Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 65-66

Sponsored Links

………….. Alhamdulillah Rayuwar tayi dai dai a wurin wainnan ma’aurata khaleel a kullum cigaba yake samu cikin Naziya ya girma sosai ta shiga wata na tara khaleel kullum cikin shopping din baby yake har online yaga sababbi sai yayi oder daki guda ya ware ya shirya kayan harda painting dakin anyi shi irin na dakin yara gadaje hudu different design itadai tace Abubuwan sunyi yawa momy tace ba ruwan ta tabarshi yayi idan taga wani Abu ma ita ke tunamai ya siya, tace “Momy toh ni ko kyalle bai siyamin ba sai baby. “Dole ne wannan kwantar da hankalin ki. Saidai momyn ta siya miki ina zaki kai kaya wasu ma fa ko kalarsu bazaki iya tunawa ba a cikin akwatin ki madam. “Kaifa akwai Wanda yakai ka tara tsumma ko bazaka saka ba,wainnan na Aure ne ka shirya zaka hada akwatunan haihuwa yaro. “Kai lallai zan hado set biyu kuwa harda na Amarya. Yafada ya gudu domin tsokana don yasan ta tsani kalmar Amaryar nan, “ba ason kayan tom. “Ke dalla har yau baki gano halin shi ba ya gane kina nuna kishin kine shiyasa yake tsokanar ki share shi Amarya sai dai yajira ta Aljannah. , momy kafa ta warke tsab zumunci tsakanin ta dasu inna Abun ba’acewa komai, yanzu ta Ajiye aiki tunda tayi jinya, don haka takan ware lokaci kawai domin fita ziyarar y’an uwan ta, ta dunke sosai da gidan kanin mijinta nata wato Alhaji Muhammadu, Rayuwa ta koya mata darasi mai zurfi harta haddace, da kanta idan taga mai bukatar taimako tana taimaka mai, har gidan su Fauziya taje tabawa iyayen ta hakuri sosai suka ce bakomai ai haka Allah ya tsara, Fauziya na nan na aikin ta tasamu wani Alhaji mai mata daya zasuyi Aure abinsu, don haka Rayuwar ta natafiya y’an da Allah ya tsara mata, ta hakura da Khaleel domin tasan baya ta ita, in akwai mace guda a rayuwar shi to itace Naziya, baya ganin wata mace a suffar mata sai Naziyan shi,

