Garin Dadi 4
©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*GARIN DAƊI…….!*
*_NA_*
_*UMMI A’ISHA*_
*Wattpad:ummishatu*
*4*
~~~Nidai har naje gida ban daina tunanin wannan bawan Allahn ba domin dagaske al’amarinsa naji ya tsaya min acikin raina amma ban iya faɗawa kowa ba duk da cewa ƙawalli tazo munsha hira domin har bayan mgriba muna tare amma ban sanar da ita ba sai hirar bikina da take ta faman yi tana cewa gaba ɗaya ma ta rasa irin shigar da zata yi ranar, kasancewar tunanin wannan guy ɗin da naji ankira da suna hashim yana ƙoƙon raina shiyasa ban sake nayita yi mata kauɗi kamar koda yaushe ba daga ƙarshe har taso ta fahimta,
“ƙawalli wai ko dai wani abu yana damunki ne?” naji ta faɗa bayan ta zuba min ido, murmushi na ɗan yi cikin ƙarfin hali sannan nima na dubeta ina wasa da igiyar dake gaban doguwar rigar dake jikina mai gajeren hannu,
“me kika gani ƙawalli?”
“to ai na ganki ne gaba ɗaya kamar kinyi sanyi”
“wallahi lafiya lau nake kawai tsabar gajiya ce, yau tunda naje office ban samu kaina ba har lokacin tashi”
“to ya kamata ki kwanta da wuri ki huta, nima bari na tashi na wuce gida, idan yaya faisal yakira a miƙa min gaisuwa”
Harararta nayi na ɗauke kaina ina cewa,
“idan dagaske gaisheshin kike son yi ga no ɗinsa nan ki ɗauka sai ki kirashi”
“kya dai ji dashi”
“ko kuma ke kiji dashi ba”
Hijabinta ta saka tana dariya tare da ficewa daga ɗakin. Ni dai yau gaba ɗaya na kasa mantawa da tunanin wannan makahon saurayin dan hatta yaya faisal ma sai da ya fahimci yau bana jin hira shiyasa ba mu wani jima ba muka yi sallama nikam sai bacci ɓarawo, washe gari da wuri na tashi na shirya domin tafiya aiki, kamar koda yaushe doguwar riga na saka ta atamfa dark purple na yafa purple ɗin mayafi sai zuba ƙamshin turaren blue nake yi wanda ya haɗu da ƙamshin Arabian oud, ina ƙoƙarin fita daga gida bayan na yiwa su Annie sallama naji ƙarar wayata, ganin yaya faisal ne ya sani yin murmushi kafin na ɗaga wayar,
“ko har kin fita?”
“a’a sai dai niyya ka ganni nan zan fita yanzu”
“to shikenan Allah ya kiyaye hanya, idan kika je office za muyi waya”
“babu matsala” na faɗa ina zare wayar daga kunnena tare da mitar kiran da yaya faisal yayi min dan gashi nan sanadiyyar hakan ban samu damar gabatar da addu’ar fita daga cikin gida ba.
Lokaci zuwa lokaci nake duba agogon dake ɗaure a hannuna domin bana son yin latti so nake na fita kamar jiya ko Allah zai sa insake gamo da hashim wanda tausayinsa da son sanin halin da yake ciki ya gama addabar ruhi na da zuciyata gaba ɗaya, misalin ƙarfe 5 dai dai na yamma na fito daga office na ɗauki drop ɗin napep muka nufi hanyar da nabi jiya, sai tsittsilla ido nake yi ai kuwa cikin ikon Allah na hangosu tsaye da wannan dattijon na jiya wanda yace shine yake tare masa abun hawa kullum, agabansu muka yi parking ina kallonsu cikin fara’a na fito ina gaida wannan dattijon,
“yarinya sai dai kuma ban ganeki ba daga ina?”
“Baba Jinjiri itace fa budurwar jiya baka gane ta ba? Wadda muka tafi tare….” jin abin da ya fito daga bakin saurayin ya sakani sakin baki ina kallon ikon Allah,
“eh an yi haka, sai yanzu na shaidata, yarinya ya aka yi?”
“baba na zone mu tafi tare dashi”
“Allah sarki to Allah ya saka miki da alkhairi kinji”
“amin” na amsa ina mai juyawa domin shiga cikin napep ɗin, kamar jiya yau ma baba jinjiri ne ya taimaka masa ya shiga cikin napep ɗin muka tafi, bayan mun fara tafiya naji yace,
“ina yini?”
“lafiya lau, ya makaranta?”
“alhamdulillah” daga haka muka ɗanyi shiru kafin na katse shirun da cewa,
“amma ya aka yi ka ganeni?”
