Miskili Ne 3-4
❤ MISKILI NE❤
Story & written
by mommyn fareesa
free Page 3&4
……..kasa furta komai sheriff yayi illah ya had’e gabas da yamma ya tamke fuska”shibe rufe motar ba shibe shiga ciki ya zauna ba” yayinda gaba d’aya k’amshin jikinsa yacika motar…..lolx” Alh ka shiga sai mu wuce ko?”yaji muryar yaron motar Abayansa “beyi mgn ba saidai kawai ya ballo mata harara yana mata Alamar ta matsa da hannu”bata matsa d’in ba saidai ta k’ara takure jikinta agu d’aya”ta kuma dena kallonsa sbd ganin yadda yazaro mata firgitattun golden eyes nashi”doguwar tsuka yaja yana shigowa ciki afusace ya zauna daga tsakkiyar su”ita tana daga gefe”suka zauna su 6 maimakon mutum 7 ya zauna”babu laifi kuma sauran sun matsa sosai yadda zai wala”gaba d’aya ya had’e rai yana duba time”da gangan ya aza k’afarsa me takalmi sawu ciki saman k’afarta ta dama”sosai taji zafi jikinta har rawa yakeyi Amma ko tari batayi ba”saima k’ara matsawa takeyi tana koma rage kusancinsu”yayinda mayataccen k’amshin turaren sa ya Addabi hancinta”yayi mamakin batayi mgn ba ko ihu”saidai tanata k’ok’arin janye k’afar tata”da yak’i janyewa sai takama kuka da hawaye”saida ya gaji dan kansa ya janye ,ya zaro ear piece ya lak’afa akunnuwansa sbd surutun mutanan dake cikin motar ya ishesa”ita kuwa bayan ya janye bacci ya kwasheta”sai sauke ajiyar zuciya takeyi”shi kuwa ya tab’e baki yana jin kamar yasameta ya mammara”dan ba k’aramin jinsa cikin takura yayi ba”yasan kuma sai sun kai kusan 8 pm su iso Kaduna”gajeran tsaki yasaki daya tuna Aikin da aka bashi”shi bema san ta yaya zai fara ba?”kawai dai zai bar mus’ab yaje yasamo duk wani information d’in yarinyar….yana wannan tunanin wayarsa tayi ringing”silent yamayar da ita sbd ganin Dr Mansoor ne ke kira”yana kuma mamakin meyasa zai kirashi a irin wannan time d’in?….jama’a ku had’a kud’i fa”cewar yaron dake gidan gaba gefen wani”kasan cewar duk mutum guda 7k zai biya” kudin sheriff 14k ne”saida yaga kowa ya bayar kafin cike da aji yazaro nasa yana kok’arin mik’a masa yaji yana cewa”keme bacci kitashi ki biya kosai Antasheki?”ya fad’a yana mik’o hannunsa zai tab’a gefen mayafinta”sheriff ya tsaresa da rikitattun idanuwansa”Atake yaji ya daburce”sai cewa yayi me gida saura naka kaima”yak’are maganar yana janye hannunsa”tamkar ita kuma An mintsineta ta farka “sheriff beyi mgn ba yamik’a kud’in….kamar Ance ya kalleta yaga ta tashi harara yasakar mata ya d’auke kansa”ranki ya dad’e baki biya kud’in kiba ko?”cewar yaron motar yana kallon ta yana washe baki”ita kuma tsuke pink lips nata tayi tana jujjuya idanuwanta Alamar zatayi kuka”kuma tak’i mgn”wani dake gefen sheriff yace”baby kina so na biya miki ne?”banza ta masa kamarma bada ita yake mgn ba”yaron motar ya saci kallon sheriff yace” me gida naga 21k ne ka bayar?ya tambaya yana d’ari d’ari”sbd haka nan yaji tsoronsa, musammun daya saka face mask”yarinyar kawai sheriff yanuna masa da hannu beyi mgn ba “hakan yasa yaron ya fahimci harda nata yabiya”saidai kuma sheriff yafara tunanin Anya yarinyar nan qlau take?tunda ta shigo motar ko tari beji tayiba”sai uban hawaye datakeyi”can kuma yad’age kafad’a Alamar ko Ajikinsa….lumshe idanuwansa yayi yana cigaba da sauraron karatun Alkur’ani me girma”yayinda ita kuma taketa zare Ido tanata y’an kalle kalle”har magrib tayi musu Ahanya “duk wanda ke cikin motar yayi mamakin irin miskilancin sheriff