Daudar Gora Book 1 Page 11
*_11_*
……….Iffah taci kuka matuƙa da ko maƙiyinta ya dubeta sai ya tausaya mata. Sai dai kuma iya juyawa su Babiy sun mata akan su gudu ta kafe akan itafa ta yarda zata aura *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majeed_*. Sosai hankalinsu yake ƙara tashi da tirjewarta. Gashi gaba ɗaya ta bikice musu ko isashen lafiya babu a tare da ita. A cikin wannan halin Babiy ya sake samun saƙon kira daga masarauta. Yana shirin tafiya sai ga Kaka. Duk sunyi matuƙar mamakin zuwan nasa, dan abune mai wahalar gaske a garesa zuwa inba da wani dalili ba. Sun tarbesa kamar yanda suka saba matsayinsa na uba. Bayan gama gaisawa ya kai dubansa ga Iffah dake kwance cikin bargo duk ta rame ta sake komawa fayau da ita, dama tun rasa ƴan uwanta ɗan jikinta ya zube, dan sam ba siririya bace. Iffah nada jiki murjajje daba za’ace mata siririya ba kuma babu mai sakata a sahun masu ƙiba. Duk da shekarunta har yanzu sunada ƙaranci ALLAH ya bata jiki na manyan mata da’a yanzu komanta yake ciff dai-dai da halittarta. Kaka ya ɗauke idanunsa a hankali tare da maidasu ga Babiy.
“Muhammadu Zayyanu ka sakama ranka nutsuwa ka cire batun barin gidan dan bashine mafita ba. Hasalima tun randa ka amsa kiran masarauta wannan gidan zagaye yake da dakarun daular ruman harta inda baka zata ba. Ko’a tunaninka zasu tunkareka da wannan maganar su baka damar kanka sannan su koma gefe da tunanin kai bazakayi wani yunƙuri ba”.
Daga Babiy har Ummu da Hanash kallon tsoro da mamaki sukema Kaka. Ya ɗan jinjina kansa alamar tabbatarwa. “Karku damu da yanda akai nasan wannan, kai dai kawai kaje ga kiran da sukai maka. Karka kuma nuna wani ja’inja kace ka amince musu suzo neman auren”.
Kuka Ummu ta fashe da shi tana kallon mahaifin nata. Yay ɗan murmushi da ɗauke kansa tamkar bai fahimci mitake nufi ba. Ganin haka Hanash da idanunsa sukai jajur cikin cinkushewar harshe yace, “Amma kaka miyasa ka zaɓa itama mu sake rasata? Wlhy nayi alƙawarin in har itama ta salwanta sai na salwantar da ran Shahan-shan da wannan hanun nawa wajen ɗaukar fansa koda nima za ai gunduwa gunduwa da naman jikina!!”.
“Ba kai ne zaka salwantar da ruhinsa ba, ni nan Fareedah bint Zayyan nice zan karya ƙarfin ikon azzalumi da hannuna, zan masa shaƙa irin wadda har sai ya mutu yana mai kallon tsakkiyar cikin ƙwayar idanuna Hanash Akhi”.
Su duka zuba mata idanu sukayi, dan a yanda take maganar babu alamar tana a cikin hayyacinta. Babiy zaiyi magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai yaje kawai….
★Kamar yanda Kaka ya umarci Babiy ya amsa kiran masarauta kasancewar a wannan karon an bashi damar zuwa ne shi kaɗai batare da dakaru sun taho da shi ba. A yanda ya samu tarba zai tabbatar maka dama a jirace ake da zuwansa. Kamar ko yaushe a wannan karon ma baiga Tajwar ba, amma dai a karon farko na tarihin rayuwarsa an kaisa har cikin fadar Shahan-shan. Inda yaga tsantsar dukiya da ainahin karagar mulki ta Shahan-shan da akayita da zallar zinare. Hakan ba’abin mamaki bane ba, saboda girman Shahan-shan koda da diamonds akai kujerar mulkinsa bazai zama wani babban al’amari ba, sannan zinare arziƙin ƙasar su ta ruman ne da bare ma kanzo ya ci balle su ƴan ƙasa musamman Shahan-shan. Karo na farko da Babiy yaga karramawa daga dattijan daular ƙasar ruman. Waɗan da ko’a mafarki bai taɓa tunanin gani ba dan su ɗin ma ba’abune mai sauƙi ga duk wani talaka ganinsu ba kai tsaye haka. Duk da a birkicen da yake ALLAH sai ya saka masa nutsuwar yi musu bayani babu ko rawar harshe a tare da shi. Sun masa godiya da tabbacin a gobe idan ALLAH ya kaimu masu neman aure zasu zo. Karramawar da sukai masa ta matuƙar basa mamaki da tsayawa a ransa, sai dai ta wani gefe na zuciya ya tabbatar da sabuwar hanyar yaudarace kawai. Cikin danƙareriyar mota aka maidasa har gida badan yaso haka ba, yayi shiru ne kawai domin bin unarnin mahaifin matarsa, dan duk da bai taɓa ambatawa ba ga kowa ya jima da tsanar duk wani abu daya shafi masarautar daular ruman..
