Ni da Patient Dina Book 1 Page 4
Page 4️⃣
Cikin bata fuska ta Murda handle din office din tashigo da sallama abakinta,atsaye tasameshi Yana faman jiranta cikin daddadar muryanta tace doctor gani wani irin malalacin murmushi yayi sannan yafara kare mata kallo daga sama harkasa idonshi kurr akan kirjinta yakafesu da ido lura da hakan datayine rai abaci tace zan iya tfy, karasowa yayi kusa da ita Yana kokarin rungumeta taja baya,ya rungumi iska , uhmm haba mekyau bekamata kinamin haka ba bakisan irin yanda nake mugun shaawarki da kaunarki ba burina kullum nakasance kusa Dake dazaki bani dama dakinga irin gata da kulawan dazanbaki sekinfi ko wace ya mace karasa maganar yayi Yana kashe mata ido Daya cikin salo irin na cikkakun Yan bariki, wani irin takaicine da bakin ciki Yakama fanan jitake tamkar tashaqeshi kozata huta, tsaki taja tare da wurga mishi mugun harara kafin tafara fadin.. kaikam wlh bakaji dadin rayuwa ba nasan idan baka da yar data kaini kakai ka haifeni Amma katsaya kana fadamin maganganun banza to bari kaji infada maka in sha Allah, allah bazetaba baka saa akaina ba. Kuma inawa kowace yarinyar fatan allah yakiyayesu daga sharrinka na neman aikata zina dasu allah yafika , bakaken magana take gaya mishi Amma shi wani irin Kara burgesa takeyi se kallon Dan karamin bakinta yakeyi kamar yaje yayi kissing nata juyawa tayi tafita a office tana Dana sanin fara aiki anan. Shikuwa gogan naku Yana tsaye Ayanda ta tafi tabarshi wani irin wutan shaawarta ne yake Kara wuruwa mishi afili yafara magana Yana fadin FANAN in sha Allah sena aureki domin in kawar da abinda nakeji akanki idankuma kinki kota halin Yaya sena sami abinda nakeso.
Fitowa tayi tana tunani kala kala aranta nayanda yanzu manyan mutane suka zubar da girmansu kowa yazama Dan Iska azuciyarta tace to Allah yashiga tsakanin nagari da mugu nikuma dake bayanta na amsa da ameen . Komawa tayi ward din sukaci gaba da aikinsu lura da mood dinta da Amira tayine tace mata bestie na meyafaru ne naganki wani iri ajiyar zuciya tayi tafara bawa Amira lbrn yanda sukayi da doctor Ib girgiza Kai kawai Amira tayi tace wannan mutumin baze taba canjawa ba allah yakyauta suka amsa da Ameen.
6:00pm Dede suka fito tare suna rike da hannun juna har suka tsallaka titi suka tare adedeta sahu amira ce takemishi kwatancen anguwar tasu me napep Dubai quarters zaka ajiyemu shiga sukayi suna yar hira harsuka iso suka sallameshi sallama sukayi kowa hanyan gida tanufa. Cike da gajiya FANAN tayi sallama dagudu auta tazo tana mata oyoyo, oyoyo autar mama anty sannu da dawowa yauwa auta Ina mama tana falo ok kawai tace tawuce falon anan tasamu mama tagaisheta amsawa tayi zama FANAN tayi akan cusion tana cewa wlh mama yau nagaji sosai murmushi mama tayi tace to sakaliya bakin dawo ba Zaki fara narkemin kamar wata man gyada dariya FANAN tayi tace Kai mama komai mutum yayi sekin sace mishi gwuiwa dariya suka sa tare tom sannu sekije kiyi wanka kizo kici abinci tom mama dakinta tawuce, samun guri tayi tazauna abakin gado ahankali tafara cire Dan kwalin kanta Sannan tasa hannu ta warware gashinta yasauko yarufe mata fuska zib din riganta taja kasa tacire rigan kallon kanta tatsaya takeyi a mirror kome ta nuna naga tasaki wannan murmushin nata mekara mata kyau karasa cire kayan jikinta tayi tashiga toilet ta watsa ruwa tafito zafi takeji ko Mai bata tsayawa shafawa ba Bude wardrobe tayi tazaro wata dogon riga mara nauyi ja me Igiya tasa tadauki hula Baki tasa tafito abinci tasamu afalo tasan mama ce ta ajiye mata zama tayi tafaracin abincin seda taji takoshi tukun Tasha ruwa takwashi kwanukan takai kitchen anan tasamu mama na girki taimaka mata tayi har suka gama suka Kai komai falo.
