Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 23

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAƊI…..!*

 

*_NA_*

 

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad :ummishatu*

PAID BOOK

23

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Ina ƙoƙarin saka fashion earrings ɗina ƙawalli ta shigo, juyawa nayi na kalleta kallo irin na neman ƙarin bayani,

“Malama fito mu tafi….” ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin, flat shoe ɗina na saka na bi bayanta, sai bayan da muka fita daga cikin gidan sannan take sanar dani ai taje ta tambayi su mama zan rakata Kurna gidan su ummansu wadda ta aiketa,

“Na gode ƙawalli……. Allah ya bar zumunci ya kuma barmu tare”

“Kar ki damu ai kin fi ga haka…..”

Napep muka samu muka hau, sai da ta fara kaini har Guest house ɗin da Samz sannan tace dani bayan ta kalleni,

“Ki saka face mask kiyi basaja idan ba so kike wani ya ganki ba, sannan ki bi a hankali dan wannan uban ƙamshin da kike zubawa kina iya tada hankalin maza, asha soyayya lafiya kar a ƙone, 6 daidai mu haɗu anan….” Shawararta nabi na saka face mask sannan na shiga, sai da na shiga harabar Hotel ɗin sannan na kira Samz,

” Hello baby…… ” ya faɗa muryarshi ƙasa ƙasa,

“Fito ina jiranka….”

Wayar naji ya kashe cike da farin ciki, mintuna kaɗan sai gashi ya fito, tunda na hango shi nake kallonsa daga ƙasa har sama kawai hango rayuwar mu nake bayan munyi aure, “Maimunatu ko ina zaki kai wannan basamuden mutumin….” wani sashe na zuciya ta ya faɗa, “Inda duk wata mace ke kai namiji, kema zaki iya” ɗayan ɓangaren ya sake bani amsa, murmushi nake yi araina ina sake hasaso yanda zamu kasance matsayin miji da mata, agabana ya tsaya sai na ganni na zama wata ƴar ƙarama a gabansa domin yana da tsayi sosai kuma yana da ɗan jiki madaidaici shiyasa za asa shi sahun giants,

“Tunanin me kike yi?” ya buƙata yana kallon fuskata, ƙasa nayi da kaina ina murmushi,

“Tunanin rayuwar mu bayan munyi aure”

Dariya naga yayi sannan ya nuna min hanya alamar muje bayan yace “let’s go baby”, jerawa muka yi har wurin wasu kujeru dake ajiye a gefen swimming pool, nan yaja min ɗaya na zauna sannan shima ya zauna, yau sanye yake da jeans black sai t shirt mai gajeren hannu itama black kansa babu hula amma duk da haka yayi mutuƙar kyau,

Kallo na yayi bayan ya zauna “Na san abin da kike tunani ai”

“ok to me nake tunani? Ka faɗa tunda ka sani”

“No ba sai na faɗa ba amma believe me na sani”

“shiyasa ai nace ka faɗa tunda ka sani”

“ok, kin yarda in faɗa?”

“na yarda” na faɗa ina ɗaga masa kai,

“Kina tunanin may be nayi miki girma ko? Shine kawai abin da zaki tuna a yanzu i know”

“a’a ni ba wannan nake tunani ba” na faɗa fuskata a dake duk da gaskiya ya faɗa abin da nake tunani kenan amma sai na dake nace sam ni ba wannan nake tunawa ba,

“ok to idan ba wannan kike tunawa ba me kike tunani?”

“ni kawai tunanin da nake yi gamu nan da yaran mu muna zaune cikin farin ciki”

“Ok na yarda but ta yaya za ayi tunanin samun yara ba tare da an tuna wannan abun ba?” haɗe rai nayi na ɗaure fuska kuma na ƙi nace komai, ganin haka ya sashi yin murmushi ya fara rarrashi na,

“is ok baby…. Am sorry, yakike”

“lafiya Lau” na faɗa batare da na kalleshi ba,

“Baby kin ƙara kumatu… Kin manta abin da na faɗa miki ko?” hararar shagwaɓa nayi masa bayan na narke fuska zanyi kuka,

“Allah ba zan yarda ba” na faɗa cike da shagwaɓa,

“To ki fara exercise” ya faɗa cikin tsokana,

“A’a” na maƙale kafaɗa, shagwaɓa nayi ta yi masa har lokacin tafiya ta yayi, daƙyar muka rabu dan nidai harda hawaye na sai da naji yace in dai kuka zan rinƙa yi idan yazo to ba zai ƙara zuwa ba sannan na haɗiye kuka na muka yi sallama na wuce inda muka yi da Ƙawalli zamu haɗu shi kuma ya koma ciki shima tasa zuciyar babu daɗi kawai ya daure ne kar in fahimta in sake shiga damuwa, ina tsaye bakin titi ina jiran ƙawalli muna waya dashi,

“Wannan kukan da kike yi baby yana taɓa zuciya ta fa gashi banda abunda zan rarrasheki dashi a yanzu….. Da dai munyi aure ne…”

Murmushi nayi nace “Idan munyi auren kanada abunda zaka rarrasheni?”

