Banana Island Hausa NovelHausa Novels

Banana Island 20

Sponsored Links

___________
Ruwa me zafi ta kai mata toilet taje tayi wanka tana dawowa taga tea yaji milo sosai ,aikuwa tasha ba laifi ta daura da paracetamol saboda yanayin feverish condition din da tajita a ciki daganan ta soma barcin gajiya sai wajen 2.30pm ganin bata da niyyar tashi tayi sallah sannan Lili ta tasheta
“Are you off?”

Miƙa tayi gamida hamma “Anyi sallah ne?”

“To 3” zumbur ta miƙe zaune “Shine baki tasheni ba ?”

“Inaso ki huta da yawa”

***
Har dare Adnan bai kira wayar ifty ba wannan abu ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba ,taci kuka a sarari tayi a zahiri ,tun Lili na rarrashinta har ta fara jin haushin Adnan ɗin
“Haba wannan ai zaluncine ka koya ma yarinya sonka ka wancakalar da ita…”

“Lili ba sonsa nike ba tausayin kaina da uwata nikeji ,ya rabani da budurcina yayi ma ƴan ƙauye mu ƙarya ya aureni”
“Kiyi hakury my love Allah sai ya wulakantashi tsiyar mazan nan kenan masu kudi sun maida mata kamar riga a kowani lokaci zasu iya cireta su sauyata ”

“He told me,mata sha biya suka zauna a gidansa ,a wawancina sai ina ganin Ni bazai mun ba ,ki jibeni fa mummuna na dani shikuma gorgeous dashi half cast”

“kyau muni wannan dai duk bashine ba laifi dai ya maki laifi kuma bazaici a bulus ba”

Ifty zatayi magana saisukaji knocking din securityn dake night shift a ƙofar ɗakinsu

Share hawayenta tayi da sauri suka buɗe mata ƙofa ta shigo
“Barka da dare iyayen ɗakina”

“Good evening ma ” suka gaisheta suna mamakin me ya kawo ta ɗakinsu dama gata gwana wajen tijara student

“Momy mercy ki zauna”

Zama tayi ta soma masu kame kame kafin ta fadi asalin abunda ya kawo ta,wato rokon kudi “Yaran nan sunan muna gadinku ne amma kun fimu hutawa ,kuna dealing da manyan Alhazan birni ,iyayenku wasune mazajenku manyan mutane .amma mu ,yunwa muke sha a wajen can ,gashi baa biyanmu albashi fiye da watanni takwas ba’a bamu albashi ba….bazan taɓa manta ƙawata ba ,Madam saude tana night shift akafe akan kujera ta jingina da ƙarfen solar lamp ɗin can na hanyar masjid ɗinku,ashe hawan jininta ya tashi ba wanda ya sani bare ya kawo mata ɗauki…. saidai da asuba mazan security sukazo suka taɓata suka ga ta faɗo akan kujeran matacciya! “Ta mutu !” Ifty ta tambaya a ruɗe

“Eh wlh shiyasa,sam na tsani aikin security ɗin nan gashi ba’a biyanmu albashin kirki ga tsadar rayuwa , 20k bazasu iya bamu ba ta yaya zamu sauya ma yaran da suke ƙarƙashin mu rayuwa”?

Cikin damuwa Ifty tace “Lili mu bude akwatin nan,muga kayan dake ciki,inda wanda za’a bata taba yara”

Kayane jibge duk ready mades sai takalma foreings bana kasar nan ba

Ifty daukan takalmin tayi tana juyawa ,kudinsu zasu kai dubu ɗari biyu da ashirin kowani guda ɗaya kimanin kuɗin Nigeria

“Momy ki siyar da wainnan kuci abinci ,Ni irin wainnan takalmar ko na saka bazaa san na saka takalmi mai tsada ba ,ko wanda suka san kudinsa ne sai sai ace anyi jabunsa ne” ta ƙaro mata da gowns masu kyau sannan lili ta haɗa mata kayan abincin su da suke dashi .

***
Tana fita Lili ta janyo sabuwar Laptop ɗin da ta hango a cikin kayan da yafi tafiya da tunaninta

A hankali ta buɗe ta kunna
Rubutu taga anyi kamar haka a jikin screen ɗin.

