Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 45

Sponsored Links

PAGE* 4⃣5⃣

Ahankali yake warwarewa har yagama sannan yabud’e yafara karantawa gabansane yafad’i ganin sunansa aka rubuta da larabci, sai wasu rubutu da shi kansa baisan menene aka rubutaba saboda mitsi-mitsine daga chan k’asa kuma sunan zarah yaga anrubuta sannan daga gefe akasa d’aya ansa _ni zarah zan mallaki yarima_ gabansane yacigaba da fad’uwa cike da mamaki yace zarah ce tasamin laya dan tamallakeni? Me take nufi da hakan? cikin sauri yaje yad’auko na toilet d’in yawarware sunansa da na zarah kawai ne jikin takardar, tsaye yayi cike da mamaki yana k’ara bin takardun da kallo,

Zarah kwance take d’akinta duk kasala ta rufeta tanaso taje part d’in yarima ammah ta kasa saboda batajin dad’in jikinta, daga k’arshe dai daurewa tayi tamik’e tad’auko alkyabbarta tasaka sannan tafito tanufi part d’insa.

Ahankali tabud’e bedroom d’insa tashiga tsaye tagansa rik’e da layar, juyowa yayi yaimata wani irin kallo, cak zarah taja tatsaya cikin ranta tace shikuma wannan mutumin me yake nufi da hakan?
Muryarsa taji ya ce abinda kikayi shirin yi toh bai yuwuba dan haka sai kicanza sabon shiri ammah ni nafi k’arfin duk wani sihiri.

Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai, ahankali tace ban fahimci akan abinda kake nufiba.

Yarima wurga mata harara yayi yace kar kimaidani wanda baisan abinda yakeba ko kin d’auka banga layun da kika ajeminba cikin toilet da k’arshin pillow na ba, zarah zaro ido tayi tace ni kuma?

Mik’amata yarima yayi yace toh ai sai kiduba kigani idan k’arya akayi miki, cikin sauri takar6a tashiga dubawa, tsoro da fargaba duk suka cikata, cikin sauri tad’ago kai takalli yarima da shima yake kallonta, muryarta tana rawa tace wlh ban aikataba bansan wanene yake neman jamin sharri ba, innalillahi wa’inna ilaihiraji’un, dasauri taje wajen yarima tarik’o hannunsa k’wallah duk ta cika mata ido tace kayarda dani wlh bani bace nakawo maka laya,
Fizge hannunsa yayi cikin d’aga murya yace idan bake bace toh wanene? Kuma sunan wanene a jiki?
Zarah kallonsa take cike da mamaki tace yanzu ka yarda zan iya yi maka asiri? Cike da rashin damuwa yace toh idan ban yardaba me kikeso inyi?
Murmushi Zarah tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace da ace ni mushrikace da ba akanka zan faraba kuma ba zan ta6a amincewa in aurekaba da tun farko zan san yadda zanyi inga ban aurekaba saboda nima inada wanda nake so, kuma da ace ina asiri da tun farko zanyi maka ba sai munkai wannan lokacinba, wlh nagaji da wannan sharrin da ake ja min komawane yaje dan kansa, tak’arashe maganar cikin kuka,

Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d’ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad’in haka tawuce tafita tabar d’akin.

Tafiya take zata koma part d’inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k’afartaba, hawaye d’aya na bin d’aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al’amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka?
Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad’i, cikin sauri taji an rik’ota tafad’a jikin mutum, d’ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad’e meyake faruwa dake ne haka?
Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik’e Zarah suka ida isa part d’in Zarah.

Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d’akin.

Zaunar da Zarah tayi saman d’aya daga cikin cushin sannan tazauna k’asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d’in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad’e meyake faruwa da ke ne?
Zarah ahankali tabud’e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.

Jakadiya gyara zamanta tayi tace gimbiya kifad’a min matsalarki ni nayi alk’awali zan taimaka miki kid’aukeni a matsayin uwa,
Zarah d’ago kai tayi takalli jakadiya har a lokacin hawaye suna zuba daga idonta cikin muryar kuka tace ya akeso inyi da rayuwata? Narasa wanene yake k’ullamin sharri da angama wanchan sai afad’a ma wannan shin ya akeso inyi? Ni zan iya hak’ura da auran inkoma gidanmu,
Cikin sauri jakadiya tagirgiza kai tace a’a ranki yadad’e kar kice haka dan Allah kifad’amin abinda yake faruwa nayi alk’awali zan taimaka miki.