“Ehh but idan na faɗa miki faɗa za muyi kuma fushi kike yi”

“Ba zamu yi faɗa ba yau, ina son ji, tell me pls”

“Seriously? OK i will hug you and kiss you…… Sannan zan goyaki”

Murmushi nayi ina rufe fuskata kamar yana kallo na,

“Ashe ni yar gata ce”

“yeah you are my baby ai, kinga dole in kula dake, i will do everything to make you happy……”

“Na gode Darling….”

“ke kuma wanne irin rarrashi zaki rinka yimin?”

“i will do the same thing for you”

“no…. Ni ba wannan nake so ba” ya faɗa cikin kwaikwayon murya ta irin yanda nake yi masa idan ina shagwaɓa,

“faɗa min abinda kake so….”

“you” ya bani amsa cikin zakin muryarsa,

“don’t worry am all yours”

“I hope soo” ya sake faɗa yana fusgo maganar daƙyar, har saida ƙawalli tazo sannan muka yi sallama muka kama hanya da Ƙawalli ina sake bata labarin Samz, har gidanmu muka je da ita tacewa su mama mun dawo sannan na rakata ta tafi.

Da daddare lokacin da muka yi waya dashi sai naji muryarsa wani iri alamar bai da lafiya koda na tambaye shi sai yace ehh amma kuma yin duniya nayi akan ya faɗa min abinda ke damunsa yaƙi daga ƙarshe ma da na matsa masa da tambaya sai yace wai kansa ke ciwo, karo na biyu kenan ina tambayarsa rashin lafiyar sa yana ƙin faɗa min idan na takura sai yace ciwon kai, haƙura nayi na rabu dashi na tambaye shi ko ya sha magani yace min ya sha, duk da bai da lafiya hakan bai hana mu raba dare muna hira ba anan ma yake sanar dani wai yayi booking flight 7 zai bar Kano domin yana da aiki a office saboda shi da NGOS yake aiki amma parmanent staff ne ba on contract ba, sai da bacci yaci ƙarfina sannan muka yi sallama na kwanta. Haka lamarin yaci gaba da gudana cikin so da ƙaunar juna tare da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin mu sai dai iya ƙawalli ce kaɗai ta san muna soyayya dashi kuma duk lokacin da yazo ganina ita ke shiga ta fita har mu samu mu haɗu muga juna,

Tuni muka yi nisa a aikin da muke yi wanda har mun ci 8 weeks yanzu, Samz koda yaushe muna maƙale da juna a waya, video call ko voice call, gefe ɗaya kuma shirye shiryen bikin ƙawalli da yaya Abdul Hakim wanda keta ƙaratowa yasake chaja min kai, ranar da Samz yazo na ƙarshe ban san wanda ya ganmu tare dashi ba har yaje gidanmu ya faɗa nidai kawai Abba ya kirani yayi min kaca kaca akan Samz sannan yace lallai lallai in rabu dashi tunda ba addininmu ɗaya ba dama ni tunda naji Abba yace,

“Maimunatu da wanne saurayi aka ganki jiya a First class Guest lodge?” naji ƴan hanjin cikina sun kaɗa,

“Abba Samuel ne” na faɗa jikina yana kyarma,

“menene alaƙarki dashi yana Christian kina musulma?”

“Abba saurayi na ne…”

Ai tun kafin na ƙarasa naji su Annie sun ɗauki salati, Annie tashi tayi zata zo ta rufeni da duka mama ta hana, nan Annie ta fara faɗa tana cewa,

“Widat kashe ni kike son kiyi ne? So kike baƙin cikin ki ya kashe ni? To wallahi daga yau ban yarda ki sake kula wannan yaronba matsawar ba musulunta yayi ha wannan kam ba zan hana ba, amma in dai kika sake kula shi ban yafe miki ba, babu ke babu shi har abada ko a hanya ban yarda ki sake kula shi ba ”

Kuka na fashe dashi saboda jin abin da Annie tace, na san ta bani horo mai tsanani domin abune da zai wahalar da zuciya ta da gangar jikina gaba ɗaya, rabuwa da Samz tamkar yanke numfashi nane a doron ƙasa, Abba kuwa cewa yayi,

“Na baki nanda watanni biyu ki fito da miji in yi miki aure idan kuma ba haka ba to zan aura miki duk wanda na samu tunda Allah ya gani nayi iya yina ganin na aurar dake ga zaɓin zuciyar ki amma kina neman ki jawo min magana kina bin saurayi har hotel kuma abin haushi saurayin ma wanda ba musulmi ba ”

Da kuka na shiga ɗakina na kwanta ranar naci kuka kamar wadda uwarta ta mutu daga ƙarshe na jawo wayata na turawa samz da text massage minti ɗaya da tafiyar massage ɗin sai ga kiransa,

” Baby me yake faruwa? ”

” Samz ka san ina sonka, kuma babban burina shine inga munyi aure mun zauna a inuwa ɗaya, kuma Hakan ba zata taɓa faruwa ba har sai idan ka musulunta, Abba da Annie sunyi min iyaka da kai sunce kar na sake kulaka har sai idan ka karɓi musulunci, hakan shine kaɗai zai ba mu lasisin mallakar juna…… ”

Girgiza kai yake yi daga inda yake zaune, bai ce min komai ba ya katse wayar wanda hakan ya bani tabbacin munyi bankwana dashi na har abada………..✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

_*Ummi Shatu*_

Back to top button