Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 17

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E17_

 

*Daga alƙalamin Boss Bature*

 

A ƙalla sun shafe kusan 30 minutes a ɗakin Danish, Ji suke kamar abarsu su kwanta a ɗaki ɗaya saboda haka su ka saba kwana a kurkuku, daga bisani Nurse tace dasu zasu tafi zuwa gobe zasu Iya zuwa su ƙara duba shi’ jiki asanyaye suka miƙe suna tafiya suna waiwayon shi musamman Angel ji ta ke yi kamar ta koma ta rungume shi.

Bayan fitar su daga ɗakin, Nurse Ta raka kowan nan su room da aka kwantar da shi, ba su so aka raba su ba, har yanzu tsoron mutanan su ke ji, ba dan Angel ta lalla6a su ba da ko babu inda zasu je, a ɗakinta zasu kwana, musamman Azeeza da jemimah ɗaƙyar Angel ta lallashesu ta lalla6asu don ta fahimci dokar asibitin ce haka ba’a haɗa mutun fiye da ɗaya a ɗaki, wata’ƙil sai idan ya kama dole, sauƙin ma kowan nan su akwai nurse ɗaya da ke kula da ɗakin shi, duk wani abu da zasu buƙata zasu yi masu, hatta toilet suna raka mutun In ya buƙaci hakan musamman gasu da basu san yadda zasuyi amfani da wasu abubuwan ba.

A daren ranar sun yi kwanan farin ciki basu da wata damuwa.

*Daular Alhaji Musa wadata*

idan nace zan tsaya zayyana maku zunzurutun Kayan alatun da ke a gidan Alhaji musa daga ni har ku zamu koma Yin Mafarkinsa ne, wato Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi ce, Katafaren Villa ne Wanda Idan ka zura ƙafarka acikinsa tamkar ka Bar Nigeria ka shiga Dubai ne, Aljannar duniyace ƴar ubansu, A ƙalla security din dake tsaron Kafcecen Gate ɗin shiga gidan sunkai su goma shabiyar, Wasu gabza gabzan Garada Masu Ƙirar sadaukan Yaƙi, Babu wasa akan fuskokin su, Bana tunanin ko aljani zai Iya gifta gate din gidan salin alin ba tare da sun cafke shi ba, Shantalelen titi ne zai sadaka da Cikin gidan kai tsaye daga bakin babban gate ɗin, yadda kasan da zallar goal aka ƙera ginin saboda ɗaukar idon gilassan Ƙofofin da Windows, ko gidan shugaban ƙasa albarka, Babu ce kaɗai ke babu agidan Alhaji musa, komai na gidanshi babu made in Nigeria, an zabga almubazzarancin dollar wurin ƙera ginin, don hatta sample dinsa da ƙwararrun da suka ginasa kaf aikin turawa ne.

Mamaki da al’ajabin dukiyar Uncle din nasa Ya hana shi Kwantar da hankalinsa, Tun Bayan da escords suka ɗauko su daga airport, Motocin suka shigo gidan gabanshi ke ta faɗuwa, saboda sabon gini ne baya a ƙasar Uncle ɗin nasa Ya mallake shi, shiyasa komai yake ɗaure masa kai, Kafin shigarsu gidan Saida shureim Ya dinga jero addu’o’i acikin zuciyarshi Yana neman tsari akan Allah ya kare shi daga shagalar duniya, Idan har zaman shi gidan ba alkhairi bane, Ya roƙi Allah da ya yi mashi silar barin shi cikin sauƙi ba tare daya sha Wahala ba.

Tun da suka shiga gidan Kamar wani baƙauye Haka ya dinga bin ko’ina da kallo, wasu matsiyatan Chandeliers saman ceilling Masu ƙyalƙyali tamkar zasu rubzowa mutun saman kanshi, Ga wasu Haɗaɗɗun twins stairs, masu ɗauke da Glass Elevator a gefensu. Idan ka shiga cikinta Kana iya hangen mutanan dake zarya a palourn Yayin da take Yin sama dakai ko take dawowa dakai ƙasa.

A katafaren Palourn gidan kuwa Wasu Jigunannun Royal Sofas set ne Ƴan ubansu masu numfashi Ga Arm chairs kalar Na sarakuna, A gefe da gefen kujerun Sofa table ne, Tiles din palourn baida banbanci da Mirrored tiles Kana kallon Fuskarka acikinsa Idan kana Tafiya, zallar haɗuwa, An zuba komai na more rayuwa, Idan nace zan tsaya zayyana haɗuwar Komai dake acikin Gidan Tabbas zamu ƙare middle step da last step acikin gidan Alhaji musa ()

Babu wanda Yasan da zuwansu, Hatta Iyalinsa Ba su san da dawowar shi a yau ba, yana ɗaya daga Cikin Halayan Alhaji musa, Idan zai yi tafiya babu wanda ke sani Matar shi ko ƴa’ƴanshi, Haka zalika Idan Zai dawo sai dai su ganshi, saboda zuwan ba zata Ya ke yi masu.

A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon Hijabi a jikinta duk ta ƙudundune kanta acikinsa, daga gaban dardumar Qur’anic Stand ne, ga dukkan alamu Bacci ne Yai awon gaba da ita a yayin da take Yin karatun al’ƙur ani mai girma.

“Zeenat! Kiran Sunanta da akayi ne Yasa ta firgita a Hazarce Ta farka daga baccin ta ɗago da kanta tana faman zazzare dara daran Kyawawan idanuwanta farare ƙal launin Ocean Blue, Masha Allah Kyakkyawar matashiyar budurwa Kamanninta sak Alhaji musa tamkar yayi kakinta, sai dai Daga gani Farar fatace Haskenta ya ɗare na mahaifinta, Fara ce sol Jawur da ita, tana da yalwatacciyar sumar kai Launin blonde har saman fore head ɗinta kwantaccen gashi ne, ga doguwar fuska, dogon hanci da ƙaramin baki launin pink, Ba ta da ƙiba ko misƙala zarratin siririya ce, abu ɗayane ke da girma a jikinta, dukiyar fulaninta acike suke kamar an jera balon balon.

“Zeenat! Bacci ki ke Yi”? Muryar Mahaifiyartace ta rasa kunnuwanta, da sauri ta zabura ta miƙe tare da wurga ƙwayar idanuwanta kan Mai shigowa ɗakin, babbar macace mai cikar kamala, Ta ɗauki wankan Shadda ajikinta launin Ja, Tasha uban ado akan fuskarta, baturiyace Siririya bata da ƙiba, daga ganin surarta a wurinta matashiyar budurwar ta gado hasken fata da launin ido, da kuma doguwar sumar kai, Hajiya Sarah Uwar gida kuma amarya awurin Alhaji musa, ta ɗaure kanta da kallabi, hakan bai 6oye doguwar sumar kanta da ta sauko har gadon bayanta, Necklace ɗin wuyanta da earrings ɗinta na zallar diamond ne sai ƙyalƙyali suke Yi da ɗaukar ido.