Zarah kallonta tayi cike da gamsuwa da maganar jakadiya sannan takwashe duk makircin da akeyi mata tafad’a ma jakadiya,

Jakadiya jinjina kai tayi tace wannan ba aikin kowa bane sai na gimbiya sumayya,
Zarah cike da mamaki tace yanzu kina ganin itace zata yi min haka?
Jinjina kai jakadiya tayi tace tabbas itace dan nasan wacece gimbiya sumayya da mahaifiyarta fiye ma da haka zasu iya yi.

Zarah share hawayen fuskarta tayi tace toh wlh zan iya hak’ura da auren inkoma gidanmu.

A’a gimbiya kar kice haka bai dace kikaraya ba, mu munsan halinsu, kuma sumayya da kikaga yarima ya aura toh auren had’ine ba auren soyayya bane sukayi.

hatta shi kansa yarima da kike gani akwai abinda mahaifiyar sumayya take k’ullawa akansa wanda ita kanta sumayya bata saniba.

Zarah ido tazuba mata cike da mamaki.

Jakadiya tacigaba da cewa akwai wani lokaci da dada ta aikeni wajen sultana sadiya, lokacin da nashiga parlour bakowa har na juyo zan baro d’akin najuyo magana k’asa-k’asa a bedroom d’in sultana sadiya tsaye nayi lokacin da najuyo tana cewa so take gimbiya sumayya tahaihu idan yaron yafara wayau tanaso tabi kowace hanya dan ganin ta kawar da yarima inyaso mijinta abashi rik’on k’warya kafin jikan nata yagirma daga baya yazama shine sarkin gari, ta san idan yahau toh sai yadda taso mulkin gidan zai tafi, dan ta tsani mahaifiyar yarima taso ace itace tahaifi d’a namiji Wanda zai gaji garin ba mahaifiyar yarima ba, ina jin haka cikin sauri nafito nabaro part d’in gudun kar taganni dan nasan idan taganni toh bazata ta6a barinaba.

Zarah cike da rud’ewa tace daman haka matarnan take? Toh shi yarima baisan halintaba ya amince ya auri d’iyarta.

Murmushi Jakadiya tayi tace tabbas yarima yasan kad’an daga cikin halayyarta dan tun yana k’arami idan yaje part d’inta wahalar dashi take dan akwai lokacin da tata6a watsa mai ruwan zafi, tagargad’e ni da idan nafad’a ma wani sai tayi sanadiyar barina aiki, kasancewar nikad’aice lokacin da abun yafaru.

Toh ba’a gane taba? Cewar zarah.
Eh toh, yarima yana da wani irin hali wanda ba komai bane yake iya bud’e cikinsa yafad’aba wannan halinsane tun yana k’arami, kuma na tabbata shi kansa yana sane da abubuwan da tayi masa kawai dai ya sharene,
indai wajen makircine toh kala-kala matarnan ta iya dan ina tunanin dasa hannunta sumayya takeyi miki wad’annan abubuwan.

Zarah jingine kanta tayi cike da jin tausayin mijin nata, Jakadiya tace ranki yadad’e kigode ma Allah da basubi ta wata hanyarba dan ganin sun kawar da ke, koda basubin boka ammah sun san makirci kala-kala.

Jinjina kai zarah tayi cike da mamakin halin su sumayya, ahankali tace duk makircinsu basu isa suyi abinda Allah bai nufa ba, kuma ina neman kariya daga ubangijina, saidai bansan yadda zanyi inshawo kan yarima yafahimceniba.

Jakadiya tace kar kice haka ranki yadad’e kuma baidace kiga laifin yarima ba tunda duk baya makircinsu da suke miki baiyi tasiriba a garesa ammah a yanzu kiduba kiga har da sunansa da naki aka had’a kinga ai bakowa bane zai iya k’in yarda, yanzu dai abu d’aya zakiyi shine nake tunani kamar zai taimaka wajen ganin kin ku6utar da kanki, zarah kallon Jakadiya tayi tace wane abune please kifad’a min.

nan Jakadiya tace kice yatambayi guards d’insa sufad’i Wanda yashiga da baya nan tunda ke kince baki shigaba,
Zarah tace anya kina tunanin zai amince?
Eh insha Allahu ai ya aminta da su yasan bazasu ta6a yi masa k’aryaba,

Zarah jinjina kai tayi tace nagode sosai jakadiya, hak’ik’a kin taimakeni a lokacin da nake buk’atar taimako nakekai kukana ga ubangijina,

Jakadiya tace kar kidamu gimbiya har cikin raina nake jinki dan kece kikafi dacewa da yarima ba sumayya ba kuma ina fatan yakasance kece zaki fara aje mana magajin yarima.

Zarah saida gabanta yafad’i dasauri tagirgiza kai tace kar kice haka, sumayya ita tafi dacewa tahaihuwa da yarima.

