Hausa Novelskawali Ne Hausa Novel

kawali Ne 13

Sponsored Links

*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

Related Articles

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*13*

 

“Rayhana tun muna asibiti hankalina yaƙi ƙwanciya,wai yaushe rabonki da ganin aladarkine?”cewar mama cikin damuwa.

Wasu hawayene masu zafi suka zubo mata na tausayin kansu tace!mama watanni uku kenan rabona da ganinta”tunkan ta ƙarasa mama ta fashe da kuka.

A hankali rayhana ta rarrafa jikinta ta rungumeta suna kuka me tsuma zuciya, tace bakinta na rawa”mama ciki ne dani ko?”

Gyaɗa mata kai mama tayi tana kuka tace”wannan yaro ya cucemu rayhana kuma har abada bazamh yafe masa ba,ya cutar damu sosai arayuwarmu amma mun barshi da Allah”Cewar mama kamar zata shiɗe dan kuka.

“mama zani asibiti aciremin mama wannan abun kunya da wanne ido zamu kalli mutanen garinnan?”ta faɗi tana kuka.

“kul rayhana karki sake ki fara,da kunyar lahira gwara ta duniya,koda wasa karki je ki zubar inkikayi haka keda Allahnki,ƙaddararkice haka inaso ki amsheta hannu biyu.ki kuma barwa Allah komai”

Tunda mama ta fara magana rayhana kuka kawai takeyi,dan tarasa da wanne harshe zatai magana.

*********

Tun daga wannan rana suka ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da firgici kullum cikin kuka,mamace ke ƙarfafa mata guiwa.

Cikin na wata Shida amma ya fito sosai,duk da ta dena fita amma hakan be hana ƴan garin gane halin datake cikinba aka fara yidasu,da kalamai marasa daɗi sede su toshe kunnansu.

***********

Acan Abuja ko an ɗaura auran rayhan sa nusayba tuni suntare agidansu,sede adarensu na farko yasamu ragowar wanice dan anrigashi.

“Babe kayi haƙuri dan Allah wallahi sone yajani”cewar nusayba bayan gari ya waye.

Murmushin ƙarfim hali rayhan yayi yace”karki damu nusayba Allah yafe mana baki ɗaya banida matsala da hakan kinji ko”

Kallonshi tayi baki buɗe,tace”kuma kana kishina kuwa babe?”

“Sabida banyi masifa ko na sakekiba shine kikayi zaton hakan da nayi ba kishi,da kuma nayi reaction kice bansan ƙaddara ba ko”ya faɗi yana murmushi.

Bata iya cewa komaiba, yatashi ya wuce toilet yana mata murmushi wanda iya fuskarsa ya tsaya can ƙasan zuciyarshi kuma wani irin zafi take masa yana ƙara danasanin rayuwar da yayi abaya,yasan duk hakan ne yaja masa.

Nusaiba sosai taji daɗin yafe mata da rashin ɗaukar abun da zafi da yayi,hakanne yasa ta ƙara miƙe ƙafa ita tayi miji.

Kullum Rayhan da tunanin rayhana yake kwana yake tashi ta hanawa zuciyarshi sukuni,kuma yana tsoron zuwa gareta kar ta sake jin haushinsa,so yake ranta yay sanyi sannan ya ƙara koma mata.

Ɓangaren kasuwancin mahaifinsa kuma beda sani sosai akai hakanne yasa ya yankawa kanshi visa zuwa dubai dan yasamo karatu akan fannin.

Nusaiba taso yatafi da ira amma yaƙi acewarshi karatu yajeyi ba yawo da mace ba ko zuwa gun shaƙatawa.

Haka ta haƙura ya shirya yayi tafiyarsa,bisa sa albarkar mahaifiyarsa.

 

COMPLETE ƊINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Back to top button