Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 47-48

Sponsored Links

4️⃣7️⃣➡️4️⃣8️⃣

*TASALLA*

Gabɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda tsananin murnar tafiya birni suna, sunan da ba a san da zuwanta ba kyma ba wai shiri suke dz wacce za ta je sunan domin ta bane kawai dai ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama. Tun da aka ce yau alhamis take ta shirye shirye saboda Tsahare ta faɗa mata cewar da sassafe za su tafi sunan wato ranar sunan kenan ranar juma’a. Kuɗaɗe masu yawa ta karɓa a wajen Malam dan ta ce masa kar a je suna babu wani abin a zo a gani dan jaka ta yaudareshi kuɗaɗen da suka fi wanda za ta yi amfani da su yawa.

Fura dakan mai ta ce za a yi, ta sha sugar da man shanu dan haka hatsi ta auna ta bayar da duk abubuwan buƙata na aikin furar da ladan masu yin furar dan akwai gidan da ake yin furar in mutum yana so sai ya biya a masa. Galan kuwa ta samu ta ɗure nono a ciki wanda za a kai gidan sunan haɗe da furar duk tana yin hakan ne dan kar Inna Azumi ta kunya tata, tana ganin in ta je da ɗan abin arziƙi ko ma menene zai zo da sauƙi.

Ƙafar nan ta sha ƙunshi kamar ba gobe sosai lallan ya kama aka ɗauki wani baƙin gishirin ƙunshi aka sanya, ga ta tanadi kayan da za ta saka idan za su tafi da kuma wanda za a ta sa ranar da za su dawo washe garin suna duk da ba haka ta so ba da son samu ne ta fi so ta zauna ta taya Inna ZAMAN WANKAN ita ma ta ɗan murmure sannan idan Innar ra tashi dawo wa sai su dawo tare . A ɓangaren Malam ma murna yake da tafiyar da Tasalla za su yi zuwa suna saboda yana ganin wannan ne abin da zai shirya tsakaninsu, yana kuma addu’ar Allah haɗa kawunan su komai ya zo ƙarshe a tsakaninsu na rashin jituwa.

Hakan ne ya sa Malam yake bada duk abin da ta buƙata kuma shi daɗi yake ji da ya ga tana murna, dan da abin har haushi yake bashi yawan fitar ta zuwa gidan Tsahare wani lokacin ma baya sanin ta fita sai ta dawo idan ya tambaya daga ina take sai ta ce ta je tambayo Tsahare ne ya shirye shiryen tafiya, ko gajiya bata yi da zuwa gidan Tsahare zancen tafiyarsu dan idan ana maganar tafiyar ba ƙaramin daɗi take ji ba, duk ta bi ta bama yaɗawa cewa za su tafi birni. Dan haka yanzu komai ya haɗu gobe kawai ake jira a ɗau hanyar Kano suna.

*INNA*

Tun bayan da ta dawo Sadiya ta gan ta da kaya riƙi -riƙe lokacin suna zaune da Imran dan har magriba ma ta kusa yi, haka ta shigo da ledojinta tana ta washe haƙora bakinta ɗauke da sallama
amsa mata suka yi kowa na kallon hannunta da mamaki, haka ta shigo ta zauna abinta tana ta fito da kayayyaki tana washe baki.

“Inna ina kika samu wannan kayan?” Cewar Sadiya tana kallon Inna da mamaki.

“Kai haba Sa’adiyya wannan tambaya ina dalili sai ka ce wata budurwa tsofai-tsofai da ni ki zauna kina mini tambayoyi kamar wata budurwa, yo Allah na tuba ai budurwa ya kamata a yiwa wannan tambayar in an ganta da wasu baƙin kaya a tare da ita, dan gudun kar ta ɓaci amma tsohuwa da ni kike min tambayar ƙwaƙwa” Cewar Inna tana kallon Sadiya tare da maida kallonta kan Imran ta ce.

“Ko ba haka ba Imirana, ai gaskiya na faɗa ko?” Cewar Inna tana kallonsa.

Haɗe rai ya yi ya kauda kai gefe.