‘Yar dariya jakadiya tayi tace tuni tayi watsi da damanta koda haka mahaifiyarta taci buri itama ammah a yanzu k’addara ta riga fata,

Zarah cike da mamaki take kallonta tace ban fahimci abinda kike nufiba?
Murmushi jakadiya tayi tace kar kidamu dasannu zaki fahimta nan ba da dad’ewaba, jakadiya tana fad’in haka tamik’e tare da d’an rissinawa tace nabarki lafiya ranki yadad’e.

Zarah d’aga kai tayi tace nagode sosai jakadiya saidai ince Allah yabaki ladar abinda kikayi min.

Jakadiya murmushi tayi tace kar kidamu ai yi ma kaine, nidai fatana kirik’e sirrin maganar da nafad’a miki.

Zarah murmushi itama tayi tace insha Allahu babu wanda zai san maganar nan bayan mahaliccinmu sai ni da ke.

Jakadiya tace nagode, nan sukayi sallama tafita, zarah tsaye tayi tana tunani cike da jinjina ma sumayya da mahaifiyarta sannan daga baya tawuce tashige bedroom d’inta takwanta, nan hawaye suka cigaba da fita daga idonta tana tunanin hukuncin da yarima zai yanke mata akan laifin da ba ita ta aikata shiba, fashewa tayi da kuka tace ya ubangiji kakawo min d’auki, kuka tayi sosai saida taji kanta ya fara ciwo sannan tadaina haka taita juyi saman gadon daga k’arshe bacci yayi awon gaba da ita.

 

Yarima bayan zarah ta fita zama yayi saman gadonsa tare da dafe kansa cike da takaici, mamakin zarah ne yakamasa dan baita6a tunanin haka daga garetaba tun daga yanayin tarbiyarta, ya dad’e zaune yana jinjina lamarin dan abun ya d’aure masa kai sosai dan idan ya ce ba ita bace toh wanene zaiyi hakan?, tsaki yaja cike da takaici sannan yakwanta abu guda yatsaya masa a rai kalmar da tafurta ta nima ina da wanda nakeso, haka kalmar yaita jinta a kunnensa tana masa yawo har daga k’arshe bacci yad’aukesa..

 

A chan 6angaren sumayya kiran sultana sadiya tayi tana yin picking bata bari tayi ko sallama ba cikin jin dad’i tace ummah na aiwatar da komai kuma ina tunanin nasara a cikin aikin namu, daga chan 6angaren sultana sadiya dariya tayi tace gaskiya naji dad’i daughter ai ina fad’a miki ta ruwan sanyi zatabar gidannan dan makirci kala-kala babu Wanda ban iyaba idan akayi wani baiyiba sai acanza wata hanyar, cikin jin dad’i sumayya tace saisa nake k’ara sonki ummana dan duk abinda nakeso kema kinasonsa na rabbata yanzu yarima zai zama nawa ni kad’ai.
Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kar kidamu d’iyata farin cikinki shine nawa, saisa nake burin kihaifo min jika wanda zai gaji masarautar nan ammah kinkasa fahimtar inda nadosa, Indai kinsan kina yin planning toh kitaimaki kanki kidaina tun kan waccan munafukar tafara haihuwa,
Gaban sumayya saida yafad’i dan bata ta6a yin tunanin hakaba, ahankali tace hakane kuma ummah insha Allahu bama zata haihuba zata bar gidan.
Sultana sadiya tace na dai fad’a miki kirufa ma kanki asiri kidaina.
Cikin shagwa6a sumayya tace toh ummah na ji.
Uhm Allah yasa dagaske, cewar sultana sadiya.
Ameen ummana.
Yauwa toh yanzu kikwanta kiyi bacci dare keyi.
Toh ummah ko mi kenan sai kinjini, nan sukayi sallama suka kashe wayoyin.
Sumayya fad’awa tayi saman gadonta cikin murna tace yes nasan zuwa gobe waccan munafukar zata koma kongon gidansu, ahaka tayi bacci cike da farin ciki.

 

Cikin dare zazza6i da ciwon kai suka tashi zarah daga baccin da take nan taita juyi saman gadon daga k’arshe k’asa tasafka takwanta, ciwon cinta yake babu wanda zata iya kira dan ko hannunta kasa d’agawa tayi daga k’arshe, tana nan tana juyi ahaka aka kira sallar asuba.

