Yar Zaman Wanka 6
️6️⃣
*Hajiya Amina*
Tun da suka fito daga cikin gidan take ta yiwa Imran nasiha, a kan zaman Inna a gidan duk da dai an takureshi amma bata nuna masa hakan ba.
“Haba Hajiya kin dai san halin tsohuwar nan, tana zuwa ta tafi ma ya aka ƙare bare kuma a ce za a zauna da ita na wani lokaci” Ya faɗa yana kauda kai gefe dan maganar da yake ma ji yake kamar ya saki kuka saboda yadda yake ji, ba komai yake ɗaga masa hankali ba illa nesanta gangar jikinsa da ruhinsa wato Sadiyarsa.
“Duk da hakan da ma a lokuta da dama muna haƙuri da wasu mutanen wanda hakan ne kawai mafita, akwai mutane da dama wanda idan da ana biye halinsu ba za a zauna da su ba. Ka ga Inna tsohuwa ce, kuma ma a al’adance wankan jego ba wani sabon abu bane tun da ana yinsa bare kuma ita da ta haifi yara biyu dole tana buƙatar a taimaka mata musamman da haihuwar ta zama haihuwar fari ce”
“Yanzu ki ga fa abubuwan da Inna take yi tun a asibiti zuwa gida, a haka za ta taimaka mata kin gani dai hatta abincin mai jego ita ke cinyewa to ta yaya za ta bata kulawar da ta dace”
“To ko ma menene kai dai ka ja bakinka ka yi shiru kuma dai ai ba za ta iya cinye ko ma menene ba, dole akwai saura, sannan tun da kai kana nan yanzu hutu ake baka zuwa wajen aiki(School teacher ne) Sai kake yiwa Sadiyar wani abun”
“To” Ya faɗa kamar ba ya so.
“Imran kar fa in ji na san halinka, yanzu magriba ta yi ba wanka za su yi dukan su yaran an goge musu jiki da zaitun, ita kuma da yake jininta ya hau ɗazu da za a sallame ta nurse ɗin ta ce kar ta yi wanka, sai zuwa gobe, duk da dai jinin nata ya sauka amma dai har yanzu akwai kumburi a jikinta, bari in je” Ta ce ganin mai napep ɗin sai horn yake mata.
“Sauka lafiya ni ma masallaci zan shiga in yi sallah”
Haka Hajiya ta tafi tana ɗan jin ba daɗi a ranta saboda tausayin ɗan nata da yanayin da ta ga fuskarsa tabbas ta san akwai damuwa a ransa duk da bai fito ya nuna hakan ba.
Sai da ya je masallacin ma ya yi alwalar da aka idar da sallar magarubar ma sai ya zauna a masallacin ya ƙi tahowa gidan.
“`MAMA“`
Bayan fitar Hajiya ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta ce.
“Inna mu ma gida za mu tafi, tun da gaki, sai dai fa kin ga Sadiya babu abin da ta ci sai ruwan shayi dan haka yanzu abinci za a bata”
“Haba Rakiya in ban da dai kina so ki ɗauki alhakina ya za ki ce haka, ni da na zo na tarar da ku a asibitin shin duk baku gabatar mata da abinci ba sai yanzu kike neman ɗora laifin a kaina saboda ga Inna kuka mai daɗin hawa ko?”
“Ba haka nake nufi ba Inna, kin san lokacin da kika zo ai tana bacci to tun da ta haihu ai bata sanya komai a cikinta ba, sai shayin da Hajiya ta bata”
“Amma kuwa yaran nan kun cika sakarkaru, wai dama kina nufin Sadiya babu abin da ta ci? Lallai in da ranka ka sha kallo, wallahi ya za a yi yarinya ta yi naƙuda da sunkuto ƴaƴa har biyu amma a barta da yunwa, ni duk zatona sai da ta ci wani abu sannan ta koma baccin, kuma da na ga ma ina tambayarta ta ci wake da shinkafar nan da na ga bata yi magana ba tunani na ƙam baki take irin na masu haihuwa kin san wasu basa iya cin komai idan suka haihu, yo da na san bata ci komai ba tun zuwanmu da na ɗora tukunya na tuƙa mata tuwo tun da shi ne zai fi riƙe mata cikin kin san cikin jego sai abu mai nauyi” Ta faɗa tana kallon Mama.