“Ikon Allah ni ma mai ya kaini tambayarka dan na san ko dai dai na faɗa ba zaka faɗi gaskiya ba uban mugun halin tsiya haushi kake ji na baiwa Abida labarinka to ya za ka yi da ni ai ni na ci dubu sai ceto” Ta faɗa tana cigaba da fito da kayayyakin.

“Wai dan Allah Inna wa ya baki kayan nan, ranar nan kin ce wanda suka ɗauke ki ne suka baki yau kuka fa”

“Oh ni Azumi na ga ta kaina, yanzu Halima dole sai kin tambaya saboda niyya, to yau ɗin ma ɗaukeni aka yi” Ta faɗa hankali kwance.

“Haba Inna kullum dai kika fita sai an ɗauke ki sai ka ce kuɗi”

“Ke dalla can yau sojojo ne abokin Imirana ya aiko sojoji suka ɗauke ni a mota suka kai masa ni, shi ne na yi yadda na yi na ƙwato kaina”

Gabaɗaya kallonta suke da mamaki sun san sai tabbas Inna babu yadda za a yi ta haɗa wannan maganar”

“Wai da gaske Inna” Cewar Sadiya tana kafe ta da ido shi ma Imran ɗin kallonta yake.

“Yo ƙarya zan miki ɗiyar nan wallahi da gaske, aikuwa sun ga tijara gaba da gabanta aljani ya taka wuta, hummm ai ni Azumi an buga an barni”

Nan Inna ta kwashe labari kaf ta faɗa musu, daga Sadiyar har Imran ɗin dariya suke yadda Inna ta yi wasa da hankalin sojojin kaɗai ya isa ya baka dariya, basu sha dariya sosai ba sai da ta fito da micijin nan ta hura ta ajiye shi suka yi ta dariya suna jinjina ƙoƙari da kuma ƙarfin hali irin na Inna.

Tun da aka yi sallar isha’i Inna ta kwaɓa lallenta dan ta ce da shi za ta kwana a ƙafarta dan ya kama sosai. Haka ta jiƙa lallen ta tanadi ledoji tana ta rawar ƙafa za ta yi ƙunshi gobe suna. Bayan ta kwaɓa lallen suna zaune da Sadiya suna ɗan taɓa hira Imran ya fita lokacin, Inna ta kalli Sadiya ta ce.

“Ke yanzu Sa’adiyya ina iliminki na mahammadiyya a ce kina da ilimin addini amma kin bari ana kawo miki Malamin da bashi da wani ilimi gida duk da dai ba da son ranki aka kawo shi ba, ai kamata ya yi ki zauna ki tofe ɗanki da addu,’a dan matsawar yaron nan yana siffar miciji to kuwa ƙwara ma ki haƙura da taron sunan dan duk wanda ya ganshi to tsoro zai sa ya gudu wasu ma ko tunkaro gidan ba za su yi ba.

” Cewar Inna tana kallon Sadiya da ta yi shiru tana saurarenta.

“Hakane Inna bari to na gani” Cewar Sadiya cikin sanyin murya, ta tashi ta ɗakko Hassan ɗin daga bedroom ta kawo shi falon inda suke. Gadon dama kawai ta ɗakko
Sadiya ta yi bismillah ta fara karanta ayatul kursiyyu, falaq da nas da sauran ayoyin kariya cikin hikima ta ubangiji tana cikin yi sai yaron ya fara sawaya a hankali a hankali da haka ya koma mutum sak, a take a wurin aka shiga bashi nono ya sha aka wankeshi aka musu shirin bacci.

Inna sai da za ta kwanta ta ƙunsa lallenta ta ƙulle da leda ta kwanta da shi.

*DARE*

Gari ya yi tsit baka jin komai sai haushin karnuka a sauran abubuwa. Imran da dama bakam ya yi babu alamar bacci ma a tare da shi ya tashi ya janyo ledar da ya shigo da ita ya ɓoye a ƙasan kujera ba tare da kowa ya sani ba. Kaya ne ya siya baƙaƙe riga da wando sai wata wacce ake ɗorawa daga sama wata buɗaɗɗiya haka ya sanya baƙaƙen kayan nan.

