Daudar Gora Book 1 Page 41
41_*
…….Shiru yay yana kallon inda ya saba iske shayinsa, wayam babu komai, ya kai zaune a kujerar cikin alamun gajiyawa, a gefe kuma tsaurin idon yarinyar da ƙarfin halinta na masa kaikawo. Shan wannan shayin ya zame masa jiki da in bai sha ɗin ba sam bama yajin daɗi, har ma yakan tsinta kansa a wani yanayi da shi kaɗai ya barma kansa matsayin sirri duk da abun na matuƙar damunsa. Har yayi yunƙurin dauriyar sharewa tunda ya ɗan sha wani amma jin abinda yake gudun na taso masa ya sashi furzar da zazzafar iska, babu shiri ya danna alerm ɗin dake isar da saƙon kira ga amintattun hadimansa. Cikin mintunan da basu wuce uku ba ko sai ga ɗaya daga cikin su ya iso. A gabansa ya zube cikin tsumar jiki yana mai ambaton…
“ALLAH ya ƙara ma Shugabana tsahon rai da ingantacciyar lafiya, umarninka shine abin jirana”.
A zuciya ya amsa da Amin, a zahiri kam babu alamar zai tanka kamarma bashi ya bukaci ganin hadimin ba. Tsahon mintuna uku ƙasaita da izza irinta saraki na dawainiya da shi kafin ya motsa lips ɗinsa a hankali cikin bada umarni.
“Miya hana a kawo shayi?”.
Hadimin ya ƙara ƙasa da kai jikinsa na ɗan rawa. “Umarni ne daga Zawjata-almilk”.
(Umarni?!) Ya maimaita kalmar a zuciyarsa cikin ƙara ƙanƙance idanunsa. (Shi kam ya zaiyi da yarinyar nan ne? Mai kama da alja…..) Ya sake ayyanawa a zuciyarsa batare da ya ƙarasa ba. Sai kuma ya kalla hadimin ya ɗauke kai. “Ina buƙatar waninsa”.
Da sauri hadimin ya ƙara gurfana yana amsa masa ransa fal mamaki da al’ajabin wannan sabon al’amari.
Fuskarsa gwanace wajen shanye sirrin dake bayyane, amma yanda ya yatsinata da lumshe idanu a yanzu zai tabbatar maka akwai magana tattare da shi…..
★★
Duk yanda taso nuna halin ko’in kula kan abinda ya farun yanzu hakan ya gagara. Dan mayataccen ƙamshin turarensa daya bambanta da wanda ta saka duk da suma nasa ɗinne ya mugun addabarta. Takai hanunta kan hanci yafi sau biyar, sai ta shinshina sai kuma ta janye tana laɓe baki. Hakan kuma bai hana anjima ta sake maidawar ta shinshina. Daga ƙarshe da taga abin na neman zama mata ɗan kaɗafi sai ta faɗa toilet ta wanke hanun da sabulu, amma dan mayata yaƙi ya daina sai da ta ɗauka ɗaya a cikin turarrukan datai amfani da su na ɗakin tasa a hannun sannan ta daina ji.
Littafinta ta ɗauka domin cigaba da nazari, sai kuma ta tsaya cak, wani tunani ne yazo mata a zuciya, dan haka ta miƙe zaraf tana ɗaukar wayarta data gani tare da littafin alamar duk ma wanda ya kawota tare da su ya kawotan. Kamar yanda ta saba idan zasuyi magana tai dawnlording sabon WhatsApp app, sai da ta daidaita komai sannan ta lalubosa. Baya online gashi kuma tana buƙatar yau suyi magana ne bawai saƙo take son ajiye masa ba. Sai hakan ya sata jin babu daɗi har walwalarta ta ɓace. “Kona masa flashing?”. Ta faɗa cikin sigar tambayar kanta. Kan ta daga alamar gamsuwa, ta fito a watsap ɗin. A karo na farko tai dailing number ɗin cikin shakku. Harta katse ba’a ɗaga ba, damuwarta ta kara bayyana. Harta sake komawa watsap ɗin ta fito ta sake danna kiran. A hankali ta sauke ajiyar zuciya har ana iya jinta daga can. Tai sallama cikin yar muryarta dake nuna zumuɗin jin an ɗaga, sai dai ba’a amsa mata ba gashi kuma tanajin alamar ana saurarenta.
