Yar Zaman Wanka 7
️7️⃣
Inna na nan zaune abin duniya ya ishe ta, jin sun yi ɗif basu da alamar fitowa, wajen gadajen yaran ta nufa sai da ta ƙare musu kallo ta gane Husainin dan bata so ta taɓa Hassan, hannu ta sanya ta ɗan jijjigashi aikuwa ya ɗan motsa ya yi ɗan kuka kaɗan.
“Ka yafe min ɗan nan ba da niyya zan yi ba ban son na ɗauki alhakinka, jihadi zan yi in ƙwato waccen shakatafin gyatumar taka, da babanka ke neman wuce gona da iri” Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
“Halima zo ɗan nan ya motsa”
Sadiya da dama ta ji ɗan kukan da Hussainin ya yi, hakan ya sanya ta ɗakko kwanon furar da Imran ya sha dan ta fito da shi, tana zuwa idanunta suka sauka a kan Inna da ke ƙoƙarin ƙara taɓa Hussainin da zuwa lokacin tuni bacci ya ƙara surarsa ya yi awon gaba da shi.
“Dama na yi zaton hakan, haba Inna yanzu meye amfanin tashin yaron nan”
“Ya koma bacci abinsa fa Halima, tashin sa ya yi amfani mana, tun da gaki kin fito dama kuma burina kenan”
Da ido kawai Sadiya ta bi Inna ta fice daga ɗakin domin kai kwanon kicin.Tana dawo wa falon ta samu Inna ta rafka uban tagumi, ji ta yi wani tausayin Innar ya kamata hakan yasa ta ce.
“Inna ko bacci kike ji ne a ɗakko miki katifa, akwai ƙaramar katifa sai a sanya miki a nan ɗin ko?” Ta faɗa tana kafe Inna Azumi da ido ganin ta yi saurin ɗauke hannunta daga tagumin.
ta saki baki ya layar mai tafiya tana kallon Sadiya.
“Ko da wani abun ne Inna?”
“Yo Allah na tuba ba dole ki ga na saki baki ba Halima, yanzu ni har lokacin bacci gareni a gidan nan ni da na zo ZAMAN WANKA?”
“Kwanan zaune za kike yi?”
“Yo ba gwara kwanan zaune ba ka san a zaune kake, ai bakam zan ke yi saboda tsaro ba wai dan tsoro ba, yo idan na kwanta na saki jiki ina bacci ai sai dai kuma a saka ki a kogin bagaruwa”
“Wai Inna bakya jin kunya Imran ya ji abubuwan da kike faɗa? Wai shin ma kin manta mace tana yin jinin biƙi idan ta haihu kurum ki ɗorawa kan ki, ki hana mutane sakat da zancen abu ɗaya?”
“Kunyar me zan ji? Na ce kunyar me zan ji Sa’adiyya, ai kunyar marar kunya tsoro ne, kuma ma da kike maganar jinin biƙi shi shaiɗan ina ruwansa da wani jinin biƙi lokacin da zai ɗau hankalinku ma kina ina, sai dai bayan komai ya lafa ku yi istigfari, kuma wallahi ni nan Azumi ƙafata ƙafarki, babu yadda za a yi in kwanta a falo sai dai mu kwanta da ke da yaran a cikin ɗakin, shi Imirana ki saka masa ƙaramar katifa a falo ya kwanta”
“Haba Inna mai gidan ne za a sakawa katifa a falo?”
“Eh mana, wato kina nufin in barku a ciki ni a nan ban san me za ku yi ba gwara dai idona idonki Sa’adiyya hankalina zai fi kwanciya kuma in san ZAMAN WANKA na zo”
Imran da ke ciki wani baƙinciki da takaici ne ya lulluɓeshi, ga kan sa da ke matuƙar masa ciwo sanadin wannan hayaniyar da Inna ke ta faman yi bakin ta ko gajiya ba ya yi.
Tuno wa da maganar mahaifiyarsa ya sanya ya miƙe zaune daga kwancen da yake a kan gadon , ya tashi dafe da kan sa yana ciccije leɓe, yana raya wa a ransa sai ya rama abin da tsohuwar nan ta masa. Sadiya ya ƙwalawa kira, da sauri ta shige ɗakin.