Sai da ya tabbatar ba ya jin motsin kowa sai tashin munsharin Inna da ke cika ɗakin. Cikin sanɗa ya ƙarasa ɗakin yana fara da addu:a kar a gano shi. Kan gadon ya tsaya ƙarewa kallo ta hasken wata ganin kowa baccinsa yake hakan ya sanya ya tabbatar har ya gama abin da zai Sadiya ba lallai ta tashi ba saboda nauyin baccin ta.

Inna da ke ta shararar baccinta na gajiya sai sakin munshari take abin ta, a hankali Imran ya yi dibarar cire mata bargon da ta rufa da shi dama ko fuskar bata rufe ba. Hannu ya kai jikin ƙafarta mai ƙunshi ya ɗan ja ƙafar shiru bata motsa ba har lokacin tana ta bacci tare da sakin munshari, ƙara jan ƙafar ya yi zuwa lokacin ta ɗan motsa cikin bacci ta ɗan janye ƙafar. Ganin bata tashi ba sai ya ƙara jan ɗaya ƙafar lokacin ne ta ɗan kai hannu ta doke inda take jin an taɓa amma idanunta a rufe suke. Duka Imran ya sakar mata ɗaɗe ai jin zafin dukan nan Inna sai gata a zaune tana rarraba ido. Kafin ta tantance abin da ke faruwa, da kuma waye wannan mai baƙin kayan Imran ya kausasa murya yadda ba za ta gane shi ba ya ce.

“A yau ne za ki koma ga Allah, za a tambayeki duk abin da kika aikata a duniya dan haka yanzu ranki ne kawai za a zare”

Wani uban bugawa ƙirjin Inna ya yi lokaci ɗaya gumi ya baibayeta, cikin tashin hankali cikinta ya bada ƙululuuuuu.

“Wayyo Allah na mala,ikan mutuwa ne, ni Azumi kenan kwanakina sun ƙare wayyo shikenan tafiya zan yi ko sunan ƴan biyun bana nan za a yi, gashi zan barwa Tasalla Malam” Cewar Inna a zuciyarta har lokacin gabanta na mugun bugawa.

Ba ƙaramin tsorata ta yi ba ganin Imran da baƙin kaya dan ƙafarsa ɗaya ya ɗora a kan gadon sai ya ɗan ranƙwafo tare da baza baƙar rigarsa hakan ya sanya Inna da ke a tsorace ta ga wani girmansa ƙiba da kuma faɗi. Gabaɗaya jikinta karkarwa yake dan a duniya Inna tana tsoran mutuwa kuma a ce yau gata ga mala,ikan mutuwa zai ɗauki ranta, babu abin da ke ɗaga mata hankali sai kwanciyar kabari wannan abu yana matuƙar tada mata hankali idan ta tuna kenan yau ita ma za ta kwana cikin kabari, yau za ta tafi inda ba a dawo wa yau za ta tafi inda iyaye da kakanni suka tafi.

Hannu Imran ya miƙa wajen ƙafarta mai lalle. Inna da tunaninta ya bata cewa ranta zai zare bata san lokacin da ta haɗiye yawun da ya taru a bakint ba ta fara ƙoƙarin haɗa kalmomi sai kawai ji ta yi ta yi ƙarfin halin cewa.

“Da lalle a ƙafar, ƙunshi ne” Wai tunaninta idan ya ji da lalle ko za a ɗaga ɗaukan ran nata wataƙila ma ba ɗaukan ran mutum idan yana da ƙunshi, amma a tunaninta.

“Ba ma son magana ki koma ki kwanta ki miƙe” Cewar Imran a fili a zuciyarsa kuma ya ce

“Ashe kina tsoron mutuwa to kuwa yau sai na tsurar da ke gabaɗaya kamar ydda kike surar da ni ki tsoratar da ni ki sani cikin bala’i da miciji”

Jirif kake ji Inna ta koma ta kwanta jikinta gabaɗaya ya saki, tana zazzare ido sai hawaye da ya fara kwaranya daga idanunta ganin ga ta ga Sadiya amma za a ɗauki ranta Sadiya bata sani ba. Ita kanta ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ta san ba a tserewa mutuwa duk inda ka je tana biye da kai ko yau ko gobe ko ɗazu ko yanzu ko anjima.