Cikin gidan na koma tana zaune a tsakiyar falon ta, tayi kiba sosai ta bude ga kyau da shekinta na nan sai ma kar’i, da tayi, cikinta yayi katoto dashi kafafun ta sun kunbura, rigar less ce a jikinta fubu domin yanzu sune suturar ta, sukawai take iya jin dadin su, madara da milo ta kwaba wuri daya tana d’an gwala,
Momy ce ta shigo dauke da plate din tuwo da miyar shuwaka, tana jin sallamar ta tafara kokarin boye d’an cup din madarar ta, “turus tayi tace ” fito da Abinda kike sha ingani. d’an tura baki tayi tace ” kai momy bafa komai bane madara ce. ” wato bazaki rufawa kanki Asiriba Naziya, anfada miki nauyin babyn nan ya wuce misali ki rage ciye ciyen nan bakyaji. matsowa tayi ta Ajiye tuwon tace ” mikon nan dama nasan tunda najiki shiru anan akwai Abinda kikeyi to nagano ki ai.
Sallamar shi ne yasa momy tayi shiru tareda juyawa gefen shi ” jinan Ibrahim yarinyar nan zata koma gefe na harta haihu tunda bazaka daina bata Abinda na hanaka ba yazaka rika biye mata kalli y’an da take Kara kunbura kullum.
“Wallahi ba ruwana momy ni ba Abinda nake bata impact nakwashe duk madarar dake gidan nan nima na hakurada shan shayin. ” ina ta samu wannan tom. Ta nuna mai wadda ke cikeda cup. Murmushi yayi mai kyau ya matso kusada ita ta dunguri kanta ” look baby karkija momy ta rabamu akan wannan Abubuwan da kike yi kinga yanda kika zama kuwa kinkusa biyuna fa, please ayi hakuri da madarar nan. Yafada kamar mai lallashin Y’ar yaye, ” wallahi inban shaba jinake kamar numfashi na zai fita don Allah kubari inrika shan kadan bada yawaba. Kallon momy yayi da fuskar tausayi ” momy ki taimaka mana kinji.
Tsaki tayi ta tura mata kwanon tuwon “sakko ki mike kafafu kici Wanda zai wanke miki yaro da nono tunkafin ki haihu maza. Tana tura baki ta sakko kasa,
Ta wuce kitchen din ta domin kawo mata ruwa, yayi saurin zama, ” baby lokacin tashi office baiyi ba fa nadawo. Dago sexy eyes dinta tayi bayan tasa lomar tuwon ta tace ” why? Duk da tasan me ya dawo dashi. “Oh don’t pretend like you don’t know, kwana nawa rabon da kibarni in huta, nakasa hakurine nadawo. Ganin momy yayi shiru, ” kai matsa mata taci abincin ta tunda kai baka lurada taci bataci ba. “Momy nima fa bawanda yadamu da damuwa ta me nadawo yi meke damuna ba Wanda yadamu nazama maraya tun yanzu, toh inta haihu ba mai komawa kaina ma gaba daya. “Ka shirya ma gida zataje wanka tunda ni kun raina ni nafadawa Kulu harma nafara yimata shiri tana haihuwa daga Asibiti sai gidansu sai tayi Arba’in zata dawo.
Dariya yayi harda jingina a jikin kafadar Naziya kafin ya kalli momy da duk sun zuba mai ido suna kallon dariyar rainin wayan shi, “Amma dai momy wannan story ne kawai ba gaskiya bane? “Tatsuniya ce kaji, zaka gani in lokaci yayi. “Gwara ta zamo ta tsuniya kuwa don bazai yuwuba, ina ban Y’ar da ba wallahi, yaron nawa yazo duniya baza akawomin shi gidan ubanshi ba afaramin yawo dashi ina. Tuwon ta takeci tana kallon y’an da ya hakikance yana zuba rashin kunya akan d’an da baizo duniya ba. Saida taci dayawa momy ta kwashi kwanonin tafita ta kyalesu, yana ganin ta fita ya mike zunbur ya dagata sama daga ita har katon cikinta, yayi cikin dakin su na bacci.
Tsayar da ita yayi ya na kallon katon cikinta abun na burgeshi sosai, wayar shi ya ciro yafara daukar ta hoto, yasaba yanzu kusan kullum sai ya mata hotuna saboda gani yake ba macen da ta taba burgeshi da ciki sai Naziya cikin yakara mata kyau da cikar haiba, tazamo hamshakiya. “Nidai kadaina daukata haka bayan nayi muni wannan cikin yasa duk nazama wata giwa. “Keke waya fada miki? Ai bazaki gane y’an da kike burgeni bane badon na matsu inga baby naba da nace kiyita zama ahaka ina more Idona, look at my wife, ba raini kinga duk Wanda ya ganki yasan yes bakya tareda lauzy man nacika ki ta ko Ina. Yafada yana wani bubbudawa.
Rigar ta tube domin zafin dake taso mata duk da iskar Ac dake hura ko ina a cikin dakin, tarage daga ita sai under wear da bra, ” nima ai ba raguwa bace kasani nima nayi kiwon ka look at you harda wani tunbi ka Ajiye fa, ka kwashe min farin fata ma. ” I agree wallahi, domin bakaramar madara nake kwankwada ba, dole aga canji a jikina baby kedin ba ta wasa bace shiyasa kike juyani yadda kikeso, to yazanyi dole in lallaba ki. Yafada yana shigewa jikinta cikin dabara da wayau, tace ” banson wayau fa da dadin baki. ” Allah ba wayau sai gaskiya, nidai a samma Almajiri yana bara don Allah. Yafada yana mai dora hannun shi saman kirjin ta tareda hade bakin su wuri daya.
Na janyo y’an kafafuna na gudu domin banason ayi aika aika ina wurin,
Sai bayan hour biyu suka fito cikin wani adon yana faman tarai rayar ta,
Ta lafe a Kirjin shi tana nishi ” nidai kajamun bayana na ciwo har wani budewa naji yanayi. “Sorry sorry kinga ki wartsake kafin momyn ki ta hauni yanzu da fada, guduwa ma zanyi office inada aiki da yawa, muje in rakaki wurinta in wuce.
Daga Kofar gidan ya juya ta shiga tana yatsunar fuska, momy na zaune tana kallon labarai a Aljazera tayi sallama.

