Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 41-42

Sponsored Links

“Gasu can a saman loka” Cewar Inna da ta fahimci mai Malam ke tunani. Idanu ya ɗaga sama aikuwa ya hango almajiran nasa zaune a kan drower, wani haushi ne ya kama shi ashe dama za su iya cin amanarsa cikin ɗan ɗaga murya tare da yin ƙasa da ita dan kar micijin ya ankara da shi ya ce.

“Yanzu Habu kai da Ƙasimu a maimakon sai kun fara kinkimata kun ɗorani sannan ku samu ku hau shi ne kuka ɗare kuka barni gani a ƙasa daga ni sai micijin ga wadona jargaf da ruwan da na zauna a kai” Ya faɗa kansa a sama yana kallonsu.

“Ruwan da ka zauna a kai ko kuwa fitsarin da ka jabga a jiki, ai fa haka za ka tashi yaraf-yaraf da ruwan fitsarinka ka haye sama in ba haka ba lahira ta yi baƙo yanzun nan micijin nan yana juyowa sai dai wani ba kai ba” Ya tsinkayi Inna ta window tana faɗa. Cikin hanzari ya tashi ya fito daga cikin katakwayen fitsarin nan sai tsiyayowa yake daga jikinsa, ga kunya da ta kama shi da Inna ta faɗa fitsari ya yi almajiransa na ji, taga-taga ya yi zai faɗi amma haka ya daure ya taka katakon gadon ya fara ƙoƙarin hawa.

Related Articles

Amma santsin jikin drower da kuma kemar futsarin ƙafafunsa suka taru suka hana shi hawa lokar. Micijin da ya hango Malam kawai sai ya nufi wurin Malam.

“Gashi nan ya taho” Cewar Inna tana dariya ai Malam jin haka ya sa ya waiwayo ƙasa aikuwa ya ga micijin ya nufo shi gadan-gadan wani tsalle da ya doka sai ga hannayensa sun isa saman drower amma shi bai hau ba.

“Kai Ƙasimu matsa gefe ɗaya mana in samu wurin zama” Cewar Malam yana nishi dan tsantsi sai neman dawo dashi ƙasa yake amma saboda ƙarfin hali da gudun ceton rai ya sanya ƙarfinsa ya riƙe gam.

“Haba Malam kai kaɗai ma fa sai ka cinye saman lokar nan idan ka hayo, baka ganin yadda kake mu ma wurin ya mana kaɗan” Cewar Ƙasimu yana wani ɓata rai.

“Lallai yaron nan to wallahi Allah sai na hayo, Allah wadaran naka ya lalace, ban da ma yau da gobe mai sa a mari amarya, kai baka san ma an ce Malamai magada annabawa bane ina Malaminka amma kake ƙoƙarin ƙin taimakona”

Banza suka masa kuma basu matsa masa ba.

” Gashi naaaaaaan” Cewar Inna har da jan na ɗin, Malam bai samu damar waiwayo wa ba dan ɗazu ma da ta ce gashi nan ya ɗau ƙarya ne amma yana dubawa ya hango shi dan haka yanzu ko waigawar ma bai yi ba ya dafe lokar da hannu ɗaya yasa ɗaya hannun ya kamo ƙafar Habu ya fisga da ƙarfi ya miƙa bakinsa cinyar Ƙasimu ya gantsara masa wani uban cizo da ya sanya suka manne a wuri ɗaya suka bashi wajen.

Haka ya yi saurin ɗanewa ya samu ya zauna a saman drower yana aika musu mugun kallo kamar zai hau su da duka amma ba hali, saboda yanayin da suke ciki. Habu kuwa cinyarsa ya dafe da hannu saboda zafin cizon da Malam ɗin ya masa.

“Ku dai shirya dan na san tsugunne bata ƙare ba” Cewar Inna tana dariya har da yiwa Malam gwalo da ke harararta.

“Muguwa to a bakin ki ta Allah ba taki ba dan na san mun masa nisa sai dai ya tada kai ya yi kallo” Cewar Malam yana ɗan leƙo ƙasa aikuwa ya hango micijin ya cake kansa a ƙasa ya ɗaga jelarsa sama yana wulwulawa.

“Allah ƙadiran, wai kuwa marar lafiyar nan haka aljannu ke maidashi miciji dama kuke rayuwa da shi a gidan nan bakwa tsoron ya zama ajalinku?” Cewar Malam har lokacin yana kallon micijin.