Danne takaicinta tai ta sake sallamar, nan ma shiru dai babu ma alamar za’a amsa. Cikin suɓutar baki taja tsoki da faɗin. “Nifa a rayuwa na tsani walakanci wlhy, shiyyasa komai nafi yarda naima kaina. Yanzu haka wani ɗan iyan dake ƙarƙashin sa ya ɗaga kiran kamar waccan ranar dana fara kira, ƴan hana ruwa gudu kenan. Nima badan ƙaddarar faɗawa hannun wannan Dodon ba da yanzu ina can ina karatuna na jaridar a daina yarfani. Kai insha ALLAHU kafin naga bayan a azzalumin nan ko sau ɗaya ne sai na hau kujerar karagar mulkin nan nayi tankaɗe da rairaya cikin duk ƴan jaridar ƙasar nan da jami’an tsaro aikin banza……”
Jin kamar sautin fitar murmushi a kunenta ya sata saurin ciro wayar ta kalla. Dai-dai ana yanke wayar. Ido ta kwalalo waje da dafe bakin. Sai kuma ta janye da faɗin, “Kai kamarfa daga cikin wayar ne sautin nan ya fito wlhy. Kai ina”. Ta sake faɗa tana ɗan wawwaigawa babu dai alamar wani a ɗakin sai itan kaɗai. “Oh ni Iffah anya bakin nan nawa bazai yankani ba wataran, yanzu hakama shine yazo ya amshi wayar inata zuba ban sani ba”. Tai tagumi cikin takaicin kanta. Kamar kuma wadda aka ɗan zabura sai ta sake ɗaukar wayar. Cikin sa’a tai tozali da ganinsa online har an amsa mata sallamarta ma. Sai kuma ta shiga kokwanton tayi magana ko kawai ta share. Wata zuciya ta amsa mata da (Kema kin san bashi bane ya ɗaga miki waya. Ki basar kawai). Da alama ta gamsu da shawarar, dan haka ta saki murmushi da buɗe saƙon.
“Sorry kin kirani bana kusa yarona ya amsa”.
Amsar data samu kenan bayan sallamarta da aka amsa. Har cikin rai taji daɗi, dan haka a fili ta furta “Alhamdullah dama naji haka a jikina”. Shi kuma ta bashi amsa da “Babu damuwa Sir”.
“kina da fahimta Shahrbano”.
“Bankai nan ba”.
Ta bashi amsa da emojin yamutse fuska. Sharewa yay da faɗin,
“Ta samu ne?”.
Itama sai ta share da bashi amsa da.
“Kusan haka. Sai dai a wannan gaɓar lamarin akwai ban tsoro Sir Ajmaal. Da gaske mutanen nan matsafa ne kuma suna aiki da aljanu”.
“Ya arrahaman! Kamar ya? Har kimsa na tsorata fa”.
“Tab tunma kan na faɗa kenan. To kama cire dan wlhy ba aljanu ba ko bataliyar ifiritai ce sai naga bayan mutumin nan. Wai fa jiya da dare nabar sashen nasa na koma inda sukace nawa kawai yau na wayi gari na ganni an sake maidoni sashen Dodon nan. Ɗakin dana kwana kuwa duk da haɗuwarsa na rantse maka a harmutse kamar anci dambe”.
“Dambe fa?”.
Ya share zancen farko ya amsa na ƙarshe.
“Wlhy kuwa Sir! Sai dai fa ni wannan bai damenba. So nake nasan ta yaya aka ɗakkoni aka maido ni inda ba nan na kwanta ba”.
“Kina da gaskiya dan akwai alamar tambaya kam. Amma ke yanzu wane mataki kika ɗauka?”.
“Komai banyiba har yanzu, nadai fara bincika irin kamshin da naji jikina nayi, inma shine ya aika aljanunsa suka ɗakkoni dan ya kashe ni”.
“”.
Ya bata amsa da emojin rufe baki alamar tare dariya.
“Bafa abin dariya bane wannan, abin a dubane. Idan kuma aka halakani kafin ƙwato muku ƴancinku ku kukayi asara Sir Ajmaal”.
“Eh gaskiya hakane kuma ranki ya daɗe. Yanzu dai ƙarasa bani labarin dan in san ina zan kama. Saboda na gama shirye-shiryen buɗe wani sashe na shiri na musamman akan wannan case ɗin, sai dai komai zai kasance cikin hikima”.
“Aiko da naji daɗi Sir, dan gara kam a fara kafin ma na mutu na dinga ji. Dama inason maka zancen wancan tashin bomb ɗin, ko ka san mutumin nan ko damuwa bai nuna ba akan lamarin tsabar bai ɗauki rai bakin komai ba. Wlhy naji kamar na shaƙesa a jiyan kowama ya huta dan takaici”.
“Wai da gaske kike zancen nan ranki ya daɗe?”
“Wlhy kuwa babu wasa. Ni ka daina kirana da wannan sunan bana so”.
“Kiyi haƙuri kin cancanta ne ai. Zawjata-almilk guda ai ba abin wasan mu bace. Nima dai tsaurin ido yasa har nake iya zaman tattaunawa da ke”.
“”.
Ta tura masa tana kashe data ɗinta. Daga can Ajmaal ya ƙurama emojis ɗin ido yana mai ƙoƙarin danne dariyarsa amma hakan ya gagara, dole yay faffaɗan murmushi har haƙoransa na bayyana yana ayyana (ƙuruciya daɗi) a zuciyarsa. Ganin ta kashe datan shima sai ya kashe kawai dan yana son sai ya nutsu yay zaman nazari akan abinda suka tattauna ɗin…..