“Hakane kam” Mama ta faɗa ba dan ta so ba sai dan son a zauna lafiya.
“To laifin waye tsakanin ni da ku?”
“Namu ne” Cewar Mama.
“Aunty Sadiya mai za ki ci?” Ashrof ta tambaya.
“Komai ma” Cewar Sadiya da ke ƙarewa Hassan kallo.
“Kai amma wannan yarinyar da nunkufurci kike wallahi yanzu dama kina jin yunwar amma kika yi shiru dan ki ƙwari kan ki? Kika bari na ci hantar nan har ta so ta min karo, ai wannan abin kunya ne wai uwa ta cinye siriki ranar aure da ba san kina so da na rage miki amma yanzu ai ga doya can da ƙwai a cikin ƙwai har ma da kayan marmari bari in baki ki ci yo ai hakan ya zama min farilla tusa a masallaci” Ta faɗa tana tashi ta zubo mata doyar da ƙwan, sai kuma Ashrof ta haɗa mata wani shayin ta karɓi Hassan ɗin ta ci ta ƙoshi, tana gamawa ta gi gyatsa.
“Ko da na ji, yo yanzu ba gashi har da gyatsarki ba, amma a ce mutum ya zauna da yunwa ai mai jego da MAI ZAMAN WANKA sai suna cika cikinsu za su iya rainon abin da aka haifa, shi yasa kika ga ni ba na ƙwarar kaina a yunwa babu yadda zan yi in zauna cikina na kiran ciroma yunwa tana ƙwaƙulata”
Ashrof wancan zamzam ɗin na fida ɗakko a baiwa Husaini kin ga ya tashi” Cewar Mama tana mata nuni da fidar.
“Mama wacce ce tashi daga ciki”
“Farar ita ce tashi, jar kuma ita ce ta Hassan”
” Kuma dai da ɗaurewa ƙarya tsantsa kuke, yanzu bulunbotin ma sai an rabawa yaran nan, baku ga Allah ma a ciki ɗaya ya haɗa su ba tsawon wata tara da kwanaki suka rayu a cikin amma saboda sanabe ace kun ware musu bulumboti (Fida) dan san ku raba kawunansu, ai kamata ya yi komai a haɗe musu ya zama guda ɗaya kokwa” Inna da ke ƙoƙarin kunna soket ta faɗa tana kallon Mama da ta ɗagawa Husainin fidar tana bashi zamzam ɗin. Ashe soket ɗin yana ja Inna da ta maida hankali kam Mama hannunta a jikin soket bata ɗauke ba sai jin wani garrrr ta yi wuta ta ja ta, da sauri ta janye hannun ta bar wurin tana rafka salati, sai da ta koma ta zauna tana maida numfashin tsoratar da ta yi ta kalli Ashrof da Sadiya da ke ta dariya ta ce.
“Haba Halima kin san sokat (soket) Ɗin yana jan mutane amma baki faɗa min ba kika barni zai shanye min jinin jikina, dama abu ba abu ba duk tsufa ya gama tafoya min da jinin jiki, ban da ma Allah ya sa ɗazu na sha kwalbar maltina guda da yanzu sai dai a nemo manyan ita ce a ɓanɓareni daga jikin dan na san mutuwa zan yi ni ban yi ZAMAN WANKAN BA an wanke ni, shikenan na tafi na barwa Tasalla Malam sai yadda ta yi” Ta faɗa tana share hawaye dan sosai yadda wutar ta jata abin ya firgita ta.
