu har date ” inna tace ” haba gaggawan me Ake ”
“Jiran me zamuyi kudin ne Babu ko me, aure dole ayi insha Allah sai ta shirya mutuwa “

Back to top button