Garin Dadi 1
©️ HASKE WRITERS ASSOCIATION
_(Home of expert & perfect writers)_
*GARIN DAƊI………!*
(Based on a true life story)
*_NA_*
_*UMMI A’ISHA*_
*Wattpad:ummishatu*
بسم الله الرحمن الرحيم، رب اشرح لي صدري ويسر لي أمري، لا إله إلا الله وحده لا شريك له، اشهد ان لا اله الا الله محمد رسول الله.
_Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoya masu karanta littattafan na,labarin garin daɗi labari ne da ya faru a gaske wanda tun lokacin da naji labarin ya tsaya min rai, ya zauna cikin zuciya ta daga ƙarshe naga ya dace in raba wannan labari ga masoya na suma su ji abinda naji duk da na fara sabon littafina a wattpad mai suna baƙo ayi min afuwa na ajiye rubuta baƙo har sai na kammala wannan da yardar Allah, asha karatu lafiya._
1
~~~Alhaji Mukhtar Garzali shine cikakken sunan mahaifinmu, mahaifinmu alƙali ne kuma mai shari’a a wata babbar kotu dake cikin garin Kanon dabo tarin Allah, mu bakwai mahaifinmu ya haifa hudu mata uku maza, yaya Abdallah shine babba sai mai bimasa yaya Abdurrahman, daga nan sai Anty khadija sai yaya Abdul hakim dake bi mata, sai Anty Salaha daga nan sai ni Maimunatu wadda ake kira da (widat) sai ƴar autar mu Bishra. Mahaifinmu sanannen mutum ne kuma ana ganin girman sa da mutuncinsa a ko ina, matansa na aure guda biyu hajiya Aisha (mama) da hajiya Fatima wadda muke kira da Annie, dukkaninsu haifaffun cikin garin Kano ne, shi Abba ɗan asalin garin takai ne wanda aikine ya kai kakansa wato mahaifin babansa zama kasancewarsa alƙali, itama mama ƴar asalin garin takai ce Annie ce kaɗai haifaffiyar garin wudil. Hajiya Aisha itace uwar gida kuma duk hannunta muka taso kasancewar Allah bai bata haihuwa ba, zaman lafiyar da suke yi yasa baƙo baya iya gane ko ƴayan waye mu, duka mazan gidanmu lauyoyi ne domin gaba ɗaya ra’ayinsu kenan na son gadar babanmu, haka a mata ma babbar yayar mu anty khadija lawyer ce, anty salaha ce kaɗai ma’aikaciyar jinya sai bishra dake da irin nata ra’ayin na karantar fannin lafiya domin a yanzu haka tana can makarantar koyon ungozoma da aikin jinya dake garin azare. Nikam dama tun ina ƴar ƙarama nake da sha’awar kutse cikin na’ura mai ƙwaƙwalwa wato (computer) a turance, tun ban iyaba nake shiga ɗakin mazan gidanmu duk wadda naga yayi wasarere da tasa ko ya saka a charge haka zan buɗe inyita yi masa bincike a ciki, duka kam na shashi babu iyaka banda punishment kala kala da suke sakani musamman yaya Abdurrahman da yaƙi jinin ya ajiye abunsa yazo ya iskeshi ba daidai ba ancanja masa matsugunni ko an taɓa masa, duk da irin duka da punishment ɗin da ake sakani hakan bai hanani cigaba da tattaɓa musu laptop ɗinsu ba har saida ta kai ta kawo sun daina ajiyewa acikin ɗakinsu kowa ya canja maɓoya, cikin haka kwatsam sai muka yi baƙo yaron aminin abbanmu wanda yasamu gurbin karatu a jami’ar bayero dake cikin garin kano, sunansa faisal kuma shima harda laptop ɗinshi yazo nan fa na samu aikin yi dan hatta makarantar islamiyya sai su Annie sunyi dagaske nake tafiya lokacin ina aji biyar a makarantar secondary ta jeka ka dawo, shi yaya faisal baida matsala koda yaushe barmin laptop ɗinshi yake yi inyita bincike na da games har sai idan abu mai muhimmanci zai yi sannan zai karɓa shi ɗinma yana gamawa zai dawo min da ita shiyasa laptop ɗin ta zama kamar wata tawa, cikin ƙirƙire ƙirƙire na wata rana na ƙirƙiri wata manhaja ta makarantar mu wadda kowanne ɗalibi za asaka bayanansa da suka shafe shi kama tun daga sunansa, jinsi, aji, report sheet da sauransu harda tambarin makarantar mu a tsakiya, wannan abu da nayi shi ya sake fito da baiwata a fili dan har gobe da wannan tsarin