Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 3

Sponsored Links

️3️⃣

Ƙarƙashin bishiyar da aka tanada dan zaman masu zaman jinya can ta nufa inda ta hango Imran ya yi, dakyar take iya ɗaga ƙafarta dan lokacin har an yi sallar la’asar amma Inna ba azahar ba la’asar dan wajen sha biyu ta baro ƙauyensu. Da jan ƙafa ta ƙaraso wajen da suke zaune a tabarma, dan tun daga nesa ta hango Hajiya Amina mahifiyar Imran, Ashrof ƙanwar Sadiya, sai kuma Ruƙayya mahaifiyar Sadiya, sai Imran da ke gefen mahifiyarsa da alama magana yake mata

“Wash Allah nah” Cewar Inna kamar an shaƙe mata wuya tana neman kan tabarmar ta zauna daɓas. Da mamaki suke kallonta su duka, Inna Azumi kwa saboda wahala ta ma manta da cewar ba a san da zuwanta ba.

“Inna!” Ashrof da Mama Ruƙayya suka faɗa da mamaki.

“Rakiya dan Allah ku taimaka min da ruwa wallahi maƙoshina duk ya bushe ƙamas ko yawu na haɗiye sai na ji wucewarsa wani garrrr yana cin birki saboda bushewar maƙoshin a maimakon na ji wucewarsa midik”

“Humm ai bari ba shegiya bace da ubanta” Cewar Imran a zuciyarsa dan yadda idanun Innar suka koma sun wani ƙanƙance kaɗai ya isa ya sanya ka dariya duk ta fita hayyacinta, ga gwaggwaron gaban goshin ya koma gefe har ɓangaren hagun ɗin ɗankwalin ya zamo ya ɗan rufe gefen idonta amma duk bata kawo a ka ba.

“Inna wai kin ganki kwa kamar wata maroƙiyar” Ashrof ta faɗa tana tuntsurewa da dariya.

Inna ji ta yi ba za ta iya magana ba, amma da sai ta ji amsa dai dai da tambayarta, amma ina! Babu hali. Hatta Mama Ruƙayya da Hajiya Amina dariyar suka ƙunshe ganin Innar a birkice sai wani faman nishi take kamar ta yi tseren gudu.

“Gashi Inna” Mama ta faɗa tana miƙa mata pure water guda ɗaya da ta ɗakko a cikin leda.

“Haba Rakiya kamar wata almajira, za ki bani ruwa ƙwalli ɗaya” Ta faɗa a fusace dan ita ba ma ruwan ɗaya bane ya ɓata mata rai, so ta yi Mamar ta ce mata ga abinci dan ta tabbatar yanzu idan ta sha ruwan nan cikinta ƙullewa zai yi.

Mama kwa faranti ta ɗauka ta ɗora ruwan har huɗu ta miƙa Innar, har lokacin tana mamakin zuwan na Inna Kano da ma yadda aka yi ta gane asibitin da suke.

Ruwan ta kalla guda huɗu ga cikon na biyar ɗin a hannunta,ta ce.

“Kai Allah na tuba wannan ruwa kamar wata saniya ina zan kai shi ma son in sha ya ƙulle min ƴaƴan hanji, mu wallahi zamanin da ba haka muke yiwa baƙo ba sai mun fara gabatarwa baƙo sanwa (Abinci) Kafin mu kai ga bashi ruwa, amma yanzu zamani ya banbanta halayya wani wurin ma sai ka je baƙunta ka tafi amma ko ruwan ma ba zaka samu ba to amma ke kin yi ƙoƙari ma da kika bada ruwa har biyar da babu gwara ba daɗi amma da ace ko kaɗan kuna haɗawa baƙi da abinci duk ƙanƙantarsa ai da hanau ƙwara mannau” Ta faɗa tana sauke idanunta a kan wasu food flaks har guda uku da ke ajiye a gefe.

“Wai Inna dai ko yunwa kike ji?” Ashrof ta tambaya tana kallon Inna da sheƙiyanci ganin duk idanunta ya faɗa bakin nan a bushe kamar mai azumin nafila.