★★….. KAUYEN JUMNA ★……
Alhamdullah dawowar Kaka da tsayuwar daka akan lafiyar Ummu yasa jikinta ƙarayin sauƙi har tana ɗan yin magana. Wani lokacin ma idan suna ƴar hira takan ɗan saka bakinta musamman idan akan Iffah ne da a mafi yawan lokuta take faɗo musu a zukata. Bawai halin da suka shiga kansu Babiy ya mantar da su ita bane, a koda yaushe tana manne a rayukansu, suna kuma binta da addu’a da cigaba da baza kunnen saƙon mutuwarta kamar ƴaƴansu na baya. Duk da dai ga Iffahn na nan shafe wata na uku kenan a daular ruman ɗin.
Yau ma kamar kullum Ummu da Iyyani na a tsakar gida suna aiki wanda kusan Ummu ce keyinsa duk da bana kirki bane. Kaka ya fita tun ɗazun wajen jana’izar mutuwa da akayi ta wani tsoho. Sauri-sauri Ummu ke ƙarasa aikin saboda rana ta ɗaga gata da zafi sosai kasancewar su yankinsu akwai sahara, danma suna ɗan samun sassauci dalilin ruwa ne zagaye da ƙasar tasu. Sai dai kuma zaman Dahab City (Daular ruman) kamar a tsakkiyar ƙasar ta ruman yasa su sunfi samun zafin yashin fiye da sanyin ruwan daya mamaye wasu jahohin dake a gaɓarsa sosai.
Sallamar da akayi ta saka Ummu amsawa tana mai duban ƙofar gidan, Iyyani ta fito tana faɗin, “Inaga mutanen Abbunku ne da basa ƙarewa. Gashi kuma bai dawo ba har yanzu ko yaya zamuyi kenan?”.
“Nima shi nake tunani Iyyani, kona leƙa na gani tunda ba’a sani ba ko baƙon mai muhimmanci ne?”.
Har Iyyani ta buɗe baki zata bama Ummu amsa sallamar Kaka ta katseta. “To Alhamdullah gamashi nan”. Iyyani ta faɗa tana kallon Ummu. Cikin fara’a kaka ya shigo, hakan yasa bayan sun masa sannu Iyyani ke tambayarsa ko lafiya?. Fuskar tasa da murmushi har sannan ya ce “Bani abun zama kedai yaron nan ne Zakariyya makwafcin su Jumimah”. Ya kare maganar da kallon inda Ummu take.
“Ah Masha ALLAH, ALLAH yasa muji alkairi to”. Iyyani ta faɗa tana ɗakko masa abinda ya buƙata har da ruwan sha ma a kofi…….
★★★…. ★★….. ★…..
Iffah kam dake ta faman tsuke fuska ita a dole taji haushi ta jawo rigar ɗazun ta maida a saman gown ɗinta ta fice. Isowarta falon dai-dai isar da sakon Tajwar Eshaan akan sake dafa masa shayi a bakin hadimin nan ga masu dafa abinci. Kai tsaye mamaki ya bayyana ƙarara a kan fuskarta. Amma sai ta dake babu alamarsa a zahiri taima hadiman wani kallo ta ɗauke kai.
Ba ƙaramin razana da ganinta a cikin kicin masu girkin sukai ba. Dan hakan zai iya zamar musu rasa aikinsu. Sai dai yanda tai kicin-kicin da fuska ya sasu kama kansu, kwarjininta da gizagonta na kere yawan shekarunta. Jikinsu har rawa yake lokacin data buƙaci ganin kayan shayin da Tajwar ɗin ke amfani da su. Daki-daki take binsu da kallo cike da nazari, sai da ta gama tsaf kafin ta juya garesu fuska a tsume. “Idan ina buƙatar wasu bayan waɗan nan a yanzun fa?”.
Cikin mamaki da tsoro suka sanar mata za’a kawo da gaggawa.
“Ina buƙatar zama da mai kawowar”.
Ta faɗa a gadarance da juyawa ta fara haɗa kalar shayi da salon dabararta batare da tayi amfani da wanda ake dafa masan ba. Wannan duk cikin shirinta ne na son ƙuntata ma zuciyar Tajwar Eshaan a cewarta. Cikin lokaci ƙalilan ta gama kasancewar ba wani mai yawa bane, ta juyesa a haɗaɗɗen butar shayi tare da haɗa komai na buƙata tai ƙoƙarin ɗauka. Da sauri hadima ɗaya ta miƙe ta amsheta. Bata musaba wajen bata dan dama ba sanin inda zata samesan tai ba.
Hadimar tai tsaye a dai-dai ƙofar ƙaramin falon alamar iyakar ta kenan. Iffah ta fahimci haka, sai kawai ta amsa batare da tace komai ba. Ba tsoro ko shakkar haɗuwa da shi take ba, abinda zai farunne idan ta shiga kawai take tunani. Tsahon minti biyu kafin tai ƙundunbalar shiga dan a ganinta wannan wata dama ce ta biyu a gareta, cikin takunta na nutsuwa da dakewarta ta tura kai bayan ƙofar gilashin ta zuge da kanta batare data tabata ba………✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
✨Ɗ ✨
( )