★A wannan dare Babiy yayi zaman kuka irin wanda ake kira kuka a zahiri da baɗinin rayuwa. Har yanaji bazai iya cigaba da yima kaka biyayya ba shikam, zai ɗauke Iffah su gudu daga ruman koda daga shi sai ita ne. Sai dai wani ɓangare na zuciyarsa na tunatar da shi maganar Kaka, yasan gaskiya ya faɗa, dan daular ruman bazata zuba ido na barinsa sakakai ba. Ajiyayyun dakarun dake a ƙofar gidansa ma kawai tabbaci ne….
A ɓangaren Ummu ma bata runtsa ba, sai dai saɓanin Babiy ita kwana tai tsaye tana gayama UBANGIJI damuwarsu da roƙonsa kariya da kuɓuta ga yarinyarta. Shi kuwa Hanash kwana yay ƙulla ta yanda zai halaka Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da kansa. Hakama Iffah nata shirin nada alaƙa dana Hanash. Ta gama yankema kanta koda zata mutu itama sai dai su mutu tare da Tajwar Eshaan. In yaso a binne gawarta a tsakiyyar ruman matsayin tarihin da za’a dinga tunawa…….
*_WASHE GARI_*
Washe gari data kasance safiyar laraba da misalin ƙarfe biyar na yamma sai ga manyan baƙi daga masarauta ruman. Baƙi masu ban mamaki, dan kuwa wasu manya ne a cikin dattijai masu faɗa aji a daular ruman. Sannan iyaye ga Shahan-shan ta ɓangaren jini makusanta sosai ga mahaifinsa. Tamburan masarauta da ɗunbin tawagar hadimai da jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi ne suka tabbatarma da jama’ar anguwa dama maƙwaftan anguwar wace tawagace. Tuni mutane suka fara ƴar rige-rigen fitowa daga gidajensu bama idanunsu abinci.
Sun tarbesu bisa jagoranci Kaka daya tsara komai tare da shimfiɗa kakkauran gargaɗi ga su Babiy. Bayan an musu masauki a cikin lambun Babiy ta ɓangaren garden ɗin da yayi domin farin ciki ga iyalansa aka cika musu gabansu da ƴaƴan itatuwa duk da babu tunanin ko zasu ci. Babiy, Kaka, da wasu dattijai biyu, ɗaya ta ɓangaren Babiy, ɗaya ta ɓangaren Ummu ɗan uwa ga kaka kenan suka zauna da su. Sun miƙa gaisuwa a garesu cikin mutuntawa da nuna tabbacin su ɗin masu ƙarfin iko ne a garesu talakawan ƙasan ruman. Hakan yayima dattijan matuƙar daɗi da yabama su Kaka. Dan haka suma suka nuna mutuntawa a garesu da basu ƙarfi matsayin waɗanda sukazo neman iri wajensu. Hakan ya ɗan bama su kaka mamaki amma sai babu wanda ya nuna. Sun gabatar da buƙatarsu, tare da bada duk wani abu na al’adar aure da ƙasar ruman ta tanada ninki wanda akanyi sau goma. Hakan sai ya ƙara firgita Babiy da bashi tabbacin yanda za’a salwantar da rayuwar ƴarsa ɗaya tilo data rage masa zai zama ƙololuwar girma fiye da ƴan uwanta kenan. To inbaice hakaba mizaice, dan dukiyar da suka kawo kawai tamafi ƙarfin ma sayen Iffah idan sayarwar zaiyi. Bai samu damar cewa wani abu ba, yadai cigaba da kukan zucinsa yabar su Kaka dayin abinda ya dace.
A wannan zama aka ƙarƙare komai har ranar ɗaurin aure dama inda za’a ɗaura auren. Daga haka sukai addu’a suka tafi bayan an shigo da tarin kayayyakin da sukazo da shi. Daga Babiy har Ummu tagumi kawai sukai suna kallon kayan da aka baza a tsakar gida. Hakama Hanash da dattijan nan guda biyu da sai gobe zasu koma tare da kaka. Kaka kuwa na gefe zaune abinsa tamkar baima san mike faruwa ba a gidan. Yayinda Iffah ke can ƙuryar ɗakin Ummu kwance cikin zazzaɓi data yini da shi…..
Washe gari su kaka suka wuce batare daya sake cewa uffan ga su Babiy ba akan komai. Yadai gargaɗi Babiy akan karya kuskura yace zai yi wani yunƙuri. Ya kuma sakasu killace dukkan kayan da aka kawo daga masarauta…..