Muryarta Adisashe ta amsa mata”mommy karatun ƙur’ani nike Yi bacci ya ɗauke ni bansani ba” ta yi maganar tana Yin miƙa haɗi da yin hamma

“Ba ki ji dirar motoci ba ne”? Ras Taji gabanta Ya faɗi, Muryarta na rawa ta furta”dad… daddy is he back “?

Ta6e baki Hajiya Sarah tayi”ya dawo tun ɗazu, yanzu haka yana a ɗakinsa, yace baya son takura, kinsan halinsa”

Hankalin Zeenat Ba ƙaramin tashi yai ba, ta rasa gane farin Ciki za ta yi ko baƙin Ciki, Tana son mahaifinta sosai, sai dai tana mugun jin shakkarshi saboda rashin sakar masu fuska da baya yi, duk da wani lokacin idan yaso yana nuna masu so da ƙauna.

Jin ta yi shiru zugudum tana faman zazzare ido Yasa Hajiya Sarah cewa”ya naga kamar baki farin Ciki da dawowarshi”? A hanzare ta girgiza kai” “I’m so happy he’s back, na yi murna ai shi ɗinne baya son takura”

Murmushi tasakar mata”Albishirinki”!
Da mamaki ta tsayar da eye balls ɗinta kan face din momyn nata
“Goro”!
“Fari ko ja”
“Fari”
Matsawa Mommyn ta yi kusa da ita Cikin raɗa ta furta mata”Ba shi kaɗai ya dawo ba, Hada Yayanki Dr shureim yanzu haka Yana kwance a bedroom ɗin da aka ware masa” Tun kafin Hajiya sarah ta ƙarasa Maganar, Zeenat ta zube saman gwiwowinta tare da ɗaura goshinta saman tiles ta yi Sujjada tsabar farin cikin jin anzo mata da sahibinta

“Ah lallai ashe Har yanzu Kina son Yayan naki, Hada Yin sujjada” ɗagowa Zeenat Tayi, tare da miƙewa tsaye Hijab ɗin jikinta sai Ja da ƙasa Yake yi.

“Mommy bazan Iya jurewa ba, Zanje wurin Yayana inyi mashi barka da zuwa” tsantsar farin cikine akan fuskarta

“No kada ki je Yanzu ki bari masu aiki su kammala Girka mashi abinci, In yaso sai ki je ki kai mashi a ɗakinsa, Daddynki ne Ya bada Umarnin A girka mashi abinci hausawa”

Zeenat da takasa rufe bakinta don Murna duk tabi ta ƙagara don a kwaɗaice take da son ganinsa
“Na faɗa maki zuwanshi ne Don ki kimtsa, Ki gyara kanki, Nasan Halinki da sanya dogon Hijabi salon kije mashi ahaka, Ki samu Ko ɗan gyalene ki yafa a kafaɗa,” turo baki zeenat tayi da ƴar shagwa6a tace”Mommy ae shima Yaya shureim ɗin yafi son mace mai sanya dogon hijabi”

“To ai bance bayaso ba, tun da acikin gidane ki samu gyale ki yafa” ta ƙare maganar da zolaya ta furta”Muslimatun matar limam” Dariya Zeenat ta sanya tana kallon mommyn nata.

“Zan koma kitchen, Ki tabbatar kin shirya da wuri”

Amasa mata tayi da toh

Bayan fitarta, da sauri Zeenat ta cire hijab ɗin jikinta, ta nufi toilet ta shige, cikin Ƴan mintuna ta fito Sanye da bathrobe (rigar wanka) fara Ƙyal a jikinta, hannunta ruƙe da short towel tana tsane sumar kanta, Bayan ta kammala tsane gashin, a gaban tafkeken dressing mirror ta zauna saman chair tana Gyara Jikinta, Hair dryer ta kunna Ta busar da sumar kanta, Bayan ta gama ta soma shafa tsadaddun Mayukan shafawarta dake a jere gaban madubin.

Zeenatu muguwar sangartacciyace ta saba tun tana ƴar ƙarama duk In za ta yi make up ko zata sanya sutura masu aikin gidansu ne ke taimaka mata, saboda ba ta Iya komai na aikin wahala ba, hatta sanya ɗan kunne bata Iyaba wahala take sha, Yau saboda zumuɗin zuwan ya ya shureim bata bari wani ya taimaka mata wurin sanya sutura ba, tun tana agaban mirror mai aiki ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta ta nemi zinin shigowa, ta tambayeta Ko tana Buƙatar wani abu, tace mata a’a taje kawai za ta yi komai da kanta, ashe da rabon tasha wahala.

Gaba ɗaya saida ta faffasa kayan kwalliyar gaban mirror, bata da natsuwa ko misƙila zarratin tana da rawar kai da zumuɗi, tun daga kan Hoda da ta ɗauko zata shafa, Ta sil6e daga hannunta gaba ɗaya ta tarwatse a saman tiles, garin hodar ya zube, Ta kuma janyo janbaki a tsiyace take murza ma la66anta nan take ya gutsire guntulan Ya faɗi ƙasa ta jefar da shi, duk kwalbar turaren data ɗauka sai ya sil6e ƙasa Ya daki tiles kwalbar ta fashe ruwan Ciki Ya tsiyaye, hakan bai dame ta ba, don ta yi asararsu.

Bayan Ta kammala ƴan shafe shafenta, bata bi takan kayan da ta faffasa ba, tsallake su ta yi ta nufi tafkekiyar glass wardrobe ɗinta, daga wajen glass ɗin kana Iya ganin jerin suturar sanyawarta ashaƙe tamkar a company, Abayas, shadda atampa leshi, material, english wears, Pakistans, ga jerin Kayan baccinta, komai fa anzuba mata su, shalelen daddy musa

Da hannu ta zuge glass wardrobe ɗin, Ta ƙura ido tana tunanin suturar da zata sanya don ta burge Yayanta shureim, idanuwanta ne su ka sauka akan haɗaɗɗiyar atampa, yatsun hannunta na kerma ta cafko ta, tana kiciniyar ciro atamfar ai ko gaba ɗayan jerin Kayan da ke a gidan tsakiya suka zazzago saman tiles, ko ajikinta, saida ta 6arar da kayan wardrobe ɗin wurin neman sutura ɗaya kacal da zata sanya a jikinta, Ga abu a fili ta ɗauka tasa shine bazata Iya ba, tafi so saita haukata komai na ɗakin tukunna a ƙarshe tabar masu aiki da wahalar gyara mata su.

