Adandi 3
*3*
Dagowa yayi fuskarsa daure tamau wanda hakan yasa gabanta faduwa be amsa Mata ba bai kuma daina kallonta bai cikin kallon dake nuna asalin qyamarka da abinda kake kallo, daqyar ta iya tattara yawun bakinta tace “in dama nazone saboda na baka hqr akan abinda ya faru jiya wlh tun jiya na kasa samun nutsuwar zuciya inason idan nayiwa mutun laifi na bashi hqr ya nunamin yafiyarsa gareni nasani tsakanin Allah da bawansa akwai yafiya da gafara Amma tsakanin bawa da bawa Allah baya shiga harsai sun yafewa pls don Allah kace ka yafemin Abdul”
Ta fada tana durqusa gwiwarta a qasa, ajiyar zuciya yayi cike da mamakin yarinyar saukowa yayi daga saman motar da yake ya juya zaibar gurin saboda mugun haushinta da tsanarta yakeji ya tsani mace mara kamun kai wadda batasan ita halitta ce mai daraja abar kawwamewa da alkintawa ba Amma tazo tana sarayar da qimarta da mutuncinta tana tallan surarta da kyawunta.
Har yayi nisa da ita ta daga murya da sauri tace “na roqeka badon niba don darajar Annabi Muhammad (S.A.W) kacemin wani abu Abdul”
Murmushin takaici yayi yace “kije ki qara ilimi akan wanene Annabi Muhammad wanne saqo yazowa da duniya sannan wanne dokoki ya shimfidawa matan musulmi tukunna kafin ki hadani dashi” memakon taji ciwon mgnrsa sai kawai tayi murmushi tace “na gde da hakanma ” kafin ta gama rufe bakinta har yayi mata nisa bayansa tabi da kallo tana murmushin jin dadi tare da qarfafawa kanta gwiwa.
A kasalance ta nufi faculty dinsu tana shiga samarin sukayo Mata cahhh suna tafi suna kiran sai Samha Allah dai ya biya Uwar dakinmu kina bada kala Hajiya aci gaba da bada wuta” murmushi tayi kawai ta nemi guri ta zauna wannan karon ta saurari lecture sosai musamman da malamin yake bayani akan alamomin kamuwa da son wani abu da kuma na qiyayya sai taji kamar don ita yake lesson din basu fito ba sai 12:30pm dake course din three credit ne suna fitowa suka nufi capteriar wani restaurant suka shiga sukayi order ta abin da suke buqata suka faraci daga idon da zatayi ta hangeshi shida abokansa a zaune a wani table dake nesa dasu kadan Ja’afar Nasir Khamal Mansur saishi na biyar ajiye cokalin hanunta tayi ta dora hanunta akan hannayenta tana qare masa kallo ta cikin glass din dake idonta saida suka gama Rams tayi mata mgn tajita shiru juyawar da zatayi taga Abdul din ta zubawa ido duk da akwai glass a idonta takaici ne ya kama Rams ta jijjigata sannan ta dawo hayyacinta ta miqe ta cire kudi a aljihun Jakarta Rams tace “namu da nasu Menson”
Tana fadin haka ta fara takawa zata fita daidai lkcn daya dago suka hada ido duk da nata a cikin glass yake, tsaki yaja tare da ajiye cokalin hanunsa Ja’afar ya kalleshi yace “yada tsaki haka?” Sake daure fuska yayi yace “na tsani mace ballagaza a rayuwata yarinyar nan tana daya daga cikin mutanen da da zaa bani dama zan kasheta saboda batada wani amfani sai yada fasadi da sabon Allah a doron duniya bata boye fasiqancinta a fili take fito dashi” dariya dukkansu sukayi sukace “Samha Sa’ad Dandoki kenan” Ja’afar ne yaci gaba da cewa “yanda yarinyar nan take burgeni bata shiga abinda babu ruwanta sannan batada hayaniya dadin dadawa qwaruwa ce ta wajen karatu sannan tanada naci akan duk abinda tasa a gabanta bata da girman kai ga wanda yayi mu’amala da ita amma tana da kwarjini, yar gatace sosai ta gaban kwatance ita kadai iyayenta