da yarinyar”dan tunda suka shiga motar zaman awa 4 cif basuyi mgn ba ,ko waya shi be Amsa ba….. Anata kiran sallar isha’i suka shigo cikin garin Kaduna”kai tsaye tasha suka yada zango”ita dai tana zaune tanata ganin mutane suna ta fitowa”saidai batada Alamar fitowa kallo d’aya zaka mata ka fahimci Atsorace take”Fahad Shariff kuwa bebi takan taba yafice Abinsa ,ya kira sarkin tasha kan yasaka afito masa da motarsa” da yazo nan da ita d’azun ya bari da nufin idan ya dawo dama yazo ya d’auka yatafi gida”bayan yabgama wayar dashi yakira Ammi yasanar mata ya sauka lafiya yanama hanyar dawowa gida”yana kok’arin kashe wayar wani ya iso gefensa cikin motar yayi parking”bayan ya fito ya gaishesa yabashi key d’in motar ya tafi”lokacin karfe 8:33 pm”kamar Ance sheriff yajuya bayansa ya hango yarinya rakub’e gefen wasu motaci tanata zare Ido,wasu maza irin k’attin tashar nan suna nunata da yatsa suna mgn”tsintar kansa kawai yayi da nufar wajen yarinyar”tun daga nesa ya hango tanata zare Ido”yana ji guda na cewa”da alama k’ilan batada wajen zuwa kaga tsuntsu daga sama gashashshe”da Ank’ara jumawa mu janyeta can baya kawai”wani irin mugun kallo sheriff ke jifarsu dashi”yana mamakin mugun hali irin nasu”dukda basu san ko waye shiba,kuma basuga fuskarsaba Amma ransu yabasu yaji kalamansu tunda yatsaya yana kallon su”hakan yasa suka gudu”yaja doguwar tsuka yana nufar inda take batare daya san mezai furta mata ba idan ya iso gabanta”ita kuwa jin motsin takunsa yasaka Atsorace ta d’ago kanta”Atake ta ganeshi sbd Akwai haske wajen”shi kuwa glass d’in yacire yatsaya d’an nesa da ita yana kallon ta da nazarinta”kasancewarsa yanada saurin fahimtar d’an Adam kodan sbd yanayin Aikinsa “abubuwa 3 ya fahimta Atare da yarinyar”na farko batada cikakkiyar nutsuwa,na biyu Atsorace take,na ukku bbu Alamar rashin gaskiya Atare da ita “yakai kusan mintina 5 tsaye shida ita bbu wanda yayi mgn”yama lura kamar tsoronsa takeji”daurewa yayi cikin had’ad’d’iyar muryansa me furgita dubban y’an mata yace”tsayuwar me kikeyi Anan ,Akuma irin wannan lokacin??batayi mgn ba saidai kanta data d’ago tana kallan bakinsa”ganin yayi shiru yasaka ta fashe da kuka”tsaki yaja sbd gudun karma ta tara masa mutane Amasa wata fassara”ke! dallah yima mutane shiru kibani Amsa kona tattakaki….nima bansan inda zanje ba”kuma yunwa da fitsari nakeji! ta furta cikin wata iriyar siririyar murya me taushi da zak’i”sosai yake nazarin kalamanta “saidai yama kasa furta mata komai”Aganinsa gara kawai ya k’yaleta karyaje yayi Abinda zaiyi dana sani”be iya furta mata komai ba yabjuya cikin nutsuwa had’e da kasaita yanufi wajen motarsa”saidai yana shiga ya ganta ta cikin glass tanata kok’arin bude back sit yak’i bud’ewa…..biyoni yarinyar nan tayi?ya tambayi kansa yana jin wani zargi na d’arsuwa Aransa “sai kuma ya girgiza kansa”ya koma kallonta Akaro na biyu yaga tanata kuka tana so ta bud’e ta shigo”yaja tsaki yabude k’ofar ya fito”yana k’ara godiya ga Allah da baizo da driver ko body quard nasa ba”sbd shi mutum ne me son sirri! bece mata komai ba yadai tsintsi kansa da bud’e mata front sit yamata Alamar ta shiga da hannu batayi musu ba ta shiga ta zauna”ya zagaya ya shiga ya zauna”duka glass d’in motar ya rufe ya kunnah AC “kasancewar motar me tinted ce ba’a ganin na ciki”yana driving d’in yana Jan tsaki had’e da tunanin yaya zaiyi da yarinyar