“Oh ni yarinyar nan ta rako mata, ji yadda take sauri kamar za ta tashi sama, ko dan tsoronsa ma take kamar wani mala’ikan mutuwa”
“Ɗakko yaran ki maido su nan, ki kai min katifar falo, ku kwanta a nan ɗin” Ya faɗa fuskarsa cike da damuwa. Shiru Sadiyar ta yi tana ɗan jin babu daɗi amma dai ta san hakan shi ne mafita a wurinsu dan tsohuwar nan sai ta sa a maimaita yaƙin badar dan kaɗan daga aikinta ta tada tarzoma.
Cikin sanyin jiki ta amsa masa, haka ta ɗakko yaran Inna tana kallonta ta shiga da su, tana kai su ɗakin duk ya ɗaukesu ya ƙara ganinsu yana jin wani farinciki na maye gurbin baƙincikin, da yake ciki ya so ace, yau su kaɗai za su kwana a gidansu da ya nuna musu kulawa su da mahaifiyarsu fiye da kima, to amma Inna ta warware komai addu’a ta riga fata.
Katifar ta ɗauka ta kawo falon ta shinfiɗa zanin gado, ta ɗora filo tsaf. Inna dai tana kallonta bata ce mata komai ba, ta koma ta ɗakko bargo ta ajiye masa, ganin Sadiya ta ce masa za ta shiga banɗaki ya kwantar da yaran yana jin ƙaran rufe ƙofar banɗakin da Sadiya ta yi aikuwa ya tashi cikin hanzari ya cire kayan jikinsa, sai da ya tuɓe tsaf daga shi sai singlet da gajeran wando gadan -gadan ya nufo falon Inna da ta hangame baki tana hamma bata ankara ba sai ganin mutum ta yi ya fito, ai bata san lokacin da ta katse hammar da take ba ta fara jero salati tana, sanya hannu a fuska tana cewa.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil, ni Azumi na ga abin da ya fi ƙarfin gani, Allah ka rabamu da mugun ji da mugun gani, haba Imirana ka manta cewa ba ku kaɗai bane a gidanku akwai ƴar ZAMAN WANKA?” Inna ta faɗa har lokacin idanunta a rufe da hannunta, a duniya ta tsani ta ga namiji haka a tuɓe.
Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan katifarsa ya kwanta ya ja bargo ya rufa. Cikin. Sauri Inna ta tashi ta shige bedroom ɗin tana neman faɗuwa a ranta tana cewa.
“Oh yaron nan bashi da kunya ko kaɗan, ko dan dama hausawa sun ce abokin damo guza, ashe dai shi ma halinsu ɗaya da abokinsa da na iske a wannan gida ya yi wasarere, gabaɗaya halittar jikinsa na leƙowa waje”
Tana nan zaune sai ga Sadiya ta shigo ɗakin, dan ita Sadiya da farko ma ta ɗauka Innar ce ta kwanta a falon da yake Imran har kan sa ya rufa da bargon sai da t shigo ne ya buɗe ya mata magana cewar ta miƙo masa wayarsa a kan mudubi.
“Halima ashe dai mijinki bashi da kunya?”
“Me kuma ya yi Inna kin ce ya koma falo ya koma to me kuma kike so ya miki?.
“Ana ga yaƙi kina ga ƙura yo ai na ga yana so ya min kora da hali, in ba kora da hali ba ya za a yi ya san ba ku kaɗai bane a gidan, kawai ina zaune sai ganin mutum na yi sangamgam ya shigo falon babu neman izini gandaƙai-gandaƙai ko suturar kirki babu, da da sanyin nan ma amma ya zauna da kayan banza”
Sai lokacin Sadiya ta gane abin da Innar take nufi, ba tare da ta tanka ta ba ta ɗauki wayar Imran tanjuya za ta fita Inna ta ce.
“Ki taho min da bargona a kan kujera, ki haɗo min da wannan sauran maltinar guda ɗaya ta ɗazu”
Tafiya Sadiya ta yi ba tare da ta ce komai ba, tana fita daga ɗakin Inna ta rafka uban tagumi, idanunta a kan gadon Hassan.
“Ni Azumi da zan yi kwana Hamsin amma tun ban kwana ɗaya ba na fara fuskantar abubuwa, ga yaro mai bayan miciji ga ubansa yana yawo da jiki babu maraba fa tsirara, haka kawai lokacin fatarar nan fa ake rashin kuɗi ya je ya sa in gamo da ganin al’aurarsa, ni Azumi in shiga uku in ma ban makance ba” Ta faɗa a zuciyarta dai dai nan Sadiya ta dawo ɗauke da bargon da maltinar, ta miƙa mata dama ta buɗe mata kwalbar maltinar. Haka ta kafa kai ta shanye tas ta miƙa kwalbar kan mudubi ta ajiye, lokacin Sadiya tana shan magungunanta.
