Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 34

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na talatin da huɗu_

_____________

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

___________

…….“Taɓa kiji yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri. Na kuma fara fuskantar wannan yanayin ne tun a rannar dinner ɗin nan dana fara tozali dake. Ni na tabbata zaki iya juyani fiye da yanda kike zato saboda ƙaunarki Khadijah, abinda kawai na tsana shine cin amana, wulaƙantamin mahaifiya da ƴar uwa, duk a yanda nake jin ƙaunar nan taki bazan iya amince miki hakan garesu ba. Domin su ɗin rayuwata ne, fatana ke da su ku dunƙule ku zame min abu ɗaya dan ALLAH Khadijah. In sha ALLAHU zakuyi alfahari da ni, sannan zaku sameni fiye da yanda kuke zato da tsammani ku duka dan na kasance rawani a tsakanin kalluba ne gareku.”
A hankali hawayen da Khadijah ke riƙewa suka silalo, murmushi ta saki mai sanyi da raunana zuciya. Hannunta dake cikin nasa ta juya, sai nasan ya koma cikin nata. Kaɗan ta matsashi hakan ya sashi kallonta, ganin hawaye ya sakashi tashi daga kafaɗarta da sauri, hannu ya kai kan fuskarta amma sai ta kauce ma hakan, sai kawai ta sake saki kuka ta faɗa jikinsa. Baida zaɓin da ya wuce ƙanƙameta da ƙyau, ya wani lumshe idanunsa sautin kukan na ratsa masa zuciya. Kusan mintuna biyu ta ɗauka a hakan, jin bata da niyyar dainawa ya ɗagota daga jikinsa gaba ɗayanta, ƙoƙarin son kallonta yake amma taƙi yarda, sai da ya kamo fuskarta cikin tafin hannunsa duka biyu biyu. Yanda ya zubama fuskar tata ido ya sata rumtse idanun da sauri wasu hawayen na sake silalowa. Sake lumshe nasa idanun yayi yana jan numfashi da fesa mata akan fuskar, sai kuma ya matsar da tasa fuskar a hankali ya saukar da lips ɗinsa masu ɗumi kan nata da hawaye ya jiƙa sukai sanyi da santsi ga taushi. Ƙanƙame jikinta tai da farko gabanta na faɗuwa, sai dai yanda yake aika mata salon sumbatar yasa cikin ƙanƙanin lokaci ya birkita mata dukkan lissafi batare data farga ba ta fara maida murtani itama. Sake rikicewa Abaan yayi, dan baima san shi ɗin yana cikin kewa da buƙatar abokiyar halittar tasaba sai a yanzu. Tuni salon ya sauya da wani irin zazzafan yanayi mai ɗunbin tarihin da su kansu sun san bazasu taɓa iya mantawa ba har gaban abadan, dan wannan rana ta kasance musu ta daban a cikin daban a rayuwarsu. Dan ta kasance musu a mafi daraja da girman dare da kowaɗanne ma’aurata kan ƙalla kuma su rubuta su ajiye a kundin sirrinsu mafi zama ƙololuwar sirri da babu wani mahaluki dakan iya bincikowa, dan koda ace da bakinsu suka faɗeshi ga wani sai dai su kamanta badai lissafinsa dalla-dalla ba dan wannan wani al’amari ne mai girma daga ƙyautar UBANGIJIN al’arashi mai rahama da jin ƙan bayi…

