Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 61

Sponsored Links

6⃣1⃣

Sumayya tunda takwana biyu ganin dagaske aurenta ya mutu gashi bata ganin yarima yasa tahak’ura tasaki ranta, ahaka akaje aka kwashe kayanta a part d’inta sannan aka rufe gabad’aya 6angaren yarima aka kaima memartaba key d’in.

 

Sumayya kwance take saman gadonta sai a ranar tajanyo wayarta takunna dan rabonta da ita tun ranar da aurenta yamutu, number d’in yarima tayi dialing da mamakinta taji bata shiga, dan haka talalubo ta zinat nan tafara ringing har ta tsinke ammah batayi picking ba, nan ma sumayya tak’ara kira saida tayi mata 3 missed call ammah bata d’aukaba dan haka tatura mata message dan daman tasan mawuyacine zinat tayi picking d’in wayar.

Bayan kamar minti biyar sai sumayya tak’ara kira da mamakinta saiga zinat tayi picking, cike da jin dad’i sumayya tagyara kwanciyarta tare da cewa Hi baby.

Daga chan 6angaren zinat a tsorace tace sumayya ya dai?

Murmushi sumayya tayi tace ke fa tsiyata da ke kin cika tsoro toh kisaki jikinki komai ya wuce.

Uhm sumayya kenan taya zan saki jikina bayan d’an banzan dukan da wannan mugun yayimin ke yanzu dai ya maganar aurenki?

Murmushi sumayya tayi tace hmm kibarsa kawai ai yanzu aurena da yarima ya k’are wlh ban ta6a tunanin zaimin wannan cin mutuncinba haka koda nasan inason yarima ammah babu yadda zanyi dole inciresa a raina tunda ko giyar wake nasha aurenmu bazai ta6a komawaba.

Zinat cikin ranta murna fal ji take kamar tazuba ruwa k’asa tasha saboda murnar auren sumayya ya mutu, a fili 6oye murnarta tayi tace Allah sarki baby ba haka nasoba toh yanzu ya su memartaba sukayi da sukaji labarin rabuwarku Allah dai yasa basuji abinda mukayi ba.

Dariya sumayya tayi tace kefa tsiyata da ke kin iya tsoro, daman fa nasan miskilancin yarima bazai ta6a barinsa yafad’aba kuma koma ba hakaba nasan yarima bazai iya tonamin asiriba saboda bayason tashin hankali, nikuma gudun kar ma yatona min yasa nayi sauri narigashi kai k’ara……nan takwashe duk abinda yawakana talabarta ma zinat.

Ajiyar zuciya zinat tayi tace gaskiya kinyi namijin k’ok’ari toh yanzu yarima shikenan ya bar gida bazai dawoba?

Hmm ba zai ta6a dawowaba, ni wlh kin ban mamaki da kika iya tafiya kikabarni ban ta6a tunanin hakaba daga gareki zinat.

Kwantar da murya zinat tayi tace kiyi hak’uri baby wlh gabad’aya rikicewa nayi ammah insha Allahu wani lokacin zan shigo.

Cikin jin dad’i sumayya tace gaskiya da naji dad’i dan gabad’aya kad’aici ya isheni Allah yakawo min ke lafiya.

Ameen baby zankiraki anjima.
Ohk, sai kin kira,,nan sukayi sallama.

 

Tun daga ranar sumayya da zinat suka koma suka d’inke kullum suna manne da juna ta waya inba wayaba toh ta chart da video call, yanzu sumayya kusan kullum tana d’akinta suna waya da zinat.

Sultana sadiya ganin yanzu hankalin d’iyarta ya kwanta yasa itama tad’an kwantar da hankalinta ammah magana bata had’asu da ummin yarima dan da taga ummi zata fara d’aure fuska koda ummi tayi mata magana indai sukad’aine shareta takeyi inkuma gaban su dadane toh shine take amsa mata ciki-ciki.
Ummi tun abin yana bata mamaki ganin ba ita tayimataba ammah da ita take gaba, daga k’arshe abun yadaina damunta.

