Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 26

Sponsored Links

Page 2️⃣6️⃣

 

Dukkansu daki sukayi dan susamu su kwanta,fadawa Gado fanan tayi tana ” wayyo qashin bayana! dan Allah suhaima dan hau bayana ki dan takamin kinji sweet sis” tsakaninta da Allah take maganar itakuma suhaima duk zatonta wasa takeyi bata kulata ba taci gaba da abinda takeyi, ganin datayi suhaima tayi banza da itane yasa cikin muryan shagwaba tace ” ayyah adda suhaima dan Allah badan niba wlh bayana kamar zefita nakeji please” cikin salon mugunta suhaima ta cije baki tace ” tom ai seki gyara yanda zan takaki dakyau din ko” cikin gamsuwa da maganarta fanan tayi rubb da ciki tana jiran suhaima, hawa gadon tayi kamar abin arziki tafara daddan na mata bayan nata ahankali can kuma ta takarkare tayi wani irin tsalle zata dira akan bayan fanan din,kamar wacce akace tajuyo aikuwa tana juyowa taga abinda suhaima take kokarinyi ba shiri tamatsa gefe suhaima tadira akan gadon , mugun kallon mamaki fanan take binta dashi ,kwafa suhaima tayi tace ” yar renin wayo !Allah yataimakeki dasede kiji qashin bayanki suna qaras_qaras ” sake da baki fanan kebinta da manyan idanunta data zaro su waje cikin mamaki tace ” suhaima yanzu tsaban iskanci muguntan dakika shiryamin kenan dayanzu banjuya ba da bayana yatashi a aiki” takai karshen maganar tana hararanta “mtsssw yanzu de kiji da kanki malama tunda kinki tsayawa inmiki to karki dameni” tsaban takaici pillow fanan tadauka ta jefa mata aikuwa cikin saa yasameta dauka suhaima itama tayi tarama nan suka fara jefi_jefin pillow sunfi 30mint ahaka seda suka gaji suka bari kowa na hararan dan uwansa se haki sukeyi kamar wanda sukayi tsere toilet fanan tashiga zatayi wanka. Cire kayan jikinta tayi kaff yarage daga ita se pant and bra sa hannu tayi ta zare ribbon din kanta nan take gashinta suka zubo har kugunta suka rufe mata fuska dama tun last kitson da suhaima tamata ta tsafe bata kara bin takanba , gaban mirror toilet din taje tatsaya tafara bubbude shampoo’s din kala uku duk seda tawanke gashin dasu ,kwantawa sukai luff se sheki sukeyi gashi yajike tsayin gashin seda yakawo dede hips dinta seda tagama da kan tukun tayi wanka tadaura towel ajikinta tadauki wani karamin towel din tanado gashinta aciki tadaure tafito, samu tayi suhaima bata cikin dakin kujera tajawo takai gaban mirror, bude loka tayi tadauko hand dryer tajonashi da socket zama tayi tasunce towel din kanta raba gashin gida hudu tayi dan bazata iya busar dashi time daya ba ahaka tadinga busarwa harta gama seda ta tabbatar duka sun bushe kafin tadau man gashi masu dadin kamshi tafara shafawa taje gashin tayi tafesheshi da hair spray wani irin yalki gashin yakeyi, daga bisani tadau ribbon tafara kiciniyar packing dinshi amma tagagara ganin zebata mata lokaci ne yasa tayi amfani da kifiya ta tsaga gida gashin biyu tasa ribbon ta kamasu setazama kamar wata yar baby , body lotion dinta tadauka tashafawa dark glowing skin dinta ta fesa turare kadan kadan ajikinta mikewa tayi ta Isa gaban wardrobe dinta tabude kayan bacci tadauko white color silky riga da wando tasa takoma kan gado tazauna tana tunanin ko ina suhaima taje oho, jawo wayarta tayi takunna data tashiga WhatsApp tana duba messages video call taga zeenat takirata picking tayi tana gyara zamanta, zaune take afalo alamun basu kwanta ba dan tanajin muryoyinsu ganin cute face dinta ya cika screen din wayar cikin daga murya tace ” barka matar babban Yaya” cike da tuhuma su fawwaz da areef harda azaad din da yaseer suka juyo suna kallanta Jin abinda taburta, itakuma subul da baka tayi, ganin sun tsareta da ido ne yasa tafuske da ” kawata meya hanaki bacci ” murguda mata baki fanan tayi kafin tace ” aike zaawa wannan tambayar! Yasu Abba da ummi!?” Yar dariya zee tayi ” suna lafiya duk sunkwanta ai mune kadai mukayi saura muna kallon wani series ne ” takarshe maganar tana kallon azaad dake hakimce akan sofa mezaman mutum biyu yana danna wayarsa fanan nakokarin magana zeenat tacire camera daga face camera tamaidashi back camera taseta azaad, kyawawan fuskanshi ne da cikekken surar jikinshi ya bayyana agaban screen din wayarta wani irin kyau yakara yana sanye da pj mask ajikinshi wani irin kwanciyar hankali taji ya ziyarceta lokaci Daya lumshe idonta tayi batasan dalili ba amma jinta take kamar wacce akawa albishir da wani babban abu, ganin yanayin mood din da fanan tashiga ne yasa zeenat tayi murmushi harseda dimple dinta yalotsa, kamar daga sama taji ance ” will you stop that nonsense” dukansu firgita sukayi dagowa tayi taga azaad ne yakafeta da sexy eyes dinshi kamar wani mejin bacci rai abaci cikin dakakkiyar murya yace” bani wayar