Yar Zaman Wanka 9
️9️⃣
“`TASALLAH“`
Tun da Inna Azumi ta fito daga turakar Malam ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, hankalinta ya tashi, ji take tamkar ta je ta dokewa Inna Azumi ƙafa ta karyata katsak ta ga da ƙafar da za ta tafi birnin, ta san dai duk nacin son tafiyarta ba ta tafi da ƙafa a karye ba.Ta so ta nemi alfarmar Inna Azumi a kan ta tafi da ita ko ta ga yadda birni yake amma kuma girman kai rawanin tsiya ba zai barta ta aiwatar da hakan ba, ko ma an yi hakan to kuwa ta san ba za ta tsallake zunɗen mutanen gari ba, a kan cewa ta tafi dangin kishiya shishshigi da neman ɗuwawun zama, bayan nan ta san duk sanda suka dawo ta jawa kanta gori har da gore-gore daga Inna Azumi wanda babu ranar ƙarewarsa .
Takaicin kishiyar tata take ta ƙoƙarin dannewa, wai har da cewa ta riƙa mata sana’ar ƙuli-ƙuli, wannan abu ya mugun tsaya mata a rai. Wato saboda ita basu da kowa a birni hasali ma bata san hanyar da ake bi aje birnin ba, shi ne Malam zai bata izinin tafiya ZAMAN WANKA har kwanaki hamsin saboda yana tsoronta.
“Tasalla ki cigaba da bani labarin mana ke d kike bani labari amma kin yi shiru kamar ruwa ya cinyeki” Cewar Malam ganin tun fitar Azumi Tasalla ta sunkuyar da kai ƙasa ita ba mai zaman makoki ba ita ba mai lazimi ba, gata nan dai kamar an dasa ta.
Dakyar ta danne wani wahaye da yake ƙoƙarin fin ƙarfinta, ta yi dariyar yaƙe ta ce.
“Ai a nan labarin ya ƙare” Ta faɗa kan nata dai a sunkuye dan tana ɗagowa hawaye ne zasu malalo mata.
“Ikon Allah ke fa kika ce mahaukacin ya biyosu suna ta shirgar gudu a titi ana ƙafa mai na ci ban baki ba, ai labarin daga ji ba a kai ƙatshensa ba amma kuma ki ce ya ƙare” Malam ya tambaya mamaki fal fuskarsa.
“Na ce maka a nan labarin ya ƙare” Ta faɗa ƙwalla na cika idanunta daf take da gangarowa amma ta hanasu fitowa dan kissa da kisisina, dan kar Malam ya ce dan Inna Azumi za ta je birni take yin kuka dan tun da ta share hawayen farko a ɓoye bata bari wasu sun biyo bayansu ba.
“To ai shikenan, bari na fita na ga tafiyar Azumi kar ta ɗauki ƙafa cewar ko tafiyarta ban gani ba, haka ya ɗora babbar rigarsa a kan kayan jikinsa ya fito ya barta, dai dai an ɗakkowa Inna Azumi kayanta.
Tasalla kwa na ganin fitar Malam sai ta fashe da kuka tana jin ina ma ita ke ƴan uwa a birni ta zo tafiya Malam zai rakata ya ga tafiyarta a bi da ita ta tsakiyar gari tana washe baki.
Amma ina gabaɗaya danginta a ƙauye suke, Malam tana jin lokacin da Malam ke cewa Inna Azumi jakar nan kamar wanda za ta ƙaura hakan ya sanya ta tashi ta leƙo ta tagar ɗakin Malam ɗin aikuwa ta yi ido biyu da jakar Inna Azumi da ke shaƙe da kaya almajiri na riƙe da ita.
“Wayyo ni dama ban haɗa kishi da wacce take da dangi a birni ba da na huta da baƙincikin tafiyar Azumi” Ta faɗa a ranta tana sharar hawaye. Tun da Malam ya fita bai dawo ba har ta gaji da zaman ɗakin masa ta fito ta koma ɗakinta, dan lokacin da ta fito ma da ta yi tozali da ɗakin Inna Azumi rufe da kwaɗo sai da ta ji kamar ta yi ta zabga ihu da kururuwa mutane su kawo mata ɗauki, dan halin da ta tsinci kanta a ciki.
