Ni da Patient Dina Book 1 Page 19
Page
Mikewa ya Usman yayi zeshiga daki Yana fadin ” toke auta wayace miki anawa mutum homework!? Aisede yayi abinshi dakansa ana nuna masa ” a shagwabe tace” ya Usman ai anty’s din ne suke cewa mudinga bawa ko mother dinmu !ko father dinmu! ko sister dinmu! ko brother dinmu! Ko; !!! Tana kokarin fadin wani Abun, suhaima takatseta da ” ko uncle dinku! Ko anty dinku ko? ” ” Laaaaah anty suhaima Taya akayi kikasan abinda anty Jenifer tafada mana ?” Gyara zama dakyau suhaima tayi tana cewa ” ai saboda muma damuke yara haka antynmu suke fada mana ‘ kinsan mu me suke fada mana!? Dasauri auta ta girgiza Kai tana sauraran suhaima , ya usman de shigewa daki yayi abunshi Dan yasan suhaima yanzu seta biyewa auta. Cigaba suhaima tayi dacewa ” to muce mana sukeyi ko neighbour dinmu Suma zamu iya Basu sumana” suhaima tana gama fadin haka takama kumatun auta tana wasa dashi ” to anty suhaima kenan anty’s dinmu Kuma sunyi teaching naku!?” Wayyo ni suhaima wlh auta nagaji dabiye miki ” tayi maganar tana bubbuga kafa , mama tace ” bari de in mike inyi daki bazan iya da shiriritan kuba ” hanyar dakinta tabi tabarsu afalon suhaima harta Bude Baki zatayi magana ya al ameen yace ” wai nikam Dan Allah suhaima bakya gajiya da surutu ne ? mutum kenan ko yaushe yenyenyen haba ” Yana maganar Yana hararanta FANAN ce abin yabata dariya ” wallahi kuwa niyanzu narasa ita da auta wayafi shirme ” ” eh din anyi din ke inkinayi wayake kulaki Allah fanan kifita a hanyata tam” tagama maganar tana wurgawa fanan harara ” baba Daya gaji da shirmen nasu Shima yamike Yana yar dariya yace to mukwana lafiya ” suka amsa da Ameen, bayan tafiyan baba ne dukansu suka watse kowa yawuce dakinsa auta binsu fanan tayi saboda zata mata homework, kwanciya sukayi dukansu akan gado fanan nata nunawa auta harsuka gama ta tafi dakin mama . Juyawa tayi ta kalli suhaima dahar lokacin tana fushi sannan tace ” haryanzu fushin ne to kiyi hakuri yar kanwata bazan Kara ba” hararan wasa suhaima tabita dashi ” ah ah kinmanta yarki ce ba kanwarki ba” dariya sukayi kafin suka fara hira har bacci barawo ya kwashesu yayi awon gaba dasu.
Karfe 2:30 nadare kwance take tana bacci cikin kwanciyar hankali kasa_kasa tafara Jin magana kamar ana magana akusa da ita Bude manyan idonta tayi ahankali tana bin dakin nasu da kallo Wanda bata kallon komai saboda wutan dakin akashe yake mikewa tayi tazauna akan gadon tana sallati, Jin datayi shuru kamar bayanzu tagama Jin magana ba yasa tagyara kwanciyarta takwanta Amma idonta biyu baccin begama daukanta ba ahankali taji sawun tafiya Sadaf!Sadaf! Rufe idonta tayi cikin murya kasa_kasa irin Wanda akeyi in baason atashi mutum a bacci taji ance” shugaba abashiyya sarauniya fa kamar tayi bacci kamar batayi bacci ba ” bakaramin girgiza fanan tayi ba jin sunan abashiyya da aka ambata SE adduah takeyi azuciyarta can taji abashiyya tana fadin ” khairatyyy bafa abinda nasaki kiyiba cewa nayi wannan sauron daya hau jikinta dazun yake kokarin Shan jinin SARAUNIYARMU nace kije kisameshi kijimin Meye ta mishi dahar yasha jininta ,inkuma da gangan yasha jininta to kika mashi kikaishi fada ayanke mishi hukunci Dede da abinda ya aikata sannan karki yarda kidawo se ankaishi dakin horo maza kiwuce ” batt khairatyyy ta bace fanan kam suman kwance tayi, Jin wayan nan maganganun datayi, can bayan mintuna taji alamar ana tsaye akanta yasa tayi saurin kallon direction din ganin bakowa ne tamike zata bar dakin da sauri, hannu abashiyya tasa akan goshinta ahankali tana fadin ” lokacin baccinki ne yanzu sarauniya kiyi bacci ” tunkafin abashiyya tagama maganar wani irin nannauyan bacci yatafi da fanan luuu Takoma takwanta murmushi abashiyya tayi sannan Takoma Bakin kofa ta tsaya tanawa sauran masu gadin sarauniyarta su magana .
Washe gari tashi suhaima tayi daga bacci tana Mika hade da salati waigawa tayi gefen fanan bakaramin mamaki Tasha ba ganin fanan akwance tana bacci haryanzu batayi sallah ba , abinda tunda take da fanan betaba faruwa ba sede inko period takeyine nanma zata tasheta seta koma bacci Amma yau fanan ce haryanzu take bacci , toilet tashiga ta dauro alwala tazo tayi sallah nanma har time din fanan tana bacci karasawa kan gadon tayi tafara tashinta tun tanayi da hankali harta farayi da karfi tsorata tayi tayi saurin barin dakin tayi falo idonta nazubar da hawaye , tana kwala Kiran mama!mama!mama! Jin Kiran da suhaima takeyi bana hankali ba yasa dukansu suka fito afalo suka tadda ita tana tsaye fuskanta jaga_jaga da hawaye , baba ne yace ” suhaima meyake faruwa ne kiketa kwala kira da safiyan nan!?” Share hawayen Daya zubo mata tayi kafin tace ” baba nafi minti 30 Ina tashin fanan abacci haryanzu bata tashi ba” aibasu ma bari tagama fadan sauran maganar ba dukansu suka duhru cikin dakin sun , yanda suhaima tafita tabarta haka suka sameta bakaramin firgita sukayi ba. babane tunda suka shigo dakin yagane abinda yake faruwa cikin kwantar da murya yace ” Dan Allah kudena daga hankalinku Ninasan Meye matsalar” da mamaki kwance akan fuskarsu suke binsa da kallo , karewa dakin kallo yayi kafin cikin sanyin murya yace ” angaisheki jakadiyar da babu irinta,yar Amana merike Amana , wacce tasan asalin halacci , uwa agun shufai da shufana, jakadiyar da babu kamanta akaff fadin masarautar NASMINAYA , fara me farar aniya , Ubangijin Allah yabiya miki bukatunki na duniya da lahira ” cike da mamaki su suhaima da su ya Usman suke kallon baba suna tambayar kansu waye yakewa irin wannan kirarin Banda mama datasan wacece agun . Bakaramin farin ciki dakuma jindadi jakadiya abashiyya tayi ba jin irin kirarin da baba yamata sannan ta fara kokarin bayyana ta…………
To muhadu a comment section semun hade tomorrow in da Rai da lfy Ina godiya sosai Yan comment section Ina alfahari daku sosai da irin comment din ku inasanku sosai.
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
NIDA PATIENT DINA
Story Written by (MRS ISHAM )
Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen.
Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci
____________________________________________