Murmushi Naga yayi wanda ya sake bayyana kyawunsa,
“na ganeki ne ta hanyar jin muryar ki, dama kuma jiya da tunanin ki na kwana, kiyi haƙuri da rashin sakin fuska da nayi miki…. Wallahi jiyan ne raina gaba ɗaya aɓace yake shiyasa”
“ayya babu komai karka damu, amma ai na baka haƙuri dangane da abin da ya faru soo bai kamata ka ɓata ranka ba”
“ba zaki gane halin da nake ji ba a duk lokacin da mutane suka yi min irin abin da mai napep ɗinnan yayi min, makanta tafi komai yawan ƙalubale, kowanne mutum ana iya gane halin da yake ciki idan har aka kalli ƙwayar idonshi to mu ba aga namu idonba bare a fahimce mu…. ”
” babu komai Allah shi ya san dalilin da yasa ya iyo ku a haka ”
Kasancewar muna ta hira dashi kafin na farga sai na ga har mun kawo ƙofar gidan nasu, yana ƙoƙarin ciro kuɗin da zai biya mai napep nace yabarshi sannan na ɗora da cewa,
” idan har babu damuwa kuma babu matsala ka rinƙa jirana kullum zan rinƙa zuwa muna tahowa tare”
Gyaɗa min kai yayi alamun babu matsalar sannan naji yace,
“amma menene sunan malamar?”
“maimunatu (widat)”
“mai tagwayen suna”
Daga haka yawuce nikuma nabi bayan sa da kallo ina murmushin da ni kaina ban san ma’anarsa ba. Yau ma kamar jiya da tunaninsa a raina naje gida haka kuma ban sanarwa da kowa ba sannan tun daga wannan rana muke dawowa tare dashi domin kullum sai na biya ta wurin da yake tsayawa mun ɗaukeshi, yau kam ban tashi da wuri ba har 6 na kai a wurin aiki shiyasa duk nabi na shiga damuwa saboda nasan hashim yana can ta yuyu har ya gaji da jirana, sannan gashi shi ba waya gareshi ba da na taɓa yi masa maganar waya ce min yayi wai waya ta masu ido ce shi bashi da buƙata,da damuwa acikin raina muka doshi inda muka saba ɗaukarsa kamar koda yaushe, can na hango shi zaune ƙasan wata bishiyar maina hannunshi riƙe da wani ganye yana wasa dashi, a hankali na sauka na ƙarasa batare da na bari yaji takun sawayena ba domin saɗaf saɗaf nake tafiya har naje dab dashi, tsayawa nayi akusa dashi ko rabin minti banyi ba da tsayawa naga ya dakata da wasan da yake yi da wannan ganyen ya ɗan karkato da kanshi kafin yayi murmushi yace,
“barka da zuwa, gaskiya yau da alama kinsha aiki dan kin makara sosai…… Har na fara yanke tsammani da zuwanki….” duk da ba wannan ne karo na farko da hakan ta faru ba amma na cika da al’ajabi mutuƙa,
“assalamu alaikum” na faɗa ina kallonsa, sanye yake da jeans da t shirt dukansu blue colour sai dai jeans ɗin yafi rigar turuwa sosai,
“wa’alaikumussalam da maimunatu”
“kayi haƙuri da zaman da na barka kayi kana jirana, tashi mu tafi”
Miƙewa yayi yana murmushi na wuce yana biye dani,
“karki damu dama naji ajikina zaki zo shiyasa zaman bai wani dameni ba”
“to yau kuma ta yaya ka gane zuwa na duk da banyi magana ba?” na faɗa yayin da muka soma tafiya,
Murmushi yayi ya ɗan juyo saitina kamar mai kallona,
“yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ƙamshin turarenki kaɗai naji sai kuma naji alamar bugun numfashinki….”
“ta haka kake gane mutane kenan?”
“eh wasu ba, amma mafi yawa ta muryoyinsu nake gane su”
“gaskiya kana da basira sosai”
“a’a daga Allah ne”
Har muka je ƙofar gidan su muna hira kuma daƙyar muka rabu zuciyar kowa cike da tunanin ɗan uwansa domin a ƴan kwanakin da muka yi muna dawowa tare tuni har mun fara shaƙuwa da juna.