Tamkar zata fashe da kuka, ruwan ido Ya hanata ɗaukar Kayan da zata sanya don ta burge Yayanta.

“Assalamu alaikum” Muryar ɗaya daga Cikin masu aikin gidan ce babbar mace wadda suke Kira da Tani.

Da sauri Zeenat ta juyo tana kallonta,
“Yawwa Tani, shigo ciki ki taimaka min narasa wasu Kaya zasu dace dani, Inaso ne na burge yaya shureim”

Baki asake Tani take bin ɗakin da kallo, Sam ba ta yi mamakin ganin yadda Zeenatu ta faffasa Kayan Kwalliyarta da turarurrukanta ba, Halinta ne yin 6arna kamar 6era.

“Haba zeenat, Dubi yadda kika zazzago da ninkakkun Kayan Cikin wardrobe ɗinki ƙasa, sannan kinbi kayan kwalliyarki da kwalaban turare duk kin faffasa su why pls? Harfa larai na turo donta taimaka maki ki shirya a tsanake amma sai ki ka ce mata ta tafi za ki yi da kanki, yanzu kin kyauta abun da ki ka yi”? Cikin kwantar da murya take Yi mata magana.

Zumbura mata Baki Zeenat tayi”Nifa bana son faɗa, Idan ma na faffasa su ai daddy zai canza min wasu, kuma ai bada gangan nayi ba ko”

Girgiza kai Lami tayi haɗi da sakin murmushin takaici “Oh, Saboda kinsan daddynki zai siya maki wasu shiyasa kika faffasa su? Ke Baki damu da asarar dukiyar da za’ayi ba kenan”?

Bubbuga ƙafafuwa Zeenatu tayi fuskarta a tur6une tace”Ni ki daina Yi min faɗa, Nace maki ba laifina bane kuma in sha Allah zan gyara, pls ki taimaka min In gyara komai kada mommy tazo taga ban shirya ba”

Gyaɗa kai Tani tayi”ai dole kam in tayaki gyarawa, idan ba haka ba hada ni zata shafa”

Ƙarasa shiga ɗakin Tani tayi, cikin ƙanƙanin Lokaci ta ɗauko Parker ta tattara Kayan kwalliyar da zeenatu ta faffasa ta zubar a trash can na ɗakin, Ta koma bakin wadrobe din ta soma ninke mata kayan da ta zubar a kasa ta jera mata su a cikin wardrobe, duk tana a tsaye ta ruƙe qugu tana kallon tani.

Wani haɗaɗɗan Cord lace ta ɗauko mata Red colour anyi mashi adon flower yellow.

“Zeenat wannan zaiyi maki kyau sosai, Red and yellow, kalar farare ce sannan kuma kyawawa irinki”

Washe fararen Haƙoranta tayi Jiki na rawa ta sanya hannu ta kar6i kayan da Tani ta miƙo mata, Sai da Tani ta taimaka mata wurin ɗaura zani da ɗaura ɗan kwali don ba ta iya ba, masha Allah Lace ɗin Yayi bala’en Yi mata kyau.

“Bari na ɗauko maki Takalman da zaki sanya” Tani ta yi maganar tare da nufar Shoe rack din ɗakin, Inda jerin takalman Zeenatu suke na gayu masu tsini da flat, ta ɗauko mata yellow kalar head ɗinta.

Ta dawo ta ajiye mata su agabanta, ta koma ta ɗauko Jewelry box dinta, ta ɗauko mata sarƙar diamond da earrings, Bayan ta kammala sanya mata su, sai da ta gyara mata make up ɗin fuskarta.

Ita kanta Tani Kyawun Zeenatu ya tafi da imaninta, Inaga wanda Akayi adon domin shi.

“Kinyi kyau sosai shalelen daddy musa, Muje kitchen ɗin in shirya maki dinner dinsa ki kai mashi”

Ta amsa mata da “Toh”

Daƙyar take yin tafiya da high hills din ƙafarta, Bawai don bata saba sanya takalmi mai tsini ba, sai don rashin natsuwarta.

Bedroom ɗinta a second floor Yake, Ƙa’ida ne idan zata sauko down stairs sai dai Ta hau elevator saboda a wurinta wahala ne taka bene.
Atare da Tani suka Hau elevator ɗin ta sauko dasu down, da kwarkwasa take yin tafiya tana taka tiles sautin na bada kwas kwas kwakwas.

Kaitsaye kitchen suka nufa, tun daga Cikin Katafaren palourn gidan kana Iya hangen Masu aikin dake safa da marwa acikin kitchen, a tsakiyar falon ta dakata da yin tafiya.

Tani tace “Bari na ɗauko maki Kayan abincin” ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi kitchen, badajimawa ta fito hannun ta ruƙe da wooden tray faffaɗan gaske, daga saman shi wasu haɗaɗɗun Warmers ne da flatware da sauran kayan abinci”

“Anya kuwa zeenatu zaki Iya ruƙe tray din nan? Naji da nauyi, ko dai In raka ƙi ɗakin nashi”?

Girgiza mata Kai tayi”a’a Zan Iya ki bani kawai” miƙa mata tray din tani tayi,
Ta rurruƙe shi da hannu Biyu, tana tafiya tana rangwaɗa, Tani dake a tsaye ta ƙurawa bayanta ido, ita tasan daƙyar zata Iya kai shi ɗakin ba tare da ta 6arar dashi ba.

Ɗakin da aka warema Dr shureim a gidan baida banbanci dana sarki saboda luxury furniture dake a cikinsa, sam ta manta ba ta tambayi Tani a wani room ya sauka ba, sai faman wurwurga eye balls ɗinta take yi a ƙoƙarinta nata gano masaukinsa, Cikin sa’a ta hango ɗaya daga cikin ɗakunan dake a rufe ƙofar shi ta buɗe hakan na nufin anan aka saukar da shi.

A lokacin Yana a kwance saman katafaren gadon ɗakin, Ya cire Jallabiyar jikinsa, Iya short ne fari, ya zame arab turban din kansa, Kwantacciyar sumar kanshi baƙa wulik, ya sanya singlet tabi shape ɗin ƙirjinsa.

Bacci ne ya ɗauke shi gefen shi wayarshi ce ajiye yana cikin kallon hotunan abar ƙaunarsa bacci yai awon gaba da shi.

“Yaya shureim ɗina” Muryar Zeenatu ce ke ƙwala mashi kira, tun kafin ta ƙarasa bedroom ɗin.