“Thank You for a most interesting day we made together…..this laptop is yours….and I’d like you to use it for chat with me”

Lumshe Ido Lili tayi ta miƙa mata laptop din da sauri ,ƙur ta kafe rubutun da ido kafin cikin fushi ta maida masa da amsa

“Ohk haka kake so mu zauna ? Kalar relationship dinmu kenan ? na zama abokiyar ɗebe maka kewa?…kana bani umurni kamar wani boss.” ta tura masu idonta maƙale da ƙwalla .zirr nashi massage din ya shigo . Caɓe baki tayi a ranta tace agogo Sarkin aiki kullum kana kan laptop.

“Eh haka nike fatan mu kasance. Kina bukatar wani abu ne bayan hakan?”

Kafe screen din da ido tayi kawai sai kuka ,da sauri lili ta taso

“Wai me yace maki dont tell me ya sake ɓata maki rai ,Ifty zanci mutuncin Adnan saidai daga baya kiji haushina ”

Tura mata screen ɗin tayi a gabanta ,itama ta karanta ,shiru tayi batace komai ba ,ta kasa banbance aure zasuyi ko zaman dadiro .

Sun kwashe kusan minti 30 kafin massages suka fara shigowa daga ɓangarensa

“Ki shirya zamuje Unguwa dake a weekend ɗin nan”

“Ina da karatu” ta tura masa amsa cikin fusata

“Ifty ni fa mijinki ne ,talk to me with some kind respect ,zamuje India a week end din nan umurni ne!”

“Mr man kana dawo da hannun agogo baya ,nasan dai cikakkiyar matar aure bata taɓa zama a Hostel ta baro ɗakin mijinta …then wani matsayi ka ajiye Ni a zuciyarka ,haryau ka kasa accepting ɗina a matsayin mata ,Ni kam ban zama ball ba da kowai Tom and Jerry zai bugani ba….” thumb up Lili ta mata wato abunda ta faɗa masa yayi daidai
shiru yayi yina ta maimaita rubutun ta ya rasa amsar da zai bata

Haushine ya cika ifty ta kama kan laptop din zata rufe kawai sai ga message ɗin sa ya shigo .

“Ban taɓa driving wata ɗiya mace a jirgi na ba,sai ke

Ban taɓa barci gado ɗaya da wata mace ba ,sai ke

Ban taɓa gabatar da wata mace ga mahaifiyata ba ,sai ke

Ban taɓa………(Yanke maganar da zai yi kawai yayi daganan ya ɗaura da bata tsatsauran umurni)
Mrs mie ki shirya week end ɗin nan zamuje India duba jikin umma za’a bata sallama upcoming Monday.”

Yina tura mata saƙon yayi switching laptop ɗinsa gabaɗaya ,yinajin wani irin matsananciyar kewarta na damunsa ,Tunzurashi da tayi ya sa masa azababben ciwon kai .

Dafe kai kurum yayi yinajin wani juwa na ɗibansa
“Bakisan abunda naji ba a lokacin da na hango maƙallallun hawaye a ƙwarar idonki ba….Bakisan wuyar da kika gana ma zuciyata ba ,for the executive 15 hours banji ɗuriyarki ba

Ina tausaya maki Ifty ,banaso in gwada maki sex style ɗina amma so lokaci yayi da zan gwada maki muhimman turakun zama da mohammedul_Adnan

 

 

 

*Mu haɗu a kashi na Uku*
Note that : Banana Island Littafin kuɗine Regular 300# vip 500# special 1k
Zaki iya biya ta katin mtn a tura ma wannan Number
09065990265
ko ta nan bank ɗin
7782217014 , Mohammed Hassana , Fcmb

Joy part ya ƙare mai dakakken zuciya ya biyoni ,don jin kalar lagwadan Sex ɗin da Adnan zai ba Ifty

Shin anya ma zata yarda ta bishi ?

Meye makomar wannan auren????

*Kiyi gaggawar Mallakar naki Kar ayi tafiyar babu ke….*

Oum Aphnan
Luv u all️ _*BANANA ISLAND*_
_(Billionaire’s paradise)_

Book 3
Page *P*
Free

Na…
Oum Aphnan ✍

“`Idan Baki karanta Book 1&2 ba bazaki ,fahimci Book 3 ba,Salon Book 3 zai sauya ma na baya shiyasa nayi masa free pages for you guys to be radiated“`

Back to top button