 

Dada da memartaba ma danne damuwarsu kawai suke akan tafiyar yarima ammah su ma suna jin abun yana damunsu cikin rai, daga inda suka tuna da abinda yayi ma ‘yar jikarsu sai kuma suji ba dad’i, dan haka ne suke nuna ma sumayya kulawa sosai ga tausayinta da sukeji saboda akanta akafara sakin aure a masarautarsu.

_________________

Zarah ganin yarima kwana biyu bai nemetaba dan yanzu har romance ya dainayi mata saidai kawai yarungumeta suyi bacci, nan abun yad’an fara damunta.

Yau ma tana fitowa daga wanka ganinsa tayi a kwance yana duba wata newspaper dan haka taje tafad’a jikinsa, kallonta yarima yayi yace Zarah sai kin ji ma babyna ciwo?

Turo baki tayi cikin shagwa6a tace au ba ma ni zanji ciwon ba babynka zanji mawa ko? babyn da yanzu andaina kulamu.

Aje newspaper d’in da take hannunsa yayi yace wajen me nadaina kulaki?

Kwantar da kanta tayi a k’irjinsa tace toh ba kai bane kadaina min komai?

Yarima ya fahimci inda tadosa ammah yanuna bai fahimtaba yace magana nadaina yi miki ko kulawa?

Girgiza kai Zarah tayi cikin jin kunya tace ka daina making sex da ni.

Murmushi yarima yayi yace toh ai naga kamar bakiso saisa nabarki kihuta.

Zaro ido Zarah tayi tace karufa min asiri taya zan k’i son lada, kawai dai babynka ne yake wahalar da ni, dan dadyn nasa jarumi ne,,,tak’arashe maganar tare da kashe masa ido d’aya.

Murmushi yarima yayi yace kar kidamu nima banason babyna yana wahalar min da ke kihuta warki kawai nayi miki uzuri.

Da mamakinsa sai yaga Zarah ta fashe masa da kuka.
Cike da mamaki yace lafiya zarah? Me kikeyi ma kuka?
Cikin kuka tace toh bakai bane.

Murmushi yayi yace toh kinaso inyi?

Cikin sauri tad’aga kai.

Toh shikenan kidaina kuka, nan yakwantar da ita yashiga lashe mata hawayen fuskarta daga nan yalalubo bakinta yacigaba da tsotsa kamar wanda yasamu lolli pop, gabad’ayansu jikinsu rawa yake dan sunyi missing d’in juna sosai, daga nan yarima yazare towel d’in da yake jikinta yagangaro da kansa a k’irjinta, ahankali yacigaba da lalla6ata har saida yaga sun samu nutsuwa sannan yabarta.

Duk da lalla6ata da yayi ammah saida jikin zarah yai ciwo dan daurewa kawai take, ko shi kansa yana lura da yadda take cize le6e.

Cike da tausayinta yashiga yi mata sannu daga k’arshe yad’auketa sukaje yaimata wanka shima yayi nasa sannan suka fito hatta kaya shi yasaka mata, jin jikinta ya d’au zafi yasa yad’auko drugs yabata sannan yad’auketa suka dawo parlour nan yakwantar da ita saman cinyarsa yana wasa da gashin kanta ahaka bacci yai awon gaba da ita.

Ganin tayi bacci yasa yarima yajingine kansa a jikin kujerar da yake zaune cike da tausayin zarah, nan family d’insa suka fad’o masa a rai, tunani barkatai yashiga yi daga k’arshe janye zarah yayi yagyara mata kwanciyarta nan yasafko k’asa yadafe kansa da hannuwa biyu, tunowa yayi da yadda yarabu da danginsa kowa yana d’aura masa laifin da bashida laifi a cikinsa, kukan da ummi takeyi ne ahankali yashiga dawo masa a kunne da lokacin da tad’ago idanuwanta da sukayi ja tasafkesu akansa,
Girgiza kai yashiga yi yace taya zan samu kwanciyar hankali ummina kin zubar da hawayenki saboda ni, ya zanyi da rayuwata.

