Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 25

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 25…. Washegari da asuba Mami ta gama shirya Ikram cikin kayan makarantarta, ba karamin kyau Ikram tayi ba cikin dark nd light pink uniform dinta, na cikin light, pinafo din dark, sae ddi take ji ta kasa barin gaban madubi bayan Mami ta gama parkin din mata dogon gashinta da ribbon, tana tsaye gaban mirror har lkcn Mami ta shigo dakin rike da breakfst dinta bayan ta ajiye na Khaleel a dinnin, Mami tace “maxa ki cinye kafin in fito Ikram” kai kawae Ikram ta gyada mata ta xauna gaban break din, Mami ta shiga wanka. Ikram ta mike ta bude kofar a hankali ta fice tayi dakin Khaleel, tsaye ta gansa yana knot din tie dinsa ta washe hakora tace “yaya Khaleel nayi kyau” grin din hakoransa yyi yana mata mugun kallo cikin tsawa yace “get out kar in taka ki, ni kike tambaya kin yi kyau” Ikram ta murguda masa baki tace “shi yasa bana sonka, kuma ko kyau ma baka yi ba, wnn abokin nawa ya fi ka kyau” kanta ya yo ta fice a guje tayi dakin Mami tana kwala mata kira, yyi kwafa ya koma dakinsa, dariya ta dinga yi kmr wata tababbiya bayan ta shigo dakin, tayi mai isarta snn ta fara shan tean ta, ko da Mami ta fito ta gama, Mami ta hade rae tace “me ya fitar da ke? Baki ji ko Ikram” ikram ta dan turo baki bata ce komai ba, Mami tace “dauki kofin nn da plate ki kai kitchen” ba musu ta dauka ta nufi kitchen da su, Khaleel na xaune kan dinnin, ta hararesa ta koma sama da sauri, karfe bakwae da minti goma suka sauko da Mami tana goye da jakar makarantarta, Mami na kallon Khaleel dake xaune dinnin har lkcn tace “ka ba Mai gadi makulli, jummae ta kira ni tana hanya” bae ce mata komae ba har ta isa bakin kofa snn yace “Allah ya kiyaye,” tace Ameen snn suka fita, gaban mota ta bude ma Ikram snn ta xaga ta shiga driver seat ta tada motar tayi warm dinsa suka bar gidan, har cikin makaranta ta shiga da Ikram ta hada ta da dari biyar kudin break nn da nn Ikram ta hade rae xata yi kuka wae ita baxata xauna ba, Mami tace “anjima kadan xan xo in dauke ki dota,” a hka ta samu suka rabu ta kama hanyar office. Ammi na xaune tsakar gida ta rafka uban tagumi sae kallon Abba da yasa ta gaba sae masifa yake mata, wae suje su sa a saki yayansa da matarsa da suka daure da ita da yayarta, sae da Ammi ta bari ya gama snn ta mike tsaye tana masa mugun kallo tace “su fara fito min da ya ta tukun, ae ko rance xanyi sae nayi naga karshen wa ennan mutanen wllh” a fusace Abba yace “kina da hnkli kuwa Aisha yayana ne fa” Ammi tace “na fi ka sanin wnn” tana fadin hka ta shige daki hawaye cike idonta don ba karamin kewar Ikram dinta take ba ko wani hali take ciki ynxu oho, su Na lado kuwa ana can station ana shan axaba, gashi bae karbi nmbr Mami ba kuma bae san gidanta ba da tuni ya fdi inda ikram take da wnn axaban da yake ci hannun yan sanda. Karfe hudu da minti goma sch bus ya ajiye Ikram a kofar gidan Mami, rana daya a sch duk ta rame ta ci kuka har ta gaji kmr warce bata taba xama a sch ba, ko dayake can gida karfe daya suke tashi daga sch, sae da teacher ta tabbatar Ikram ta shiga gida snn motar tayi gaba, Ikram ta karasa bakin kofar shiga gidan da gudu tana kwala ma Anty kira cikin kuka, Jummai ce ta fito tace “sannu da xuwa yarinya” Ikram ta shige gidan ba tare da ta kalleta ba ta haura sama da gudu sae dakin Mami amma taga ba kowa, saukowa tayi tana kuka tana kallon jummai tace “ina Anty” Jummai tace “tana nn xuwa yarinya xo kiyi wanka kici abinci kafin ta dawo” Ikram ta fasa ihu tana tsalle tana kiran Anty, da kyar da kyar jummai ta lallabata ta cire uniform tayi wanka snn ta bata abinci ta ci, tana ci kuwa tayi bacci nan kan kujera a falon, karfe biyar Aliyu ya shigo gidan sanye da kananan kaya, suka gaisa da jummai dake faman girki a kitchen snn yyi gun Ikram, a hankali ya durkusa gabanta yana kallon fuskarta, hannu yasa ya shafi fuskar ya kira sunanta murya can kasa ta bude idon da sauri, mikewa tayi ta xauna tana mitsike ido tace “ni kaina ciwo yake min” ya kamo hannunta yace “da gske, Ikram ta gyada masa kai” yace “kinci abinci?” ta gyada masa kai nn ma ya mike da sauri ya haura sama ya shiga dakin Mami sae gashi ya sauko da magani ya dauko mata ruwa a kitchen, ba musu ta karba ta sha tana yamutse fuska, yace “ya sch Ikram” ta bata fuska tace “ni baxan sake xuwa ba wllh bna son makarantar” shiru yyi yana kallonta, shigowar mota da yaji yasa ya mike da sauri ya leka yaga motar Khaleel ne, ya dawo ya xauna yana kallonta yace “sbda me Ikram” kmr xata yi kuka tace “malamar muguwa ce wllh” dariya Aliyu yyi yana kallonta, Khaleel ya shigo gidan ba tare da ya kallesu ba ya haura sama, Aliyu ya mike ya dagota yace “xo muje in gaya maki abu” ba musu ta mike da dan gown dinta iya gwiwa, Jummai ta fito da sauri tace “Dr Mami tace kar in bar kowa ya fita da ita wllh” yana murmushi yace “ae ba nisa xa muyi ba kuma Mami sae takwas xaki ganta ta tafi meetn,” da dan damuwa tace “to ni dae ka rufa min asiri snn ka bari in canja mata kaya” yace “karki damu” bae kuma jiran me xata ce ba yaja hannun Ikram suka fita daga falon.
[2/25, 08:28] Zjy: ~

Back to top button