“Sannu Inna” Cewar Mama tana ɗan ƙunshe dariyarta.
“Yawwa sannu Rakiya, ai yau dai na leƙo barzahu, wai da kallo zan kunna kin san ni da son kallo kamar me”
“Hakane Allah tsare”
“Amin”
“Wai Inna ya kika ji ne, ni fa ban ankara ba sai kawai na ga kin zauna a kan kujera kamar an jefo ki, har kina neman yin tuntuɓe da ƙafar Aunty Sadiya” Ashrof ta faɗa har ƙyaƙyataww take.
” Aniyarki ta biki Asharofa, masu irin halinki ko a lahira wutarsu da ban ce amma ba na miki fatan shiga wuta ni nan Azumi wallahi na ci dubu sai ceto kuma ina nan har sai kin tsufa ni ban mutu ba in ma so kike in mutu ” Ta ce tana goge hawaye.
“Sorry Inna ke yanzu sai ki bari har in tsuga kin raye ai ba za ki kyan gani ba”
“Soriyo, na ce soriyo ban…
Sallamar Imran ce ta katse maganar da suke, shigowa ya yi.
“Mama ta ce.
“Ta tafi Hajiyar”
“Eh tun daɗewa ma”
“Imirana ashe dai sokat ɗin gidan ka jan mutane yake, daga taɓawa wuta ta jani ji kake wani girrrrr duk jikina ya ɗauki rawa baka ji ba yadda ta jijjigani, amma Asharofa da matarka har da dariya”
“Daman ma sumar da ke ta yi a kai ki asibiti mu ga ta yadda za ki yi ZAMAN WANKAN” Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma ya ce.
“Eh za a gyara ne”
“Ai gwara a gyara amma ni yanzu ai ina ga sai ka samo min madarar ruwa gwangwani uku na sha”
“To” Kawai ya ce ita ma kuma sai ta ja bakinta ta yi shiru.
“Hajiya ta ce sai gobe za ta yi wanka sbd kumburin jikinta in ji likitoci” Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa.
“Eh sai gobe har yaran ma ai sai goben tun da an goge musu jiki da zautun kuma saboda mura kuma yanzu ai dare ya yi” Mama ta bashi amsa.
“Allah kaimu” Cewar Imran kuma dama ya yi hakan ne dan Inna ta ji kar ta je ta tarki yiwa yaran wanka.
“Halima ki sa yaron nan a nono mana tun da ya tashi ko babu ruwan nonon in yana tsotsa zai zo” Inna ta faɗa tana kallon Sadiyar.
“To” Ta ce Mama ta miƙa mata Hussainin ta sanya shi a nono.
“N a dama za ki fara bashi, kuma koyaushe za ki bashi kike fara yin bismillah kafin ki bashi, sannan kike lura wajen bashi nonon dan kar ya danne masa hanci in yana sha, kuma sai kin tiƙe nonon a hannunki in zaki basu kin san nauyi yake musu idan aka bar musu ba a riƙe ba” Cewar Mama tana ɗan nuna mata yadda za ta yi.
“To Mama”
“Wayyo Allah na wallahi ciwo”
“Haka za ki daure”Cewar Mama.
“Ke ma Rakiya da wani abu yo wane haka za ta daure, bada nono ai ya zama wajibi ciwo ko dole ne, Allah na tuba kika haihu ma, ai fitowar ɗa shi ne babban abu” Cewar Inna.
Babu wanda ya tanka, Sadiya kwa sai rurruntse ido take jin zafin da nonon ke mata da yaron ya kama kan.
“Ashrof ba Inna Hassan ɗin mu tafi kin ga har an yi ishsha’i” Cewar Mama.
Gaban Inna ne ya bada wani diririmdim, jin wai an ce a bata Hassan.