Tana shiga ɗakin ta zauna a ƙasa ta shiga rasga kuka kamar wata ƙaramar yarinya kowacce aka ce ubanta ya mutu, sai da ta yi mai isarta ta nemi wuri ta kwanta tana ta saƙar jaki, ta saƙa ta kwance, addu’a take ta yi a zuciyarta Allah ya sa Inna Azumi su faɗi a machine ta ji ciwon da zai hanata tafiya birni ZAMAN WANKA. Jin shiru-shiru bata dawo ba kuma ba a kawo mata wani labari ba ta san cewar Inna Azumi ta tsallake.Haka ta tashi tana ta ƙuncin rai ta ɗora tukunyar danbun rana tana jin a ranta cewar yanzu kenan ita za ta ke ta ɗorawa da sauke wa tun da Azumi birni ta ɗauka.
A haka ta kammala danbun ta raba ta baiwa kowa nasa, Malam kuwa saƙon tafiyarsa wani ƙauye kusa da su ɗaurin aure ya aiko mata, hakan ya sanya ta zuba danbun nata ta shiga ɗaki, zaune take a ɗakin nata ta sanya danbun a gaba amma saboda tsabar kishi da baƙinciki ta kasa cin ko da loma ɗaya ne.
“Ni da cin danbu yana shaƙe min wuya ina korawa da baƙin ruwa ita kuma tana can za ta ke cin shinkafa da miyar ɗanyen kaya ta kora da lemon kwalba ta yi kuɓulɓul da ita” Ta faɗa tana jin wani takaici. Haushi ne ya sa ta sanya ƙafa ta hankaɗe kwanon danbun ba tare da ta ci ko da loma ɗaya ba.
Bayan ta kammala tuwo dab da magariba, lokacin Malam yana waje wurin almajirai ana karatun yamma. Ɗaki ta koma har lokacin ranta ba daɗi a kan tafiyar Inma Azumi birni dan wunin yunwa ma ta yi saboda baƙinciki. Tana ɗakin ta tsinkayi sallaɓar Tsahare aminiyar Inna Azumi, duk a tunanin Tasalla Inna Azumi sun faɗi a machine ne Tsahare ta samu labari ta taho dubiya.
“Wataƙila tana asibitin bayan gari” Ta faɗa tana tashi har da taka rawarta ita ala dole Inna Azumi bata samu tafiya birni ba, sai da ta gama taka rawarta ta ɗaga murya ta amsa sallamar Tsaharen, ta fito baki a washe tana ta fara’a kamar ranar salla.
Mamaki ne ya kama Tsahare ita dai ta san duk ranar da ta zo gidan nan konda Tasalla tana tsakar gida Inna Azumi na ɗaki to kuwa Tasalla ba za ta amsa sallamarta ba sai dai Inna Azumi ta amsa mata, amma sai gashi yau wai ita ce har da washe mata baki. Gaisawa suka yi cikin mutunci Tasalla tana jira ta ji ta ce mata ya mai jikin amma sai ta ji ta ce.
“Ikon Allah ashe dai da gaske ne?”
“Hatsarin wai?”
“Subhanallahi! Su waye kuma suka yi hatsari?”
“A’a ba hatsari aka yi ba, kawai dai na faɗa ne” Cewar Tasalla cikin wayancewa ganin babu alamar Inma Azumi ta yi hatsari dan ga mamaki nan ƙarara a fuskar aminiyarta.
“To da mai kike tambaya da gaske ne?” Tasalla ta faɗa tana tana wani haɗe rai tamkar ba ita ce ke washe haƙora ba yanzu, jin haƙarta bata cimma ruwa ba.
“Ni fa mai machine ne ya je gidana ya xe min wai Azumi ta ce ya faɗa min ta tafi birni ZAMAN WANKA babu ma ranar dawowarta, wai tafiyar ce ta zo mata a bazata, shi yasa bata je min sallama ba, wai in shirya in je ranar suna, to shi ne fa na ce bari in je gidan in tabbatar to kuma ina shigowa kwaɗon ƙofarta ya tabbatar min da gaskiyar al’amarin” Cewar Tsahare tana washe baki.
Wani haushi ne ya turnuƙe Tasalla kawai sai cewa ta yi.
“Wai sun isa Garkin lafiya kenan?”
“Lafiya ƙalaw dan mai machine ɗin da ya kaita ma ya ce sai da motarsu ta Kano ta tashi ya kamo hanyar dawo wa”
“To ai shikenan, kuma za ki je sunan?” Tasalla ta tambaya tana kafe Tsahare da ido.
