Nasarar Rayuwata 47
*Talented writers forum*
*47*
Zee ta zube tsakiyar falon Ammi tana kuka Ammi na cewa ” kema ai kinsan Bai kamata ki fito fili ki Fadi wannan munanan kalaman bah daurewa zakiyi” “haba Ammi kina Gani ko mum dina fushi take dani tun lokacin da naje mata da zancen ta koreni, na rasa mafita duk abunda nayi a banza ba dole nabi duk wata hanyar da nake tunanin zai min amfani ba ” anty sofy Dake zaune a gefe ta tabe baki tace ” wallahi ke abin ya shafa amma jinake tamkar ni za’ayiwa kishiyan , na tausaya Miki sister na gaya miki kwanaki Beb ya samu wata ya like mata dakyar fa na samu na rabasu kedai bari abin Babu dadi ” ” kinsan Allah anty sofy Babu abunda ya Kara tunzura irin yadda naga pix din yarinyar kyakkyawa ce ta karshe Kuma just imagine kawar kanwata fah Kinga ni ba mate nata bane ” gyara zama sofy tayi Ammi ko ta tashi ta wuce d’aki tana son Kiran anty Balqis don Neman Karin bayani.
” Don’t tell me kawar Ummeey kenan , Kai amma namiji munafuki ne ” bari anty sofy bari ma Kiga pic nata ” ta Ciro wayarta tana share hawayen ta shiga screenshot ta Bude pix din Aman da Hajjo, saura kadan numfashin anty sofy ya dauke ” Kee….. Wannan yarinyar annoba ce wallahi itace itace iswear she is the one ”
“Itace tayi me anty?”
“Same girl da nake Baki labarin ta likewa Beb dina kinsan Allah ba karamin kudi na kashe ba kan nagane kan mijina , Kai zaman Nigeria Baiyi ba gara na kama kayana mu koma inda muka fito ban Isa ba da Yan matan naija sai bibiyan mazan mutane suke abu kadan sai Karin aure Kai inaa… tagumi zee tayi tana Neman mafita anty sofy tace ” Bude aljihu zakiyi a Miki aiki a rabasu har abada ko kallon inda take bazai kara ba ”
“Anty kiwa Allah ki taimaka ni yanzu bani da kowa sai ke kece gata nah ki rufamin asiri ko nawa zan kashe indai akan Aman ne ”
“Ba ruwana Allah ne gatanki Amma dai zan taimaka Miki ki shiya kisaka Rana sai muje can suleja malamin yake ”
“Ni ko yanzu ma sai muje ” “A’a ba dai yau ba mijina na hanya sai dai ko jibi ” “Allah ya kaimu “.
Ammi kuwa shigar ta d’aki ta kira anty Balqis 3 times Bata d’aga ba haka ta hakura ta bari.
Kamar yadda anty Balqis ta tsara hakan kuwa akayi ya Yusuf ya kira Baban Hajjo a waya ya fada masa komai yace ba matsala Allah ya nuna musu, ya Yusuf ya kira Dad din Aman ya sanar dashi yayi farin ciki matuka nan ya shaidawa Aman murna kamar yayi Yaya take ya kira anty Dada yace tazo ta hado masa lefe, yana ta Kiran abokan arziki yana fada musu daga karshe ya fadawa Ayman ta Whatsapp.
Yau Hajjo ta shirya zata Kaiwa Babanta ziyara a gidan da yake aiki saboda tun bayan dawowarsa Basu Hadu ba sai ta waya , ta shirya ta masa siyayyan kayan tea dasu sabulu da kayan bukatun yau da kullum tana matukar tausayin mahaifin nata Yana rayuwa tamkar maraya.