“Ni da nake ta shan maltina kayan ruwa, ko ya zanyi da fitsari, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, ni mai yawan fita fitsari cikin dare, bare na cika cikina da kayan ruwa, wannan kurman mutumi falo” Ta faɗa tana kallon Sadiya.
“Shi da yake gefe ɗaya a kwance kuma ina ke ina shi”
“A’a Halima nake ƙetara mutum ina fita wa ya san fita nawa zan yi”
Sadiya dai bata kulata ba ta yi shirin kwanciya ta hau gadon ta kwanta.
“Inna ki kwanta mana, na ga dai gani gaki gani kuma menene zai hanaki kwanciya?”
“Hankalina a kwance yake, kawai dai ina jin kunyar gadon ne, yo na kwanta a gadon yara”
“Sai ki kwanta mana, ai babu komai ke da jikokin ki”
Wannan kalaman da Sadiya ta mata yasa ta ji ƙwarin gwaiwa ta kwanta ta rufa da bargonta, ita ma Sadiya gadon yaran ta tashi ta maido gefen gadonta kusa da ita dan ma haɗe yake da net ɗinsa sauro ba zai cije yaran ba.
~DARE~
Wajen ƙarfe biyu na dare Imran ya tashi zaune, dan dama ya ji tashin Sadiya wajen ɗaya saura yaran sun motsa, ya basu ruwansu yana dai ji har ta kwantar da su, bai sani ba ko sun sha nono ko kuma nonon bai zo ba, sa’a ma aka yi yaran ba wasu masu rigima bane. Ɗakin tsit baka jin komai sai ƙaran minsharin Inna tun da ta kwanta bata motsa ba, haka ya tashi cikin sanɗa ya leƙa bedroom ɗin sai da ta tabbatar bacci suke sannan cikin sanɗa ya shiga ɗakin drower ɗinsa ya buɗe ya ɗakko farar jallabiyarsa, tare da wata farar rigar sanyi mai haɗe da hula, haka ya lallaɓa ya rufe drower ya fita ba tare da sanin su ba, dan Inna kamar wata gawa haka kawai sai sakin munshari take.
A ransa ya ce
“Kina wannan munsharin koma me mutum zai yi da matarsa sai ya yi baki sani ba, ya faɗa yana jan tsaki tare da yin ƙwafar ganin Inna ta maye gurbin makwancinsa. Jallabiyar ya sanya sannan ya ɗora rigar sanyi a ka sai ya bar zip ɗin a buɗe, haka ya fita ya je bayin nasu ya cire ƙwan fitilar ya dawo ya kwanta.Zuwa can ya ji motsin Inna ta tashi tana cewa.
“Dama na san dole na tashi fitsarin nan duk ya cika min mara”
Da hanzari ya ɗakko filillikan kujera, ya jera a kan katifarsa ya dai daita su kamar mutum ya rufe da bargo, yana gamawa ya lallaɓa ba takalmi
ya tafi banɗakin.
_INNA_
Haka ta tashi ta kunna fitilar ɗakin, ta kalli Sadiya da ke baccinta cikin kwanciyar hankali ta ce a fili.
“Allah da hikima yake, shi yasa ya sanya mata ke zubar da jini bayan sun haihu (Jinin haihuwa) Amma ba dan haka ba Allah kaɗai ya san yawan matan da matansu za su ke maida musu mahaifa nan da nan (Su yi tarayya da su) Musamman in aka samu kudurarru masu jaraba, tuni za su haƙƙewa mai jegon saboda basu san wahalar naƙuda ba, shikenan mata su ringa haihuwar kwenika” Ta faɗa tana gyaran ɗaurin ɗankwalinta ta taso ta fito. A hankali ta leƙa falon dan tabbatar da Imran ɗin yana bacci, ganin filon da ya jera sai ta ɗauka shi ne ke bacci da yake ma fitilar falon ma a kashe take bata kunna ba dan bata so ma ya tashi.