Zarah da tafarka tun lokacin da yajanye mata kai, ido tazuba mashi tana sauraren duk abinda yake cewa tausayinsa ne yakamata dan sau tari daman yarima yana k’ok’arin ganin ya 6oye damuwarsane saboda ita saidai inaaa tuni ta gama karantar hakan, safkowa tayi daga saman kujerar tadawo k’asa kusa dashi tazauna tare da dafasa,

‘Dago kai yarima yayi yakalleta murmushi yasakar mata tare da 6oye damuwarsa sannan yace kin farka?

Zarah k’wallah ce tacika mata ido tace taya kake tunani ni zan samu kwanciyar hankali alhali kai bakada shi?

Ido yazuba mata cike da mamaki sannan yace wa yace miki bana cikin kwanciyar hankali?

Hawayen da take dannewane suka zubo tace suhail me kamayar da ni, ko duk farkawar da kake cikin dare katashi kayita tunani ka d’auka ban san komai ba?

Mamaki k’arara yabayyana a fuskar yarima yace Zarah wa yafad’a miki haka?

Fad’awa tayi jikinsa tana kuka tace yarima babu abinda ban saniba sau tari kana k’ok’arin 6oye damuwarka idan kana a gabana saidai in bamu tare shine kake zama kayita tunane tunanenka, meyasa kake haka, kai doctor ne kasan illar yin haka tunda kuna fad’a ma wasu sudaina yawan damuwa ammah sai gashi kai kanayi.

Yarima rintse idanunsa yayi da k’arfi yana jin wani iri a ransa dan tunda yabaro iyayensa bai ta6a samun kwanciyar hankali ko na second d’ayaba saidai yana k’ok”arin 6oyewane saboda Zarah ga kuma ciki da take d’auke da shi bayaso ta silarsa wani abu yasamesu,
janyeta yayi daga jikinsa tare da bud’e idanunsa da suka kad’a sukayi ja, cikin sanyin jiki yace Zarah kukan ya isa haka, kidaina sa damuwa a ranki idan kin ganni haka, kinga bake kad’ai bace kar wani abu yasameku ke da babynmu.

Girgiza kai Zarah tayi tace taya hankalinmu zai kwanta bayan wanda muke a k’ark’ashinsa yana cikin damuwa? Taya zan yafe ma kaina bayan ta dalilina karabu da kowa naka?
K’ara fashewa tayi da sabon kuka sannan tace banso karabu da sumayya ba dan ‘yar uwarka ce ko bakomai itace matarka ka tafarko, indai har saboda ni kasaki sumayya toh wlh na yafe mata abinda tayi min duniya da lahira, please ka amince mukoma gida kamaida matarka kazauna cikin danginka, ko da ace hakan zaiyi silar mutuwar nawa auren.

Wani irin abu yarima yaji ya soki mak’ogwaronsa jin ta ambaci rabuwa da shi, tureta yayi daga jikinsa cikin 6acin rai yace Zarah na sha fad’a miki ko babu ke zan iya rayuwata, ammah kar kik’ara min zancen sumayya dan na riga nayi mata saki ukku kuma kidaina tunanin ta dalilinki nasaketa wlh ko d’aya, na saketane saboda wani dalili nawa kuma idan kin gaji da zama da ni zaki iya fad’amin,,,yana fad’in haka yamik’e yad’auki key d’in motarsa yaficce yabarta nan zaune dan gabad’aya ya kashe mata baki ta ma rasa abinda zatace masa.
Cigaba tayi da kukanta kamar wadda aka aiko ma da sak’on mutuwa, ita takaicinta rabuwar yarima da danginsa gashi kwata-kwata ya kasa fahimtar inda tadosa, dan ita tasan tanason yarima sosai, k’ara sautin kukanta tayi cike da tausayin kanta da mijinta saida tayi mai isarta sannan takwanta nan k’asa.