“Yo Allah na tuba yunwa sai ta karni za a san ina jinta, cikin nan nawa kaɓar an yi shara ko motsin ɗiyan hanjina bana iya jiyowa duk sun yi likimo ko kuwa suma suka yi” Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

“Asharofa kar fa ki min fassara ato, ni ba wai ina roƙon a bani abinci bani kawai dai ina koyawa uwarki abinda ya dace ta yi ne, idan ta yi baƙi amma ba wai kaina nake yiwa tanadi ba”

“Wannan tsohuwa da shegen ɓatawa mutane suna take, wai asharofa sai ka ce wata tinkiya, ni ta ce min Imirana kamar wani gatari, sannan ko Sadiya ma Sa’adiyya ko kaɗan bata iya seta bakinta kamar wacce aka gutsirewa gefan harshe” Imran ya faɗa a ransa yana aika mata da harara a ɓoye.

Kunya ce ta rufe Mamar Sadiyar jin furucin da Innar ta yi, ga sirikinta ga Babar sirikin amma ko kaɗan Innar bata san kunya ba.

” To da yaushe ma ta zo, ko gaisawa fa ba a yi ba amma har ta ɗora min laifin rowa, ni ban taɓa ganin tsohuwa mai rangwangwan irinta ba” Mama ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

“Inna wallahi ina shirin baki abinci ne ka wai dai wani lokacin an fi fara gabatar da ruwa kafin abincin ne”

“A’a Rakiya a lokacin zafi ba amma a lokacin sanyin nan ai an fi jin yunwa a kan ƙishirwa, amma ba wai ina nufin ina cewa yunwa nake ji a bani abinci ba, kawai da ku ɗauka hira ne muke kowa yake faɗar abinda ya dace a yiwa baƙo idan ya kai ziyara ” Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba.

“Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan” Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Inna Azumi.

 

“Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana” Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina.

“Da me ya kai ki bin Imran yaron da ni ma addu’a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa’a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku da ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare”Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.” Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba.

“Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan” Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Inna Azumi.

 

“Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana” Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina.

” Humm Inna kenan, a nunawa na rigingine farin wata, ai ni sai dai na bada labarin Imran, dan ma ni yana raga min kasantuwata mahaifyarsa, kema da gangan ne ai, duk wanda ya sayi rariya ai ya san za ta zubda ruwa, me ya kai ki bin Imran yaron da, ni ma addu’a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa’a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku daga ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare”Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.

“Sannu Inna gaskiya kin yi ƙoƙari, wallahi kai kuma Imran ka kiyayeni a kan me za kake gudu baka ganin tsohuwa ce?” Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Imran da ke wani haɗe rai yana kauda kai gefe irin bai yi laifin ba ma.

“Hajiya baki san yadda tsohuwar nan ta takura min bane, ta kasa fahimtar ni ko ganinta ban son yi” Cewar Imran a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce.

“Sorry Hajiya” Ya faɗa yana sosa ƙeya.

“Au Allah, wato sorre, a soron gidanku na kwana, kai kenan taƙidarancin naka har uwarka bai baka bari ba to Allah wadaran naka ya lalace wallahi” Cewar Inna tana jijjiga kai irin na ga abinda ya fi ƙarfina.

Mama kanta ta kawar gefe tana jin wata irin kunya ganin gabaɗaya Inna tana kwance musu zani a kasuwa.

“Ina za a kai wannan abin kunyar? Ta faɗa a ranta.

“Haba Inna ki yi shiru dan Allah” Ashrof ta faɗa jin ɓaran-ɓaramar Inna ta yi yawa.

 

“Ashrof miƙo mata abincin” Mama ta faɗa dan ta kawo ƙarshen maganar.

Idanun Inna a kan kwanukan abincin wani mai jan murfi da ratsin yellow shi ya fi tafiya da hankalinta dan tana tunanin wataƙila a samu abinci mai daɗi a ciki, cikin ikon Allah kwa sai Ashrof ta miƙo mata shi, hannunta har karkarwa yake wajen karɓar tana washe baki.

“Yawwa Asharofa kamar kin san shi nake hari shi ne a raina” Cewar Inna a zuciyarta lokacin da ta kama kwanan da hannu biyu ta buɗe.

Fuskar Inna ce ta sauya har suka lura da hakan, ba komai ya sanya fuskar Inna sauyawa ba sai arba da ta yi da wake da shinkafa.

“Ni da na sanya ran wankin ciki, in samu jar miya idan hali har da naman kaza amma in ga wake da shinkafa da mai da yaji, to Allah suturibuƙui inji kishiyar mai doro” Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta yi saurin gyara fuskar ganin kowa ya lura da ɓata ran da ta yi ta sanya hannu ta kai kyawawan lomomin guda biyu, hakan ya yi dai dai da buɗewar da Ashrof ta yiwa ɗaya daga cikin flask ɗin aikuwa Inna ta yi ido biyu da shinkafa da miya ga wani uban namomi a saman.