“Ba fa marar lafiya bane ba me aljannu bane, jariri ne mahaɗin wanda ka gani ɗazu ka tambaya haihuwa aka yi to shi ne yake sawaya ya koma haka” Cewar Inna.

“Jariri? ” Cewar Malam yana zare ido.

“Rass kuwa ” Cewar Inna.

“Amma shi ne ba a sanar da ni komai ba aka bani komai a rufe aka barni na kawo kaina ” Cewar Malam a fili a zuciyarsa kuma ya ce.

“Shikenan garin yin zamba cikin aminci na cuci kaina matar nan jiya tana ta so ta min bayani amma saboda kar ta ga kasawata a ɓangaren malunta na ce na san komai”

Inna kuwa baki ta taɓe bata ce komai ba Malam kafin ya gama tunani sai ganin micijin ya yi ya taso wani shuuuuu ya iyo sama wajensu kafin ka ce me ya ɗare fanka, sai gashi a kan ɗaya daga cikin abubuwan fanka guda ukun nan yana reto da yake fankar a kashe take.

Malam da almajiransa sai suka fara cakuɗa waje ɗaya gashi kuma wurin ba wani faɗi gareshi ba sai suke neman faɗowa, gabaɗaya micijin ya naɗe jelarsa a jikin fankar sai ya miƙa kansa waje su Malam yana kallonsu su duka a kiɗeme suje basu dawo daga mamakin yadda aka yi ya taso sama ba, shi ba iska ba, sannan gashi ya naɗe jikin fanka wai kuma a hakan an ce musu jariri ne.

“Wayyo yau mun kawo kan mu gidan mutuwa, ni dama ban zama Malami ba bare a ɗakoo ni ruƙiyyar aljannu yau gashi na ga ta kaina sai dai addu’a da fatan Allah ya tsallakar da ni” Cewar Malam yana rushewa da wani kuka.

“Haba mai sittin wata kan wata kai ne ke da na sanin zama Malamin ma baki ɗaya haba kai da ke taimakon mutane kana cire musu aljannu ka tura su bangon duniya ko birnin sin” Cewar Inna tana dariya. Banza Malam ya mata dan ba ra ita yake ba ga kuka almajiransa ya cika masa kunne.

Inna kuwa zuwa ta yi ta ɗakko wani dogon icce ta dawo windown ta tsaya sai da ta ga Malam ya juyar da kansa can baya hango ta sai ta sanya iccen ta cikin windown ta miƙa har sai da ta kai iccen wajen wuyan Malam ta zungura iccen ya dungurewa kan Malam ta kuma caka masa a wuya, da sauri ta janye iccen ba tare da Malam ya gani ba.

Wani uban ihu da Malam ya saki duk ya kiɗime ya gigice sai wata karkaɗa kai yake da sauri da sauri yana sanya hannu yana dukan wuyansa ya ce.

“Shikenan kuma yau aljannu za su yi yaƙi a ɗakin nan, dan sun fara caka mini farcensu a wuyan da kaina sun ƙi bayyana yau kuma sai yadda hali ya yi ni da almajiraina” Ya faɗa yana ɓare baki kamar wani ƙaramin yaro, Inna kuwa tsabar dariya ta kasa furta komai har sai da ta tsagaita da dariyar sannan ta ce

“Ka cewa aljannun su miƙo maka dorinarka da galan ɗin ruwan addu’ar da kuka zo da shi da kuma waccen hular ba kai bane mai fitar da su ai sai ku shiga fafatawa”

“Rufa min asiri dan Allah wallahi ba dai ni ba, ina ni ina yaƙi da iyayena”Cewar Malam yana kuka har lokacin.

“Iyayenka kuma aljannun ne iyayenka?” Inna ta tambaya cike da mamaki.

“Au wallahi suɓutar baki na yi, ku yi haƙuri mutanen ɓoye, yo abinka da su ba ganinsu ba ake yi” Cewar Malam yana wani waige-waige dan kar aljannun su fara masa hukunci tun ba a je ko ina ba.