_________★

Jikin doctor Giɗaɗo ƙalau ya sauke wayar daga kunnesa. Yayinda matuƙar mamaki ke ratsashi jin yanda Alhaji Abaan ɗin ya amsa masa batun albishir da yay masa kan batun cikin kainaat. Ba haka yay zato ba sam, tabbas bai yi tsammanin samun hakan ba. Dan a zatonsa idan ya sanar masa Abaan ɗin zai kasance cikin ɗunbin farin ciki tamkar ya fasa wayar dan daɗi, dan shi shaidane irin wahalar da suka dingayi da matar tasa akan neman irin wannan damar. Amma sai gashi yanzu yaji sabanin hakan. (ayyah) kalamarfa da Abaan ɗin ya amsa kawai kenan da ita lokacin daya sanar masa da maganar ciki a jikin Kainaat na kwakin da basu wuce sati ɗaya ba ma, daga ƙarshe kuma yace masa yanada uziri sai kawai ya yanke kiran. Shigowar Nadwa ya sashi jan ajiyar zuciya ya fesar, sai kuma yaji wani daɗin ganin nata dan koba komai zata fiddashi a duhun da yake ciki yanzu..
Sun gaisa da girmamawa, batare da ya jira jin miya kawota ba ya jeho mata tambaya. “Hajiya Nadwa nikam ko zan sami wata number ɗin Alhaji Abaan a hannunki, dan inata kiransa nai masa albishir amma yaƙi ya ɗagamin, kin san manyan nan da uzirori”.
Ɗan jimm tai, sai kuma can ta ce, “Wani abu ya faru ne kake neman number ɗin sa?”.
“A’a babu abinda ya faru sai alkairi, kawai ina son masa albishir ne game da rashin lafiyar Hajiya Kainaat”.
Da sauri cikin waro idanu ta ce, “Albishir ɗin mi?”.
“A ke kam na faɗa miki kuma na ragema kaina lissafi, ai nai alƙawarin sai mijinta ya fara sani kafin kowa”.
Kallonsa ta tsaya yi kamar bazatace komai ba sai kuma ta ja numfashi, cike da kissa ta ce, “Kasani ko idan ka faɗamin ɗin na zama silar da za’a ninka maka goron albishir ɗin naka. Common faɗa min mike faruwa in har kana son number”.
Yasan halinta, tunda tace hakan saifa ya faɗa, ƙasa ya sake yi da murya ya ce, “Dan ALLAH amana fa, dan nafi son ya sani ta bakina kafin kowa”.
“Baka da matsala ina dai wannan ne”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya matso da fuskarsa a cikin raɗa ya ce, “Na gano tana ɗauke da cikin kwanaki takwas ne”.
Sosai Nadwa ta waro idanu waje har tana ƴar zabura ta furta, “Ciki kuma doctor?”.
Da sauri yay mata alamar ta rage murya, sannan ya amsa mata da, “Tabbas kuwa ko tantama babu ciki, Kinga kuwa ai wannan albishir ni ya kamata na fara sanarma Alhaji Abaan”.
“Ai ba nashi bane. Domin kuwa kusan shekara ɗaya da wata biyu kenan da rabuwarsu. Wannan yaron da kaga ya kawota shine mai cikin dan shi ta aura. Idan kace zaka kira ABAAN maimakon goron albishir ɗan karen bugu zakaci ma. Sannan idan ka sanar da Kainaat ko mijinta batun wannan cikin ma komai zai iya faruwa. Dan haka inada da bara, idan ka bani haɗin kai ni da kai duk sai muci arziƙi mu bar arziƙi a inda yake, kadai san ni ai bana kawo maka aikin banza”.
“Tabbas hakane Hajiya Nadwa yanzu yaya kike son ayi?”.
Wani shegen murmushi ta saki da kashe mar ido ɗaya, sai kuma ta miƙe tana ɗan duƙawa saman decks ɗin ta yanda har yana iya ganin jikinta. Yawu ya haɗiye da ƙyar yana sake ware ido shi yaga banza. Cikin kunne ta gwargwaɗa masa maganar da nima banji ba, a take suka saki ƴar dariya, ta bashi hannu alamar su tafa, cikin rawar jiki ya miƙa mata nashi shima yana wani karkatar dakai da leƙata. Yi tai kamar bata fahimci ina ya dosa ba suka tafa ta koma ta zauna a mazauninta….

