Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 11

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
( _Home of experts & perfect writers_)

 

*GARIN DAƊI…….!*

PAID BOOK

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

 

*11*

~~~Wuni guda cur nayi a gidan su Hashim sai zuwa yamma nayi sallama da Iya, tare muka jera dashi ya rakani wanda har sai da muka yi tafiya mai nisa muna tafe muna hirarmu, kallo ɗaya zaka yi mana ka gane masoya na waɗanda basa son rabuwa da juna, daƙyar muka rabu na hau napep don ya ƙarasa dani gida shi kuma ya juya, ni kaina saida nayi mamakin doguwar tafiyar da muka yi da Hashim a ƙafa wanda idan ni kaɗai ce nasan koda kuɗi ban isa nayi wannan tafiyar ba,

Gidan su ƙawalli na fara tsayawa na shiga bakina har kunne murna fal ciki na kuwa yi sa’a yau bata je islamiyya ba, cikin farin ciki na zauna kusa da ita ina zame ɗan gyalen dake kaina,

“Albishirinki……. Ƙawalli idon Hashim ya buɗe kuma kin san wani abu?”

“a’a ban sani ba sai kin faɗa” ta faɗa tana kallo na kamar yau ta fara ganina,

“Daga ni har shi mun yi wa juna, wallahi ada inata jin tsoro da fargaba kar ya ganni ban yi masa ba amma koda na ɗan bugi cikin sa sai naji ba haka bane nayi masa 100%”

“Allah sarki, to Allah ya bar ƙauna yasa ta ɗore…”

Kasaƙe nayi ina kallonta tare da jin haushin kalamanta musamman na ƙarshe wai wani nan Allah yasa ta ɗore,

“to me kike nufi?” na faɗa cikin gimtse fuska,

“ah kinga ni kar kiyi min fassara babu abin da nake nufi sai alkhairi…..”

“to ai naji ne kamar baki ɗauki maganar tawa serious ba”

“ni kinga duk ba wannan ba, kin san me? Nima nayi saurayi kuma insha Allah nanda ɗan wani lokaci zai fito neman aure na”

Duka na ɗaka mata cike da mamaki nace “shegiya ƙawalli dama kin yi kamu shine baki faɗa min ba sai yanzu?”

“uhmm ba haka bane ƙawalli, ada bai bayyanar min da kansa bane sai yanzu, kuma ma dai na gida ne”

“kamar ya? Ban gane na gida ba, waye?”

Bata amsa min ba ta janyo wayar ta dake ajiye kusa da ita ta buɗe sannan ta miƙo min, cike da mamaki na ɗago na kalleta bayan na gama kallon pic ɗin,

“Yaya Abdul hakim…..”

Murmushi tayi ta ɗaga min kai tana kallona,

“Wallahi ƙawalli ku munafukai ne daga ke har yaya Abdul hakim ɗin….. Tun yaushe kuka fara soyayya?”

Dariya ta fashe da ita sannan ta jingina tana kallo na,

“Mun kai 4 years muna soyayya amma babu wanda ya sani, sometimes muna tare dake zaki ji an kirani to dashi nake waya bada kowa ba, dan ke kanki shaida ce banda saurayi, shi kaɗai ne”

“amma kuna soyayya shine daga ke har shi baku taɓa nunawa ba ƙawalli? Ni kaina ban taɓa ganewa ba fa”

“iya takune kawai na yayanki”

“uhmm lallai, ai kuwa ba kiyi dacen miji mai haƙuri ba ga shegen muguntar tsiya”

Dariya ta sake yi kafin tace “ya isheki haka kibar zagar min miji”

Tashi nayi na haɗa nawa inawa na tattara na tafi tana biye dani har zuwa gidanmu, muna zuwa bakin gate yaya Abdul hakim na fitowa, basarwa yayi saboda azatonsa har lokacin ban san suna soyayya da Maryam ba, dariya kawai nayi zan wuce naji yace,

“Ke, dariyar me kike yi?”