Ganin miciji ya daina kai kaisa wajen su Habu ya miƙo wajen Malam tuni ya manta da batun aljannu wani irin haɗiye kukan da yake ya yi yana dannewa dan kar ya yi kukan, kallon kallo ake shi da micijin Malam ji yake kamar ya ɓace ɓat ko kuma ya suma dan ya daina ganin wannan micijin a kusa da shi in yaso idan micijin ya tafi sai ya farfaɗo. Ahankali micijin ya ɗauke kansa daga kusa da Malam ya koma da shi jikin fanka ya shiga warware jekar daga naɗewar sai da ya gama idanun Malam da su Ƙasimu sun zazzaro su har sai da suka ji jijiyoyin idanun sun ɗame duka wato babu yadda ma za a yi su ƙarawa idanun nasu fitowa saboda sun gama fitar d su har ƙarshe. Kafin meye wannan micijin ya yi wani tsalle sai gashi a tsakaninsu, dama Habu da Ƙasimu a jere suke sai Malam daga gefe, a tsakanin Ƙasimu da Malam micijin ya sauka sai Ƙasimu da Habu suka haɗe a wuri ɗaya Malam ya kasance warewa, shi kaɗai a gefe idanu ma Malam ya runtse saboda yadda zuciyarsa ke buga masa da mugun ƙarfi kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito. A take micijin ya shiga juyi kamar mai rawa yake kawai, Inna kuwa sai dariya take cikinta har ciwo ta ji yana mata dan ta daɗe bata yi dariya haka ba, ko sararawa bata yi.

Wani uban tsalle Habu da Ƙasimu suka yi sai gasu sun diro a tsakar ɗakin sun bar Malam shi kaɗai a sama.
“Kash lallai in ba mutuwa to akwai tsofa, yau na ga ranar samartaka, in ba dan tsufa ba, ina za a barni a kan lokar nan, da lokacin samartaka ta ne ai da na riga kowa dirowa” Cewar Malam yana kallon micijin fuska shaɓe -shaɓe kamar dai ba shi ne Malam mai sittin wata kan wata ba.

“Yanzu ma lokci bai ƙure maka ba ka diro in ya so in ka karkarye sai a tattara ƙasusuwan naka a watsar” Cewar Inna da har lokacin bata bar masa dariya ba. Malam yana shirin bata amsa sai gani ya yi micijin ya ɗan tashi sama kaɗan sai da ya je saman kansa ya tsaya , Malam ba ɗaga kai ya yi ba idanunsa ne suke kallon saman kawai lumfashinsa ma ya tsaya cak, ko idanunsa ba ya so ya ƙifta tsabar tsoro da kaɗuwar da ya yi.

“Suma ka yi ko mutuwa ka yi, nanga ka kafe idanun naka a sama?” Cewar Inna sa ke kallon idanun Malam kafe a kan micijin. Malam dai babu bakin magana kawai kallon yadda micijin ke tsaye a kan iska ya miƙe duka tsawonsa.

Kafin Malam ya ankara kawai sai jin micijin nan ya yi a wuyansa gabaɗaya ya masa ƙawanya ya nannaɗe sai da micijin ya gama naɗe jikinsa tsaf a jikin Malam sai kuma ya kwallaso kansa ya dawo da shi saitin fuskar Malam ɗin ya zamana sun yi ido cikin ido. Malam bai san lokacin da ya saki numfashinsa ba wanda ya riƙe, ya maido da idanunsa daga kallon sama zuwa kallon fuskar micijin.

Irin halin da Malam ya tsinci kansa a ciki abun ba a magana shi kansa ba zai iya misaltawa ba ya san dai yana cikin gagarumar matsala da tashin hankali. Bakinsa yake so ya buɗe ko Allah zai sa ya iya tuno wata aya daga cikin qurani ya karanta ko kuma wata addu’a daga cikin addu’o i ya karanta dan neman ceton Allah maɗaukaki dan ya san yanzu shi kaɗai ne zai iya kawo masa ɗauki dan almajiransa ma sun juya masa baya, amma gabaɗaya sai ya ji bakin nasa ya masa nauyi ya kasa furta ko da kalma ɗaya ce. Cikin dddagewa ya fara iya motsa laɓɓansa suka fara ɗan motsawa kaɗan amma ba komai yake cewa ya, da ya fara ƙoƙarin maganar ma sai ya ji babu wani sauti da ke fitowa daga bakinsa. Abin da kawai ya sani yana iya jiyo saukar hawayensa daga idanunsa tamkar wani ne ya cika buta da ruwa yake kwararo masa a fuska haka yake jin zubar hawayensa da gudu ko ƙaƙƙautawa babu.

Haka dai ya rinƙa yaƙi da bakinsa dan karanto addu’a amma ina bakin Malam dai ya yi mirsisi tusar ango, babu alamar ma zai bashi wata dama da zai furta komai a fili bare kuma a zuciyarsa, zuciyar da tun da micijin ya naɗe wuyansa ya ji ta doka da uban ƙarfi har zuwa lokacin bata tsagaita ba da bugawa bare ta bashi wata dama ko ta samu natsuwar da za a yi addu’a a zuciyar.