Tufff Inna ta tofa da duka lomar abincin da ta take bakinta taf da shi ta ce.

“Amma Asharofa baki da imani wallahi, akwai wannan abincin mai rai da lafiya amma kika bani wannan ci ka mutun?” Ta kai ƙarshen maganar tana ture flask ɗin gaban nata.

Gabaɗaya suka saki baki suna bin Inna da kallon mamaki.

“Inna abincin Aunty Sadiya ne fa da za ta ci idan ta falka”

“Ka ji ni da yarinya mai shegen iyayin tsiya yo Allah na tuba meye marabar dambe da faɗa? Abinda ya yi ni ai shi ya yi yarinyar nan, in kuma kin manta ne in tuna miki” Ta faɗa tana janyo kwanan gabanta.

“Ikon Allah na zaune ya faɗi, lallai in da rai da rabo” Cewar Inna lokacin da ta luntuma hannu cikin abincin ta cika hannu ta kai bakinta ko bismillah babu.

Mama dai kan ta na ƙasa dan ta rasa bakin magana, dama abincin Sadiya ne Hajiya Amina ta girka mata takanas ta koma gida ta iyo girki dan ta samu ta ci idan ta falka.

“Ya rabb, matar nan ta addabemu” Cewar Imran a zuciyarsa yana dafe goshinsa da hannu.

Loma ɗaya biyu, a ta uku sai kawa Inna ta saki kuka, kukan da ya sanya duk waɗanda ke kusa da su suka waigo suna kallonta, dan wasu ma zatonsu ko mutuwa aka yi.

“Inna lafiya?” Mama ta tambaya da mamaki.

“Haba Rakiya ba dole in yi kuka ba, yanzu a ce kuna cikin irin daular nan amma ko ki ce in zo in yi ko da shekara ne a marmarce ni ma in yi wankin ciki amma kika barni ina fama da karta kafura (Miyar kuka) Da tuwon masara wanda in Tasalla ta tuƙa da yake bata iya ba kana ci yana maka dariya” Ta faɗa tana ɗaukan cinyar kaza ta yagi tsokar har wani lumshe ido take.

“Na shiga aljanna na maƙale” Cewar Ashrof da bata san ma maganar ta fito ba.

“Yo waye zai shiga aljanna ya fito ɗiyar nan kowa ya shiga ai ya ga wajen zama” Ta faɗa tana suɗar hannunta da take jin daɗin miyar har tsakar kan ta.

Gabaɗaya mutanen wurin dariya suka saka, wani saurayi da ke tsaye yana kallon Inna daga can gefensu a ransa cewa yake.

“Tsohuwar nan da za ta yarda in ɗauketa vedeo in sanya a status na san duk wda ya gani sai ya ci dariya kamar me sannan na san kowa ya gani sai ya yi replay har na rasa saƙon wanda zan duba, wallahi za ta yi kyau da comedy sosai ma” Ya faɗa a ransa yana kallon Inna daga can inda yake yana ta dariya.

Imran kwa ganin hankulan mutane duk ya dawo kan su hakan ya sanya a fusace ya bar wurin.

Sai da ta cinye abincin tas duk da yawansa ta suɗe kwanan ta maida murfin ta rufe, ta ɗauki pure water biyu ta kora ta ce

“Kai garin daɗi ba kusa ba, Allah sarki Malam da ƴar Tasallar sa suna can ana fama da dambu ni kwa nan na samu abinci na ci na yi nak” Ta faɗa tana miƙa hannunta can gefen tabarmar ta tilla wani pure water ɗin ta wanke hannunta.

“Jama’a ina wuninku” Ta faɗa tana kallon Hajiya Amina da Mama.

Dariya Hajiya Amina ta yi dan wallahi sosai Inna ta bata dariya wato sai da ta ƙoshi ne ma za a gaisa, ita mamakinta ɗaya ma da Inna bata tambayi mai haihuwar ba bare ma abinda aka samu ba, sai ta abinci ma take.

“Lafiya ƙalaw Inna, kin zo lafiya” Ta faɗa har lokacin tana ƴar dariya dan wallahi ta kasa riƙe dariyar.

“Lafiya ƙalaw, wallahi” Ta faɗa tana maida kallonta kan Mama ta ce.