★★★_______★
Tamkar da gayya cikin kanƙanin lokaci gari ya ɗauka Shahan-shan zai yi aure, alamu kuma sun nuna ana shiryama auren da shiri na musamman duk da amaryar bata kasance ƴar kowa ba. Hasalima ahalinta nada tabon Shahan-shan a dalilin salwantar ƴaƴansu biyu kafin ita. Dukkanin waɗan nan ƙananun magana na faruwane a bakunan mutane da ƙaramar murya, yayinda a kafafen ƴaɗa labarai da fejikan yaɗa zumunta babu mai iya ɗaga murya yayin faɗa sai fatan alkairi kawai. Mutane sun sake samun tabbacin wannan aure na musammne daya sha banban dana baya sakamakon fara shelarsa a kafafen yaɗa labarai domin gayyatar manya-manyan ƙasar kamar kowane Tajwar da jama’ar majalissarsa da talakawan garinsa. Da yanda ake wasu ƴan gyare-gyare a daular ruman wai duk na tarbar zuwan ranar ɗaurin aure ne. Humm abin faɗa taf bakunan mutane sai dai babu damar faɗar. Idan kuma suke ganin zasu sami wani ƙarin bayani an toshesa dan babu mai ikon shiga gidan Babiy a halin yanzu kasancewar zagaye yake da dakaru tako ina, acewarsu suna bama *_Zawjata-almilki_* tsaro ne. A cikin gidan kuma babu mai fita hatta da Hanash dake zuwa babbar makaranta…
A haka kwanakin biki da suka rage suka cigaba da shurawa batare da wadda ake iƙirarin zama amaryar ta sake tada kai ta dubi wani abu daya shafi auren nata ba koda da kallo. Ta dake matuƙa tamkar ba itaba, hatta da ciwon dake cinta a tsaitsaye taki bada damar da su Ummu zasu fahimta. Ta ƙeƙashe idanunta ƙam ta hana hawaye zuba daga cikinsu. Ta tattare gaba ɗaya hankalinta ta maida ga rubuce-rubuce da babu wanda ya fahimci na minene a gidan, dan bata bari kowa ya duba mata shi. Sai dai ga duk mai hankali a duba ɗaya da zai mata zai fahimci tana cikin matsananciyar damuwa, mai busar da zuciyar mai ita da zai iya aikata komai da zai iya zama komai akan komai..
Kamar ko yaushe yau ma bayan ta kammala ayyukan gidan da take taimakawa Ummu da su ɗaki ta koma tana kukan zuci daya zame mata abokin rayuwa. A idaniyarta kam babu alamar ɗigon hawaye, sai dai raɗaɗin wanda ke kwaranya a zuciya ya maida launin idanunta sirkin ja har kana iya ganin jijiyoyi a cikinsa. Duƙufe take akan littafinta tanata rubutu da sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ummu data shigo ɗakin takai zaune a kusa da ita tana mai tsurawa rubutun idanu na wasu sakanni.
“Ibnati!”.
Karan farko Iffah ta ɗago ta kalla Ummu duk da tun shigowarta ta jita sarai. Wani irin miskilin murmushi ta saki tare da maida kanta a hankali ta duƙar..
“Kina ganin laifinmu ko?”.
Cak ta tsaya da rubutun data cigaba, sai kuma ta saki murmushi. Tsahon sakkani uku kafin ta ɗago ta dubi Ummu. Ta ɗan girgiza kanta da ajiye biron hanunta. “Ummuna idan har zanyi zargin wani akan wannan al’amarin to kaina ya dace na zarga. Ku ɗin nagartattun iyayene abin alfaharin kowane irin ɗa. Ni ya dace nazo muku da wannan maganar, domin nice na saka zukatanku a damuwa da ɗunbin fargaba. Na tabbata a kowane sakan, a kowane minti, a kowane awa, a kowane kwana na waɗan nan kwanakin kunayinsa ne cike da fargabar shuɗewarsu da gabatowar su. Kuyi haƙuri ku ƙara haƙuri ku gafarceni. Koda baku faɗamin ba, baku faɗama duniya ba nasan irin raɗaɗin da kukeji a zukatanku domin nima makamancinsa nakeji. Sai dai ina muku albishir Ummuna, koda zakuyi kuka a wannan gaɓar bazakuyi irin na baya ba. Na muku alƙawarin kukan ku zai kasance tare da dariyarkune a lokaci guda. Dan ruhina sai ya amso muku diyyar su Nina Arfa kafin yabar gangar jikina. A duk randa saƙon mutuwata zai riskeku insha ALLAHU zai riskekune tare da na mutuwar azzalumai. Dan haka ina roƙonku kar kuyi baƙin ciki a wannan karon, zaku sadaukar da ruhin da zaije muku yaƙin neman ƴancin kai ne ku da al’ummar ƙasar ruman…..”
Kai Ummu ta shiga jujjuyawa hawaye na kwaranya a idanunta, “Ibnat…”
“Na roƙeki kar kice komai Ummuna, albarkarki itace mafi ƙololuwar buƙata ga ruhin daya daɗe da zama cikin tahin gawa. Ƙaddarata rubutacciya ce tun daga alƙalamin da idan yay rubutu babu wani duster dake iya gogesa”………..✍
ALLAH sarki Iffah, ALLAH ya baki damar yaƙi irin wanda ya dace da fatanki na alkairi
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
✨Ɗ ✨
( )