“Ni har ga Allah tun da aka ce yaron yana da fatar miciji a bayansa nake jin tsoronsa gashi ni ce MAI ZAMAN WANKA dole dai ni zan wankeshi, wayyo Allah na shigenge” Inna ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
“Yo ku bari mana a ɗan jima muna hirarmu ai kwa rage dare, ko kuma in Halima ta gama shayar da Husainin sai in karɓeshi ki bata Hassan ɗin shi ma ta bashi nonon.
“Haba Inna tun jiya da dare fa muka baro gida muka zo nan kwanan zaune muka yi, tana naƙuda da sassafe muka tafi asibiti dama mun je asibitin a daren suka ce da saura mu koma gida kuma yanzu har an yi ishsh’i bamu tafi ba tun da dai Allah ya sauketa lafiya yaran ma suna cikin ƙoshin lafiya kuma gaki ai sai mu je gida sai kuma gobe in muna raye” Cewar Mama cikin sanyin murya dan ta harbo jirgin Inna kawai dai Hassan ne bata son karɓa.
“Ni Azumi na ɗakko ruwan dafa kaina” Ta ce a ranta a fili kuma ta yi dariyar yaƙe ta ce.
“Kayya Rakiya, ai ban sani ba, to, to, babu komai ai, da yanzun da anjiman duk ɗaya ne Allah bamu alheri”
“A gaba ma wallahi sai kin gwammace ko Kano baki zo ba bare gidan Imran” Cewar Imran a ransa.Ya tashi ya fita.
“Amin Inna” Cewar Mama.
“Inna ga mijinki Hassan” Ashrof ta faɗa tana dariyar ƙeta a ranta, a fili kuma tana danne dariyar yadda ta ga Inna na wulwulga idanu.
“Ba dai wannan rabi da rabin ba, rabi mutum rabi maciji, mijina Malam yana can a ƙauye” Ta ce a ranta a fili kuma ta ce.
“To ai ni Husainin ne mijin Hassan ɗin na sake shi”
“A’a Inna ai aure da ke babu saki, ke da shi mutuƙaraba” Ashrof ta faɗa tana ɗorawa Inna Hassan a cinya, Inna ji ta yi kamar Ashrof ta ɗora mata miciji a cinya haka dai ta daure ta riƙe yaron gabanta na duka uku-uku.Sallama suka musu suka tafi, Inna dai ko sallamar tasu bata karɓa ba.
“Halima kar fa a shiga haƙƙin yaron nan ki karɓeshi shi ma ko bashi nonon” Inna da ta sanya hannu ta ɗan jijjiga yaron ya buɗe ido dama da niyya ta yi hakan.
“Inna shi ma fa wannan ɗin ba sha yake ba, kawai dai ciwo nake ji”
“Yo ai dai shi ma ko fatar ce ya tsotsa dan kar Allah ya kama ki kin nuna musu banbanci” Ta faɗa tana ta Allah -Allah Sadiya ta karɓi Hassan, Haka ta zarewa Hussaini nono, aikuwa ya tsallara ihu, a hakan Inna ta miƙa mata Hassan ɗin take lallashin Hussainin.
Bayan sun yi bacci yaran Sadiya ta sanya kowanne a gadonsa ta kwantar tare da sanya bargo ta lulluɓesu. Zuwa can Imran ya dawo gidan dan dama yana waje a zaune takaici ya hanashi shigowa gidan, dan shi bai saba zuwa yawo ba. Da dai ya gaji da shaƙar sanyin sai ya kulle gidan ya shigo, lokacin Inna jakarta na gabanta ta fito da bargwanta tana maida kayan. Yana shigowa bayan ya yi sallama Sadiya ta amsa sai ya wuce bedroom Sadiya ta tashi ta bi bayansa.
“Ba ni da raƙumi da akala ba” Cewar Inna lokacin da Sadiya ta bi bayan Imran.
Tambayarsa ta yi abin da zai ci, dakyar dai ta lallaɓashi ya amince zai sha fura, Inna da ke falo ta ce.