“Ya ya shureim am coming” kasancewar tana da zaƙin murya mai tsiwa har cikin kunnanshi yake jin muryarta.

“Yaya shureim” firgigit! ya farka daga baccin haɗi da miƙewa zaune la66ansa na ambaton sunan Allah, idanuwanshi har sun canza launi saboda bacci.

ɗakin Yabi da kallo a ƙoƙarin shi na ya gano ta inda zata 6ullo, sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin shi ga kallon ƙofar ɗakin.

Daƙyar ta ke tafiya, sai faman zabga murmushi take yi akan fuskarta, tun da ta shigo ɗaki ta tsayar da blue eyes ɗinta akan fuskarshi, da ƙarfi ta furta hubby na” kamar a mafarki shureim ke kallon zeenatu, kamar yau ya fara ganinta sam ya kasa motsawa daga zaunan da yake saman gadon.

Ganin yadda take yin tafiya babu natsuwa yasa shi yin saurin furta”bari nazo na taimaka maki” maimakon ta dakata da yin tafiyar tun da yace zai taimaka mata, sai ma ta ƙara saurin tafiyar da take yi, a hanzarce dr shureim ya haura ƙafafuwanshi ya sauko daga saman gadon sai dai kafin yai saurin zuwa gareta, Cikin rashin sa’a takalmin ƙafarta ya karkace ai ko Gaba ɗaya Ta saki tray ɗin hannunta Ya kife saman tiles kayan abincin ciki duk suka tarwatse, Nan take zanin da aka ɗaura mata Ya warware Ya zame ƙasa, Daga Ita sai ɗan pant ɗinta.

Runtse ido dr shureim yai, ba arziƙi ya dakata da yin tafiyar.

Jikinta sai kerma yake yi, Kunya duk ta isheta muryarta na rawa ta soma magana”wayyo Allah na, Am sorry yaya shureim wlh duk zumuɗin ganinka ne bansan ya akai zanin ya warware ba, gashi na zubda maka kayan abincin” ta yi maganar tana faman yarfa hannayenta, Kunyar duniya ta ishe shi

“Yaya shureim bari na koma Tani ta gyara min ɗaurin zanin, yanzu zan dawo maka da wani abincin tun da wannan Ya 6are” saboda tsabar ruɗu Anan tabar mashi zanin da kallabinta da ya warware, da takalmanta, da gudu ta juya ta fuce daga ɗakin

A hankali dr shurem ya buɗe idanuwanshi Yana kallon 6arnar da Zeenatu tayi mashi, rashin natsuwar yarinyar ba ƙaramin burge shi yake yi ba, Saboda yana samun nishaɗi sosai, tsabar shiririta ita da tace za taje a gyara mata zani ta tafi tabar zanan a ƙasa.

Yaushe rabon da ya yi dariya irinta yau harya manta, Hada dafe cikinsa tun da zeenatu tabar ɗakin bata ƙara dawowa ba saboda Kunya gare ta, kamar ba jinsin turai ba, Tani ce tazo ɗakin ta bashi hakuri game da 6arnar da zeenatu tayi mashi yace mata bakomai ai yarinyace yana yi mata uziri, Bayan tani ta kwashe kayan da ta 6arar mashi, Ta koma kitchen ta canzo mashi wani abincin ta dawo ta kawo mashi, kafin Tani tabar ɗakin sai da ta tattara kayan zeenatu da ta bar masa zaninta da ɗan kwalinta da takalman duka ta kwashe ta fuce da su, dr shureim yaso ta dawo suyi fira sai dai yasan abune mai wuya ta bari su ƙara haɗuwa yau sai dai zuwa gobe idan kunyar ta sake ta.

*PRISONERS MIDDLE STEP❤*

Ƙarfe 7 na safe agogan San antonio ta buga, adai dai lokacin Sojojin sun zo duba marasa lafiyansu daga headquater, mutun uku ne Commender, Major, tare da Captain sun zo cikin shigarsu ta kaki, A office ɗin dr. Laura davis suka fara zama domin tattaunawa.

A6angare Angel tana ƙudundune cikin bargo tasha baccinta, sai mutsu mutsu take yi duk ta yamutsa bedsheet ɗin ga dukkan alamu mafarki take Yi, A firgice tafarka Haɗi da yakice bargon ta wurgar da shi gefe ɗaya, hannayenta biyu saman fuskarta, cikin shaƙaƙƙar murya take ambaton sunan Danish, Mummuna mafarki tayi akanshi Ya farka Ya rikiɗa ya zama dodo Yana shan Jinin mutane, Hankalinta duk yabi ya tashi haiƙam gani take kamar mafarkinta zai iya zama gaskiya.

Ta yi zurfi acikin tunaninta muryar Nurse ta Fargar da ita
“Barka da safiya Masoyiya Angel, fatan kin wuni Lafiya” da sauri ta ɗaura idonta kan fuskar nurse ɗin

In a cool voice ta amsa mata Lafiyalou

“How are you feeling today? Are you experiencing any pain?” girgiza kai Angel tayi”A’a”
“Okey, nasan zaki buƙaci shiga toilet, ki gyara fuskarki, akwai sojoji da suka zo suna son ganawa dake, Amma kafin nan Zan kawo maki breakfast ɗinki ko kina da za6i na abunda kike son ci”?

Girgiza kai Angel tayi”a’a”
Okey daga haka Nurse ɗin ta juya ta fuce, Saukowa tayi daga saman gadon abakin ƙofar shiga toilet ta zura slippers dake ajiye saman carpet, kafin ta tura door din ta shige ciki.

A hankali take tafiya tana bin ko’ina na toilet ɗin da kallo A tsaftace yake fari ƙyal Kamar ba’a ta6a amfani da kayan Cikinsa ba.

Agaban mirror Ta tsaya tana kallon Kyakkyawar fuskarta, batasan lokacin da murmushi Ya kubce mata ba, nan take dimples ɗinta biyu suka lotsa, yatsun Hannayenta, ta tura cikin sumar kanta, a hankali ta soma barbaza gashin, aranta ta ayyana inama akai su saloon Agyara masu gashin kansu ba ƙaramin kyau za su yi ba, fanfo ta kunna Ruwa Ya soma kwararowa cikin sink, ta shigo da niyar ta wanke fuskarta sai kuma ta tsinci kanta da sha’awar son Yin alwala, nan take ta canza ra’ayinta, Tsarki ta fara yi kafin ta soma Yin ta a tsanake, bata manta komai na daga yadda akeyin alwala ba, bayan ta kammala Yi, ta fito daga Cikin toilet ɗin tana Tunanin tayaya zata Iya yin sallah bayan babu Hijabi? Buɗe ƙofar da akayine yasa ta ɗago tana kallon mai shigowa nurse ce ta shigo hannunta ruƙe da tray na kayan breakfast ɗin Angel asaman table ta ɗaura mata shi.