 

Har akayi sallar isha’i yarima bai dawoba dan haka Zarah tana nan zaune inda take, sallah kawai take tayar da ita, koda yadawo taddata yayi inda yabarta tahad’e kanta da gwiwa cikin ransa duk sai yaji ba dad’i haka yawuce yashige bedroom nan yai wanka yashirya har ya hau gado ya kwanta sai kuma yaji bai iya barinta a wannan halin dan haka yamik’e yafito parlour.

Zarah da tana jin shigowarsa ammah tashare jin bai kulataba ya wuce bedroom yasa siraran hawayen bak’in ciki suka zubo daga idonta, tunani tashiga yi anya yarima da yace yanasonta da gaske yake? Anya ba kawai ya fad’a bane dan yakwantar mata da hankali?, tana cikin haka sai jinsa tayi ya dafata, ahankali tad’ago kanta takallesa,
Cike da damuwa yarima yace Zarah meyasa kikeson d’aga min hankali? Menene abin kuka, ke kuka baimiki wahala na lura, yanzu dai taso muje kiyi wanka ga ice cream chan nasiyo miki kisha kinji?

Zarah shuru tayi nan yarima yataimaka mata tamik’e suka shiga bedroom saida yad’auko mata towel sannan yaje yahad’a mata ruwan wanka, lokacin da yafito har tacire kayanta ta ma d’auka zai taimaka mata tayi wankan ammah sai taga ya je yai zamansa dan haka tawuce taje tayi tana mamakin yarima yadda kwata-kwata shi bai iya lallashin maceba saidai shi a lallashesa.

Bayan ta fito wankan lotion kawai tashafa sai humra sannan tawuce taje tabud’e wardrobe tad’auko sleeping dress d’inta tasaka, zuwa tayi tahau gadon takwanta, yarima kallonta yayi yace bazakisha ice cream d’inba yau?

Kamar tace masa eh ammah ganin tanason sha yasa tamik’e batare da tayi magana ba taje tad’auko tazauna tasha, saida tashanye roba d’aya sannan tamik’e taje tasaka sauran cikin freezer taje tawanko bakinta tadawo takwanta, lokacin yarima har ya kwanta, daga gefensa itama takwanta dan yau haka sukayi kwanciyarsu batare da sunji d’umin junaba, tana jin yarima yana ta juyi batasan ya yak’areba har bacci yai awon gaba da ita.

 

Da asuba bayan sunyi sallah baccinta takoma inda tabar yarima zaune yana dannar system d’insa.

Wajen k’arfe goma da tafarka da mamakinta baya nan, kallon agogo tayi taga har k’arfe goma ta yi, mik’ewa tayi tafito parlour nan ma bainan dan haka tasan ya je wajen aiki, gyara d’akin tayi sannan tashiga tayi wanka tashirya.

Bayan ta gama fitowa tayi main parlour nan tatarar da jamila zaune tana kallo,
Cikin sakin fuska zarah tagaisheta.
Murmushi jamila tayi tace maman baby kin farka, ya gidan.
Lpy lou Aunty jamila, halan har sun ficce.
Dariya jamila tayi tace lokacin kina bacci suka fita dan prince cewa yayi akwai theater d’in da zai shiga k’arfe tara saisa tun 8:30am suka fita.

Numfashi zarah taja tace gaskiya Aunty jamila kina k’ok’ari tun da safe kike tashi kina had’a breakfast.

Toh zarah ya muka iya, indai kace bazaka girka da wuriba ai sai miji yafita batare da yayi breakfast ba daganan kuma sai afara cin abincin masu siyarwa nikuma natsani inga mijina yana cin abincin waje ke ni ko na ‘yar aiki banaso inga yana ci.

