Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 8

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of experts & perfect writers)_

 

*GARIN DAƊI……!*

 

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

*Wattpad:ummishatu*

 

From the writer of

KAMAR DA WASA
KUMALLON MATA
MIJIN MATACCIYA
SO DA ALAƘA & Rest…..

*8*

 

~~~Sai da na ɗan nisa kaɗan sannan na kalli iya zuciya ta cike fal da farin ciki nace,

“iya ban tari numfashinki ba kuɗin zasu kai har naira nawa….”

Jugum naga tayi kuma ta rafka tagumi alamar tunani, zuwa can ta ɗago ta kalleni,

“ƴarnan kuɗin nan fa da yawa dan tun a lokacin malam ɗan bahago aminin mahaifinsu cewa yayi muddin wannan malamin zai yi mana aiki to sai mun bada kuɗi sama da dubu dari biyar a lokacin, tun lokacin haka yace bare yanzu da komai ya sake tsananta abubuwa duk suka sake yin tashin gwauron zabi….. ”

” hakane, amma iya a ina za asamu shi aminin baban domin a sake jin dahir ɗin inda za asamu shi mai maganin? ”

” ehh to, a gaskiya yanzu ba nace ga takamaimai wurin da za a samu ɗan bahago ba domin mafatauci ne, yawo yake yi ƙasashen duniya, wuri daban daban yake zuwa yau yana nan gobe yana can, ko lokacin da mahaifin su hashimu ya rasu da iyalinsa tazo gaisuwa cewa tayi shi ɗin yana can ƙasar Mali, sanin takamaiman inda yake sai an dangano da iyalinsa…. ”

” to iya a ina iyalin nasa suke? Ai sai aje a tambayo su inyaso sai su haɗamu dashi yayi mana bayani….. ”

” to shikenan sai inje, suna can wajen Kano daidai wannan ɗan dajin dake tsakankanin kano da Katsina…. ”

” yawwa iya sai ki daure kije”

“zan je in Allah ya yarda”

Tashi tayi taje taci gaba da ƴan aikace aikacenta domin Amira bata nan, shirun da muka yi gaba ɗayanmu nida shi na katse ta hanyar faɗin,

“wai lafiya kuwa naga kayi shiru ranka ya daɗe?”

Ɗan kawar da kansa yayi kafin ya bani amsa da,

“gaskiya maimunatu ɗawainiyar da kike yi dani tayi yawa…… Tunda muka haɗu ban taɓa yi miki wani abu na kyautatawa koda sau ɗaya ba amma ke kullum cikin yi min wahala kike, anya wannan tarayyar tamu babu ƙwara aciki?”

Tamke fuska nayi nasha kunu kamar yana kallona cikin ɓacin rai nace,

” ohhh kulawar da nake yi da kai ashe dama wahala ce ban sani ba? Ashe dama tsakaninmu akwai ƙwara ni ban sani ba? Hmm to ai gara da ka tunatar dani abin da na manta” daga haka na ɗauki handbag ɗina na zira takalmi na nayi gaba dama sai da na hanga na hango na tabbatar iya bata kusa,

A bakin ƙofa na tsaya daga waje domin nasan dole zai biyo baya na, ban kai ga gama tunanina ba kuwa sai gashi ya fito, baya na juya masa,

“Haba maimunatu menene kuma abin yin fushi daga magana? Kiyi haƙuri ban san cewa hakan zai ɓata miki rai ba”

Sai lokacin na juyo na kalleshi, ƙura masa ido nayi duk da nasan shi ba ganina yake yi ba, “baki haƙura bane? Ki sani duk punishment ɗin da kika ga yayi daidai da laifin da na aikata”

Dariya nayi na ɗan rausaya “ta yaya zan baka punishment? Ka rufa min asiri ban isa yin wannan ɗanyen aikin ba”

“waye ya faɗa miki cewa ɗanyen aiki ne? Karma ki ƙara faɗa”

“to shikenan bazan sake ba, nidai yanzu daga nan gida zan wuce, ka faɗawa iya na tafi”

“zan faɗa mata kin yi fushi shiyasa ko sallama baki yi mata ba”

“nayi fushi abaya amma yanzu na huce, kuma dama ai kaine ka saka nayi fushin”

“to ina neman afuwa”

“kin wuce wannan matsayin agareni, duk laifin da za kiyi min komai girmansa na yafe miki tun kafin kiyi”

“ka jika ko, so kake ka shagwaɓani kenan inyita cin kare na babu babbaka tunda an ce an yafe min”

“ki yi min duk abin da kike so in dai nine na yafe miki”

“nagode da wannan karamcin da karramawar, ubangiji Allah ya baka lafiya…..”

“amin mai tagwayen suna, nagode, Allah ya kai min ke gida lafiya, agaida min su mamana”

“basa cin miƙe” na faɗa daidai lokacin da muka fara tafiya zamu bar ƙofar gidansu,

“to ai ba laifina bane laifin maimunatu ne da bata rakani na gaishe su ba”

“hmmm wato har ka samo hanyar da zaka kare kanka ko”

“to ba gaskiya na faɗa ba?”

Kafin ya bani amsa Amira ta ƙaraso tare da ƙawayenta guda biyu, gaishemu suka yi sannan suka wuce suna bin mu da kallon sha’awa, kai bama su ba ku san duk wanda ya ganmu sai yaji mun burgeshi domin munyi mutuƙar dacewa da juna ta ko ina. Daƙyar muka rabu na shiga napep na tafi, ina sauka na hangi yaya Abdul hakim tsaye shida ƙawalli ko me suke cewa oho na raya hakan acikin raina, tun kafin inƙarasa yaya Abdul hakim ke faman bina da harara dama can bama shiri to bare yanzu da yake jin haushina naƙi auren yaya faisal,