nan?”yasan dai ko giyar wake yasha bazai kaita gidan Ammi ba”kawai saiya kira mus’ab”bugu biyu ya d’auka da sallama yana fad’in Abokinah da Alama ka dawo ko?”uhmm! shine Abinda sheriff ya iya furtawa kenan”daga d’ayan bangaren mus’ab yace”Akwai wani abu da alama dan nasan bazaka kirani bbu wani dalili ba?kana Ina yanzun?”Ina gidana mana”okay kasameni get house d’ina yanzun pls karkayi delay”okay kawai yafad’a,shi kuma ya yanke wayar yana Jan tsaki yazare face mask d’in fuskarsa”ita kuwa kuka takeyi saidai ganin kyakykyawar fuskarsa ta bayyanah saita dena ta tsaresa da Ido tanata kallonsa”shi kuwa besan tanayiba driving d’in kawai yakeyi ga gajiya daya kwaso”can ya kalleta suka had’a Ido “lafiya malama zaki tasani gaba kina kallo nah?”yafad’a yana sakar mata harara “ta d’auke kanta batayi mgn ba”shi kuma yaja tsaki yana danna horn”get man yabud’e masa k’ofa ya shigo da motar ciki”saidai beyi parking Anan ba,sai yawuce can wajen k’ofar shiga main parlour sannan yayi parking yafito”ya bude mata k’ofar ta fito ya maida ya rufe beyi mgn ba yabude k’ofar parlour suka shiga Atare da ita”gaba d’aya zuciyarsa atsaye take dan yama fidda ran ko wani yaturo masa ita sbd acutar dashi”ko zama be bari sunyiba ya nuna mata k’ofar toilet beyi mgn ba “ita kuma bata fahimci me yake nufi ba tana dai tsaye”dallah ki shiga ga toilet can kiyi fitsarin dakika fad’a “yak’are maganar yana zama kan d’aya daga cikin kujerun da suka k’awata parlourn”yana sauke Ajiyar zuciya da tunanin yaje ya sauke sallar magrib da isha’i dake kansa”saidai yana lura da ita ta cire takalminta” yana jin kuma bazai iya mata mgn ba yagaji da surutu”dan gani yakeyi yayi surutu me matuk’ar yawa yau”ita kuwa bbu takalmi ta shiga toilet d’in”tsaye kawai tayi sororo tana k’arema cikin toilet d’in kallo”kamar me tuna wani abu ta nufi wajen famfo ta kunnah sai ruwa yafara zuba”tayi shiru ta duk’a tayi buk’atarta”bayan ta gama ta mik’e tsaye ta wanke k’afafuwanta batare data kama ruwa ba”shi kansa fanfon kasa rufewa tayi”tafi mintina 10 Aciki sannan tasamu ya rufe wajen wasa dashi”sai sannan ta fito ta sami sheriff na sallah”ta zauna k’asa kan carpet tanata kallonsa tayi tagumi da alama tunani takeyi “Ahaka mus’ab yaturo k’ofar ya shigo…..dam! k’irjinsa yabuga sallamar dake cikin bakinsa ta mak’ale”yana mamakin meya had’a Abokinsa da wata mace agidansa shi kad’ai cikin wannan lokacin?”sai kuma yatuna tunda yakirashi kan yazo yasamesa kilan taimakon ta zasuyi game da Aikinsu”hakan yasa hankalinsa yad’an kwanta sbd yasan waye sheriff”sallama yamata saidai amamakinsa bata Amsaba sai kallonsa takeyi da Alamar tsoro Asaman fuskarta”saidai Aransa tasbihi yakeyi dan yatsorata da kyawun halittar yarinyar…..K! bakiji Ana sallama ne?”cewar sheriff cikin tsawa bayan ya sallame sallar tasa”Babu damuwa Abokinah idan ka lura yarinya ce”ita dai bata yadda ta kallesaba tayi k’asa da kanta jikinta har rawa yakeyi”sheriff yamik’e tsaye yanata faman cin magani da k’yar ya furta muje daga waje muyi mgn….tana ganin yanufi k’ofa itama ta mik’e tsaye ta d’auki mayafinta zata bishi”wata rikitacciyar tsawa yadako mata”Babu shiri aguje ta fad’a saman kujera ta fashe da kuka tana shure shuren k’afafuwa”duk yadda mus’ab yaso yab’oye dariyarsa saida ya murmusa”uban gayyar kuwa doguwar tsuka yaja yafita yana dana sanin jajibo ma kansa yarinyar dayayi”ya fahimci kamarma