“Doctor har yanzu baka sanar min mike damun matata ba, ko result ɗin bai fita bane?”.
Kai doctor Giɗaɗo ya jinjina yana yana jawo wani file a gefensa. Sai kuma ya kalli Dafeeq yana ɗan murmushi. “Afuwan abokina, result ɗin matarka ya fito, sai dai muna jiran na ƙarshe ne shiyyasa bance da kai komai ba. Amma tunda ka damu bari na baka wannan ɗin. Alhmdllh ba wani abu ke damunta ba sai infection, yayi tsanani ne sosai da har yake sakata ciwon mara, sai dai kada ku damu yanzu haka mun fara treatment ɗinta kuma komai zai zama normal”.
Wani shegen kallo Dafeeq ke masa, dan abinda Doctor bai sani ba duk tattaunawar da sukai da Nadwa yaji ta, abinda kawai bai ji ba maganar datai masa a kunne, itama kuma ya gama tsara hanyar da zai san ko minene. Da yake makirine bai nunaba ko a fuska, sai ma damuwarsa daya nuna sosai akan ciwon Kainaat ɗin. Babu musu kuma ya amshi takardar magunguna yaje ya saya. Ɗakin da Kainaat ɗin take ya koma, ya samu Nadwa na bata shayi, zama yay a kusa da ita cike da kulawa yana jera mata sannu, ƙasan ransa kuwa ji yake kamar ya shaƙe banza dan ba abinda zancen cikin nan ya ƙara masa a zuciya face ƙara jin tsanarta. Da gaske shifa bai shirya haihuwa ba yanzu, koma zai haihu bada wannan tsohuwar guzumar ba mai bakin iyaye aka. Da Khadijah kawai zai iya yarda ya haihu, dan itace kawai ta dace da hakan.
Kulawa sosai da hidima yake mata har abin na bama Kainaat mamaki, harma tana tunanin akwai abinda yake shiryawa a ransa amma ta gagara gane komai. Kwanansu biyu aka sallamesu. A ranar kuma Nadwa ta sanar mata tana da ciki. Shiru Kainaat tai tana kallonta kamar wata wawuya, sai da Nadwa ta zungureta tana murmushi. “K wai lafiya naga kin saki baki. Murna fa ya kamata muyi, dan ni tun a asibiti da doctor ya gaya min na gama shirya planing ɗin komai wlhy. Wannan cikin ai alkairi ne garemu baki ɗaya, ga shi kwata-kwata sati ɗaya ne da wasu kwanaki, kin san dai doctor Giɗaɗo kamar maye yake wajen gano ciki komai ƙanƙantarsa…..”
“Yaron nan Dafeeq yasan da batun cikin?”. Kainaat ta jeho mata tambayar cikin katse ta. Kai Nadwa ta girgiza mata, “No bai sani ba, dan na hana doctor sanar masa. K hasalima ni kaɗaice na sani sai ke yanzu dana sanar miki”.
“Alhamdullah yau zan koma asibiti a zubar da shi”.
“Zubarwa fa?”.
Nadwa ta tambaya cikin zare idanu, a zafafe Kainaat ta bata amsa da “Yes zubarwa, dan bana buƙatarsa. Abaan kawai nake fatan haifama ƴaƴa. Bandama rashin adalcin wannan cikin bai shiga a inda nafi buƙatarsa ba sai a gidan ƙazamin shashashan yaron nan. Ai ni abinma kunyane gareni ace inada cikin wannan ɗan tayin yaron wlhy. Dukiyata duka ta dawo hannuna, lokaci yayi da zan rabu da shi na komawa Abaan ɗina….”
“Wannan shine dalilin daya sa bazan bari ki zubar da cikin ba ai Kainaat”. Nadwa ta katseta itama. Kallon Nadwan ta tsaya yi kamar ta samu tv. Kai Nadwa ta jinjina mata da faɗin, “Yes Kainaat bazaki zubar ba. Dan wannan cikin shine makamin da zai kai nasararki komawa ga Abaan kuma kici riba. Dan haka ma na hana Doctor Giɗaɗo sanarma sakaran yaron nan kinada cikin yace masa infection ne dake. Bari nayi miki kai tsaye, doctor Giɗaɗo zai kwantar mana da cikin nan na jikin ki, ke kuma zakiyi duk yanda zakiyi yaron nan ya sake ki a cikin watan nan. Zamu je wajen malamin nan da Mom, wanda yay miki aikin farko akan Abaan yazo da kansa ya maida ki. Bayan kin tare da kamar wata ɗaya sai a tada cikin, kinga zai zama matsayin na Abaan kenan, dama abinda kike fata shima yake fata hakama mahaifiyarsa kenan.”
“Woow Nadwa dama haka kike sona ban sani ba?”. Kainaat ta faɗa cikin wani irin farin ciki hawaye na zubo mata, sai kuma ta rungumo Nadwa jikinta tana sake fashewa da kuka. Ta jima a haka kafin ta ɗagota. “Amma Nadwa kin manta doctor Giɗaɗo likitan Abaan ne, hasalima ta sanadinsa na sanshi. Kina ganin bazai ci amanarmu ba”.
“Ko kaɗan bazaiyi hakan ba. Dan na shirya masa abubuwa kashi-kashi da koda wasa bazai taɓa iya cin amanarmu ba. Shine kuma kawai zai iya mana aikin Abaan ya yarda saboda da kike gani komai nasu nada ƙa’ida da tsari, idan ba likitan daya sani bane yace masa kinada ciki zargi zai iya shiga tunda nasan babu yanda za’ai batun aurenki bazai je masa ba. Dolene ma ai tunda yasan sai kinyi auren zaki halatta garesa”.
“Tabbas hakane wannan kuma gaskiya ne Nadwa, nagode sosai ALLAH yabar zuminci. Shiyyasa a kullum nake sake jin banda wani ahali a duniya sama da ke da Mom. Kumin abubuwa da yawa wanda iyayena suka gagara mun.”
“Common baby share kawai, ai ALLAH ne ya haɗa wannan ƙaunar tsakaninmu. Yanzu dai abinda zance miki mataki na gaba shine ki tattaro duka takardun kaddaririnki da kuɗaɗenki ki maidosu wajen Mom kafin ki fara yaƙin amsar sakin ki. Dan wannan yaron hatsabibine wlhy, bar ganin ya dawo miki da komai akwai abinda yake ƙullawa ne”
“Na sani wlhy Nadwa, shiyyasa na shirya ta yanda zan san minene shirin nashi. Amma shawararki tayi kam, daga nan zuwa Monday in sha ALLAHU zan kammala haɗa komai na danƙashi ga Mom, na miki alƙawarin kafin cikar sati ɗaya wannan auren ya zama tarihi”.
Dariya suka kwashe da shi harda tafawa, sai kuma duk suka gimtse bakuna suna kallon ƙofa. Kainaat ce ta fara sakin nata da faɗin, “Oh ashefa shegen baya nan ya fita. Sai kuma suka kwashe da sabuwar dariya suna tafawa.
Wani kalar cije lips Dafeeq dake ta bayan windows duk yana jinsu yayi, sai kuma ya saki wani kalar makirin murmushi da faɗin, “Ni da ku za’a banbance shegun ai. Dan zan tabbatar muku CUTA CE TA ƊAU CUTA”………✍️

*_ZAFAFAN DAI_*

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*❤‍❤‍❤‍

*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K’ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button