makarantar mu suke amfani dashi kuma lokacin har karramani aka yi domin na faɗawa principal cewa saboda asamu sauƙin fitar da sakamakon jarrabawa na ƙirƙiri application ɗin duba da yadda naga malaman mu na shan wahala wurin marking da harhaɗa marks har su fitar da position sannan ga yawan kuskure da ake samu duk da muna taya su da recording amma daga ƙarshe sai kaga anyi ba daidai ba, wannan abu da nayi shi ya kawo sauƙin aikin da class masters ke sha shiyasa nima darajata ta ɗagu a idon kowa ranar da aka karrama ni kuwa harda sabuwar laptop mai tsada ƴar ƙarama mai kyau principal ta bani lokacin ina zango farko a aji 6,tun daga nan na goge kuma na ƙware a harkar computer ba tare da wani ya koya min ba karambani nane kawai yasa na iya, dan tsabar karambani ni na tsara invitation cards ɗin bikin anty salaha kuma kowa ya yaba domin na ɓata lokaci akansa ina yi masa ado. Bayan na kammala makarantar secondary sakamako ya fito na tafi makarantar koyon ilmin na’ura mai ƙwaƙwalwa a garin kazaure nan na sake gwanancewa dama abune da nake so, shekara biyu na gama nadawo gida ɗauke da sakamako mai kyau, babu ɓata lokaci na faɗa jami’ar bayero dan karantar computer science, nan ɗinma nayi na gama cikin nasara nayi service na gama, lokacin ne na fara tunanin abinda yadace nayi domin samun ƴan canji duk da Annie kullum maganar aurena ce a bakinta acewarta lokaci yayi wanda yadace in fitar da miji inyi aure duk da ni har lokacin ban samu wanda hankalina ya kwanta dashi ba domin Allah ma ya sani ni ina da choice acikin maza, akwai irin mijin da najima ina yi wa kaina fata da kwaɗayin samu sai dai yawancin samarin da nake haɗuwa dasu su kuma ba hakan suke ba shiyasa soyayyar tamu bata ɗorewa sosai, a gefe ɗaya kuma yaya faisal ɗan aminin Abba wanda yayi karatu a gidanmu shima sona yake dan ayanzu haka ya jima da kammala karatunsa kuma yana aiki da wata ma’aikata ƙarƙashin gwamnatin tarayya a garin Abuja. Nidai sama sama nake kula yaya faisal bafa wai dan yayi min ba a’a sai dan kawai bana son wulaƙantashi, cikin haka naga wata sanarwa online wai wani kamfani yana buƙatar waɗanda suka iya computer zai ɗaukesu aiki, kamar wasa nayi applying cikin kwanaki biyu suka kirani interview kuma tun awurin suka ce sun ɗaukeni Monday zan fara fita aiki, wannan abu ba ƙaramin daɗi yayi min ba domin kamar irin a mazaunin trainers aka ɗaukemu mune zamu rinƙa koyar da ɗalibansu computer lokaci ƙanƙani na faso gari yanzu babu ruwana da tambayar su Annie kuɗin pads ko kuɗin powder domin albashi ake bamu mai tsoka banda allowances da muke samu, gaba ɗaya yanzu na zama wata busy kullum cikin bincike nake saboda koyarwa sai da research gudun kada students su tsuyeka ko su ƙureka, yaya faisal kuwa yau ina dawowa gida daga aiki naga saƙonsa ta kafar sadarwar Instagram wai gobe insha Allah zai shigo Kano anan ma zai yi weekend ya kira wayata bai same ni ba, shiru nayi ban amsa masa ba domin nidai bana farin ciki da wannan zuwan nasa haka kuma bana baƙin ciki, ƙawata tun ta ƙuruciya wato childhood friend mai suna Maryam ita na yi wa text massage na sanar da ita halin da ake ciki cewar ina da baƙo gobe, reply ta dawo min dashi cewa zata zo anjima inyaso sai mu san abin da zamu shirya domin tarɓarsa, kashe wayata nayi na jonata a charge sannan na saka kayan shan iska na fita, babu kowa a falon mama sai tv dake ta faman aiki ita kaɗai kai tsaye sashen Annie na wuce can na iske su suna girkin abincin dare tare da mai taimaka musu wurin aikace aikacen gida madina, zama nayi ina kallon Annie dake gyara gyaɗar miya,
“Annie bishra bata dawo bane daga gidan anty salahan?”