Bayan sallah mangrib baba da ya Usman suka dawo abinci sukaci suna hira cikin nishadi kafin sukayi sallama FANAN Takoma dakinta kwanciya tayi kafin tajawo wayarta WhatsApp tashiga tafara Bude sakon ni wata group tagani ansata mesuna manyan yara tsaki tayi sbd ta tsani irin wayan nan group din left tayi ta ajiye wayar Dan yau agajiye take adduah bacci tayi ta kwanta.
Misalin karfe 12:00 nadare wata farar motace ke sharara uban gudu akan hanya kamar bazata tsaya ba domin kuwa me motar kansa ba lalle in Yana hayyacinsa ba duk iya kokarinsa na ganin yataka birki motar ya tsaya Amma ina abin yacitura , ganin dayayi saura kadan yafada wata katuwar Rami ne yasa yafara Kalmar shahada cikin kankanin lokaci mota ya wantsila cikin ramin bayan 5mint motar ta kama da wuta nafitan hankali.
Karfe 5:00am wani Dan saurayine yafito zeyi bayan gari acikin dajin kawai yaga motor nadanci da wuta kadan kadan karasawa yayi Yana me adduah allah yasa ba mutum aciki domin inde akwai zeyi wahala yarayu gama duba wajan yayi kaff bega kowa ba harya fara tafiya yadanyi nisa kadan cikin ciyawa yaga hannun mutum cike da fargaba azuciyarsa yakarasa wajan aikuwa kwance yaga bawan Allah kwance kamar gawa babu alamun daze nuna maka Yana Raye domin kuwa jini yama jikinshi wanka, salati yasa gashi ba cikin gari bane balle yanemi taimako haka yasabashi akafada yafara tafiya Yana Nishi dakyar harya samu yafito titi duk motocin Daya tsayar basa tsayawa, dakyar wata mota tatsaya bayani yayi WA mutumin cikin jinjina lamarin me motar yafito yataimaka mashi suka kamashi suka kwantar dashi abaya tada motor yayi direct asibitin gombe SPECIALIST suka wuce suna shiga nurses sukayo kansu aka shigar dashi emergency room akashiga dashi tsabar yanda sukaga yayi mumunar raunata dakuma jigata doctor’s din ko takan police Basu biba, rufuwa sukayi akanshi suna bashi taimakon gaggawa awajan ward kuwa wannan saurayin ne da mutumin suke zaune sunyi jugum dukda Basu sanshiba Amma sunyi matukar tausaya mishi bayan kamar 1hour doctor yafito ya rubuta magani yabasu yace agaggauta siyowa yanzu nan karban takardan mutumin yayi cikin sauri yaje yasiyo yakawo musu Karba sukayi suka koma 2hours later doctors din suka fito Suna goge gumi karasowa kusa da doctor din sukayi fuska asake doctor din yace musu alhamdulillah munsamu numfashinsa yadawo Dede, alhamdulillah suka fada atare suna musabaha, sannan doctor yace sede wani hanzari ba gudu ba yashiga coma inba iKon allah ba ze Kai wata Daya ko fiye da hakan kafin ya farfado. Kallon juna sukayi yanzu yazaayi gashi yanzu niba mazaunin gombe bane a Yola nake dama inakan hanyane nahadu da wanann bawan Allah yace intaimaka musu ah ah bakomai karku damu inde bazakuna samun daman zuwa akai akai ba Munada nurses kwararru wayanda zasu bashi kulawa yanda yakamata kafin yadawo hayyacinsa. Masha Allah shikenan yanzu doctor kamin lissafin duk wani charges din abinda akamishi dakuma Wanda zaa mishi nan gaba har izuwa time din daze samu lfy sannan kaban phone number ka sbd indingajin lfyr sa . Kallonsa doctor yayi yace Gsky alhaji kanada kyakyawar zuciya duk da bakasanshi ba gashi kataimakeshi inba damuwa zan iya sanin sunanka, sunana alhaji badamasi me ruwa Kara kallon sa dakyau doctor yayi yace dama kaine alhaji badamasi me ruwa iKon Allah yau de naganka dariya sukayi kafin yayi WA doctor transfer 2million domin yanasan abawa wanann bawan Allah de besan awata duniya yake ba kulawa na musamman. Sallama sukayi wa doctor tare da alkawarin zasuna zuwa dubashi akai akai.