Jinjina kai zarah tayi tace wlh nima Aunty jamila banaso inga mijina yana cin girkin ‘yar aiki ammah ba yarda na iya.
Murmushi jamila tayi tace toh ya kuka iya ai gidan sarauta ya gaji haka, kedai shawarar da zan baki kikula da mijinki sosai dan kinsan ‘yan matan yanzu bare ma irinsu yarima na tabbata bakowace mace bace zata gansa batare da taji ya burgetaba, dan rannan mijina ya fad’amin a hospital har ‘yan mata sun fara shige masa dan ma baibasu fuska saisa suke yin baya da shi.

Ajiyar zuciya zarah tasafke tace toh ya zanyi Aunty jamila jin dad’inama da baya kulasu ammah ni kaina indai zai fita hankali baya kwanciya sai yadawo kuma dai gashi badaman ayi masa kulle.

Dariya jamila tayi tace kinjiki da wata magana wai kulle, kedai kicigaba da addu’a Allah yakare miki mijinki.
Ameen y rabb,,nan zarah taje tahad’o breakfast tadawo tazauna tana yi suna hira.

Bayan sun gama a tare suka shiga kitchen suka had’a lunch sannan zarah tawuce part d’insu tayi wanka tashirya.

Wajen k’arfe ukku gabad’ayansu parlour suka dawo suka zauna suna kallo suna hira jefi-jefi har akayi sallar la’asar ammah su yarima basu dawoba, jamila kallon zarah tayi tace mutanen shuru basu dawoba.
Uhm wlh kau Aunty jamila nima tunanin da nake kenan Allah dai yasa lafiya.
Ameen y rabb,,,cewar jamila, suna cikin haka sai ga su yarima sun shigo da sallamarsu.

Juyowa sukayi suka kallesu tare da amsa musu sallamar sannan sukace sannunku da zuwa.

Amsawa sukayi,
jamila ce tace tun d’azun muna ta jiranku ammah shuru.
Dr mu’az kallon yarima yayi sukayi murmushi sannan yace munje neman auren prince ne dan cewa yayi yanaso ya auri ‘yar garin nan,,,yak’arashe maganar tare da kallon zarah da tacika tayi fam.
Jamila ma kallonta tayi tace laahhh my har da kai ake had’a baki dan ak’aro ma gimbiya abokiyar zama? Gaskiya ni ban goyi bayankuba.
Zarah saboda bak’in ciki kamar tad’aura hannu saman ka tafasa ihu,
Yarima murmushi yayi yace toh ya aka iya tunda ina so, yanzu dai bari inshiga ciki ind’an watsa ruwa, batare da ya kalli zarah ba yawuce yashige yana dariya ciki-ciki.

Murmushi mu’az yayi yace sorry gimbiya kar kiga laifina prince ne yaimin dole saisa nabisa mukaje,
Jamila k’unshe dariyarta tayi tace ku dai kukasani nidai ina bayan gimbiya.

Zarah shuru tayi kamar ruwa ya cita ta ma rasa abinda zatace,
Nan dr mu’az yashige yana dariya ciki-ciki.
kallonta jamila tayi tace ranki yadad’e kitashi prince fa na chan yana jiranki.
cike da k’ulewa tace Aunty jamila toh me zanyi masa.
Rik’e baki jamila tayi tace haba Zarah banyi tunanin jin haka daga garekiba ai na d’auka ko da ma kishiyarce bazata firgitakiba tunda kinsan kinriga kin zarce mata, kinga tashi kije kitaimaka ma mijinki nima kinga tafiyata.

Zarah ba dan tasoba tamik’e tanufi part d’insu lokacin da tashiga bedroom tsaye taga yarima gaban dressing mirror yana shafa da alama daga wanka yafito.

Tsaye Zarah tayi tana kallonsa, shareta yayi yai kamar baimasan tana wajenba, bayan ya gama ta gefenta yazo zai gifta yawuce sai a lokacin ya kalleta ta cika tayi fam, danne dariyarsa yayi Sannan yace kekuma fa?

Ai zarah kamar daman jira take yayi magana nan tafashe da kuka,,,,da mamaki yake kallonta yace Allah yabaki hak’uri daga tambaya sai kuka? Toh indai tambayarce toh nadaina nan yawuce yai tafiyarsa yabud’e wardrobe.