“Zuwa kamar da ƙasa ma kuwa, kin san ko bikin jikar tata Sadiya wacce ta haihun yanzu mun je bikin kwanana uku, bare kuma samun ƙaruwa ai mu dole ne ma birni ta ɗauka” Ta faɗa tana washe baki dan ta turawa Tasalla haushi, tun da ba wani zama lafiya suke ba da Inna Azumi dan haka ko lokacin bikin ma bata gayyaci Tasallar ba.
Taɓe baki Tasalla ta yi ta juya ta shige ɗaki abinta, ita kuma Tsahare ta fita daga gidan tana jin daɗi cewar gaske ne Inna Azumi ta tafi birni ashe wannan karon ma akwai wankin ciki da na baki.
Tasalla na shiga ɗaki ta rinƙa gewaye -gewaye ta rasa abin da yake mata daɗi, dan haka ta ci alwashin da Tsahare za su je sunan nan sai dai ta fanjama fanjam ta san abin da za ta faɗawa Malam ya barta su je birnin.
“`MAMA“`
Tun a napep ɗin suke ta jajanta halin da zaman Inna zai kasance a gidan Sadiya yadda Imran yake da faɗin rai ga girman kai rawanin tsiya, bugu da ƙari ma baya ƙaunar mutane su raɓeshi, ga Inna kuma da ɓaranɓarama, kwata -kwata bata yin abin da ya dace sai ta saki baki ya layar mai tafiya ta rinƙa zuba kamar lalataccen famfo babu ruwanta da mijin Sadiyar bare kuma mahaifiyarsa, tabbas dai akwai gwarama dan Imran ba ƙyalewa zai ba ita ma kwa Innar bata tsoron ta mutu bare ta yi rai kawai komai ta fanjama fanjam.
“Amma Mama bakya gani tsofa ne ke sanya Inna waɗannan abubuwan?” Ashrof ta tambaya tana kallon Mama.
” Haba Ashrof ko ma da tsufa ai da sha’anin Inna wani abin ai dole take kauda kai, ki ga fa daga cewa Sadiya tana naƙuda shikenan ta haɗo kaya shimili guda ta taho ZAMAN WANKA, ba tare da ta sanar da kowa ba”
“Kuma haka ne, amma gaskiya ya kamata ta canja halinta Mama ko dan take ja mana girman mu a wajen Hajiya da kuma Imran ɗin ma dan irin wannan ai sai ya ta ja mana raini”
“Yo na nawa kuma an ce da kuturu a gama lafiya, ai sai dai kar a ƙara kuma in da sabo ai su ma zuwa yanzu sun san wacece Inna”
“To Allah kyauta”
“Amin”
A haka dai har suka isa gida suna fitowa daga napep ɗin Mama ta buɗe musu gidan suka shiga. Bayan sun ɗan huta suka rama sallolin da ake binsu, sai Ashrof ta fita ta siyo musu awara suka ci suka kwanta suna ƴar hira.
“Wai Mama baki lura da yadda idon Inna suka firfito ba lokacin da zan miƙa mata hassan, bakinta sai mutsi yake kamar mai zikirin safiya da maraice” Ashrof ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya.
” Yo tsoronsa fa take, dan ta ji an ce fatar bayansa irin ta miciji, ban da Inna menene na tsoro ita da za ta yi ZAMAN WANKA, wankansu fa da shirya su har ma da goyo da raino duk ita fa za take yi” Mama ta faɗa tana ƴar dariya hasasho yadda za ta kaya tsakanin Innar da Hassan da ma ubansa Imran.
“Allah Mama ni fa tausayi take bani, yanzu wanann ƙatuwar tukunyar ta yaya za take ɗorawa a murhu da ruwa ai ba za ta iya ba ma, idan kwa ta tarka wallahi wataran sai dai ta tumbulu cikin ruwa dan hantsilawa ciki za ta yi” Ashrof ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya.