Ɗagowa tayi suka hada ido da juna”Is there anything you need?”

Da sauri tace”Hijabi da abun sallah inaso zanyi”
Da murmushi akan fuskar nurse ɗin tace”are u muslim”? Ɗaga mata kai Angel ta yi alamar eh, nurse ɗin tace”Okey, ki jira ni yanzu zan dawo”

Fuce wa tayi daga ɗakin, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tana ƙare ma ɗakin kallo, shigowa nurse ɗin tayi hannunta ruƙe da hijab da Prayer mat ta miƙa mata, Farin Ciki a wurin Allah bakinta yaƙi rufuwa.
“Thank u so much” nurse ɗin na murmushi tace da ita”never mind” ita kanta batasan Ina ne alƙibla ba, sai da ta tambayi nurse ɗin tayi amfani da wayar hannunta wurin yi mata bincike ta gano mata Alƙiblar da zata fuskanta tukunna ta shimfiɗa carpet ɗin, a tsanake ta kabbara sallah, saman chair nurse din ta zauna tana jiranta, Raka’a Biyu Angel tayi kafin ta sallame sallar, wani irin daɗi take ji yau tayi sallah, bakinta yaƙi rufuwa, tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tana karanto addu’o’ kirari tafara yi ma Allah kafin tayi ma ƴan uwanta da suka rasu addu’a, da su kansu a ƙarshe ta roƙi Allah akan Ya haɗa ta da ƴan uwanta ba tare da ta sha wahala ba, Allah yasa daddynta Yana araye, da auntynta Aneelerh. bayan ta kammala Yin addu’ar, Ta shafa a fuska, ta yunƙura ta mike, ta nannaɗe prayer mat ɗin da hijabin ta dubi nurse ɗin

“Kin gama” ɗaga mata kai Angel tayi alamar eh, Miƙewa tayi tare da zuwa gaban angel ta kar6i carpet din da hijabin juyawa tayi ta nufi closet ɗin ɗakin ta buɗe ta sanyasu aciki.

“Aduk lokacin da kika buƙaci yin ibadarki zaki iya ɗauka ki yi” godiya Angel tayi mata, daga bisani ta zauna zaman Cin breakfast, lafiyayyan kalaci aka haɗa mata, tana ci tana tunane tunane sam tamanta da sojojin dake jiranta.

Sai da ta kamalla cin abincin ta ƙoshi, Nurse ɗin ta tattara komai ta fuce dashi, Zama tayi gefen gadon idonta akan ceilling ta ƙurawa haɗaɗɗen kwan ɗakin ido, Yayin da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru.

Ba zato ba tsammani ta tsinkayi muryoyinsu a yayin da suke shigowa ɗakin, A hanzarce ta miƙe tana faman zazzare gray eyes ɗinta akansu, sojojinne tare da likitocin, saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna a jere suna fuskarta, Dr Laura davis ta zauna gefenta, Kamar wata mara gaskiya duk ta kama kanta, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba.

“Masoyiya Allah fatan Kin wayi gari lafiya? Ya jikin naki” muryarta adabarbarce tace”da sauƙi sosai” cikin kulawa suke Yi mata magana da harshen turanci

Dr Mark jackson ne ya fara yi mata magana”mun nemi jin bayani daga bakin ɗan uwanki Gabriel sai dai bai bamu haɗin kai ba, Yace duk abunda muke son sani ke ce zaki amsa mana.

Jin wannan maganar yasa hankalinta ƙara ɗugunzuma.

Fahimtar yanayin ta ne yasa dr mark cewa” Ki kwantar da hankalin ki, Bamu zo da niyar mu takura maki ba, Ƴan tambayoyi ne zamuyi maki da zarar kin amsa mana zamu tafi, munfiso ki natsu kiyi nazari kafin ki amsa mana”

“Kin shirya”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, duk tabi tasha jinin jikinta.
“Da farko zamu so ki fada mana Ya akai kuka tsinci kanku A daji? Waye ya kai ku can? Sojojin kasar mu suna hasashen ɗan Ta’addan daya gudu zuwa canne Yai garkuwa daku don ya kare kanshi daga farmaki da suka kai mashi, shin dagaske ne ko kuwa? Ƙura masu ido ta yi ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu, tsabar fargaba ƴan hanjin cikinta sai kaɗawa suke Yi, Tarasa Tayaya zata fara basu amsar tambayarsu? sam ba ta jin zata Iya faɗa masu ainihin Abunda Ya faru da rayuwarsu, ita aganinta kamar idan suka ji zasu guje su ne, musamman idan Danish Ya farka a matsayin giant ba ƙaramar masifa zaija masu ba, Zaiyi wuya su yarda da abunda zata faɗa masu, saboda Labarin baƙar izayar da suka sha a prison ba kowane zai gasgata kalamanta ba, zama su Iya tunanin ƙarya take yi masu, bayan haka tana tsoron ta fada masu, su kuma su tara Ƴan jarida su sanar dasu a ɗauki hotunansu ayi share da labarin prison tabbas yin hakan zai jaza masu babbar matsalar da zata Iya ja su rasa rayukansu don tasan dole Shuwagabannin kurkukun ƙaddara su bibiyi rayuwarsu ko dan saboda abu biyun nan na farko Garkuwar kurkukun da su ka gudu da shi, Na biyu don kada su tona masu asiri.

duk da sanyin A.c dake ratsa fatar jikinta hakan bai hanata zubar da zufa ba, ta ko’ina take tsastsafo mata, Hakan ba ƙaramin ɗaure masu kai yai ba, farat ɗaya suka fahimci akwai wani gagarumin al’amari atattare da yarinyar sai dai zaiyi wuya ta iya sanar da su gaskitar zance.

Gyaran murya Commender yai mata, A hargitse ta wurga eye balls ɗinta akan fuskarshi

“Kin yi shiru baki ce komai ba meyasa”?

Dafa kafaɗarta dr laura tayi da hannu ɗaya”Ki kwantar da hankalin ki my daughter, Ki natsu ki bamu amsa, a shirye mu ke da mu taimaki yaruwarku, haɗin kanki kaɗai muke buƙata, kuma muna tabbacin zaki Amsa mana tambayoyin mu”

gaba ɗaya ta ruɗe saboda saƙe saƙen da zuciyarta ke yi mata, wani sashe Yana jan kunnanta akan karta kuskura koda gigin wasa tace zata faɗa masu abunda ya faru a rayuwarsu, Yayin da wani sashe na zuciyarta ke Jan hankalinta akan ta faɗa masu wata’ƙil su taimaka masu wurin kawo ƙarshen Azzaluman kurkukun ƙaddara, Yanzu idan ta 6oye masu taƙi faɗa masu gaskiya kwatsam wani abin da ba’a fata ya zo ya same su har su rasa rayukansu shikenan tarihin kurkukun ƙaddara zai cigaba da wanzuwa ne.