Har aka gama sallah akan kunnenta ammah takasa tashi dakyar tasamu tamik’e tana dafa bango har tashiga toilet, saida tahad’a ruwan d’umi tayi wanka sannan tad’auro alwallah daga zaune tasamu tayi sallah sannan talalubo paracetamol tasha, nan saman darduman tayi kwanciyarta har saida gari yafara yin haske sannan tamik’e tajanyo alkyabbarta tasaka, cikin rashin k’warin jiki tafito duk wanda yaganta ya san batada lafiya, ko da kuyanginta suka gaisheta hannu kawai tad’aga musu taku take dak’yar tana dafa bango tana tsayawa tahuta ahaka ta isa part d’in yarima.

Tana murd’a k’ofar bedroom d’in yarima tsaye tayi tare da jingine kanta jikin k’ofar tana maida numfashi,

Yarima da daidai lokacin yasafka daga saman gadonsa tsaye yayi yana k’are mata kallo ko da cikin fushi yake da ita ammah hakan bai hana yaji wani iriba da yaganta cikin yanayin.

Zarah ahankali tatako tamatso kusa da shi, yarima d’aure fuska yayi yace meyakawoki wajena? Ko wani abun kikazo kik’ara shirya min?

murmushin k’arfin hali tayi sannan ahankali tace nasan kana jin haushina akan abinda yafaru, shuru tayi nad’an lokaci sannan tace ammah dan Allah ina neman alfarma guda,
saida takalli cikin idonsa sannan tacize le6e cike da dauriya tace kataimaka kayi bincike kafin kazartas da hukunci, katambayi guards d’inka sufad’a maka wanda yashigo part d’inka da bakanan dan ni wlh duk jiya ban shigoba sai dare, k’wallah ce tacika mata ido tace bawai na ce kar kad’auka ba ni bace sannan kuma ban hanaka d’aukar matakiba idan kagane niceba kawai ina tunatar da kai ne kar kayanke hukunci batare da kayi bincikeba, a kullum addu’a ta Allah yabayyanar da gaskiya bazan ta6ayin bak’in cikiba idan hakan yazama k’arshen tarayyarka da ni, saboda ni nasan gaskiya bata k’arewa saidai k’arya tak’are,

Yarima cike da mamaki yake kallonta koda ya san har cikin ransa ya san maganganun da tafad’a gaskiya ne ammah hakan baisa yanuna a fili ya aminceba, zarah dafe kanta tayi ahankali tace na barka lafiya juyawa tayi tana fara tafiya nan jiri yakwasheta tayi baya zata fad’i.

cikin sauri yarima yatarota tafad’o jikinsa, ahankali yafurta ya salam, saboda wani irin zafi da yaji jikinta saikace zafin garwashi, rikicewa yayi yama mance da abinda yafaru cike da damuwa yace zarah daman bakida lafiya? Me yake damunki? Lokaci guda yajero mata tambayoyin duk ya rud’e.

Zarah dak’yar tabud’e idonta tare da dafe kanta da yake sara mata, cikin muryar kuka tace kabarni inma mutuwa nayi babu abinda yadameka, wlh abinda akeyi min ya fi wannan ciwo kabarni kawai inmutu kowa yahuta, k’ila idan namutu zaka yarda da magana ta,
Yarima cike da rud’ewa yace kidaina cewa haka zarah, kifad’amin abinda yake damunki,

Zarah turesa tashiga yi cikin kuka tace ni kabarni wajen mamana zanje nasan su zasu fahimceni tunda sunsan abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iyaba.

Yarima rungumeta yayi a jikinsa yace kidaina cewa haka zarah, baisan lokacin da yayi su6ul da baka yace nima na yarda da ke.
Zarah idanuwanta suna lumshe batare da ta bud’eba tace dagaske ka yarda da ni?
Shuru yarima yayi yana mai nazarin maganar sai kuma chan yace eh.
‘Dan guntun murmushi tayi sannan ahankali tace nagode.
Chak yarima yad’auketa yad’aurata saman gadon yakwantar da ita, wayarsa yad’auko yakira Dr feedoh (babbar likitace ta 6angare mata da take aiki a hospital d’insa) bayan sun gaisa yace kizo gida kisameni, cikin sauri tace toh ranka yadad’e, kashe wayar yayi tare da kallon zarah da taketa cize le6e tana girgiza kai daga ganin yanayinta kasan tana jin jiki, sannan yace ina zuwa, yana fad’in haka yafita
wajen guards d’insa yaje suna ganinsa duk suka duk’a suka kwashi gaisuwa,
yarima hannu kawai yad’aga musu sannan yakallesu d’aya bayan d’aya……….

 

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_*Wannan page d’in tukuicine agareki mummyna chubad’o muhammad, hak’ik’a kin wuce duk yadda kike tunani a zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare mummy*_

Back to top button