Driver yayi parking a dai dai address din da Baba ya tura mata ta fito tayi knocking bakin gate maigadi ya leka suka gaisa ta shaida masa tazo wajen malam Sule ne ” toto…shigo shigo Hala kece diyar tasa dama ya fadamin diyarsa zata kawo masa ziyara Bismillah…maraba sannu sannu ” hajjo dai murmushi take ya Bude kofa ta shiga , ” zauna Bismillah ki zauna Saman kujera yanzu zai fito yakai sakon Alaji ne wato Basu Dade da dawowa ba ai kinyi sa’a da zakizo Baki samesa ba ai shi Alaji baya zama ” ta zauna bisa white chair dake kusa da d’akin maigadi, Baban nata ne ya fito daga cikin gidan Yana hangota ya fara murmushi ya karasa ” y’ar Baba har kin karaso toh sannunki ya hanya ”
ta rusuna ta gaishesa ya amsa cikin fara’a ” a nan kika zauna da mun karasa can falon namu ai ” “A’a nan yayi Baba bawani dadewa zan ba ”
“Ya wajen mahaifiyar taku Ina Sadeequ ”
“Duk suna lafiya tace a gaisheka ” “Masha Allah nagode sosai da ziyara Allah ya Miki albarka, toh yanzu ya Ake ciki sai ki samu lokaci ki rubuta min abubuwan da kike bukata zamuga abunda Allah zaiyi ”
“Babu komai Baba kada ka d’aga hankalinka komai zaizo da sauki insha Allah” ” lokacin ne Yana saurin tafiya yanzu gashi kwana ashirin da ya rage idan Muna raye” murmushi tayi ta sunkuyar da Kai, horn aka danna nan maigadi ya tashi ya wangale gate motar Aman ta danno Kai Hajjo tabi motan da kallo it looks familiar kamar tasan me wannan motar, ya Bude kofa ya fito Yana waya… dum..dum gabanta ya Fadi dama nan gidan iyayen Aman ne, dama gidan da Baban nata yake aiki gidansu Aman ne, gaskiya ya zama dole Baba yabar aiki a yau .
Ya shige cikin building din Hajjo ta Kalli Baban nata cike da tausayawa tace ” Baba ni zan wuce ”
Ya tashi Yana gaba tana baya suka fita daga gidan, bayan ta fiddo ledojin da kawo masa tace ” Baba gaskiya zanso kabar aiki a wannan gidan ka nemi wata sana’a daban”
“Meyasa uwata ”
“Saboda.. saboda nan ne gidansu…” Sai Kuma tayi shiru ” gidansu waye ki fadamin”
“Gidan Wanda.. zan.. aura ” cike da mamaki yake kallonta” waye kenan kodai Aman da nake Jin ana zancen aurensa ” gyada Kai tayi Baba ya girgiza kai yace ” rashin sani kenan, toh Allah ya mana Mai kyau inaga shi Kansa Alajin Bai sani ba amma ya zama dole na fada masa Kuma tabbas dole nabar musu gidansu saboda tsira da mutuncin ki, don gaskiya matar gidan Bata da Hali ” shikenan Baba ni na wuce sai munyi waya” ta shiga mota Yana d’aga mata hannu kafin ya koma cikin gidan Yana zuba mata albarka.
Cikin mota tunani take yanzu dama duk Neman mahaifin nata da suke Yana cikin garin Abuja Kuma gidan masoyin nata Allah kenan maiyin yadda yaso a lokacin da yaso , tana zuwa gida ta zayyanawa inna komai salati inna tayi tace ” ai kuwa dole yabar musu gidan kafin wannan y’ar balain tasan da wannan zance, dama Ina son Miki magana nace bansani ba ko Sule din zai yarda a daura musu aure da Maman Nana na kirata zata dawo jibi ” murmushi hajjo tayi
” Gaskiya inna kinyi tunani me kyau ni kaina banason zaman nasa a haka gara ya samu wacce zata kula dashi Kuma maman Nana mutum ce Bata da matsala wallahi , nasan insha Allah Baba bazai Musa ba ni zan Bada sadakin Allah ya kawota lafiya” Ameen..inna ta amsa shiru sukayi kowa da tunanin da yake ” Amma Ina wace sana’a kika ganin Baba zai iya sai a basa jari ya fara ”
” Toh ki fara tuntubarsa dai kiji ra’ayinsa sai a kama musu gidan da zasu zauna ” “shikenan anjima zan kirasa Muji ya sukayi da maigidan ” wayar hajjo yai ringing Aman ne ke kira tana satar kallon inna ta tashi inna na murmushi ta gudu tayi d’akinta.
“Angon shatu ” ta furta cikin Wani salo tana murmushi ta zube bisa gado” wash..nagaji my..” ta fada a shagwabe tana dariya ta mirgino bisa gadon tace ” uhmmm..nidai ban fara Shirin komai ba but next week zamuje maid da aunt dina, … No kawai Nima bansani ba tace dai na shirya zan rakata…
Ok zanyi magana da Ummeey but ni dama Fulani day kadai zanyi sai walima… No no..bahaka bane I want to expose my culture ne fah…ok toh shikenan missed you more takkia muah…ta katse Kiran tana dariya, yanzu da gaske auren nasu saura Yan kwanaki, wane irin rayuwa zatayi a gidansa da wannan jarababiyar matar tasa, koma menene dai a shirya take bcos she is ready to do anything idan dai akansa ne Kuma anty Balqis ta Kara karfafa mata guiwa akan kishiya ba Abar tsoro bace dole ta jajirce ta kwato y’ancinta Kuma sai ta gama mamaye zuciyar mijin kafin ta Maida hankali kan kishiya haka dai ta cigaba da tunane tunanenta.