Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 26

Sponsored Links

*26*

 

Kamata tayi ta dorata saman gadon tace “kiyi hqr kada wannan hatsaniyar ta dameki Aisha laifin iyayenki ne da suka nisanta ki da gdannan tun farko da tuni kin saba qaramin rikici bazaike daganki hankali ba amma yanzun ma tunda kika shigo babban gda zaki saba kiyi hqr da yanayin mijinki wani irin baudadden mutum ne nina haifi Abdullahi amma tsoro yake bani saboda tun yana qarami shi mutum ne me kafiya da rashin yarda nayi mamaki matuqa lkcn da yazomin da lbrn yanasonki sannan ya qara zuwarmin da zancen abinda ya faru tsakaninku ki kwantar da hankalinki baki da wata matsala a gdannan ki saki jiki dani da yayyanki da qanwarki kuyi rayiwa ta zumunci zamuyi farin ciki da hakan kinji don Allah kada ki bamu kunya munasa ran jinin Hussain ya danne na Lubabatu a jikinki Aisha”

Related Articles

 

Kuka takeyi sosai tanajin wani ciwo da baqin ciki a ranta ko kadan batason mgnr data shafi Abdul ji takeyi kamar ta hadiyi zuciya ta mutu saboda haushin auren da takeji tayi alqawarin duk yanda zatayi sai tayi ta kubtar da kanta daga sharrinsa don ta lura idan tayi masa sanyi baqar wahala zatasha a gurinsa waishi miji har yana da bakin da zaiyiwa uwarta rashin kunya.

 

Miqewa fulani Amina tayi ta fita daga dakin saboda jiyo hargowar Mamy a parlour tana fita ta shaqota tana zare ido tana billahil lazi Amina kinyi kadan kece munafukar da kikaje kikasa mijina yayimin kishiya to wlh ba kishiya ba ko uwarki ce zata dawo duniya ki aura masa sai tsinannen tambadadden debabben dan naki ya saki yata tunda bake kika haifamin ba ba kuma uwarkice ta haifamin….”

 

Dad ne ya daka mata tsawa yace “Lubabatu ki kiyaye ni aurene an daura baki Isa kuma ki hana ba kuma wlh naji wata rigima ko tashin hankali ya bullo a cikin gdana ko gdan Mainah Abdu zakisha mamaki na fara gajiya da rashin albarkar ki Lubabatu….” Daga masa hanu Mai martaba yayi yace “ya isa haka Hussain Amina aje a fara shirin miqa amarya dakinta nayi nayi da Abdullahi ya zauna a bangarensa na gdannan amma yaqi duk da haka zasu zauna anan sai an gama bikin al’ada tukunna sai su koma gdansu” zare jikinta tayi daga na Mamy ta juya ta nufi bangaren bayi ta kira wadanda suke da alhakin shirya Samha sukazo daqyar ta lallabata ta tashi akayi mata wankan aure kamar yanda al’adar take sannan akayi mata wankan nono aka kuma yimata wankan turare kai ranar Samha taga bidiri bayan an gama wannan sannan aka kuma zaman kamun farko akayi mata wanka aka shiryatabaayi Mata kwalliya ba saida akayi sallar Isha.

 

Sannan aka qarasa shiryata ana tsaka da shiryata tana kuka Mamy ta shigo a zafafe ta finciketa daga tsakiyar mutanen dake dakin ta nufi bangarensu da ita ta zuba uban sauri kamar zata tashi sama itadai Samha harda gudu saboda irin saurin da Mamy takeyi duk abinda yake faruwa akan idon Dad saida ta shiga ta sanyata a daki ta kulle ta zauna a kusa da ita tace “wlh azeem akan yaron nan tsaf zan tsine miki albarka saboda na fahimci kema sun shanyeki kamar yanda suka shanye ubanki to bari kiji ni lubabatu nafi qarfin iskancin dangin miji bari muga dan iskan da zaizo yace nabashi ke ba kwanan turaka ba ko kwanan mene yaudai bazakiyishi ba ban haifawa wannan dan iskan yaron yar da zai kwanta da itaba duk abinda suke taqama dashi nafisu suzo su sameni daidai nake da kowanne dan iska an gaya musu Gidado damuna yayi da har zan daga hankalina don yayi aure auransa din banza”