“Wa ankarahu ake ankara dai, ana yi dai ana zaman ƙuda da buzuzu, wato zaman doya da manja” Ta faɗa cikin ɗaga murya. Suna jin ta babu wanda ya yi magana, har Sadiya ta fito ta ɗauki furar a falo, da yake a cikin kwanon sha take haar luday akwai a cikin hannun frige ɗin haka ta ɗauka ta koma cikin bedroom ɗin Inna dai sai taɓe baki take.
“Bari dai in cire atamfar nan ta akwatin ƙarfe kar in kwanta da ita alharamun giya a gidan liman” Ta faɗa tana ɗakko wata doguwar riga marar nauyi a jakarta ta sanya ta linke atamfar ta sanya a jakat ta rufe ta ajiyeta gefe. Bayan ta koma ta kwanta jin tsit babu motsin su ta tashi cikin sanɗa ta je baki ƙofar bedroom ɗin ta tsaya ba tare da sun sani ba, ta kama labule a hankali ta ɗan leƙa. Imran ta gani zaune a bakin gado sai Sadiya da ke zaune kan bed side drower tana bashi fura a baki. Da sauri Inna ta saki labulen ta dawo ta zauna daɓas dan ita hankalinta bai kwanta ba da kasancewarsu su kaɗai a cikin ɗaki.
“Ni Azumi ba da ni ba wai gyaɗa a kabari, ya za a yi ina gidan nan ni da na zo ZAMAN WANKA in bari a yi aika-aika ai yadda na gan su ɗin nan kusa da juna a zaune shi a bakin gado ana jimawa sai dai in ji sun rufo ƙofa” Ta faɗa a zuciyarta, sai kuma ta ce.
“Halima, Halim, Halima” Har sau uku amma bata fito ba kuma bata amsa ba Sadiya kwa ta tashi za ta fito sai Imran ya riƙe hannunta ya marairaice mata, hakan ya sa bata fito ba shi kuma da gangan ya yi hakan dan kawai ya ga abin da Innar za ta yi.
“Sa’adiyya, Sadiyya, Imirana, wai bakwa ji na ne” Ta faɗa tana tashi tsaye daga zaunen da take.
” Ko dai basa cikin hayyacinsu ma dai, kar fa kudirarren yaron nan ya je ya ɓarkewa yarinyar nan ɗinkin da aka mata, ita ban da ma shashanci jiki duk faci amma za ta biye wa namiji” Ta faɗa tana tafa hannuwa, jin shirun ya yi yawa sai ta nufi ƙofar ta kusa zuwa jikin labulen sai ga Sadiyar ta fito da sauri ta koma ta zauna a kan kujerar kusa da hanyar bedroom ɗin ta wayance dan da a kan kujerar wajen bakin ƙofar falo take a zaune.
“Inna gani” Sadiya ta faɗa tana haɗe rai.
“Dama na ji shiru ne nake kiranki”
“Haba Inna shirun me kuma me zan miki to”
“Babu komai ɗiyar nan taimakon ki zan yi dan kar ki hau dokin zuciya yaron nan ya kai ki ya baro ki”
“Haba Inna wai wacs magana kike haka ne, kar fa ki manta mata da miji muke fa”
“Yo dan an ce mata da miji kuke sai me to, ai yanzu kin haramta a gareshi”
“In ji wa”
“To halasta masa kan ki wallahi kika sake ya janyo ruwa a rijiyar nan Allah sai kin ɗauka a injin markaɗe aka saka ki”
Takaici ne ya sanya Sadiya ta juya ta koma ta bar Inna tana sababi ita kaɗai.
Masu son grp zaman wanka 09030283375
Masu tambayar Beelal ina baku haƙuri sai ranar monday in sha Allah za a posting.
ƳAR ZAMAN WANKA
(KWANA ARBA’IN)
NA
MAMAN AFRAH