“babu komai yaya kawai dai wani abu na tuno” daga haka na wuce na barsu shida ita tsaye, sai bayan da na jima da shiga gida sai gata ni duk tunanina ma ta koma gida ashe tana wurin mutumin.
***
BAYAN WATA TAKWAS
**
Tun bayan samun lafiyar Hashim babu wata matsala da zance munci karo da ita a soyayyar mu, mun shaƙu iya shaƙuwa dan koda yaushe muna tare sannan har yau nice ke yi musu siyayyar kayan abinci duk ƙarshen wata duk da uban tulin bashin dake kaina wanda ban gama biya ba, me zai faru? Kwatsam sai na fara ganin canji a wurin Hashim duk da babu wani abu na saɓani da ya haɗamu,

Yanzu ba sosai ma muke haɗuwa ba saboda baya zama agida kullum yana da wurin zuwa musamman yanzu da yayi friends maza da mata, kullum sune yawon zuwa birthday party, picnic da sauran bukukuwa na manyan yara, ƴanmata kuwa abun ba acewa komai saboda Hashim na da kyau irin kyawun da yake ɗaukar hankalin kowacce mace, a yawon zuwa party ɗinsu ya haɗu da wata sugar mommy hamshaƙiyar mai kuɗi wadda mijinta ya rasu ya bar mata dukiya kaca kaca, gashi bata taɓa haihuwa ba, a haife zata kai kimanin shekaru 50,tana zaune harabar hotel ɗin New Era su Hashim suka shigo yana sanye da ƙananan kaya, duk wani motsinsa akan idon hajiya Sharifa, wani daga cikin ma’aikatan hotel ɗin ta tura domin ya kira mata Hashim, bai yi musu ba yaje, kujera ta nuna masa ya zauna yana mamakin kiran da tayi masa,

“ƴan samari yakake? Ina zaune anan naga shigowarku, idan ba zaka damu ba ina son za muyi wani business da kai?”

“Business? Wanne irin business?”

“firstly we have to introduce ourselves…. Am Sharifa Mukhtar, and you?”

“Hashim Musa” ya faɗa yana kallon wani waje,

“Nice name….. Wato Hashim akwai wani business ɗina da ake kula min dashi anan cikin garin Kano amma sai na dakatar dashi saboda ana ha’intata tare da cutar dani amma kai kallon farko da nayi maka na san cewa you can make it….”

Ajiyar zuciya ya sauke har lokacin bai ce komai ba,

” if you are not ready now don’t worry yourself zuwa gobe sai muyi magana, bari na baka room no ɗina da phone no ɗina ”

Wayar hannunshi ya miƙa mata nan ta tsaya tana kallon wayar tare da jujjuya ta saboda ganin tecno p3 duk da touch screen ce, girgiza kai tayi,

” yaya classic guy like you zai rinƙa amfani da wannan wayar? No, no, this phone doesn’t deserve you, am soo surprise, bari insa a kawo maka waya latest one”

Cike da mamaki yake kallonta, fara ce sol kamar balarabiya ga kyau ga kuɗi ga hutu wannan dalilin ne yasa tsufanta baya bayyana saboda ya samu gyara gashi ba taɓa haihuwa tayi ba sannan bata da girman jiki caan, jin wayar da take yi yasa shi dakatar da tunaninsa ya maida hankali kanta yana sauraro,

“Ina hotel ɗin yanzu haka…. Wacce irin waya da wacce kuke da ita?…” ɗan jim tayi sannan yaji tace,

“No, kawo iPhone ɗin dai, classic guy ne zai yi using da ita not me and am very sure bazai so sauran kamar wannan ba tunda kusan itace yanzu latest phone and it will suit him”

Cigaba da kallonta yayi har zuwa lokacin da ta kammala wayar ta kalle shi tana murmushi,

“yi haƙuri ka ɗan jira for some minutes nasa za a kawo maka new phone ka daina using wannan wayar mai araha, haba big guy kamarka da wannan…. Beside gaka handsome”