 

Haka Mamy ta rinqa tujararta can sukaji ana buga qofar miqewa Mamy tayi tace “wayene” fulani Hadiza tace “nice Shuwa bude kiji wani abu” budewa tayi ta shigo ta mayar da qofar ta rufe ta juyo tace “banji dadin abinda kikayi ba kinsan halin yaron nan ba kunya ce dashi ba gashinan zaizo yana zuwa ki bashi matarsa sauran mgnr ni dakene wlh kowacci tuwo damu miya yasha tsura Shuwa nice fa kema kece bashi ita ke kuma…” Ta damqi kunnen Samha tace “wlh kika yarda wani abu ya shiga tsakaninki dashi zaki gauraya damu” itadai Samha kuka kawai takeyi saboda gabadaya tsoro ma Mamy take bata ta lura kamar baa cikin hayyacinta takeba daidai lkcn sukaji guda a bangaren miqewa Samha tayi da sauri mutanen suka shigo mutum ukune harda amaryar Dad ta hudu suka shigo sukayi sallama a parlourn bude qofar su Mamy sukayi suka fita suna fita suka gansu Mamy tayi baya da sauri tace “meye suwaye ku?” Cikin nutsuwa sukace yar’uwarki muka rako ku gaisa” batace komai ba taja numfashi ta juya ciki daidai lkcn da Abdul da Dad suka shigo kai tsaye dakin da Mamy ta shiga suka shiga babu kunya Abdu ya matsa har gaban gadon ya dago matarsa ya nufi qofar fita ya juyo ya kalli Mamy ya daga mata hanu yace “mu kwana lfy surukata”

 

Suna fita ta fara qoqarin janye hanunta daga nasa ya riqeta sosai yana murmushi yace “kada kiyimin gardama ko kadan bana daukarta ki kwantar dakai mu gina rayuwa me tsafta kada ki bani matsala Ayshatu na roqeki aurenmu akwai rikici da yawa akansa” daga haka bai kuma cewa da ita komai ba har suka isa inda ya ajiye motarsa ya bude yasata a ciki shima ya shiga suka nufi wani bangare na gdan har yanzu kuka takeyi yanajin kukan nata na taba zuciyarsa sunayin parking ya bude ya fito ya bude mata tana ciki taqi ko motsawa sai jan zuciya da takeyi saboda kukan da taci harta godewa Allah sunkuyawa yayi ya dagota ya mayar da qofar ya rufe yanajin ninkin farin ciki tare da qaunar matarsa da ubangiji ya bashi bayan yasha fama da zuciyarsa daketa kukan rasata wani jan carpet aka shimfida suke takawa har suka shiga parlourn da yake cike da kuyangi suka rinqa zubewa suna kwasar gaisuwa miskilin ko tanka musu baiyi ba balle Samha da yakejan hanunta wata qofa aka bude suka shiga nanma wani madaidaicin parlour ne mayar da qofar dogarin yayi ya rufe ya kuma jan hanunta har saida suka shiga cikin wani madaidaicin daki da aka qawatashi da qaton gado na alfarma.

 

Tsayawa yayi a tsakiyar dakin ya kamota ya matso da ita jikinsa sosai yana sauke numfashi ya sanya hanunsa ya janye alqabbar data rufe fuskarta da ita ya sake mata murmushin sa yace “muje muyi alwala muyi sallar gdy ga Allah daya nuna mana wannan ranar a lkcn da bamuyi zato ba” bai bata damar yin wata mgn ba ya kamata suka shiga bathroom din sukayi alwala yajasu sallar bayan sun idar ya dora hanunsa akanta zaiyi mata addu’a ta janye tare da miqewa da sauri shima miqewar yayi yana kallonta rintse idonta tayi tace “na tsani ganinka Abdul na tsanek…” Rufe mata baki yayi yana murmushinsa na isa yace “nafison duk wadannan kalmomin suzo daga baya yau rana tace a gdan nan ba taki ba gobe itace taki saboda haka zanyi komai batare da kin isa ki hanani komai ba Samha sharadine na fada gobe sai an fita da qyallen budurcinki ya zamuyi yanzu meye mafitar mu?”

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/15, 9:22 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

 

 

Back to top button