Can karshen kujera takoma ta zauna dakyar, momy ta kare mata Kallo tace ” kai zamani yazo ya wahalar da ita da tsohon ciki abanza, kai khaleel ai dama ina ganin d’an banzan yaron nan nasan me yadawo dashi gida. A zuciyar ta take surutun ta saida taga ta zamo kasa tareda janyo trow pillow ta kwanta akasa, tace ” ina shi Ibrahim din? ” ya koma office yanzu. “Hmmm. Taci gaba da kallon ta saida taga juyin yaki karewa tace ” ke meke faruwa ne? “Bakomai momy. ” idan da akwai matsala kifada muje Asibiti yanzu kinji. “Aa babu komai momy.
“To tashi a kasa ki shiga cikin daki ki kwanta kinji kar jikin ki yayi ciwo. Dakin momy ta wuce taje ta haye gadon ta ta kwanta da kyar, maganar gaskiya khaleel yaja mata domin jin bayan ta takeyi kamar zai cire, sai can taji ya tsagaita ta d’an yi Ajiyar zuciya ta gyara kwanciya, tana tunanin halin khaleel, kamar magnet haka ya koma mata gashi baya taba fushi indai akan hakan wannan Abun ne sai yasan y’an da yayi ya mata wayau ya more, All this months bayan dawowar su daga bangkok yaki Y’ar da yaje ko nan da can saboda ita duk da yanada appointment dayawa bai Y’ar da ya tafi ba sai dai yayita wakilta manager dinshi, domin yaso yaje da ita momy ta hana, saboda cikin tace ba inda zaije yakai mata yarinya da ciki sai ta haihu.
Har bacci mai dadi ya dauketa ta zabura tareda tashi zaune domin wani irin amsawa bayanta yayi da ma marar ta bana wasa ba, tuni ta sakko tsaye tafara kai kawo, momy dake falo duk hankalin ta nakan ta tataso ta shigo, y’an da taganta ne yasa tace ” ke nakuda kikeyi, kinga y’an da kike gumi, ina kayan haihuwar taku ko baku hada ba ne? Tace an hada suna side din mu Amma momy ai EDD na bai kaiba.
“Banson shirme nidai ina zuwa ta wuce Abinta cikin sauri ta dakko Karamar akwatin ta fita da ita ta. Driver ta Kira tace ya gyara mota zasuje Asibiti,
. koda ta koma abun fa da gaske ne duk ta gigijce tayi saurin saka mata hijabin ta ta rikota suka fito tana yimata sannu,

Ba bata lokaci suka karbeta lokacin tanajin kamar marar ta zata fashe saboda azaba, sai salati takeyi tana Addu’a , Sukace ai Abun yazo gadan gadan don haka sai labour Room, saboda sauri ko wayar su bata kwaso ba, bare ta Kira khaleel din, shikuwa y’an da yaga Tanayi yasa yayi ta Kiran ta bayan fitar shi, wayar kuma na gefen ta, bata dakko ba don tayi ta ringing shiru. Haka ya daure yaci gaba da aikin dake gaban shi domin bayaso ya kuma barin office sai ya gama, can ya kasa daurewa ya Kira layin momy shima shiru lokacin tana Asibiti itama tata na gida.
Bai kawo komai ba ya ci gaba da aikin shi,
Bayan minti talatin ba tareda doguwar nakuda ba ta sunkuto katoton d’an ta kyakkyawan gaske mai farin fatar ta da fuskar ubanshi,.