Sun tasata gaba kamar sun sami tv, duk sun ƙagara da su ji amsarta, gashi taƙi buɗe baki tayi magana.

“Idan har baki bamu amsar tambayoyinmu ba, zamu maida ku Dajin da muka ɗauko ku”! Acewar Major

Ras Taji gabanta ya faɗi, Lokaci ɗaya ta fashe masu da matsanancin kuka mai ratsa zuciya Cikin shessheƙar kuka take faɗin”Ni bansan komai ba, Bazan Iya tunawa ba, Namanta komai, ɗan uwana danish shi ya sani”

Ta ƙara rikita masu lissafi, Captain yace”kun haɗa baki ne? Mun tambayi ɗan uwanki Gabriel ya faɗa mana cewa ke kaɗaice kika san komai, Yanzu kuma mun tambayeki kince kema bakisan komai ba A tambayi Danish! Why kuke son Yi mana yawo da hankali….? Da alama Ya Hasala ne dan muryarshi a kausashe yake mata magana.

Da sauri dr laura ta katse shi”Sir, bata da ƙoshin Lafiya, Ni a ganina bai kamata mu tsareta da tambayoyi ba a yanzu, ƙaramar yarinya ce sai ana lalla6ata”

Sassauta fushin fuskarshi Yai, Cikin kwantar da murya yaci gaba da cewa”Okey, Share hawayenki, ki daina yi mana kuka bama so” Muryarta Na rawa ta amsa mashi da toh.

Miƙewa Dr laura ta yi ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauko mata fanta me sanyi, ta haɗo mata da tissue, Ta dawo gefen gadon ta zauna tare da miƙe mata tissue ɗin, Hannayenta na kerma ta kar6a ta soma goge ƙwallarta da hancinta, Bayan ta gama share hawayen dr laura ta miƙa mata lemun kar6a tayi tare da yi mata godiya.

kamar tasan Mayyar fanta ce, Buɗe wa tayi agaban su ta kur6i ruwan lemun kusan sau uku tana sha, Sun tsareta da ido suna kallonta, hakan ba ƙaramin rikitar da ita yake yi ba.

“Pls Masoyiya Angel, Ki taimake mu ki taimaki rayuwarki da ta sauran ƴan uwanki, Ki faɗa mana gaskiyar abunda Ya faru a rayuwarku wanda yai silar haifar maku da ciwon damuwa, Idan har baso kikeyi mu maida ku daji ba” acewar Captain.

“Abunda mukeson sani shine Ya akai kuka tsinci kanku a ƙurmin dajin Evil forest? saboda ɗan ta’addan ƙasarmu da muke hasashen shine Ya kai ku can mun titsaye shi akan ya faɗa mana menene alaƙar shi da ku, Ya faɗa mana cewa Baisan komai dangane da ku ba, Ya taimaki wasu daga Cikin ƴan uwanku ne, Munyi dogon nazari akanku, da farko munyi tunani ƴan ƙasarmu ne ku, sai kuma muka ji kuna magana da wani harshe wanda bana nahiyarmu ba! Mun rasa gane daga wani Jinsi ku ke? sannan menene maƙasudin haddasa maku ciwon damuwa da baƙin ciki? lamarin ya ɗaure mana kai da ƙananun shekarunku? hada me fama da ciwon zuciya! Wani abun al’ajabin ɗaya daga cikin Ƴan uwanku yaƙi farkawa daga bacci mun rasa gane meke damun shi……” tun da major ya soma yi mata magana a tsanake ta tsare shi da ido tana kallon la66ansa har ya ƙare maganarsa, tukunna ta fara magana
“Gaskiya ne abunda ɗan ta’addan ya faɗi, bashi ne yakaimu daji ba, Mun jima Acan kusan zance tun kafin mu mallaki Hankalin mu, bazan Iya tuna abunda Ya faru arayuwar mu ba, kome yakai mu Dajin, abunda na sani shine Munci baƙar wahalar rayuwa dani da ƴan uwana, wanda silar hakan yajaza mana depression….”
Kallon Juna su ka yi, still sun fahimci bazata faɗa masu abunda suke son ji ba, sam bata son su sani babu alamun zata yarda da su.

Murmushin gefen fuska Major ya sakar mata”Ni dama tunda naga idanuwanki da ƙaramin bakin nan Naki raina ya bani kina da wayau sosai,” duƙar da idonta ƙasa Ta yi zuciyarta na bugun uku uku.

Dr. Laura sam ba ta so suka matsa mata da tambayoyi ba, tuntuni ta basu shawarar su bari Yaran su saba da su tukunna amma da yake Sojoji ne Yana ɗaya daga cikin Halayansu, Idan suna son jin bayani daga bakin mutun ba wani uziri da suke Yi mashi dolenshi ya amsa masu.

“Yaren da ku ke yin magana da shi na wace ƙasa ne”? Captain ne Ya jefa mata tambayar.

Muryarta na ɗan rawa ta furta”Ni.. geria” Tsabar mamaki ne yasa su kallon Juna.

“Kina nufin daga Nigeria ku ke? Tayaya hakan zai yiwu? Dama Nigeria suna da farar fata ne acikin su? a iya sanina baƙar fatane mutanan Nigeria, Sannan matansu kuma basu da dogon gashi, kuma Launin idonki Kalar na mutanan ƙasarmu ne”
Dr. Mark jockson ne Yai maganar da alamun mamaki akan face ɗinsa
Dr. Laura na murmushi ta dube sa”kada ka bani kunya mana, ko mu a ƙasarmu ai akwai black americans, zai Iya yiwuwa suma suna da alaƙa da fararen fata ne ina nufin half cast”

“Dagaske Ku ɗin Ƴan Nigeria ne? Jinjina masa kai tayi”Eh, ai yaren da muke yin magana dashi hausa ne na nigeria, zaku Iya bincikawa”
Ba ƙaramin mamaki suka yi ba, Hatta turancin da yaran suke magana da shi sak Na america ne bana Nigeria ba.