suka haifa mahaifiyarta Shuwa’arab ce babanta kuma Bakatsine ne suna sonta fiye da duk hangenka Abdul tunda ta taso a rayuwarta batasan fada ba balle duka batasan babu ba komai takeso shi take samu ciki harda karatu anan B.U.K itace ta dage sai tayi karatu anan kamar yanda kaima ka dagewa mai martaba saida ya qyaleka ya turoka kake basaja Abdul Samha tantiriya ce ta gaban misali zata kashe ko nawane wajen holewa da rayuwar nishadi Daddynta yana Abuja da Mamynta ita kuma gdanta yana nan Janguza siya matashi Daddynta yayi kawai saboda tayi zaman karatunta anan Samha bata less kuma bata zina kamar yanda kowa yake tunani barta da lashe² da tabe²nta click dinsu yan lesbian ne kuma mazinata ne amma banda ita saboda alqawarin data yiwa mahaifinta zatayi komai amma banda shiga qungiyar asiri banda zina banda less kuma banda shan Alcohol bayan wannan har hodar iblis wani lkcn tana shaqa aminiyarta Rams itace take bani wannan lbrn sama da shekara daya kenan dana nuna inason rayuwa da ita sannan ta gargadeni koda wasa kada na furta mata kalmar so saboda abune me sauqi taci mutuncin mutum akan so kullum furucinta daya ne abune me wuya ta bada so amma idan taba dashi bata qwacewa wannan shine kadan daga cikin tarihinta saboda na lura kai baka sani ba”
Ajiyar zuciya yayi tare da yarfe hanu yace “wannan ba abinda ya shafeni bane amma wlh qaryane akayi maka wannan yarinyar tasan maza wlh bazata rinqa wannan tantirancin a banza ba” nan ya kwashe duk yanda sukayi da ita tun daga jiya har kawo yau ya sanar dasu.
Wata uwar ashar Nasir ya saki yace “Abdul kanada lucky a rayuwarka tunda har Samha ta bigeka a mota ta tsaya kuma harta qara binka domin baka hqr da kanta yawanci saidai ta tura yaranta subawa mutum hqr wannan shine tsarinta” wani kallon banza ya watsa musu yace “ku dama a gurinku saa ce tunda halinku daya nikuwa a gurina asara ce banga wani abun burgewa ba don wannan karuwar yarinyar ta shigo rayuwata shine har na zama me sa’a?” Khamal ne ya cafe da cewa “yess ni ta kulani ma mana aida naji dadi Samha fa ake fada maka babbar yarinya yar ministan kudi ce fah su qasar takeyi dasu tunda tazo skull dinnan bata tabayi session biyu da mota daya ba kuma naji wasu ma sunce bata taba maimata sutura ba”
Miqewa yayi batare da yabasu amsa ba don ya gaji da shaqar kayan takaicin nan nasu suma miqewa sukayi suka bisa suka fita daga capteriar suka nufi Department dinsu suka fara daukar darasi.
A bangaren Samha kuwa rayuwa ta fara sauya mata duk abinda take daukansa me sauqi a baya yanzu shine yake bata wuya abinda take dauka jin dadi yanzu ta fahimci ba shine jin dadi ba asalin jin dadi yana tattare da samun soyayyar abinda kakeso gskyr Dr Zaks da yace babu abinda yakai soyayya dadi kasancewa da abinda kakeso yafi komai dadi da sanya farin ciki itama shaida ce saboda yanda takejin dadi da nishadi hadi da farin ciki Idan ta hangi Abdullah ko daga nesa ne.
Ta mayar da gurin zamansa yana nazari gurin zamanta takan zauna ita kadai a gurin ta dauki handbook tana dubawa wanda a zahiri bawai karatun takeyi ba kawai kallonsa takeyi lokuta da dama takan gwada yi masa mgn amma yakan shareta kamar bayajin me take cewa hakan yana damunta amma bata taba nuna masa ba itadai kullum burinta shine ya fahimci halin da take ciki ko ya tausaya Mata.
*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk_*