“ke dai ba baki son zuwa ba? Tunda ita ta tafi ai sai kibarta ta kwana biyu” mama ta bani amsa tana yankan alayyahu, hannu na kai na ɗauki alayyahun na fara tayata gyarashi ina miƙa mata tana yankawa,
“ai ni ban taɓa ganin yarinya mai ƙulafucin gida irin widat ba, duk inda zata je hankalinta baya kwanciya in dai ba a gida ta ganta ba” Annie ta faɗa tana ƙoƙarin tashi daga kan kujerar da take zaune,
“a’a widat kam akwai ƙulafuci, lokacin da tana ƙarama bata ɗaukuwa” inji mama,
“to ai yanzu gashi sai labari” madina ta amsawa mama,
“ai har yanzun ma haka take bata iya tafiyar kwana biyu tabar gida in dai ba makaranta taje ba”
Ina jin su ban ce komai ba domin wani tunanin nake yi acikin raina kawai tunanin aure nake, wato duk ranar da aka raba ni da gidan mu aka kai ni wani garin tofa angama dani dan nasan zan jima ban daina kewar gidan mu ba wannan dalilinne ma yasa ban fiya son inyi saurayi wanda ba ɗan Kano ba saboda bana son yin nisa da gida shi kansa yaya faisal sai munyi ta da wajewa idan har Allah yayi shine mijina to sai dai ya nema min gida a Kano ya ajiyeni inyaso shi sai ya rinƙa zuwa duk lokacin da ya samu dama amma gaskiya bana jin zan iya binsa Abuja ɗinnan, sallamar Maryam ce ta katseni daga tunanin da nake yi, miƙewa nayi tsaye lokacin da suke gaggaisawa dasu mama bayan sun gama muka nufi ɗakina dake can cikin sashen mama domin acan duk aka yi mana ɗakuna yaran gidan, bishra ce kaɗai take ɓangaren Annie, ɗakin dake mazaunin nawa muka shiga Maryam ta zauna bakin gado tana kallo na yayin da nake duba wayata wacce ke jone jikin sucket tana charge,
“yan mata ya aka yi ne?” na fada cikin murmushi batare da na kalleta ba, itama murmushin tayi sannan cikin tsokana tace,
“saurayinmu me yafi so acikin nau’in abinci da abin sha? So nake mu burgeshi ƙarshen burgewa sannan ya koma gida yana santin girkin mu…”
Ɗan taɓe baki nayi kafin na ajiye wayata na koma gefen gado na zauna ina tattare ƙasan dogon wandon cotton din da yake jikina,
” ƙawalli nifa wallahi bana wani ɗokin zuwan bawan Allahn nan saboda kawai ina kulashi ne sakamakon akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin iyayenmu amma ni ba shine zaɓina ba……”
Numfashi taja sannan ta kalleni bayan ta ɗan yi tagumi kamar wata sabuwar marainiya,
” ƙawalli kenan, sau da yawa kalamanki na bani mamaki kuma na kan rasa a gurbin da zan ajiye su, wai menene laifin yaya faisal? Kin san asalin sa, kin san halayansa da ɗabi’unsa, yana da iliminsa yana da aikin sa sannan ko halittar da Allah yayi masa bashida muni to me kike nema? ”
