Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 40

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*40*

“My Aman zan tafi gida inna tana son ganina ” ta fada a shagwabe wato salon nata ke Kara fusgarsa yasa Wani lokaci yake Jin bazai iya kira ta kammala karatun kafin suyi aure ba, ” kayi shiru my..”
“So kike ki kasheni baby nah wallahi kullum sonki dada karuwa yake cikin zuciyata Anya zan iya jira kuwa ” juya idanu tayi tace ” why not just 1 year ne fah da few months”
” 1 year is too much baby gaskiya let’s be frank kawai ayi auren ki cigaba a gidanki seriously” um um..nidai nafison sai na gama durling ” Wani numfashi ya sauke take idanunsa suka fara canza launi kallo d’aya ta masa ta dauke Kai” baby kinsan me? I wanna kiss you ” hararinsa tayi tace” u are not serious ni zaka rainawa wayo, ka koma gida wajen matarka ”
“Haka zaki ce koh , wato Baki kishina Allah am serious I want to feel you ” kallonsa tayi tayi kwafa sannan ta Bude kofa tace” bari na tafi gun innata kafin ka lalata mata ni ” dariya ya tuntsire yace ” yaushe zan shiga na gaisheta ne ya kamata tasan da zancenmu fah ” just go home sai munyi waya ”
ta rufe masa kofa tare da d’aga masa hannu ya d’aga mata gira tare da kashe Ido d’aya ta girgiza kai tace ” mara Jin magana kawai” ta juya ta wuce gida , inna tana ba Sadeeq custard hajjo ta shigo da sallama Ayman na kwance bisa 2 seater ya rufe fuska da tafin hannunsa tamkar me bacci, zama tayi ” inna gani” sai yanzu kika ga daman zuwa ?” Shiru tayi tana kallon kasan kafet ” ba Dake nake ba, daga Ina ma kike ? ” Um..na dan fitane ”
“Kin fita kinje Ina? ” Shiru tayi daga bisani tace ” kiyi hakuri inna ” Ina son ki fadamin inda kikaje ” gabanta ya Fadi , saukar Marin da taji ne ya dawo da ita hayyacinta ta dafe kunci Ayman ya tashi zaune Yana magana a hankali” haba inna meyasa zaki dake ta, kiyi hakuri please ki mata a hankali ” Ayman rabu da yarinyar nan naga ta fara canza hali dole na saita mata zama ta dawo hayyacinta,don bazan bari tarbiyan da na gina mata ya rushe cikin kankanin lokaci ba” hawaye ke zubowa ta kasa d’aga kanta tana rike da kumatun ran inna ya Kara baci ” bazaki fadamin inda kikaje ba koh ” cikin muryar kuka tace ” baqo nayi ” bako fah bako fah kika ce ko kunya Baki ji , wato kin girma kin Isa fita zance Bada izinina ba koh hajjo ” kuka ta fara Ayman ya runtse Ido Yana Jin kukan nata har cikin zuciya ” inna please kiyi hakuri ki yafe mata please n please ” kwafa inna tayi ta tashi tabar falon saboda ita kanta kaunar da takewa hajjo yasa Batason ganin hawayenta tana matukar kaunar yarinyar har cikin kogon zuciyarta. Ayman ya cire handkerchief cikin aljihunsa ya Mika mata taki karba ta zauna kasa tana rera kuka, ya dawo kusa da ita yakai hannu tamkar Yana tsoro ya fara share mata hawayen Yana magana” sorry lil sis is ok ki daina kukan haka if not you’ll have a headache ok ” sai faman sauke ajiyar zuciya take ajere , qamshin turarensa dake jikin hanky din ta shaqa tana lumshe Ido don qamshi ne me sanyaya zuciya. Kura mata Ido yayi idanun nata a rufe suke Yana kallon kyakkyawar fuskarta Yana Jin sonta na dada fusgarsa tamkar ya rungumeta ya rarrasheta, yakai 4 minutes Yana kallonta kafin ya dauke idanunsa ya tashi ya koma bisa kujera yace ” ki daina yawan Bata mata rai please duk abunda Bata so just avoid it” cikin sanyin murya tace ” Yaya Ayman bafa Wani bane ba Aman ne fah, Kuma dama mun Dade da reuniting kawai ban gaya mata bane Amma kwanan nan na shirya gaya mata komai saboda ya fara min zancen aure ”
“Shi Aman din ne ya fara Miki zancen aure?” “Ehh yacemin Yana son ya turo iyayensa dama nice ban basa dama ba ”
“Ok toh ke kina sonsa ne ?” Kai ta gyada alamar ehh, murmushi Mai ciwo yake sannan yace ” is ok.. I’ll talk to inna about it” thanks Yaya nah ” daga haka ta tashi ta wuce bedroom din inna ta sameta a zaune ta buga tagumi Sadeeq yayi bacci , kanta ta kwantar bisa cinyar inna tace ” innata kiyi hakuri ki yafe min please daga yau duk Wanda yazo wajena sai na nemi izinin fita a wajenki don Allah ki yafemin bazan jure fushinki ba ” lumshe Ido inna tayi tana Jin dad’in yadda y’ar tata tayi saurin Gane kuskurenta. Hannu tasaka tana shafa gashin kanta tace ” ke din ce Wani lokaci Baki ji ”
“Kiyi hakuri inna bazan sake ba ” toh shikenan tashi kije Allah ya Miki albarka ” “Ameen na gode momsi nah ” murmushi inna tayi hajjo ta tashi zata fita tace ” ohh na manta d’ana na falo nabarsa shi d’aya ”
“Zan fara kishi fah don naga ya samu babban matsayi awajenki ” suna dariya suka fito tare ,cike da mamaki Ayman ke kallonsu ya kasa boye mamakin nasa ya Kalli inna yace ” wato sanyin idaniya daban take ko inna , idan kana son Abu baka iya fushi dashi koh ”
“Sosai wallahi bazan iya fushi da itama sai dai Wani lokacin tana kaini makura ” murmushi yayi Yana kallon Hajjo ta tura Baki tace ” nifa zan fara kishi da kaine don naga inna tana Ji da Kai sosai” murmushi yayi sosai Wanda ya fito da asalin kyaunsa hajjo ta kauda kanta gefe saboda yawan faduwar gaba da take fuskanta a duk lokacin da ta hada Ido dashi, d’aki zata shige inna tace ” jeki dafa masa indomie tun dazun yacemin Yana sha’awa ki saka ganyen albasa kadan ” Kai tsaye kitchen ta wuce tana shiga store don daukar indomie cikin zuciyarta kuwa dadi taji wato dai ta iya dafa indomie tunda gashi yauma ya nemi ta dafa masa irin na ranar .
Ayman ya Kalli inna yace” cewa tayi Aman Yana son ya turo magabata ” tabe baki inna tayi tare da cewa” badai nan gidan ba wallahi bazan iya da wannan uwar taku ba ” Amma Kuma suna son juna sosai” “Allah zai Bata Wani daban ” haka suka cigaba da tattaunawa inda inna ta nuna rashin goyon bayanta dangane da soyayyar hajjo da Aman har ta gama girkin ta kawo masa.