mura zata kamata sbd sanyin da akeyi da iskan mota data shak’a”kan resting chairs dake bakin k’ofar shiga parlourn suka zauna”sai jan tsuka sheriff keyi kamar zai Huda harshensa”b’acin rai goma da ishirin sun masa sallama”musammun idan yatuna lokacinsa daya b’ata kan yarinyar nan…..yaka mata kayi hakuri kasanar mun meye had’inka da yarinyar nan?”sannan hakuri zakayi ka rage yimata tsawa na fahimci yarinya ce sosai”Agogon dake daure a damtsan hannunsa yaduba kafin cikin mintina 2 zuwa ukku yayiwa mus’ab bayanin had’uwarsu da ita har zuwa biyonsa datayi”daga k’arshe yace”pls mus’ab meye mafitah yanzun?”wlh na gundura da ita kuma haushi take bani”bana son kowa yasan inada wata alaka da ita shiyasa ko get man ban bari ya gantaba”yak’are maganar agundure yana kallon fuskar wayarsa da Ammi ke kira…..shiru kawai mus’ab yayi yana tunani”can ya sauke Ajiyar zuciya yana fad’in “tabbas shigowar wannan yarinyar rayuwarka yanada Alak’a da kataimaka mata”haba Abokinah! Ina tausayin nan naka yake dason bima mutum hakkinsu?karka manta sbd irin wa’annan halayen naka ka zab’i ka karanci criminology! tabbas inda yarinyar nan baka taho da itaba da tuni wa’annan b’ata garin sun gama lalata rayuwarta”karka manta duk wanda yayi dan Allah bazai tab’a tozartaba duniya da lahira”yanayin dana ganta dukda bawai nata kallonta bane na fahimci bata hayyacinta ,sannan bbu Alamar da za’a iya had’a baki da ita Acutar da wani Atare da ita”pls sheriff ka taimaketa nima insha Allah zan baka goyon baya…..shiru kawai yayi bece komai ba saidai da Alama kalaman mus’ab sunyi tasiri Azuciyarsa”da k’yar ya iya fad’in Ina zan kaita ta kwana kuma tace yunwa takeji??”wajen kwana bazai zama matsala ba”zamuje gidan mlm na ta’ala kasan Abokin yaya Ahmed ne”kuma mahaifiyarsa baba ladi tayima Hjy Aiki yanzun tadena”zamuje muyi musu bayani saita kwana acan zuwa safe zamuyi mgn da mlm d’in ko Akwai wani taimako dazai mana”kuma zamu iya saka Dr Mansoor yadubata koda tanada wata matsala….matsalar da bana so kenan zai faru”kasan Atsarina bana son kowa yasan wani abu game dani”na sani kuma insha Allah bbu wanda zai sani”saidai idan ko baba ladi da mlm d’in zasu fidda maganar nasan kuma basuda matsala”Ayanzun adubata da lafiyarta shine Abinda yaka mata kayi kafin ka maida ita wajen iyayenta ko danginta”sheriff beyi mgn yayi shiru yana tunani”can ya mik’e tsaye yana fad’in bara na kirata mu tafi daga can zan wuce gidan Ammi”dato mus’ab ya Amsa shi kuma anutse yakoma cikin parlourn fuskarsa Ad’aure”tana kwance inda yabarta tanata kuka idanuwanta sunyi jajir sun kumbura”tana ganinsa Atsorace taja da baya ta kama Ido ta rufe jikinta na kirma”yatab’e baki yayi tsaye gefen datake zaune”cikin tattausan muryansa yace”K! k’in mgn tayi”yatab’e baki yana fad’in zaki tashi mu tafi ko saina mareki?zaki wani kama Ido ki rufe sbd gulma”ko gajiya da kuka ke bakyayi ne? duk yana maganar ne cikin tsawa”ita kuma tana yadda take bata bud’e idon ba”matsowa yayi gefenta”bbu tausayi yasaka yatsunsa biyu ya d’alli dogon hancinta daga sama…..Babu shiri ta bud’e idanuwanta da sukayi jajir ta watsa Asaman kyakykyawar fuskarsa “ya gallah mata harara”yana mata Alamar ta tashi da hannu”shi kuma yaja tsaki yanufi k’ofa”sai rawar sanyi takeyi haka ta d’auki mayafinta ta fito”suna tsaye yanata masifar shifa gaskiya ya gaji bakinsa har yafara ciwo sbd mgn “mus’ab nata bashi