“Baki da dama Ashrof wato dan kin ga Inna bata nan ko, shi sa kike faɗar hakan amma da tana nan si ta baki amsa dai dai da ke”
“Mama har hango Inn fa na yi ta faɗa ruwan tana iyo kamar kwaɗo tana neman ɗauki, Yaya Imran yaƙi fiddota, tana cewa Imirana ka ji tsoron Allah ka fiddoni, idan na mutu nauyi ya rataya a wuyanka, shi kuma ya ce mata in kin mutu dama kwananki ne ya ƙare” Ta ƙarasa faɗa tana dariya har da riƙe ciki hango yadda za a yi diramar kawai take.
“Ke ki kiyayeni, in ke kakarki ce ai ni uwa ce a wurina” Mama ta faɗa tana dariyar ita ma, dan ta san tabbas da ace hakan za ta faru Imran ba zai fito da Innar ba musamman in aka ce Sadiya bata kusa ko da zai fito da Innar daga tukunyar to sai ta sha wahala ita ma kuma idan ta fito sai ta rama ta wata hanyar dan bashi ya ci daga haka suka kwanta abinsu.
“`HAJIYA“`
Tun da ta sauka a napep ɗin ta shiga gidan nata jiki sanyi ƙalaw dan kwata -kwata haɗin Inna da Imran bai yi ba musamman da ya kasance za ta shiga haƙƙinsa na rabashi da kwana wuri ɗaya da masoyiyarsa dan ta san Inna ko giyar wake ta sha ba za ta bari su kwana ɗaki ɗaya ba ma bare kuma wuri ɗaya sai dai ta san Imran dai dai yake d Inna duk ta yadda ta ɓullo masa sai ya zame duk da dai ta gargaɗeshi a kan zaman Innar a gidan.
“`INNA“`
“Imirana kar ka jinkirta wajen amsa kirana dan Allah ina cikin halin ƙaƙanika yi” Cewar Inna har lokacin hannunta da gabaɗaya jikinta ma tsuma suke suna karkarwa kamar an jona jikinta a wutar nepa ko transpomer.
Imran kuwa yana jinta banza kawai ya mata dan ya san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, tabbas ya riga da ya san cewa arba kawai ta yi da bayan Hassan. Jin kiran nata ya cika masa kunne tare da karaɗe gabaɗaya gidan hakan ya sanya ya kwantar da Husaini a kan kujerar ya tashi a hankali ya leƙa ta jikin labule ba tare da ta sani ba.
Hangota ya yi a zaune magashiyan ga uban baho ɗauke da ruwa, sannan ga Hassan ɗin a hannunta sai jijjiga hannunta ke yi.
“To fa ga zara ga wata” Ya faɗa yana komawa ya zauna a kujera yana dariya ƙasa -ƙasa yadda ba za ta jiyo ba.
“Imirana wallahi ina cikin matsala dumu-dumu, ka zo kar yaron nan ya koma maciji gabaki ɗaya, in shaga uku, dan idan na ganni da riƙe da miciji muraran babu shamaki suman da zan yi sai ya fi cikin carbi idan ba dakyar ba ma na ƙarasa ƙiyama a haka” Inna ta faɗa tana sakin kuka.
Jin shiru dai babu alamar motsin Imran gashi ta san ko ta kira Sadiya ba jinta za ta yi ba dan tana can a bayi, kuma bayin a rufe, sannan ma ita kawai so take a taimaketa a rabata sa yaron a karɓeshi daga hannunta dan ta ma kasa jajiyeshi.
“Imirana wallahi mutsu-mutsun da yake a hannu na yana motsi ji nake kamar maciji na riƙe, yo ina daɗi ace ina riƙe da ajalina, yo maciji ai mutuwa ne, wannan ai mutuwa kusa ne” Ta faɗa tana ɗaga muryarta dan Imran ya kawo mata ɗauki.
“Wannan tsohuwa da zan san inda MALAM Abubakar bilhaƙƙi mai magununan nan da ake tallarsa a tv wallahi da na ce masa ya zo ga wacce za take masa talla ba sai ya sha wahala ba dan tsaf za ta ke karaɗe gidan talabijin da wannan shegen surutun nata marar kan gado marar kai da ƙafa.Ya faɗa yana tasowa daga kan kujerar ua nufi ɗakin.
“Yawwa ɗan albarka ai gwara da ka tausaya min ka zo”
“To wai meye kika dameni da kira kamar wata makauniya” Ya faɗa yana kallonta.
“Haba Imirana da rashin kira karen bebe ya ɓata”
“To gani ai”
“Riƙa nan riƙa Imirana” Ta faɗa tana ɗago Hassan ɗin.