Rasa abin da zai ce yayi domin acikin ransa cike yake da tsananin mamaki, wannan wacce irin mace ce daga haɗuwa sai kyautar waya mai shegen tsada? Sunkuyar da kansa yayi ƙasa yana ɗan nazari wanda nazarin nasa yana da alaƙa da yanayin yanda ya samu kansa a yanzu saboda tun bayan da idonsa ya samu lafiya ya buɗe ƴanmata ke rububi a kansa sunata rushing na introducing kansu a wurin sa,

“uhmmm ya kayi shiru? Ko da akwai wani problem ne?”

Girgiza kai yayi domin bai da amsar da zai bata a wannan lokaci, kawai kallon tsananin kyaun da Allah yayi mata yake, gaskiya tana cikin sahun gaba na mata masu kyau da ganin ta shuwah Arab ce dan daga nan inda yake yana iya jiyo ƙamshinta wanda ya cika masa hanci ga uban tulin gashi yalo yalo da ta tufke kamar gammo yana hangowa ta cikin mayafin da ke kanta,

“shakka babu irin waɗannan matan sune suka dace dani…. Irin matan da idan na kalle su komai girman damuwata da ɓacin ran dake tare dani zan ji ya gushe……. To amma ya zanyi da Maimunatu?” wani ɓangare na zuciyar sa ya tambaye shi,

“A gaskiya Maimunatu bata daga cikin jerin mata irin wanda nake so sannan suka dace dani….. Saboda bata da kyau na azo agani, idan har na cigaba da kasancewa da ita har ta kaimu ga aure to tamkar wata alfarma nayi mata saboda kwata kwata ba ajina bace….. ” duk waɗannan maganganun yana yin su ne cikin ransa babu wanda yaji. Zama suka cigaba da yi tana ɗan jansa da hira har zuwa lokacin da wanda zai kawo wayar ya ƙaraso, nan ta karɓa kuma a take tayi transfer ɗin kuɗin wayar wanda ke neman hauka ta Hashim dan bai taɓa tsammanin zai iya riƙe waya mai tsadar wannan ba a tarihin rayuwarsa,

“lucky is by my side” ya faɗa cikin zuciyar sa, miƙa masa wayar tayi sannan ta karɓi no ɗinshi tasa cikin wayarta, wayar hannuta yake bi da kallo wadda kusan irin tashi ce babu bambanci sai ko na colour, yatsun hannunta sunsha jan ƙunshi rangaɗaɗau sannan ga rings na gold jere a yatsunta,

“masha Allah…..” ya faɗa can ƙasan maƙoshinsa, gaba ɗaya ya rasa wacce irin godiya zai yi mata, hannu ta ɗaga masa alamar bata son godiya, sallama yayi mata ko ta kan friends ɗinsa bai bi ba waɗanda suka zo tare yayi gaba abinsa,

Tun a daren ranar suka fara chaten da Hajja Sharifa, ni sam ban san abin da ke faruwa ba na dai ganshi online amma baya amsa magana ta sai kamar after 20 minutes har daga ƙarshe na kashe data ta na kwanta domin har 11 tayi, shi kuwa Hashim hajja Sharifa ta gama kwaɗaita masa business ɗin da zasu yi inda tace gobe yazo ya same ta zata kai shi ta nuna masa boutique ɗinta wanda ta jima da rufewa amma zata dake buɗeshi kuma zata sabunta shi zata je Dubai ta kawo kaya ta zuba gaba ɗaya shagon zai zama ƙarƙashin kulawarsa sannan akwai barbing saloon aciki, ni duk ban san abin da ke faruwa ba haka nayi bacci na hankali kwance amma na tashi da niyyar tunkarar Hashim da maganar aurenmu kamar yadda ƙawalli ta bani shawara kan yakamata inyi masa magana dan mu san inda muka sa gaba ita kam already an gama maganar bikin su da yaya Abdul hakim………….✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

*_Ummi Shatu_*

Back to top button