“Kin ji Rakiya yaushe kika koyi mugun hali ne, ace ke baki gaisheni ba ni na gaisheki amma kuma kin kasa amsawa sai ɓata rai kike kamar na miki mugun abu, yo in shinkafar da na ci da nama ne ai rabona ne ya tsaga, ita kuma wake da shinkafar shi ne rabon Halima haka Allah ya tsara tun fil azal ni Hajiya Amina ta girkawa abincin tun da rabona ya rantse sai na ci kin san rabon kwaɗo ba ya hawa sama”

“Ina wuni Inna” Mama ta faɗa kamar ta yi kuka dan wallahi yau dai Inna ta gama zubar musu da kima da mutuncin a idon siriki da uwar sirikin ma baki ɗaya.

“Yawwa ko ke fa, lafiya ƙalaw ya abin da aka samu, mai ta haifa Halimar?”

“Ƴan biyu ne duka maza?”

 

Salati Inna ta ɗauka tamkar an yi wani abu, sai da ta gama salallamewa ta ce.

“Amma wallahi kin cuceni Rakiya, yanzu a ce jikartawa ta haifi tagwaye duka maza amma tun zuwana wajen nan kika kasa faɗa min har sai da na ci na gwatse?” Ta faɗa tana sakin wata gyatsa.

“Ki yi haƙuri Inna dama jira nake na faɗa miki to kuma na ga kina ta ƙoƙarin ki ci abinci”

“A’a babu niyya ango ya kwana da wando, yo bana ci abinci ba, lafiya ce ta kawo haka, yanzu da za ki bi ɗakunan marassa lafiyar asibitin nan, za ki tarar ana ta fama da su a kan su ci abinci, to duk dan basu da lafiya mu kuma da muke da lafiya ai sai mu ci ba sai an faɗa mana ba”

“Allah bar mana Inna” Cewar Ashrof tana dariya dan ta m daina jin haushin abin da Innar ke yi kuma dama inda sabo sun saba da halinta kuma mai hali ai baya canjawa.

“Amin ƴar nan, in da gaske kike, dan na san wani so yake ma ka mutu y bar ganinka saboda ba ya son ganinka amma babu yadda zai yi da kai sai kallo” Ta faɗa tana kallon inda Imran yake amma sai ta ga wayam ba ya nan, baki ta taɓe ta kalli Mama ta ce.

“Wai ina mazajen nawa ne, ko sai na roƙa za a bani in gan su, kuma ita Halima da ake ta faman cewa bata falka ba, ragwanta ta yi a haihuwar har ta suma ake jiran falkowarta?”

“A’a allurar bacci suka mata, saboda tana buƙatar hutu” Cewar Mama tana miƙa mata yaron hannunta.

“Kai duniya inda ranka ka sha kallo, wato yaron ma yana hannunki amma baki bani ba, ni kuma ban lura ba ko dan an ce hankali ke gani ba ido” Ta faɗa tana karɓa yaron ta buɗe shi tana ta yaba kyansa.Babu wanda ya ce wani abu, sai da ta gama ganinsa ta ce

“Wai ina ɗayan ko ba za a bani su lokaci ɗaya ba dan kuna tsoron in gudu da su?” Ta faɗa tana kallonsu.

“Wannan tsohuwa da ɗaukan ƙafa take” Cewar Hajiya a ranta a fili kuma sai ta ce

.”Kin ga ɗayan Inna, wannan Husaini ne, shi ne ƙaramin wannan kuma shi ne Hassan ɗin, an haifeshi da wata baiwa ne” Ta faɗa tana ɗorawa Inna a cinyarta daga gefe sai ya zamana gefe ɗaya Hassan ɗaya gefen Husaini.

“Allah sarki bawan Allah, ashe da baiwa aka haifeshi, yo banda abinki ai an fi son ƴan baiwa” Ta faɗa tana buɗe fuskarsa tana ta sakin murmushin farinciki.

Ashrof kwa dariya take dannewa dan ta san yanzun nan Inna za ta tsorata in ta ji baiwar da ke tare da yaron.

 

“Ai gabaɗaya fatar bayan Hassan ɗin ce kamar jikin miciji, kin san wasu ƴan biyun ma ana haifar ɗaya mutum ɗaya miciji saboda baiwa ce id…

“Jikin miciji fa kika ce Amina?” Inna Azumi ta faɗa tana zaro idanu jikinta gabaɗaga ya ɗauki karkarwa dan tsoro…

Next page.

Yanzu fa aka fara wasan

Masu son grp ɗin ƴar zaman wanka

09030283375

 

ƳAR ZAMAN WANKA‍

(KWANA ARBA’IN)

NA

 

MAMAN AFRAH

 

Back to top button