Garin Dadi 28
©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_
*GARIN DAƊI…..!*
PAID BOOK #500
*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*
FROM THE WRITER OF
SO DA ALAƘA
MIJIN MATACCIYA
KUMALLON MATA
KAMAR DA WASA & REST…
*wattpad:ummishatu*
28
*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*
~MAI DA TSOHUWA YARINYA
~FEMALE CARE
~REODEO
~VIGOR MAX
~ LONGZIT
~B CLEAR
*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*
~~~Ji nayi tamkar in shiga cikin wayar in gano me ke faruwa dashi a daidai wannan lokaci, cikin raina kuwa addu’a nake yi,
“ya Allah ka bawa bawan nan naka lafiya….. Ya Allah ka tsawaita rayuwar sa, ya Allah ka bashi nisan kwana kada ka ɗauki rayuwarsa yanzu ko dan halin da zan shiga…. Ya baki farin ciki a lokacin da na yanke ƙauna da sake samun sa cikin rayuwa ta….. Ya mallaka min komai dan ganin na dawwama cikin farin ciki….. Ya bani lokacinsa da duk wani abu da yake da iko dashi dan kawai in yi farin ciki, ya soni a lokacin da wani ya ƙini…. Yana burin zama dani tun a lokacin da wani ya guje ni…. Ya Allah ka tausaya min kada ka sake yanke min wannan farin ciki….. ” na faɗa hawaye na sauka kan kumatu na,
” Baby…. ” naji muryarsa ta daki dodon kunnuwa na duk da a hankali yayi maganar sannan kana ji ka san baida cikakkiyar lafiya,
” Dear… Sannu ya jikin naka? ” na faɗa cikin hawayen farin ciki, ashe dai bai mutun ba yana nan a raye,
“Da sauƙi….. Amma ina fushi dake”
“kayi hakuri dear…. Menene laifi na?”
“Ba ki zo kin dubani ba”
“zan zo gobe goben nan insha Allah, dama kara nayi da alkunya amma tunda har yanzu kana kwance dole in zo…”
“A’a kiyi zamanki…. Na samu sauƙi”
“nidai duk da haka sai na zo…. Dama burina ka samu sauƙi kayi lafiya sosai”
“ba kya son ayi bikinmu ina kwance…..”
“Akan me zan so ayi biki angona yana kwance”
“Kar na kasa baki kulawa ko?”
Share hawayen fuskata na shiga yi ina murmushi ohh wannan mutum ya iya jan magana, daga faɗin abin da ke raina shikenan shine har an juya min magana,
“Kuka kika yi ko?” ya sake tambaya ta,
“A’a….”
“Ga voice ɗinki nan ya sauya…. Waye ya saki kuka? Faɗa min”
“Babu kowa…. Kawai nayi missing ɗinka ne”
“I miss you more baby….. Zaki zo goben in turo miki kudin flight?”
“uhmm uhmm nidai karka turo” na faɗa cikin shagwaɓa,
“no zan turo miki”
Sallama muka yi nan na shiga haɗa kayana cikin traveling bag duk wani abu da zan buƙata na haɗa kayana saboda dama anty nata son in je a fara gyara ni tun kwanakin baya amma naƙi sai aiko min da kayan take amma babu wanda na taɓa amfani dashi dan ƙawalli ta gama tsoratar dani wai wallahi idan na yi wa waɗannan abubuwan shan hauka Samz kashe ni zai yi gara ma in yi sama sama,
A ranar na siyi ticket online nagama komai kuma daga wannan lokacin bamu ƙara magana da shi ba sai kuɗin flight da ya turo min kamar yadda ya alƙawarta daga nan ya kashe wayarsa, ko bacci rabi da rabi nayi asubar fari na yi wanka duk da bana wankan sassafe amma ranar na asuba nayi gashi dama ina fashin salla jikina na mulke da madarar turare sannan na shirya cikin doguwar riga kamar yadda na saba dan tashin wuri zamu yi.