Nurses sai santi sukeyi suka shirya su duka uwar da d’an, aka fitowa da Momy da sunkucecen miji, ta karba jikinta na rawa tace “Ahmed dina ya dawo kalle shi sak Ahmed saboda fatar shi da idanun shi, taganshi sak d’an ta mai hakuri, wasu irin hawaye suka zubo mata a fuskar ta, ta fara tofeshi da Addu’a tana Allah ya sa ka gado hakurin mai sunan ka. Momy da karfin hali tuni ita ta lakaba mai suna. Saida aka fito da Naziya dakin hutawa ta tuna da ita taga miji jiki na rawa bakinta har kunne sai lokacin ta tuna da zancen waya, tace ” kinga saboda rudu ban dakko wayata ba. Saida ta shiga sadin da aka kwantar da ita ta shinfida yaron kusa da ita tace “Sannu Naziya kinji Allah ya miki Albarka kinga Abinda Allah ya Azurta mu dashi, bari insa driver ya dakko min waya ta a gida nabarta kema taki na can kar khaleel yakira bai san halin da ake ciki ba.
Ta fito tafadawa driver wayar ta na falon ta yasa mai aiki ta bashi ya kawo.
Yana shiga harabar gidan misalin karfe hudu khaleel na shigowa da motar shi, badon ya gama ba yadawo sai don yakirasu basu dauka ba, fitowa yayi cikin sauri ya gaida khaleel din yace “ranka ya dade su Hajiya na Asibiti yanzu ma wayarta tace indakko mata.
“What Asibiti? Meyasa tunda ka kaisu baka kirani kafada min ba? Come on bani hanya ya koma motar ya yi reverse ya fita aguje, kardai ya bantalo aiki ne gashi lokacin haihuwar bai gama cikaba sai nan da sati biyu, don haka a high speed ya isa Asibitin, ko wani rufe motar bai tsaya yiba ya wuce da sauri, ganin momy tsaye tana leken hanya ya karasa da gudun shi ” Me ke faruwa momy ina babyn take meke damunta ne? Duk ya rude jikinshi har rawa yakeyi karyayiwa kanshi asara, daure fuskar ta tayi kamar mai fushi tace “kai meye haka tana ciki ga dakin can. Ko jira baiyi ba ya tafi a sittin tabi bayan shi tana dariyar rudewar shi,
Tunda ya tura dakin yayi turus domin ganin jariri kwance a gefen ta yana motsa hannu yana cilla kafafu yana kuka tareda tande baki saboda yunwa.
Idanun shi a waje na mamaki yakasa koda motsi saida momy tace ” ko in shafa maka ruwa ka suma ne? Cikin tsokana, ” momy baby….. my baby…. Da gudu ya karasa ya na kokarin sunkutar yaron ya kasa, “tsaya malam inbaka, kallon Naziya yayi data runtse idanun ta saboda marar ta dake ciwo kadan kadan, karbar shi yayi bakin shi har kunne saboda murna da farin ciki ya zauna gefen ta “baby look at our baby yafada yana kallon kyakkyawan yaron shi tareda riko hannun Naziya daya ya naji kamar ya mayarda su ciki, kukan da yaron yakeyi ne yasa ya ce “momy ko yunwa yakeji ne kinga y’an yake bude baki yana kuka. Yafada yana kallon jan bakin yaron d’an mitsili dashi,
“Ai wannan Yaro zaiyi ci tun da yafito yake wannan tande baki, ga uwar na fama yabari ta d’an huta sai a wanke nonon yasha. “Sai an wanke me za awanke they are clean momy tabashi kawai. Yafada yana kokarin kwantar da yaron, momy tabishi da kallon bakada ta ido, shi ko a kwalar shi, “kai bari ta huta kawoshi inbashi ruwan zam zam da Zuma.