“Yanzu dai bazaki faɗa mana gaskiyar abunda ya faru da ku ba ko! To Shi ɗan uwan naki da kika ce yasan komai tayaya zamu Iya farkar da shi daga bacci”! Anzo dai dai wurin da tafi so, marairaice masu fuska ta yi”maganinshi Yana a nigeria, dan Allah ku taimaka ku maida mu ƙasarmu, idan ba haka ba ɗan uwanmu zai Iya mutuwa” hada ƙwallarta
“Meke damun shi ne” Dr Brown ne yai mata tambayar, batare da ta yanke shawara da zuciyarta ba tace”nima bansani ba, Idan yafara bacci yana ɗaukar tsawon lokaci bai farka ba, to akwai maganin shi kuma yana acan ƙasar”
Murmushi kowannansu ya saki, hakan yasa tasha jinin jikinta, Commender yace”Kin Iya acting, da farko kince bazaki Iya tuna komai daya faru a rayuwarku ba, amma ayanzu kin faɗi inda za’a samu maganin ɗan uwanki hakan na nufin tunaninki yana nan baki manta komai ba ko”? ɗaure mata fuska yai “Zaki faɗa mana gaskiya ne? Ko kuwa kunfi so mu je dake can headquater Ki amsa mana tambayoyinmu ta tsiya” tashin hankalin da ba’a sanya mashi date
Maganar commender tayi matuƙar tsoratar da ita Jikinta Ya hau yin kakarwa duk tabi ta rikice, A ƙarshe data ga dagaske zasu titsayeta saita amsa masu tambayoyi ko su tafi da ita headquater, aiko da ƙarfi tasa wata irin gigitacciyar ƙara data firgitar dasu, Hannayenta Biyu ta sanya ta daddafe kanta tana faɗin”Nace maku ni bansan komai ba! Dan Allah ku maidamu ƙasarmu Nigeria, ɗan uwana zai Iya rasa ranshi, Na roƙe ku idan har dagaske zaku taimaki rayuwarmu to ku maidamu Nigeria wurin danginmu,” kamar mahaukaciya haka tadinga nanata masu akan su maidasu Nigeria.

Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda Ƙwayar idanuwanta suka burkice Launin Ciki Ya 6ace sai zallar farin idon, Jijiyoyin wuyanta dana Gaban goshinta shatunsu ya fito ruɗu ruɗu, Jefar da robar fanta hannunta ƙasa ta yi, a zafafe Ta miƙe saman gadon kamar ƴar daba, ta dunƙule hannayenta, taci gaba da ambaton Ku rabu dani ku ƙyaleni, Ku maida mu ƙasar mu Nigeria nace ku kaimu ƙasar mu, can muke son zuwa”

Har suna haɗa baki wurin lallashinta”sorry ki kwantar da hankalin ki, zamu tafi yanzu, Ki daina kuka ki kwantar da hankali, Ki koma ki kwanta, babu wanda zai Ƙara tambayarki wani abu” sun firgita da ganin haukan Angel.

Dr laura duk tabi ta ruɗe Sun rasa gane kanta.

Kallon Sojojin ta yi”Pls, Ku ƙyale yarinyar nan, Muje office muyi magana, idan ba haka ba za’a Iya samun matsala” gyɗa kai sukayi ba don sunso ba suka Juya tare da fucewa daga ɗakin tare da Likitocin, Ya rage da ita sai Dr laura.

“Pls My daughter kukan Ya isa haka, Ki koma ki zauna muyi magana kinji”? Lallashinta tashiga yi, Daƙyar Angel ke iya kallonta sumar kanta duk ta rufe mata fuska, dagangan ta ƙirƙirarma kanta Ciwon hauka.

Marairaice mata fuska Angel tayi”dan Allah ki taimaka mana, su maida mu ƙasarmu, banaso mu rasa ɗan uwanmu zai Iya mutuwa, maganinsa yana can, Nayi maki alƙawarin idan ya farfaɗo zan fada maku duk wani abu da ku ke son ji dangane da mu”

saukowa Angel tayi daga saman gadon, A sukwane ta zube saman gwiwowinta agaban Dr laura, Idanuwanta sun cicciko tab da hawaye take faɗin”Na roƙe ki Ki taimaka mana, kamar yarda Allah Ya taimake ki, Kice ma sojojin can sumaida mu Nigeria, Idan ba haka ba Ɗan uwana danish zai mutune, ba zaku Iya sarrafa shi ba, maganinsa yana acan, Ni na yarda ku sanya jami’an ku, su bimu can kasar don su shaida abunda na faɗa masu su sanya mana ido’ Muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar.
Tsananin tausayintane Ya kama dr. Laura har cikin ranta ta aminta da yarinyar, Miƙa mata hannu tayi”miƙe tsaye” da sauri Angel ta ɗaura hannayenta asaman na dr laura, ta yunƙura ta miƙe, ba zato ba tsammani taji ta rungumeta a kirjinta, ƙamshin turarenta Ya daki hancin Angel sosai ta ƙankameta tana faman sauke ajiyar zuciya.

Shafa sumar kanta dr laura tayi a hankali take yi mata magana
“Ni tun farko banso suka tsareki da tambayoyinsu ba, sunyi gaggawar yin hakan, But Inaso ki kwantar da hankalin ki, Zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin sun maida ku ƙasar ku, idan har kikayi min alƙawarin zaku faɗa mana abunda ya faru da ku bayan ɗan uwan naki ya farfaɗo kamar yadda kika ce”
Cikin sanyin murya Angel tace”Nayi maki alƙawari shiyasa ma nace su sanya jami’an da zasu bibiyi rayuwarmu” ta ƙare maganar tare da raba Jikinta daga na Dr laura
Shafa fuskarta tayi”is ok, Zanje muyi magana da su yanzu ki koma ki kwanta ki huta”

Amsa mata Angel tayi da toh, Bayan fitar dr laura, Daɗi kamar zai kasheta, don tana ji aranta zasu amince masu su koma Nigeria, juyawa tayi tana neman robar fantar data jefar a ƙasan tiles can ta hangota gefen nightstand zuwa tai ta ɗauko lemun ta koma gefen gadon Hankali kwance taci gaba da shan lemun fatanta Allah yasa su amince masu.

Gaba ɗayansu sun Hallara a katafaren ofishin dr laura, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna saman haɗaɗɗun kujeru, table ne Ya ratsa tsakaninta da su,.