_________
Bayan sati biyu Ayman ya sayi dankareren gida Mai kyau a can Asokoro kwame khuruma street daga nan suka koma gidan nasu da zama Failuzaa na tambayarsa yaushe zasu koma saudia yace ba yanzu, ya Maida hankali sosai kan harkar kasuwancin nasa kullum wutar son Hajjo na dada karuwa cikin zuciyarsa donhaka ya dukufa da adua ba dare ba Rana Yana Neman Allah ya yaye masa. Aman da hajjo kuwa sai zuba soyayyar suke kamar zasu hadiye juna , sultan da Kansa ya gane hajjo tana soyayya da kaninsa saboda ya taba ganinsu tare yayin da ya Kai mata ziyara school donhaka ya janye kudurinsa ya rike girma a matsayinnsa na babba . Ummeey Bata taba yiwa hajjo maganan Aman ba haka nan Hajjo Bata ce mata komai ba suna dai kawancensu Babu abunda ya canza sai dai hajjo Bata fita da Aman idan Ummeey na nan sai idan Basu tare, yaune sun gama magana da Aman cewa zai turo iyayensa Neman aure bayan yasha fama kan ya shawo kanta ta amince donhaka ta Yanke hukuncin sanar da Ummeey kafin su koma gida ta sanarda inna. Sun fito lectures kenan zasu wuce parking lot hajjo ta Kalli Ummeey tace ” besty Ina da magana dake” ok toh mu karasa mota man ” no kizo mu zauna a nan,” ta nuna wasu kujerun zama nan suka zauna ta fara magana ” I don’t know ko kinsan cewa Ina soyayya da mijin yayarki Kuma bansan wane kallo zakimin ba after hearing all these, nida Aman mun kasance…” Masoya tun kafin haduwarsa da anty zee ” Ummeey ta karasa zancen , Bude Baki hajjo tayi tana kallonta Ummeey na dariya tace ” yes nasan komai saboda kin taba fadamin cewa sunan first love naki Aman, sannan ranar da mukaje gidansa I observed your reaction d both of you ” shiru hajjo tayi ta kasa magana” Kuma nasan cewa kin sake koma masa Kuna soyayya n Banga laifin Hakan ba saboda Koda nice iya abinda zan iya kenan , ni ban taba ganin laifinki ba Kuma am not against you yau Koda mijina ne bazan hanaki aurensa ba bare Kuma mijin yayata ” jikin hajjo yayi sanyi ta rike hannunta” please besty ki fahimceni kada ki daukeni maciya amana mun dade Muna son juna dani dashi Allah baisa zamuyi aure a wancan lokacin ba but yanzu Muna fatan Hakan amma bansan da wane Ido zan Kalli family naki ba shiyasa Wani lokacin nake ganin rashin dacewar auren namu , wata zuciyar tana gayamin na hakura da kudirin nawa shine mafita ” no please..aure da mutuwa duk lokacine Kuma idan Allah yayi Babu me hanawa donhaka Ina Miki fatan alheri” shiru tayi Ummeey ta jawota tace ” c’mon chill don Allah ki daina yin Abu kamar mara gaskiya you have any right to marry him wallahi am supporting you har cikin zuciya and I mean it” rungumeta hajjo tayi tana Jin Wani sanyi cikin zuciyarta daga nan suka wuce mota sukadau hanyar gida.

Check Also
Close
Back to top button