Ni da Patient Dina Book 1 Page 3
Page3️⃣
Babane yace to kutashi aje ayi sallah isha mikewa yayi shida ya Usman suka tafi masallaci. Mama itama dakinta ta tafi don gabatar da sallah, ita kam FANAN kasancewar bata sallah seta wuce daki takwanta tajawo wayarta tashiga buga game . Gajiya tayi ta ajiye wayar tamike tashiga toilet tayi wanka tafito tashafawa jikinta mai da turare kayan bacci tadauko pink color me laushi tasaka sannan tahau gado tunani tashigayi gobe fa zata shiga asibiti inda rai da lfy zatayi kokari tashiga da wuri sannan tayi adduah bacci ta kwanta.
Washe gari
Karfe 7:00am ta tashi daga bacci brush tayi tayi wanka sanan tafito ta saka dogon hijab har kasa tafito taje dakin baba ta gaisheshi daga nan tayi wajan mama suka gaisa tambayar mama tayi Meye zaayi na karyawa , mama tace kiyi Dan wake da tea kawai amsawa tayi to tamike , kitchen tawuce tahada kayan wanke wanke tafito dasu kafin Takoma tana kokarin hada kayan karyawa. Wanke wanke takeyi cikin kwanciyar hankali hartagama taje tajera komai yanda yadace a kitchen sannan tayi shara da mopping komai da komai daga nan Takoma kitchen tacigaba da hada kayan karyawa. Bayan takammala ta juye tea a flask takai falo da food flask ta ajiye direct dakin mama taje tasameta tasanar da ita tagama murmushi mama tayi tace allah yamiki albarka ta amsa da Ameen bari inje inyi wanka to kawai mama tace mata.
Komawa daki tayi tacire hijab din wanka zata sakeyi sbd ta gaji tahada zufa, bayan 10mints tafito sanye da towel ajikinta Bude wardrobe tayi tafito da uniform nata da handbag da takalminta a tsanake take shiryawa gyara gashinta tayi tahadeshi waje daya tayi donot dashi. Uniform tasa ajikinta wayanda suka kasance white color tadaura dankwali Amma seda sajen gaban kanta yafito powder Tashafa sannan tasa kwalli a idonta tasa libs stick adan karamin bakinta yayi kamar tasa janbaki.tubarkallah Masha bakaramin kyau tayi ba agogo tadaura a hannunta tasa after dress Baki asaman uniform din hijab dinta Wanda bewuce cikiba tasa feshe jikinta tayi da perfume sannan tadau handbag dinta tafito falo tasamu harsun kammala breakfast, mama ce tasamata kayan karyawanta zama tayi tayi Bismillah taci badayawaba ta ce mama zantafi allah yabada saa mama tamata sannan tace kije babanku na daki wucewa tayi dakin baba tayi sallama yabata umarnin shigowa mamana harkin shirya eh baba nagama dauko Dari 500 yayi yabata sannan yamata adduah allah yabata saa Ameen babana sena dawo tamishi sallama tafito kenan taci karo da ya Usman yafito da machine dinsa,ya usman ina kwana lfy Lau kintashi lfy ta amsa lfy Lau alhmdllh zokihau in ajiyeki tace to hawa tayi suna tafiya suna hira har suka Isa bakin asibitin SPECIALIST ajiyeta yayi yajuya duba time a wayanta tayi taga 9:30 tafiya takeyi harta karasa addimission ward tana shiga tahango Amira nasawa wata patient drip karasawa tayi gaisawa tayi da Yan wajan cikin sakin fuska da murmushi dauke afuskanta tamusu ya jiki amsawa sukayi dasauki nurse. Karasawa tayi wajan patient’s dinta Dake kwance gaisawa sukayi kafin tace mata yajikin naki fatan dasauki washe Baki tayi tace ahh dasauki sosai murmushi kawai FANAN tayi magungunanta taduba taga duk tashasu akan lokaci, nayaune kawai batasha ba dogo Kai FANAN tayi tace kin ci abinci ne amsa mata matar tayi da ah ah banciba Ina mijinki bedawo ba tukun mamakine Yakama fanan tashiga tunanin wannan wani irin mijine matarsa nagadon asibiti bata da lfy sannan ace tunjiya haryanzu bedawo ba balle yasan halin da take ciki allah yakyauta. Kallon matar tayi taga jikinta tayi sanyi cikin tausayawa tace ya sunanki ahankali tafurta sunana balki, murmushi tayi tace anty balki karki damu mijinki yakusa isowa.yanzu Meye yake miki ciwo ah ah nurse yanzu kam jiki alhamdulillah sedan ciwon Kai da rashin karfin jiki ne kawai okay to Allah yakara sauki suna cikin haka mijinta ya karaso wajan Yana wani bata rai yagaida FANAN amsawa tayi tana kallon iKon Allah,cikin Shan kamshi yace ma balki ya jikin tace dasauki daga nan bekara cewa komai ba,FANAN ta lura kamar akwai Dan matsala kallonshi tayi tace inba damuwa inasan magana dakai okay badamuwa fitowa Bakin ward din sukayi . Cike da girmamawa da natsuwa tafara mishi mgn bawan allah ya nunanka sunana Abdul yabata amsa, murmushi tayi cikin tsigan zolaya tace kaikuma malam Abdul haka akeyi , katafi karba masoyiyar taka ita kadai bakowa nata balle naka Yan uwan bataci abinci ba gashi nazo zan bata magani ba abinci Anya ba kishiya kakeson mata ba kuwa takarasa tana Dan dariya shikuwa Abdul wata irin kunya ce takamashi Jin abinda nurse tafada mishi seyaji gaba Daya bekyautaba shuru yayi yarasa bakin magana itakuwa FANAN ganin tayi nasarane jikinshi yayi sanyi tacigaba da mgn malam Abdul kaga bata da lfy kadaure kadinga kula da ita koba komai itadin amanace awajanka aurenta kayi domin kunason juna sannan tace allah yabaku zaman lfy takarasa maganarta tana kallon idonshi, cikin sanyin jiki yace Ameen Ameen nurse nagode sosai da sosai murmushi tayi tawuce ciki tabarshi agun shikuwa daga nan abinci yaje yasiyowa matarshi yakawo mata taci dakanshi yabata maganinta se kallonshi takeyi tana Kara godewa allah dayakawo wannan sauyin dakuma nurse fanan Dan tasan harda taimakonta.
Duk nurses din wajan sunata kula da patient dinsu wani babban mutum ne yashigo wajan yanda ake ta gaisheshi ze tabbatar maka da shine in charge na asibitin. Hango Amira yayi yakirata ta karaso bayan sungaisa ya tmby ta Ina fanan ko yauma batazo ba ah ah tazo bari inkirata Yana tsaye agun Amira suka jero tare da FANAN Yana ganinta yawashe Baki Yana kare mata kallo kamar wani maye ciki ciki FANAN tace mishi Ina kwana amsawa yayi yata washe baki kamar gonar auduga, tafiya yafarayi yajuyo yacewa FANAN kibiyoni office Dina. Tsaki FANAN taja saboda yanzu inda Wanda tatsana bewuce in charge nasu ba sbd yanda yasata agaba da maganar banza. FANAN kije kiji Meye damuwarshi Kuma yau hmmm kawai fanan tace tawuce office nashi…….
To zamuji yanda FANAN zata kare itada in charge nasu
Please kudingayin comment
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
⚕️⚕️NIDA PATIENT DINA
Story written by ( MRS ISHAM )
Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen
Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci
____________________________________________