Wuce su nayi zan shiga gida, muryar ƙawalli naji tana cewa “ba faɗa meya kawo gaba ƙawalli”

“au dama kune? Ai ban ganku ba” daga haka nayi ciki, murmushi tayi ta kalli yaya Abdul hakim,

“me kayiwa ƙawata da har laifinka ya shafeni?”

“wannan ƙawar taki ai bata da kunya” daga haka ya wuce masallaci ita kuma ta shigo ciki, ina rage doguwar rigar jikina ta shigo ta iskeni,

“gaskiya baki da mutunci ƙawalli, yanzu mu kike cewa wai baki ganmu ba?”

“ai yaya Abdul hakim ɗinne sai ana yi masa haka, haba mutum yabi ya takura min sai faman haushina yake ji dan kawai ban auri abokinsa ba, to ana dole ne?”

“dan Allah wannan maganar ta wuce, a fuskanci gaba kawai, dan yanzu shima maganar da yake yimin wai yaya faisal ɗinma har ya samu mata, ya ma tura gidansu”

“dama can wataƙila suna tare, kawai yaudara ce irinta maza”

“ba lallai suna tarenba, ta yuyu dai yanzu suka haɗu kuma Allah yayi abin cikin gaggawa”

“koma dai yaya ne su ya dama, nima ai na samu nawa masoyin”

“nidai yanzu kinga tafiya ta, sai an jima dan tun ɗazu na fito daga gida na zo muka sha hirarmu da su Annie har yaya Abdul hakim ya dawo, na wuce gida sai kin shigo”

“to shikenan bari nayi wanka sai in shigo”

Fita tayi nikuma na ɗauki wayata na soma duba number din farida wadda aka ɗaukemu aiki tare, ada dai sanin da nayi suna yin adashe amma ni ban taɓa yiba, jin ta ɗauka yasa nayi saurin mayar da hankali na kan sallamar da take yi min,

“yawwa farida dan Allah har yanzu kuna yin wannan adashen ne?” na buƙata bayan mun gaisa, shiru naji ta ɗanyi kafin ta bani amsa da cewa,

“ehh gaskiya mun kwana biyu ba muyi ba amma muna son mu fara daga this month, za kiyi ne? ”

“ehh ina son yi amma na nawa nawa za ayi?”

“last time dai da muka yi na 20k muka yi mu 10 Kinga 200k kenan…. Yanzu kuma da zamu daure sai muyi na 30k amma sai yadda aka tsara dai”

“yawwa farida dan Allah ayi hakan kuma ina buƙatar alfarma a bani ɗaukar farko saboda wata matsala ce ta taso min kuma inada buƙatar kuɗi wallahi cikin gaggawa”

“to shikenan zan tuntuɓesu inji, duk yadda aka tsayar da magana zaki jini, Allah ya wuce mana gaba”

“amin ya Allah nagode farida”

Daga haka muka yi sallama na ajiye wayar ina jin farin ciki yana shiga kowanne lungu da saƙo dake cikin zuciya ta domin hashim ya kusa ganin fuskata, ya kusa ya daina hasashe ko in ce laluben kamannina, madalla da ubangiji mafi tsarki fiye da komai.

Daren ranar duk na ƙarar dashi ne wurin tunani tare da ƙulla ƙullar ta yadda zan samu tsabar kuɗi kuma zunzurutunsa har sama da naira dubu ɗari biyar daga ƙarshe naga bani da wata mafita illa guda ɗaya, mafitar kuwa itace inci bashi daga bankin da nake hulɗa dasu ma’ana salary account ɗina kuma dama anan ne nake ajiyar kuɗaɗe na, kwata kwata zuciya ta bata gamsu ko ta amintu da in sanarwa wani ko in nemi shawarar wani ba koda kuwa acikin gidan mu ne domin ta yuyu a iya sace min gwiwa daga wannan kyakkyawan ƙudurin nawa wanda na san zan samu tagomashin lada har a wurin ubangiji na,

Dole ta sa nayi amanna da shawarar da zuciya ta tabani na in ciyo bashi daga banki sannan gefe ɗaya in fara zuba adashen da su farida zasu yi wato ƴan office ɗinmu,

Ban sanarwa da kowa ba washe gari kafin naje office na biya ta banki domin gudanar da buƙatata, har wurin manager aka kaini, ɗan kyakkyawa dashi matashi dan bana tunanin ma ko auren fari yayi duba da irin yadda yake wani lallaɓani yana yi min kirki dan abun bai wani ɗauki dogon lokaci ba daga ƙarshe yace wai inbashi no ɗina duk yadda ake ciki zai kirani ya sanar dani, godiya nayi masa na tafi domin har na ɗan makara akan time ɗin da na saba zuwa office, ina zuwa office na iske su farida har sun haɗu sun gama tatraunawa kan maganar adashen da za muyi kuma kowa ya amince saboda dama su sun saba yi lokaci zuwa lokaci dan har na 50k suke yi yadai danganta da halin da aka samu kai, daƙyar suka amince zasu bani ɗaukar farko saboda kusan kowa yana son ɗaukar farkon, ajiyar zuciya na sauke domin insha Allah ina sa ran na gama da wannan matsalar yanzu saura ƙiris, da yardar ubangiji sai na zamo silar murmushin hashim sai na zame masa sanyin idaniya na har abada……… ✍

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Back to top button