Dalibina Hausa NovelHausa Novels

Dalibina 39-40

Sponsored Links

Littafina na kudine sister please in kina son karantawa 300regular vip 600 via
2378022567
Aisha Mohammed
Zeinith bnk

Dan girman Allah karki karanta min littafi in Baki biya ba

3️⃣9️⃣⏏️4️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Cikin shagwab’a tace”abbu ”

Yar dariya yayi cikin zolaya yace”ba wani wayau Nan bàyan an paka Ni gefe daga zuwa karb’a Baki sainaji d’aurin auren

Ta rufe tace”abhu wallahi Nima ban sani ba sai d’azu Abba ke fad’a min ”

Yace”toh Inna tace ki zogida gobe”

Tace in na tashi a makaranta Zan Zo

Yace”ok but ayi ta d’aukar izini Fatima yanzu ba kamar da bane da Zaki fita kanki tsaye shi namiji Dan son girma ne ki ajiye son girmanki kiyi biyayya kin gan dai jarrabawar da Allah yayi Miki cikin hukuncinsa yayi Miki rahama ya dafa Miki a lokacin da bamuyi zato ba Dan girman Allah Fatima kiyi min alkawari zakiyi biyayya ga mijinki ki bawa marad’a kunya masu jira ta kwabe ayi dariya

Cikin sanyi jiki tace”Abba nayi maka alkawarin zanyi biyayya ga mijina

Yace”toh ya’ta sai kin taho given ki taho da kayanki munyi magana da abbanki yace”ki zauna a nan har tarewarki”

Tace”toh”

Suna Gama waya ta sauke akwatunan ta ta Fara had’a kayanta da zata tafi dasu

Tana cikin zuge zip sai ga umma da anty amarya sun shiga biye da juna

Kallonsu tayi sai ta cigaba da abinda take

Fuskarsu a washe Suka ce anty Fatima zuwa mukayi muyi Miki Allah ya Sanya alkhairin”

Ta d’au lokaci kafin tace”toh nagode”

Umma tace”ya na gan kina had’a Kaya tafiya zakiyi ne?”

Tace”eh a takaice

Anty amarya ta karasa ta zauna a bakin gado tace”Yar Nan ai yanzu ba lokacin tafiya bane gyara zakiyi ki killace kanki ai”

Ko uhrmm Bata ce musu ba Suka karaci zamansu sanan Suka bar d’akin ta bi bayansu da harara

A Daren yau batayi bacci ba in har ta tuna Wai yau da aure a kanta sai taji wani irin dadi,data lumshe Ido imagining rayuwar da zasuyi take da aliyu dinta

Murmushi ko Haka tayi ta sakinta Kamar sabuwar kamu karshe ma bugewa sukayi da wayar dare Dan shima beyi baccin ba saboda zumud’i

Washe gari’ tana tashi tayi sallah ta gyara d’akinta ta wanke bayi sanan ta koma bacci Bata farka ba sai wajajen 10am ta gan tarin missedcalls da chart dinsa duk na good morning

Murmushi tayi ta Shiga messages sai ta gan alert din makud’an kudade ta lumshe idanunta ta sake Shiga chart sai ta gan ya rubuta wanan kudin na gyaran jiki ne ciki da waje ki tabbatar an gyara min ke please

Murmushi tayi ta girgiza Kai ta mike ta shiga wanka ta fito kenan sai hafsat Yar anty amarya da wani flask Wai an kawo Mata abin Kari

Abin mamaki ya Bata tace”kin gan hafsat tafi dashi ban fiya son karyawa da wuri ba

Hafsat tace”mama fah tace”ki daure ki Sha ko kad’an ne ”

Tace”ok ajiye ”

Ajiyewa yariyar tayi ta bar d’akin itako ta hau shiri zuwa makaranta

Saf ta shirya cikin Riga da skirt na atamfa yayi Mata mugun kyau ta d’au babban mayafi Mai kyau ta yafa daga Kai sai ta karasa gaban mirror tana kallon kanta ta saki dariya harda tafawa in har ta tuna Wai tayi aure sai taji wani farin ciki abindai Kamar almara

Saf ta shirya ta d’au jakarta laptop dinta da wata karamin handbag sai makullin mota ta fita

Abin mamaki sai ta gan duk yayan gidan da sukayi aure a babban falon harda Masa suna ganinta aka Fara washe Baki kowa sai gaidata yake

Abin ya mugun Bata mamaki yau Kuma ta Kuma yarda aure daraja ce kowa sai Mata barka ake umma harda cewa ai yau be dace ki tafi makaranta ba haha ”

Tace na rigada na cewz student Dina Zan Basu test so I can’t skip dan bana Saba alkawari

Har mota aka rakota ta Zama celeb dadin abin tun jiya ta Kai akwatinta mota Dan ba dawowa zatayi gidan ba

A hankali take tuki tana Jin Kira’a a ranta ko sai godiya takewa Allah da ya nufe ta da yin aure a lokacin da batayi zato ba

Kiran numbersa take but ba a d’aga ba sai ta ajiye me chart akan ta tafi makaranta

Parking tayi ta saka kafa ta fito

____________

Yana gindin wata bishiya shi da Habib suna duba wata asighnment yaji kamshinta ya Dake shi d’agowa yayi ya gan ita dince ya mike ya bar Habib yayi wajenta

Shi kanshi Dan ya ganta ya Zo makaranta,yana zuwa yace”good morning mummy ”

Juyawa tayi Dan ya tsorata tayi fari da Ido da Bata San tayi ba

Tace

 

Maman Nur

Back to top button