Yau da na tsaya ɗaukarsa ban ganshi ba kuma koda na tambayi baba jinjiri sai yace dani wai yau kwata kwata hashim bai zo ba abin da ya tayar min da hankali kenan har nakasa jurewa sai da na bishi gidan su, ginin gida ne irin na talakawa, ɗakuna guda biyu ne babu ko siminti sai ƴar baranda, suna zaune a barandar shi kuma yana kwance ga tukunyar da aka dafa masa ruwan maina nan agefe, sallama ta ya sanya duka hankalinsu dawowa gare ni, wata ƴar dattijuwa ce wadda daga gani itace mahaifiyarsa sai wata ƴar budurwa baƙa,
“maimunatu ce wadda nake baki labarinta, dama nace miki zata zo” na jiyo muryarsa cikin alamun ciwo yana sanarwa da mahaifiyar tashi, cikin girmamawa aka shinfiɗa min tabarma, muka gaggaisa anan suke sanar min da rashin lafiyar tashi wai tun daren jiya bayan ya dawo da zazzaɓi ya kwana har yau ɗinnan,
“sannu hashim….. Allah ya baka lafiya ai dama tun da naga shiru kuma naji an ce baka zo ba nayi tunanin ko ba lafiya ba, amma ya sha magani kuwa?” na ƙarashe maganar ina kallon mahaifiyar tashi, dukkansu shiru suka yi babu wanda ya amsa min, sai wannan yar budurwar ce naji tace,
” a’a bai sha magani ba, ba a samu kuɗin siyowa ba… ”
” amma yaci abinci? ”
” a’a, yau ba mu dafa komai ba, dama iya ke yin waina ta siyarwa kullum da safe to yau da asuba ta tattara min kuɗin dan inje in yi mata cefane wasu suka ƙwace…..”
“subhanallahi ubangiji Allah ya rufa asiri, bari ina zuwa”
Wayata na ciro daga cikin jaka na kira bishra amma har tayi ta katse bata ɗauka ba, anty salaha na kira ina jan tsaki sakamakon rashin ɗaukar da bishra bata yi ba, itama anty salahan sai dab da zata katse sannan ta ɗauka tana cewa “widat ya aka yi?”
“anty dan Allah magani nake so ki tura min zan siyo, na zazzaɓi da ciwon kai”
“akwai amai ne ko kasala haka?” ta tambayeni, kallon iya nayi na tambaye ta ko akwai amai tace min babu dan baima ci komai ba nan na faɗawa anty tace to bari ta turo min amma babba ne ko yaro marar lafiyar nace mata babba ne, sallama muka yi sannan na miƙe ina cewa su iya bari naje ina dawowa yanzu. Kai tsaye wani babban shago na wuce na fara yi musu siyayya, buhun shinkafa, taliya, macaroni, mai ƙaramar jarka, maggi, gishiri, duk wani nau’in kayan abinci sai da na siya musu na fito da atm card ɗina aka cire kuɗin sama da dubu arba’in, wayata na duba naga anty ta turo min sunan drugs ɗin nan na shiga pharmacy na siya masa na haɗa masa da drinks, napep na ɗauka ya kaini gidan sannan ya taimaka min ya shigar min da kayan ciki lokacin ana ƙoƙarin kiran sallar magriba, har lokacin suna zaune tsuru cikin yunwa, ganin wannan kayan iya ta fara salati tama rasa irin godiyar da zata yi min nace babu komai su godewa Allah domin shine ya basu ba ni ba, fito da drugs ɗin nayi na miƙa mata nayi mata bayanin adadin yanda zai sha idan yaci abinci wanda tuni wannan budurwar da naji iyan ta kira da Amira tana can tana ƙoƙarin ɗora musu, ganin magriba tayi ya sani yi musu sallama na tafi suna ta yi min godiya, ni kuma ina ta jin daɗi acikin raina domin na yaye musu damuwa da ƙuncin da suka wuni aciki, tun jiya rabonsu da abinci suna zaune cikin yunwa kuma dama abbanmu kullum maganarshi akanmu mu yawaita sadaka da taimako da albashinmu, kar mu yadda mu ɗauki salary har yaƙare ba mu cire wani abu mun yi sadaka ba shiyasa duk lokacin da na ɗauki albashi sai nayi canji ƴan hamsin hamsin na dubu biyu na rabawa mabuƙata dake hanyar zuwa wurin aikina, bama ni kaɗai ba ku san duk ƴan gidan mu haka suke domin abba ya jima yana karantar damu falalar ciyarwa da sadaka saboda kowanne azumin duniya kullum sai an dafa abinci rabin buhu banda ƙosai da kunu duk na sadaka ne. Bayan na koma gida yaya faisal ya kirani mun ɗan sha hira kaɗan ya soma tambayar wai size ɗin takalmi na domin lefe na ya gama haɗuwa saura ƙiris kuma nan da wani watan may be za akawo, faɗa masa nayi muka yi sallama ina jin wani sabon tunani yana ziyartar zuciya ta……………. ✍
*_Ummi Shatu_*