“Kamar ya na riƙa Inna, ni zan masa wankan ne?”
“Haba Imirana shin kusan haka jikin yaron nan yake amma aka bari na tuɓeshi tsirara na yi mugun gani”
“To menene a ciki”
“A’a sa komai a ciki mana, kasan kowa da kiwon da ya karɓesa wai maƙocin mai akuya ya sayi kura”
“Ki masa wankan mana”
“To inda riƙeshi in dubo Halima a bayi”
“Haba Inna in mafaɗin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa bane” Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma ya ce.
“Bari na dubo miki ita da a kan dubo Sadiyar ne kike ta wahalar da kan ki har da kuka Inna”
“Ka karɓesan dai ni na dubo ta, ka san mutum baya ƙin ta mutane wai an ce ɓarawo ya gudu”
“Inna magana fa zarar bunu ce, ke kika ce mun san jikin yaron nan haka yake kika tuɓeshi yanzu kuma kin canja maganar kenan”
“Bari dai in fito maka a mutum Imirana, karɓi yaron nan dan ba zan iya tashi in ɗorashi a gadonsa ba saboda yadda jikina ke tsuma ga arangamar da na yi jiya da dare duk jikina ciwo yake, ka karɓeshi kar in je in luntumashi a ruwa, dan ni ban ma yarda ɗan mutuma bane wannan”
“Ɗan nawa ne ba ɗan mutum ba, to wallahi kika saka shi a ciki sai mun yi shari’a”
“Yo in ba ɗan aljan…Shiru ta yi da faɗar aljannun tunowa da ta yi da yadda suka kwashe da aljani da dare har ta ƙarasa kwananta a ƙasan gado hakan ya sa ta saki akalar maganar ta kama wata.
“Da za ka yarda ku kai shi bakin ruwa a gani indai ya gangara ya shige ruwa to dama ɗan ruwa ne, in ba haka ba tayaya zai yi rabi mutum rabi miciji”
Kan ta kai ƙarshen maganar Imran ya sanya hannu ya karɓe ɗansa cikin zafin nama da jin haushin Inna yana raya wani abin da zai mata dan bashi ta ɗauka cewa ɗansa ɗan ruwa da ta yi.
“Wash Allah, ai gwada da ka karɓeshi, ai dama kowa da kiwon da ya karɓeshi wai maƙocin mai akuya ya sayi kura, wato ga Inna ƙaramar danga mai daɗin tsallaka, kamar ni a ce a sanya min linzami a baki yo da bakina wa zai hanani magana, aikin banza harara a duhu” Ta faɗa lokacin da ta sauke wata ajiyar zuciya ta tashi ta zauna a bakin gadon tana sakin maganganu. Wani kallo Imran ya watsa mata yana ji kamar ya shaƙeta.
“Aikin banza harara a duhu, ni ban san harara ba sai ido ya faɗo” Ta faɗa tana tana gyatsinan gefen hanci.Imran da ke ƙoƙarin fita daga ɗakin sai kawai ganin kan Hassan ya yi yana wani kamar lanƙwasa kawai sai ya koma kamar yadda kan maciji yake lokacin da ya fasa kai, sai ganin fatar cikin yaron ma ta fara komawa irin fatar bayan, Inna bata lura da abin da ya gani ba dan haka cikin sauri ya kalli ƙasa inda shawul ɗin Hassan da Inna ta ajiye ya ɗorashi a hankali, cikin hanzari ya fita daga ɗakin tare da rufe ƙofar ɗakin ya sanya mukulli.
Inna da ta lura da fitarsa bata san ya ajiye Hassan ɗin ba sai ƙaran rufe ƙofar kawai ta ji, Ta zabura za ta tashi sai ji ta yi Imran ya ce
“Inna kalli Hassan ki gani gashi nan na ajiye miki shi”
Idanu Inna ta zaro ganin fatar cikin yaron ta rikiɗe zuwa irin fatar bayansa, wani uban ƙara ta ƙwalla, dan yaron a setin hanyar da za ta sada ta da ƙofa yake gashi ma ta ji Imran ya rufe ƙofar tare da sanya mukulli…
Masu son grp na zaman wanka
MMN AFRAH 09030283375
ƳAR ZAMAN WANKA
(KWANA ARBA’IN)
NA
MAMAN AFRAH