Haka ta nufi bayin gadan-gadan har tana haɗawa da sauri jin fitsarin ya matseta. Imran da ke cikin bayin jin takun Inna yasa ya ƙara jingina a jikin bangon da ke kallon ƙofar bayin ya baza hannu ya sanya hular sai ya sunkuyar da kai. Inna jin fitsarin na nema zubo mata ganin fitilar a kashe sai bata kunna ba kawai ta shige bayin. Sai da ta je tsakiyar bayin kawai sai ganin abu ta yi fari ƙal,kallon abun ta yi da kyau ta ga mutum ne a take ta ji ƙafafunta sun fara karkarwa, hannu ta miƙa ta dafe jikin bango tana cewa.
“Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahim, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba” Ta faɗa har lokacin tana karkarwa, so take ta gudu amma ƙafafunta sun ƙi bata dama, ji take kamar a wurin aka dasa ta.
Imran ganin tarkonsa ya kama tsuntsu ya ce a ransa.
“Mu zuba ni da ke mu gani, ba dai kin ce ke ZAMAN WANKA za ki yi ba ai ga wurin nan”
A hankali ya fara takowa yana nufota, dama ƙafarsa ko takalmi babu, Inna ganin aljani ya doso ta a nata tunanin kenan, sai haƙoranta suka fara haɗuwa da juna kafkafkaf, gaba ɗaya ta tsure ji take aljanin nan yana dafa ta mutuwa za ta yi, ji ta yi kawai fitsarin nan ya ƙwace mata, yana bin ƙafafunta, aljanin na matsowa a hankali ita kuma faɗuwar gabanta na tsananta. Imran kwa duk nufotan da yake bai ɗago kan sa ba, jib Inna ta zame ta zauna ƙafafunta sun kasa ɗaukanta, ganin dai da gaske aljanin na miƙo hannu hakan yasa ta fara rarrafe domin ƙwatar kan ta, tana rarrafawa yana ƙara matsota har suka fito daga bayin, dan Imran rage tsawo ya yi sai ta ga ɗan guduldili ne aljanin, tana rarrafe tana salati dan so take ta yi ihu amma ta kasa gabaɗaya bata da karazana.
Ta fito daga bayin yana biye da ita tana rarrafawa duk ta zubar da takalmanta, suna fitowa ta juya tana rarrafe dan rarrfenma dakyar take yi sai Imran ya yi saurin juyawa cikin sanɗa ya koma cikin bayin, Inna sai da ta kusa shiga falon da rarrafe ta waiga aikuwa sai ta ga babu aljanin hakan ya sa ta ɗauka ɓacewa ya yi.
Hakan ya sanya ta cigaba da rarrafen duk da tana jin kamar aljanin zai rafkota ya maidata bayin. A haka ta shigo falon, kallon katifar Imran ta yi ganinsa lulluɓe yasa ta cigaba da rarrafe dan ba za ta tsaya a falo ba tashinsa sosai take jin tsoro, haka ta wuce cikin ɗakin tana jin rigarta jigif da lemar fitsarin da ta saki.
“`Imran“`
Tun da ta waiwaya ta ga baya nan, sai ya laɓe daga bayin ya cire kayana ya bar singlet da gajeran wandonsa, sai da ya dai dai ci Inna ta kai bedroom cikin sanɗa ya dawo falo ya ɗauke filillikan ya mayar da su mazauninsu ya sanya kayan da ya cire a ƙasan filo ya koma ya kwanta ya rufa.
“`INNA“`
Gadon ta kama hannunta nankarkarwa so take ta hau amma ta kasa hawa ga bakinta ya kasa magana, hannu ta kai ta kamo ƙafar Sadiya ta kama babban yatsan Sadiya take ja, dan bakinta ba zai iya kiran sunan Sadiyar ba.
Sadiya da gabaɗaya ta yi nisa da bacci bata san Inna na jan yatsanta ba. Imran ya tabbatar yanzu Inna taa cikin halin ƙaƙanika yi dan haka ya miƙa ƙafarsa ya bugi jikin kujera, ai Inna na jin ƙaran sai ta ɗauka aljanin ne ya biyo ta, ganin Sadiya ko motsi bata yi kamar gawa hakan ya sanya Inna ta lallaɓa ta shige ƙasan gado…
Masu son shiga grp zaman wanka 09030283375
ƳAR ZAMAN WANKA
(KWANA ARBA’IN)
NA
MAMAN AFRAH