Ƙarfe goma daidai na sauka garin Abuja, kamar koda yaushe Anty ce tazo ta ɗaukeni zuwa gidan ta, gidan babu kowa sai mai yi mata aiki da yarinyar dake tayata renon Fawas wacce ake kira da Labiba, tun bayan sauka ta a garin hankalina ya tafi ga Samz domin ban san a wanne hali yake ciki ba, so nake kawai in ganshi inga yanda ya koma, magana nayi wa Anty nace zan tafi duboshi nan ta fara yimin faɗa wai ni na cika gaggawa da rashin ta ido idan nayi haƙuri ma ai nan da ƴan kwanaki ne za a aura min shi in zauna tare dashi a inuwa ɗaya, shiru nayi ban ƙara maganar ba har sai da ta kirani da kanta tace in fito mu tafi bayan ta kammala shirya masa abinci, ina riƙe da Fawas muka tafi me renonshi kuma tana baya,
A Wani ƙaramin asibiti muka tsaya ina biye da anty a baya har cikin asibitin, ɗakin da aka kwantar dashi muka shiga babu kowa awurinsa sai abokinshi kaɗai Ahmad wanda shima bamu sameshi ba ya ɗan fita zai je ya dawo, shi kaɗai ne kwance yana bacci, ganin bacci yake yasa anty juyawa suka koma gida suka barni ni kaɗai, ɗakin nake bi da kallo wanda dama na zaman mutum ɗaya ne saboda bashi da wani girma sai toilet aciki, gefenshi naje na zauna na ɗauko wayata ina dubawa dan rabona da hawa online tun jiya, status ɗin Hashim na buɗe kamar yadda shima yake buɗe nawa duk lokacin da na saka kawai dai magana ce bama yi amma muna ganin status ɗin juna, hotonshi na gani shida wannan farar matar Hajja Sharif a Sharifa wadda a ƙasan hoton nasu ya rubuta Hajjaju nah, murmushi nayi dan ni abin nasu ma dariya yake bani ba haushi ba, kallon gefe na nayi na kalli Samz dake kwance idsnuwanshi lumshe yana bacci araina nace “Ga inda namiji yake….”
Kashe wayar tawa nayi na zuba masa ido ina kallonsa kamar yau ne nafara ganinsa, ya ɗanyi rama kaɗan amma ba wani caan ba sai haske da yayi wanda kana gani ka san ba na daɗi bane, ina nan zaune in kalli can in kalli can naji ya riƙo hannuna, juyawa nayi na kalleshi shi ɗinma ni yake kallo yana yimin murmushi,
“Ka tashi…. Sorry”
“Baby….” ya faɗa yana murza hannuna dake cikin nashi,
“ya jikin”
“Da sauƙi….. Yasu Abba”
“Suna gaishe ka…. Tashi ka ci abinci”
Tashi nayi na zuba masa white rice & stew ɗin da anty ta dafa masa sannan na koma gefen gadon na zauna duk da naga ɗakin ɗauke yake da abubuwa na nau’in kayan ciye ciye da shaye shaye amma hakan bai sa na zubo masa abincin kaɗan ba, filet na ciko masa na zubo masa nama sosai sannan na koma kusa dashi inda yake zaune yana kallo na sanye cikin jeans da t shirt, zama nayi kusa dashi nafara bashi abincin a baki yana ci muna hira a haka har abokinshi ya shigo nan muka gaisa bayan Samz ya gabatar dani a wurin sa, sake fita yayi ya bamu wuri muka cigaba da hira, wayar shi ya kunna ya nuna min hoton gidanmu wanda ya siya mana, suman zaune nayi ina kallon gidan da irin yanda ya haɗu,
“Ni kaɗai zan zauna acan ko?” na tambayeshi cikin tsokana ina gefen jikinshi na kwantar da kaina kan kafaɗarshi shi kuma ya ɗora kansa bisa nawa muna kallon hoton,
“Duk yadda kika ce… Idan ma kince bayan an ɗaura auren baki buƙatar ganina a gidan zan iya dawowa Abuja a ranar in barki Kisha zamanki……”
“uhmm kai ɗin?” na faɗa kaina a ƙasa,
“Ehh ni mana, bazan iya bane?”
“zaka iya….”