baki “yadako mata tsawa yana bud’e back sit”tazo ta shiga”shi ya zauna gefen me zaman banza”mus’ab ya Amshi driving d’in lokacin karfe 9:25 pm”directly tudun wada suka nufa”wanda Ahanya da k’yar sheriff ya bari mus’ab yamata take away”Anan cikin motar yabata taci ta k’oshi”bbu Abinda ta rage har ruwan da lemon dukta shanye”mus’ab na lura da ita”Aransa yace kotun yaushe rabonta da Abinci?”yayinda Shariff tunda suka d’auki hanyar gidan baba ladi A zuciyarsa yake sak’a da warwara”koda suka iso k’ofar gidan mus’ab ne yafara fita sbd yayima mlm bayani shida mahaifiyar tasa”sannan daga baya su shigo tare da ita”kamar yana jiran mus’ab d’in yafita yafara zuba mata fad’a gun cewa”idan ya dawo zamu shiga ciki kika sake kikamun sakarci ,ko zan tafi ki biyoni saina tattakaki”kuma acan zaki kwana “zancen kuka kije kiyita yi”saiya numfasa yaja gajeran tsaki”ita dai batama fahimtarsa saidai tasan fad’a ne yake mata”kuma batayi kukan ba”shi kuwa sai tsaki yaketa ja sbd ganin mus’ab d’in shiru”can kuma yadawo”hakan yasa yafito”ita kuma tana ciki”yadafe kai yana fad’in mus’ab pls zan bar maka komai kan yarinyar nan bazan iyaba gaskiya “me kuma yafaru?”yanzun saina ce ta fito ne?”mus’ab beyi mgn ba ya matsa ya bude k’ofar motar hakan yasa ta fito”ya nuna mata k’ofar gidan yana fad’in muje”da sallama suka shigo matsakaicin gidan name k’aramin k’arfi”da tausayi sheriff ke kallon gidan”mlm na zaune kan buzu baba ladi na kan tabarma tana jin redio”kan tabarmar da aka shimfid’a musu suka zauna”yayinda ita take tsaye”gashi besan sunan taba”mus’ab ne yace” zauna mana k’anwata”k’in zama tayi tanata b’ata fuska hawaye sun ciko mata a Ido”sheriff ya hasketa da flash light d’in wayarsa”kamar tana jira tasaka kuka”tsabar takaici kasa mgn yyi yana jin dasun bar gidan zaicire hannunsa kan lamarin yarinyar “shi kansa yanzun yana bukatar ya hutu yaci Abinci Amma dalilinta hakan be samu ba….mlm na kok’arin yimata mgn baba ladi ta fad’i k’asa tana wani irin Shure Alamar iska yahau jikinta”subahanallahi! Mlm da mus’ab suka fad’a Atare”yayinda baba ladi ta bud’e baki cikin wata iriyar murya tana fad’in…..✍️
wannan book d’in na kudine
Regular grp 300
Vip grp 1000
Special group 2k wato 3pages in a day
zaku biya kud’in ku ta wannan acc number2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what’s app number d’ina 08100084251
300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d’in ta acc ne
banason transfer d’in Kati ko vtu photo d’in katin MTN zaki d’auka saiki turo dan Allah banda kira❌
Y’an nijar kutuntub’i wannan n +227 88 01 90 50
Normal grp 500f
Vip grp 1000f
Special people 2000f
dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan Baki shiryaba
https://chat.whatsapp.com/JHvLho4664m0KcDHi1EDmF
1) *Invitation card, video invitation card*
2) *Book cover 3d mackup, normal book cover 3 colors*
3) *Data flyer, Account number sticker*
4) *3d mackup logo, normal logo*
5) *Ideogram ai logo*
6) *How to remove background*
7) *How to download icons*
8) *Yanda zaki haɗa document na littafi,da kuma yanda zaki cire password idan aƙwai a jikin littafi*
9) *Zan bada application guda 3 waɗanda ba’a samun su a play store*
*Kuɗin da zaki shiga Class ɗin da zaki samu wannan garaɓasa ₦300 idan kin shirya ki turo kuɗin ki ta 1632036584 Saadatu Balarabe Access Bank ki turo shaida ta wannan number 07032895551 ko katin MTN*