“Ɗiɗiiiiit, jiiiiiin” Cewar Malam dan komai ya kwance masa shi yasa ya fara hourn ɗin mota. Ƙasimu da Habu duk da halin sa suke ciko sai da suka fashe da dariya.

“Minjaye” Cewar Inna da ƙarfi dariya na cin ta dan ta lura addu’ar ma ta gagara a wajen Malam, Malam kuwa da ke cikin halin neman taimako jin abin da Inna ta faɗa bai tsaya wata-wata ba ko tunanin me Innar ta faɗa na sai jin bakinsa ya yi kamar wanda aka yiwa dabaibayi a bakin aka kunce, haka ya ji, saurin fisgo maganar ya fara faɗar abin da Inna ta faɗa dan sai ya ji tamkar ta sanya shi a hanya ne ta sama masa mafita. A take ya fara biya abin da ta faɗa.

“Minjaye, mi’ara, ba ta ɗauri ba, baba kenan” Cewar Malam yana kuka yana fitar da maganar kamar wani ya masa dole. Tun da ya faɗa yake ta faman maimaitawa ko tsayawa ba ya yi Inna kuwa kamar ta samu Tv haka ta maida Malam babu abin da ke bata dariya iron yadda ruwan hawayensa ke kai komo, a fuskarsa kamar wanda ya wanke fuskar, gabaɗaya hankalinsa a tashe yake da yadda micijin yake har lokacin nannaɗe a jikin wuyansa kansa kuma a wajen fuskarsa.

“Wa maa ƙadarullaha haƙƙa ƙadrihi” Cewar Habu dariya na cinsa ai kuwa Malam ya kama ayar gagam ya riƙe sai maimaitawa yake yana kuka.

Dan a take ya saki waccan jiniyar motar da yake yi ya kama wacce Habu ya faɗa masa. Sai da ya maimaita kusan sau hamsin ko dakatawa ba ya yi sannan a take ya tuno da wani karantun ya fara.

“Wallaili iza yagshe, wannahari iza ta jalle, wama kalaƙazzakara wal unsee, inna sa’ayakum lashatte,wa ammaa man a’aɗawattaƙe” Haka ya rinƙa janyo ayoyin yana kuka, amma daga ya je iya ayar da ya karanta sai ya dawo farko ya kasa ƙarasa surar har zuwa ƙarshe. Yana cikin yi sai Ƙasimu ya ƙara ɗora shi a kan wata surar.

“Wadduhe”

“Wallaili iza saje, ma wadda aka rabbuka wama ƙale” Cewar Malam cikin sauri-sauri dan duk wanda ya ji ya janyo masa aya sai ya saki wacce yake karantowa ya kama wadda aka karanto ɗin dan shi kawai so yake ya kamo ayar da za ta masa sha yanzu magani yanzu. Su Ƙasimu da Habu da kuma Inna da suka shagala da masa dariya ya yi dibara ya sauke idanunsa ƙasa ya hangi yadda suke dariya wani haushi ne ya turnuƙeshi ji yake da zai iya sai ya fita ya shaƙo Inna ta ƙarfin tsiya ya shigo da ita ɗakin ya sanya musu micijin a wuyansu ita da su Ƙasimun su ji yadda ya ji.

“Allahu, Arrahmanu, Arrahimu, Almaliku Alqudusu Assalmu” Malam da ya runtse idanunsa da ƙarfi dan ya daina ganin takaicin abin da almajiransa da Inna ke masa da kuma ganin fuskar micijin a kusa da tashi ya kamu sunayen Allah yake karantowa. Idanunsa na rufe ya fara jin riƙon da aka yiwa wuyansa ya sassautu, a hankali ya ɗan ƙyalla ido ɗaya ya buɗe aikuwa sai ya ga babu kan micijin a kusa da fuskarsa kawai sai ya buɗe ɗaya idon ma a take ya fara gani ashe micijin ne ya shiga warware jikinsa daga wuyansa, daɗi ne ya ziyarci zuciyar Malam yana ganin micijin har ya bar jikinsa ya yi wani uban tashi ya sauka daga kan drower ya je ƙasa wurinsu Ƙasimu ya nufa da ke yiwa Malam dariya ko lura basu yi da micijin ba sai ji suka yi ya nannaɗe wuyansu lokaci guda su biyun ya haɗa wuyansu ya kanannaɗe su.
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

 

Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

Back to top button