Murmushi yayi ya shafi kumatu na batare da yace wani abu ba, har magriba muna tare sai bayan salla sannan anty tazo muka tafi, bayan na koma gidan ma sai da muka yi waya dashi kuma muka jima muna hira yana sanar dani wai irin ɓacin ran da yake shiga duk lokacin da ya ganni da mayafi wai in koma saka hijabi har ƙasa, cike da farin ciki muka yi sallama na kwanta bacci washe gari kam tunda safe na tafi wurin sa dan ni na bashi breakfast ma yaci ganin na zo yasa Ahmad abokinsa ya tafi, tare muka wuni dashi har dare,dan sauƙi kam ya fara samun sauƙi sai dai har yanzu asibitin basu sallameshi ba. Ina da kwana biyar da zuwa aka bashi sallama ya tattara ya koma gida, har gidan muka je tun daga nan kuma bamu sake komawa ba sai dai a waya muke gaisa wa dashi, acan Kano kuwa shirye shiryen karɓar lefe na akeyi dan anty ma har ta tafi tunda safe, zuwa yamma ƙawalli ta kirani a waya ina ɗauka naji tace,
“Amaryar Samz…. Irin wannan uban kaya haka, gaskiya samz ya kashe miki kuɗi”
Video ɗin kayan tayi ta turo min ta WhatsApp nan naga akwati na goma har kit na sha ɗaya su kansu akwatinan sun haɗu ballantana uban kayan da suke ciki, waya yamin yana tambaya ta wai idan akwai abin da bai yimin ba in faɗa sai a canjo min, murmushi nayi nace ni ya rabani da wani maganar kaya yanzu ta lafiyar sa nake, gidan uncle ɗin shi sune suka haɗa komai sannan sune suka kawo kayan da matar uncle ɗin shi Anty siyama da sauran dangin mahaifinshi amma babu dangin mommy ko ƙawayenta ko mutum ɗaya dan gaba ɗaya ta tsame hannunta daga al’amuran da suka shafe shi ga uban rashin arziƙi da take tatawa daddy kullum masifar safe daban ta rana daban ta dare daban abu kaɗan sai tace wai shi ne ya rabata da ɗan ta ya janyeshi kuma wallahi ta ɗauki alwashi ba zata taɓa yafewa ba sai ta ɗauki fansa dan da ta cigaba da ganin irin wannan tashin hankali da ɓacin ran gara Samz ɗin ya mutu kowa ma ya rasa, irin waɗannan kalaman nata sune suke tayarwa da daddy hankali, alla alla yake a ɗaura auren nan a huta dan a yanda yake ganin take taken mommy zata iya aikata komai wurin ganin ta rusa auren nan musamman ma yanzu da ta sake haɗe kai da Madam comfort wanda kullum suke sa ƙafa su fita ba zasu dawo ba sai dare,
Samz kuwa shi da kansa ya gane ƙarfin addu’ace da ikon Allah kawai suka ceceshi shiyasa abun ya tsaya a iya jinya wannan dalilin ne yasa ya sake riƙe addu’a da kyau kullum cikin sake ɗora masa wata nake yi amma ta waya dan tunda aka fara yimin gyaran jiki anty ta ƙi yarda ya ganni ta hanamu haɗuwa dashi kwata kwata duk da ƙishin ruwan ganin juna da muke yi gyara ake yimin na kece raini nabi nayi ɓulɓul dani duk da fargaba bata barina ina cin abinci ina ƙoshi, gashi taƙi barina in koma kano wai sai ana saura kwana uku biki da nayi magana kuma saboda ƴan shirye shirye na sai tace ai ni ƴar gata ce ga ƙawalli na can da Bishra suna yimin komai, a daddafe dai duk na iya zama har kwanakin da ta ɗiba min suka cika, samz kuwa har lokacin bamu haɗu ba sai dai ta waya, gida sun gama duk wani shirye shirye, ranar Litinin muka bar garin Abuja muka nufi Kanon dabo tumbin giwa nida anty da yaran ta gaba daya harda masu yi mata aiki dan ba zata dawo kwana kusa ba sai angama komai na biki ta huta sannan, su a mota suka tafi ni kuma jirgi nabi dan haka na riga su sauka………..✍
*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*
_*Ummi Shatu*_