Bayan tafiyansu time din har 9:00am yayi akafito dashi aka kaishi private ward inda SE Wanda ya Isa zeyi jinya aciki. Komai na more rayuwa akwai sa aciki ansa duk wani abinda zaawa coma patient amfani dashi akwai. bayan sungama seta mishi su oxygen da pulse oximeter, ventilator machine etc. Fitowa sukayi suka shiga office din doctor ammar suna tattaunawa akan waya kamata su tsayar akanshi wanda zedinga bashi kyakyawar kulawa Daya daga cikinsu yace ni aganina abawa nurse mufida koya kuka gani girgiza Kai doctor Ammar yayi yace noooo tanada rawan Kai Gsky bari zuwa karfe 12 narana zanbi list din nurses din dabasu fi 1yrs dafara aikiba acikinsu semu tantance waye ya kware dabawa patient kulawa yanda yadace dakuma sakin fuska da nutsuwa duk kansu sun yarda da shawaran Daya kawo.
FANAN tagama duk wani aikin data sabayi kullum tayi wankanta tashirya tafito falo tayi breakfast sannan tayi musu sallama ya Usman ya ajiyeta Yana zolayanta yau naga kamar yar kanwar tawa da farin ciki ta tashi dariya tayi wlh kuwa ya Usman kome yasani haka oho dariya yayi yace tom Masha Allah ai haka akeso tafiya yayi tana mishi bye bye tashiga asibitin.
Bayan tashiga tafara duba patient’s duddubawa tayi bataga bestie ta Amira ba alamun bata karasoba tukun.
Amira batashigo ba SE 11:30 tana shigowa kuwa wajan FANAN tayi kawata yau kam kinyi latti mtsssw tsaki tadanja kede bestie bari kawai bestie bakisan meyafaru ba daddy ne yasamomin addimission a pen resources wai zanyi degree Dina acan rungumeta fanan tayi cikin farin ciki tace wlh bestie natayaki murna sosai. Zuba mata ido kawai Amira tayi kafin tace nikuma wlh banaso nafijin dadin haka na wani degree ne zedameni wlh kwata kwata banasonyin nisa Dake duka FANAN takai mata kekam wlh se adduah sannan kuma ai ba rabuwa zamuyiba nasan inkin dawo school zakizo asibiti ko eh in sha Allah haka nakeso suna tsakiyar magana wani security yashigo yasamesu yace Dan Allah, Tambaya nake sukace allah yasa munsani dorawa yayi dacewa doctor ammar ne yake neman Fatima M Umar dakuma Aysha abubakar wada kallon juna FANAN da Amira sukayi kafin sukace mune allah yasa balefi mukayi ba ah ah bansaniba Gsky cewa yayi de inkiraku okay tom Bismillah muje, tafiya sukeyi Yana gaba suna binshi abaya harsuka Isa office din doctor ammar sallama sukayi suka shiga gaishesa sukayi Amsawa yayi yana tsokanansu Anya ku ba Yan biyu bane kuwa kullum Kuna tare dariya kawai sukayi. Tom yanzu de kuzauna zama sukayi kafin yace Meye sunanku fada mishi sukayi……
To masu sauraro koya zata kasance kubiyoni kuji.
⚕️⚕️ NIDA PATIENT DINA
Story Written by ( MRS ISHAM )
Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen
Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci
___________________________________________