Dagudu zarah taje tarungumesa tabaya tacigaba da kukanta.
shuru yarima yayi yana jin kukan nata yana ta6a har cikin ransa,
ganin baida niyar yin magana yasa zarah cikin kuka tace menakeyi maka da kakeso kayi aure? Dan Allah indai wani abu nakeyi maka kafad’amin wlh zan daina,
juyowa yarima yayi yakalleta yaga haik’an take ta kukanta, murmushi yayi yace zarah ni na ce kinmin wani abu?
Girgiza kai tayi tana mai cigaba da kukanta.
tallabo fuskarta yayi yace kuma ni kikaji nace aure zanyi?
Nan ma Girgiza kai tayi.
murmushi yayi sannan yace tsokanarki fa daman mu’az yake dan yaga yadda zakiyi sai kuma gashi ya gani.
Zarah fad’awa tayi jikinsa tana cigaba da kukanta, dariya yarima yayi yace lallai ashe matar tawa tana tsoron kishiya ai na d’auka da jaruma nake zaune.
Duka zarah takaimasa a k’irji cikin kuka tace kai ko? Wlh ban yarda sai na rama,
dariya yarima yayi yace toh nidai bani nayi maganar ba.
‘Dago kai zarah tayi takallesa tare da tsagaitawa da kukan da take tace ina sonka sosai akanka ba abinda bazan iyaba idan mace tara6eka ji nake wani iri sumayya ma dan ba yadda na iya nasan idan nace zanyi kishinta toh banyi ma kaina adalciba.

Murmushi yarima yayi yace aiko sai kinyi hak’uri dan yarima mijin mace hud’une.

Turo baki zarah tayi tace insha Allahu a haka zaka tsaya ba k’ari.
Dariya yayi yace lallai yarinya sai kinji ana gud’a ankawo min amaryata sabuwa gal.

Harararsa tayi cike da k’ulewa tace ai nima d’in gal aka kawo maka ni,
K’unshe dariyarsa yayi sannan yace toh ni mekikaji na ce?

Marairaicewa zarah tayi tace dan Allah kayi hak’uri akan abinda nayi maka jiya insha Allahu ba zan k’araba, wlh bana jin dad’i inga kana fushi da ni duk sai inji wani iri.

Goge mata hawayen fuskarta yayi yace kar kidamu ni ban rik’ekiba daman ai ke bakya laifi.

Murmushi zarah tayi tace ka dai fad’a dai kawai nidai yanzu kashirya muje kayi lunch dan nasan ka kwaso yunwa.
Toh ranki yadad’e yadda kikeso haka za’ayi.
dariya zarah tayi tace au abun harda tsokana?
uhm ni na isa intsokaneki,

nan zarah tataimaka mashi yashirya sannan suka fito inda suka tadda su mu’az suna zaune suna jiransu.

Ganinsu yasa mu’az yakyalkyale da dariya yace prince har ka gama lallashin?
Harararsa yarima yayi yace tunda ka had’aba.
Zarah duk’ar da kanta tayi cikin jin kunya.
jamila tace ammah dai nasan saida akasha da-ga kafin kashawo kanta.
Murmushi yarima yayi yace baby toh gaki gasu kisan zaman da kike dasu dan so suke suga ank’ara miki kishiya.
Turo baki Zarah tayi tace kabarni da su ai insha Allahu dagani ba k’ari ni kad’ai na isheka ko?
Dariya sukasa mata dan yanayin yadda tayi maganar ya basu dariya, yarima murmushi yayi yace kekad’ai fa kin isheni baby.

nan suka wuce dining suna dariya, zarah ganin tsokananta suke yasa tasharesu nan sukayi lunch, bayan sun gama nan taja yarima suka koma part d’insu sukaita shan love d’insu

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_
[5/3, 9:52 PM] Sis Naj Atu:

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

Back to top button