Ta bude kayansu ta ciro wani d’an mitsilin cup da spoon ta fita ta dauraye ta dawo ta bude zam zam da kwalbar Zuma mai kyau ta diga ta zauna tareda cewa “mikon shi saika tashi ka Sanar wa su kulu da gidan kawun ku dasu zarah.
Cikin doki ya mike ya fara kiran number Malam suka fara gaisawa tace mikon nan don tasan baida kunya sai yanzu yayi Abinda zai sata a kunya ita, ta karba tace “Sannu malam ya kokari’ to dai kayi Aboki kafadawa kulu tasamu miji na kwace. Yayi hamdala tareda godewa Allah yace toh Masha Allahu Allah ya barmana ya raya bari in shiga infada musu.
Kafin kace me kowa yaji wannan haihuwar kafin wani lokaci Asibitin ya cika makil da d’an gi saida momy ta koreshi, su Shukrah Aunty Aisha Aunty Raliya su Zarah sai hira akeyi, ganin yaron na d’an gine Asibitin na cika likita yace zasu iya tafiya ai komai normal ne daga, d’an har uwar don haka zuwa magrib sun gama hada kayan su ta kirashi bayan ya idar da sallah tace yazo ya kwashi Naziya yakai gidan malam an sallame su. Ta kashe waya, Aunty Zarah dake Rungume da yaron tace ” tab Aunty bakiso zaman lafiya Khaleel din ne zai bari atafi da Naziya wani wankan gida y’an da yake wannan rawar kafar.
“Yoh biyemai zamuyi, kinsan y’an da nake fama dashi ne ni zanso taje tayi wankan ta mai kyau a gida cikin natsuwa. “ai momy tunda kina nan da kinbarta malam bazai bari ba ma don bayason wannan al Adar. Inji Raliya, ai kuwa malam ya Kira yakai karar Momy yace ” ai baza ayi haka ba Ibrahim bana bin wannan Al Ada, dakinta zatayi wanka kaji karka damu.
Yayi Ajiyar zuciya ya buga mota yayi gidan shi saboda yasan yayi tsiya, suna jin shiru momy tasa zarah ta Kira driver ya kwashe su, tace wato saboda nace yazo ya kai ta gidan shiyasa ya gudu ko? Toh tun baizo duniya ba nake hawa mota d’an ubanshi, su Aunty sai dariya sukeyi itadai tayi tsit tana jiran karon su dashi, don ita tagama murna zata je wurin Inna, don wannan ce kawai damar ta idan ta wuce shikenan sai dai ziyara aje adawo gashi idan taje gida baya barin ta ta dade ya rika damun ta kenan ta dawo gidan shi kamar zata gudu,

Suna shiga harabar gidan sukaga motar shi momy tace su wuce nata gidan da Naziyar zataga tsiya, haka aka kaita har gadon momy Aunty Zarah ta shirya ruwan zafi tareda na jariri, Momy tace” Raliya taimaka wa Naziya tayi wankan bari inyiwa yaron. “Toh tace ta taimaka mata tayi wankan tsab ta gyara jikinta su Aunty Aisha suka gyare gadon tareda baza turare ko Ina na baza kamshi, Aunty Zarah ta shiga kitchen ta samu mai aikin ta shirya farfesun naman kaza da yayi lugub ta hado mata da tuwon shinkafa da miyar Agushi, tana fitowa ta shirya, momy tace su Aunty Raliya suje su kwaso mata duk Abinda zata bukata itada yaron su kawo nan kafin su wuce domin dare nayi.

Oga khaleel na can yana tunanin ta inda zai bullowa Al amarin yaji sallamar su Shukrah, tashi yayi cikin jin kunya dama a shirye yake kawai yana tunanin rigimar da zai tarar yagansu, “Aunty yaushe kukazo? Yafara kame kame ” ai mundade da dawowa kayan Naziya zamu kai gefen momy tana can itama……….. 🖊

Back to top button