“Shawarar da zan bada shine bai kamata mu takura masu da tambayoyi ba, duba da Yanayin yaran akwai ciwon damuwa atattare da su, tursasa masu zai Iya haddasa masu wata matsalar da bama fata” Dr laura ce ta kora jawabin idonta akan faces din sojojin
Commender yace”Ya zamuyi kenan? Menene Mafita don muna buƙatar son Jin ainihin abunda ya faru da su a dajin nan”
Numfasawa dr laura tayi”Munyi magana da yarinyar, tabbas bata manta komai ba, tasan abunda ya faru da rayuwarsu sai dai rashin yarda da tsoron fargabar abunda zai biyu baya idan ta faɗa mana sun Hana ta sanar damu, abun duba anan shine Babu yarda za’ae su saki jiki damu don ta yanzu, saboda basu sanmu ba bugu da ƙari kuma ba ƴan kasar mu bane, donni na yarda da maganarta, Idan har munaso muci nasara akansu dole sai mun yi masu abunda su ke so, ta hakanne zasu saki jiki damu har su faɗa mana gaskiyar abunda mu ke son ji daga gare su, sannan suna buƙatar wadda zata Kula da rayuwarsu tamkar mahaifiyarsu, Ta hakanne zasu saki jiki da ita har su Iya faɗa mata damuwarsu, abu na biyu shine Muyi masu abunda suke so! Musamman ita Angel din ta roke ni akan mu maida su ƙasarsu, Akan idonku kunga haukan da tayi mana tabbas akwai ƙamshin gaskiya a maganarta, tace maganin ɗan uwansu yana acan, kuma tace zamu Iya sanya jami’ae su bi su har can kasar sannan tayi alƙawarin idan harya farfaɗo zata faɗa mana duk abunda muke son ji.

Shiru suka ɗanyi na wani lokaci kowan nan su Yana nazarin maganar dr laura.

Numfasawa Major yai kafin ya soma magana”Me zai hana mu damƙa Case ɗinsu ya koma hannun Hukumar Isod? (Intelligence Special Operations Division) Tun da shugabansu Ɗan ƙasar Nigeria, su kaɗaine zasu Iya bincikar Ainihin abunda Ke faruwa da yaran, saboda suna da ƙwarewa a 6angaren.

Jinjina kai Commender yai da alama ya gamsu da jawabin Major

“Hakane ka kawo shawara mai kyau, case ɗin yafi dacewa dasu, Tunda Aikinsu ne Yin binciken sirri Harma da fafatawa idan ta kama kuma duk muna atare dasu banbancin kaɗan ne mu ba jami’an sirri bane su kuma duka sun Haɗa sunayin aiki a matsayin sojoji sannan kuma jami’an sirri”

Captain Yace”Nima na goyi bayan hakan, amma fa zaiyi wuya mu iya samun chief ɗin nasu a waya, So the best way to contact him is through email, We need to start making our request for the case through their email, If they show interest in the case, we will turn everything over to them.”

Commender yace”shugaban nasu ai Yana a Washington (babban birnin america) kuma naji raɗe raɗen kamar cikin weekend da zamu shiga zai bar ƙasar ya koma Nigeria, duk da bani da tabbaci kunsan aikin nasu na sirri ne babu mai sanin shiga da fucen su, Idan har muka samu ya nuna interest akan case ɗinsu komai zai zo mana da sauƙi, In yaso sai mu damƙa mashi Yaran ya tafi da su can, mu kuma zamu dinga bibiyarsu don jin ya ake ciki”

Murmushi Dr laura tasaki, Har cikin ranta ba ƙaramin daɗi taji ba, Fatanta Allah yasa Chief ɗin Isod Ya amince da case ɗin Yaran, ko dan saboda Yarinyar da ta roƙe ta akan amaida su ƙasarsu”

“Doctor, how long do you think it will take for the children to be discharged”? captain ne yai mata tambayar,

Dr. Laura ta bashi amsa da cewa “After the three-day injection course is completed, we will be able to discharge them, Shima Ɗayan Yaron mai fama da ciwon zuciya Zamu Iya sallamar shi idan har aka Kiyaye sharuɗɗan da zamu rubuta na bashi kulawa ta musamman, ” ta ƙara da cewa”zasu Iya zama a asibitin namu har zuwa lokacin da shi chief ɗin zai Amsa mana buƙatar mu”

Commender yace”dole ne mu sama masu wadda zata Iya kula da su tamkar ƴa’ƴanta kamar yarda kika bada shawara, wadda zata Iya tarairayarsu ta basu kulawar da zasu Saki Jiki sosai,” Yai maganar yana kallon fuskar dr laura
Major yace”why not bazamu damƙa amanar kula da yaran a hannun UMMIN AMERICA ba? Tun da itama Ƴar Asalin ƙasar Nigeria ce, hatta yaren da naji Yaran suna magana da shi itama tana jin shi sosai” Jin Major Ya ambaci sunan Ummin america yasa Dr Mark da dr brown Kallon Juna ga dukkan alamu sun girgiza da jin an ambaci sunanta, Dr laura ta zaro ido tana faɗin” The Baddest mistress? There’s no way we can leave the children in her care, She’s a dangerous woman. How could she possibly know how to take care of them?” hankalinta bai kwanta da zancen miƙa yaran ga Ummin america ba saboda sanin wacece Ita.

Bayan ta ƙare magana Major yace”Ai ba yau tafara Yi mana aiki ba, tana taimaka mana sosai akan irin case ɗin nan, Ina da tabbacin zata Iya! Fiye da yadda baki tsammani”Kwa6e fuska Dr laura Tayi don ita har aranta Fargabar Ummin americe take ji, Kowa yasanta sananna ce a 6angare Iya karuwanci tantiriyar ƴar bariki ce, tayi ƙaurin suna america shiyasa su ke yi mata laƙabi da Ummin america, tsabar Iya shaiɗancinta har award ake bata akan Iya Karuwanci.

“Mu zatayi ma aiki, bai shafi sana’arta ba, Kawai munaso Yaran su kace a hannunta amatsayin guardian ɗinsu, Kafin Mu damƙa mata su zamu yi yarjejeniya da ita idan har ta amince to lafiyalou ba zamu samu matsala da ita ba” ta6e baki dr Laura tayi”amma dai ba’a asibitin mu za’a gayyato mana ita ba, Don ina jin fargabar ta rikitar mana da ma’aikatan mu da surar jikinta”

Gaba ɗaya suka sanya dariya jin abunda tace, ta faɗi hakanne don tasan Ummin America kamar maganaɗisu take awurin Iya jan hankalin mutun da surar Jikinta, Dirine da ita na bala’e’
Sunjima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani Commender yace

“Dr mun gode sosai da shawarar ki, Zamu koma bakin aiki Yanzu, Idan har Chief din isod Ya amince da buƙatar mu zamu tuntube ku”

Daga haka Sojojin sukayi Ma Dr laura sallama, Har bakin parking space na asibitin ta rakosu, Bayan tafiyar sojojin suka dawo Cikin asibitin.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button