Lumshe idanuwa nayi ina sakin ajiyar zuciya nasan duk yanda zan kai da kwatanta mata abinda ke kai komo acikin raina ba zata fahimceni ba, kai bama ita kaɗai ba kusan kowa ba zai gane abinda ke raina ba,
” ni babu abinda nake nema ƙawalli, kawai dai ina son in auri mijin da nake jin sonsa da ƙaunarsa har cikin jinin jikina wanda zai zauna a zuciyata, wanda ko laifi yayi min idan na kalle shi zan ji na huce saboda tsabar son da nake yi masa….. Wallahi idan na auri yaya faisal ba fa lallai in iya faranta masa yadda yakamata ba saboda bana jin ina yi masa irin wannan mahaukacin son da nake ji a jikina zan yi wa mijina….. ”
Dariya Maryam ta sheƙe da ita kafin ta dafa kafaɗa ta tana kallo na,
” wannan yarinyar akwai motsi akanki, to waye ya faɗa miki yanayin yanda muke jin so ɗaya ne? Kowanne ɗan adam da irin yadda yake jin soyayya, ƙiyayya, kwaɗayi, wasu suna zurfafa soyayya ko ƙiyayya yayin da wasu kuma ƴan i don’t care ne, kuma kema kina daga cikinsu saboda baki taɓa yin saurayi kinji kina tsananin sonsa ba ko Kiji kin damu dashi irin totally ɗinnan, dan haka kima cire wannan batun a ranki, nasan insha Allah daga ranar da kuka zama ma’aurata zaki so shi kuma zaki ƙaunaceshi”
“gaskiya ƙawalli bana jin hakan zai iya zama gaskiya acikin rayuwata domin ni kaɗai nasan abinda ke kai komo acikin raina, sannan ni ban yarda da kalamanki ba da ki kace wai mutane suna da bambanci wurin jin raɗaɗin so ko soyayya, duk wani mahaluƙi yana jin so acikin ransa mutuƙar yasamu wanda yake so haka kuma yana jin ƙiyayya acikin ransa idan har aka yi rashin dace jini bai haɗu ba ko kuma idan an ɓata masa”
Mayafin jikinta ta cire ta ajiye gefe sannan tayi gyaran murya ta dube ni,
“wai baki yarda da maganata ba kenan da na ce miki akwai mutanen da sam kwata kwata basu jin son kowa acikin ransu haka kuma basa jin tsanarsa? To bari na baki misali da jin ƙamshi, a duniyar nan tamu akwai mutanen da su gaba ɗaya basa jin ƙamshi haka kuma basa jin wari, su awurinsu da ki saka turare da kar ki saka duk ɗaya ne domin basa bambance ƙamshinsa da warinsa, yayin da wasu mutanen ke masifar jin ƙamshi ko yaya kika saka turare sai sun ji ƙamshinsa to haka so yake ko ince zuciya, wata zuciyar tana da ƙulafucin so sannan babu wahala ta faɗa so yayin da wata zuciyar babu ruwanta komai kyautatawa da kulawa bata zarmewa cikin soyayya to ke taki zuciyar irin wannan ce shiyasa kowanne saurayi sai kiga bai yimika ba komai girman haɗuwarsa kuwa”
Ɗan damm nayi batare da nayi magana ba face jujjuya maganganunta da na keta faman yi acikin raina, ina sake tambayar zuciyata wai dama ana samun irin haka kamar yadda ƙawallita ta faɗa??………………………. ✍
*_Ummi Shatu_*