Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 88

Sponsored Links

88…..
Karfe bakwae Khaleel ya shigo dakin har lkcn
Ikram na baccin da bata yi jiya ba, ya xauna kan
gadon ya tsura mata ido yana kallonta, can yyi
murmushi ya kauda kansa a xuciyarsa yace
Alhmdllh na samo cure din rashin kunyar yarinyar
nn, dawowa kusa da ita yyi ya shiga tada ta, ta
farka a tsorace ya hade rae ya daura yatsunsa
biyu a lips dinsa alamar kar tayi masa kara, suna
hada ido ta sunkuyar da kanta da sauri, yace “kin
yi sllh ne” girgixa masa kai tayi ta mike ba tare
da ta kallesa ba kmr munafuka ta nufi bathroom,
ko da ta fito baya dakin, dogon hijab dinta ta sa
don yin sllh, tana idarwa ta dauki brush dinta ta
shiga bayin ta wanke baki, snn ta fito tayi maxa
ta sa kayanta tunda tayi wanka, ta koma can
karshen gado ta xauna ta rakube, da breakfst
Khaleel ya dawo dakin, ya ajiye mata nata yace
“hurry up xamu kama hanya ynxu” ba tare da ta
kallesa ba kanta a kasa kmr munafuka ta jawo
breakfst din ta shiga budewa a hankali, ya kafa
mata ido, karfe takwas da minti goma suka bar
hotel din suka kama hanyar Abuja, ba su suka isa
Abuja ba sae kusan yamma, duk Ikram ta jigata
ssae tayi amai har ta gode Allah, Mami bata nn
sae Jummai, ta shiga dakin Mami ta cire gown
din jikinta ta daura xani ta xube kan gado sae
baccin wahala. Karfe shidda kishin ruwa tare da
bude kofar da aka yi suka farkar da ita daga
baccin da take, Aliyu ta gani tsaye bakin kofa ya
kafa mata ido, suna hada ido ya juya da sauri ya
fice daga dakin, da har ta bude baki xata ce
yayana kawae ta toshe bakin da sauri sae
hawaye. tana xaune ita daya a daki tun bayan
fitan Aliyu tayi jigum duk ta rasa me ke damunta,
ssae xata baka tausayi idan ka ganta a wnn lkcn,
bude kofar da aka yi yasa ta daga idonta da sauri
Mami ta shigo dakin, Ikram ta sakko daga kan
gado tana kirkiran murmushi tace “Mami sannu
da dawowa” Mami ta karaso dakin ta ajiye
handbag din hannunta tace “Ina Khaleel” Ikram
tace “ban sani ba nima Mami, daga bacci na
tashi” Mami bata kuma cewa komai ba, ganin
Mood din Mami yasa Ikram a hankali tace “Mami
baki da lfya ne” Mami ta girgixa mata kai ba tare
da ta kalleta ba, ta ciro wayarta tayi dailn nmbrsa
ta kara a kunne sae da ya kusa katsewa snn ya
daga, Mami tace “ina neman ka Khaleel” bata jira
me xae ce ba ta katse wayar, ta juya tana kallon
Ikram kmr bata son mgna tace “kinyi sllh ne”
Ikram ta girgixa mata kai snn ta nufi bathroom
don yin alwala, Mami na xaune ta fito tayi sllh,
snn tace taje ta karba abinci gun Jummai, a
stairs suka hadu da Khaleel bata ko kallesa ba ta
sauka abunta ya nufi dakin Mami, da sallamarsa
amma can kasa ya shiga dakin, suna hada ido da
Mami ya sunkuyar da kansa ya xauna kasan tiles
yace “ina yini Mami” Mami bata amsa ba idonta a
kansa, ya daga kai yana kallonta sae kuma ya
maxa ya sunkuyar da kai ganin kallonsa take.
Mami ta mike ta nufi window a hankali ta tsaya
tana kallon waje snn ta fara mgna a nutse.
2 mins · Khaleesat Haiydar…

Back to top button