nan ” yafada yana mika mata hannunshi fanan najin haka cikin sauri tayi hanging din kiran, su yaseer dabasu san meyake faruwa ba suka zuba musu ido, cikin inda_inda tace ” am sorry ya azaad” tsawa yadaka mata wanda suma dasuke wajan seda suka tsorata ” before the count of 5 hand me the phone ” ganin hawaye yacika a idonta ne yasa yaseer cewa ” we’re sorry dude amana afuwa” ko kallon inda yaseer yake beyi ba balle ya saurarare shi so yake yasan wacece zeenat take video call da ita dahar zata juya back camera tana kallonshi dan yasan ba nusaiba bace balle aneesa dan dukkansu basa good time bawani shiri sukeyi ba, kuka tafara hawaye nazuba a idonta tasan inde ya azaad yakarbi wayanta ba lallai yabata ba inma zebata to bayanzu ba cikin sanyi jiki tamika mishi wayar takoma wajan fawwaz ta rungumeshi tana kuka kasa_kasa shafa bayanta yakeyi dan babu yanda suka iya inyayi magana shima yanzu laifin zeshafeshi, Allah sarki fanan baiwar Allah duk setaji badadi she felt guilty akan abinda yafaru danasanin daga wayar tayi dan tasan yanzu kan zeenat abin ze koma tana zaune duk tayi zugum da ita , unlocking wayar yayi dan dukkansu yasan abinda sukasa a password dinsu yashiga WhatsApp wajan calls yashiga ganin number datayi waya dashi last yayi an rubuta OTHER HALF , without hesitating yayi dialing din number yafara ringing fuskan nan adaure tamau , tana zaune shuru tana tunanin koya zeenat takare da Mr azaad oho taji wayarta na ringing dasauri taduba ganin friend zeenat ne, hamdala tayi cike da jindadi tadaga , daskarewa tayi ganin face din Mr azaad akan screen din,bin fuskanta da kallo yayi gashin kanta data daure kamar wata karamar yarinya yakalla daga bisani yadan ja tsaki ” me kika wani tsareni da wannan idon naki kamar wata mayya !?’ yafada yana kallon cikin idonta dasuke farare tass dasu gasu manya masha Allah, gwalo idon waje tayi jin abinda yafada can ciki_ciki yanda bazejitaba tace” aikaima idonka manyane kilama sunfi nawa girma kaima mayene kenan” afusace yace ” ke nikike cewa maybe?” Sam batayi tunanin zeji abinda tafada ba cikin muryan firgici tace “Nashiga uku na lalace Mr azaad dan Allah kayi hakuri badakai nakeyi ba wani quda ne yazo wucewa yake kallona ni badakai nakeyi ba” wani irin dariya yaseer da fawwaz suka kwashe dashi Jin abinda fanan tafada wai ita da quda ne ko a ina taga qudan awannan daren,Kara tamke fuska yayi yajuyo yakallesu aikuwa mitt sukayi kamar basune suke dariyaba yanzu , kwafa yayi yamaida kallonsa kanta cikin husky voice yace ” meyasa dazun kike kallona ” tarin mamakine yakamata taya akayi yasan shi take kallo shida yake danna wayarshi bugo da qarima kujeran dayake zaune bakusada zeenat yakeba,Satan kallonshi tayi dakyau tarasama mezatace mishi ganin yanda yatsareta da ido duk yasa takara birkicewa idea ne yazo mata cikin dabara tace” am dama budurwarka ce tace induba maka lafiyanka shisa nacewa zee ta juyamin inganka domin aiwatar da sakonta and now I can see you’re extremely fine byebye good night ” ko tsayawa taji mezece batayi ba takatse kiran kirjinta nadukan tara_tara dan tasan haduwansu nan gaba bazeyi kyau ba .
Suman zaune azaad yayi jin irin karyan da fanan tazuba mishi dan takare zeenat aranshi yana fadin” wato kullum tsiwan yarinyar nan Kara karuwa yakeyi ” sukansu su fawwaz mamakine yakamasu dama fanan na magana har hakane, lallai yau de tadibo ruwan dafa kanta dan tabari suka hadu da ya azaad hmmm , yaseer kuwa se kumshe dariyan daya taho mishi yakeyi dan karya bito dan yasan bazasu wanye tadadi da azaad ba, one by one suka dinga barin falon zuwa daku nan barcinsu dan karya juyo kansu harsuka watse yarage dagashi se yaseer cigaba yayi da pressing din phone nashi.

Related Articles

Shigowa suhaima tayi da soccer ahannunta cike da snacks ta ajiye musu atsakiyar gadon ganin yanda fanan tayine kamar wanda taga abin tsoro yasa ta tambayeta ko lafiya fada mata abinda yafaru tayi ” Tabb lallai fanan sannunki da kokari meya hadaki dama wannan karya mutumin da zan iya rantsuwa baya dariya shine kika tabo ai babban mafita shine koda wasa karki bari kuhadu” ta karashe maganar tanakai snack bakinta , Kara rudewa fanan tayi jin abinda suhaima tafada kuma koda bata fada ba tasan sarai Mr azaad bakyaleta zeyi ba kallon cikin soccer tayi jitayi cikinta akoshe yasa takwanta taja blanket tarufe jikinta tana cewa suhaima ” inkin gama kikashe wutan dakin” tayi adduah bacci tarufe idonta .

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story & Written by ( MRS ISHAM )

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

Free book

Alhamdulillah nakusa gama book 1

&________________________________________&

 

Back to top button