“Sa’adiyya gaki da nauyin bacci da na tada ki kin ga tafiyar kakarki Azumi mai ƙaunarki ina ƙaunarku Sa’adiyya ke da Asharofa da Malam amma zan tafi in barku fatana ake min addu’a bayan mutuwata” Cewar Inna a zuciyarta tana zubar da hawaye. Imran kuwa dariya ce ke neman ƙwace masa yadda yake ganin Inna na rarraba idanu ta saki jiki gabaɗaya ita ala dole mai mutuwa.

Ganin ya miƙo gannunsa sai jikinta ya fara karkarwa tana raya wa a ranta shikenan ita kuma tata ta ƙare shikenan ranta zai zare.

“Kai gwara dai ki miƙa hannu ki tashi Halima ai gwara dai a ce da wani a kusa da ke lokacin ɗaukan ranki lokacin da za ki bar duniya, oh ni Azumi duniya budurwar wawa duk ƙaunarka da duniya haka za ka koma ka barta to Allah kasa can ta fi nan” Cewar Inna a zuciyarta tana ƙoƙarin kai hannunta na hagu mai lalle wanda shi ne daga gefen da Sadiya ke kwance, tana ƙoƙarin miƙa hannunta kan Sadiya Imran ya lura sai da sauri ya ce.

“Ba a son motsi in ba haka ba za a zare miki ran da ƙarfi”

Da sauri Inna ta janye hannunta tana ta addu’a a ranta kar a zare mata rai da ƙarfi saboda ta san an ce fitar rai akwai azaba bare kuma a ce da ƙarfi.Hannu Imran yake miƙowa yana ƙoƙarin kai hannun jikin Inna ita kuma sai ɗan takure kan ta take tana ɗan ƙoƙarin matsawa ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ba dama.

Hannunsa ya miƙa ya kamo hannunta na dama saitin dantsen ta ya riƙe gam sai ya sanya ɗaya hannun ya kamo yatsanta na tsakiya, ai gabaɗaya sai Inna ta fara wata karkarwa, karkarwa take gifgifgif gadon har jijjigawa yake ita ala dole an zo mawar zare mata rai.
“La’ilaha illalahu, muhammadur rasukullahi, S.A.W” Cewar Inna tana kuka gabaɗaya ta sanya a ranta shikenan ita da duniya kuma an yi ban kwana tana ta fatan ta samu dacewa a can.

Wannan karkarwar da take da salatin da take ita ala dole shirin ɗaukan ranta ne da ake take yi dakyar Imran ya iya danne dariyarsa saboda bai taɓa ganin Inna ta shiga ɗimuwa da tashin hankali haka ba ya so akwai haske yadda zai ke ƙare mata kallo amma ina.

“Kai ni Azumi ashe haka tafiyar za ta zo, ashe haka mutuwa za ta zo mini ban shirya ba, duk da dai dama babu wanda yake mata shiri haka kowa ke tsintar kansa haka take zuwa ba sanarwa bare sallama, Allah sarki ni Azumi ko wasiyya ban bayar ba, shikenan sai tafiya mutuwa haka take zuwa shi ma tashin ƙiyama an ce haka zai zo bagatatan” Cewar Inna tana runtse idanunta hawaye na kwaranya.

“Saura sati biyu ne ashe ba yau bane dan haka ki rufe idanunki sai kin daɗe sannan za ki buɗe” Ya katse wa Inna zancen zucin ta.

“Allah na gode maka ai har na bayar sa wasiyya in nemi yafiyar jama’a” Cewar Inna a zuciyarta.

“Kuma ba a baiwa kowa labari ki ja bakin ki ki yi shiru”.

“Bakina ƙanin ƙafata” Cewar Inna cikin rawar murya.

Ai Inna da ta rufe idanunta gam, ko alamar ɗagawa bata yi ba, har Imran ya lallaɓa ya tsugunna ya fice daga ɗakin da rarrafe amma Inna ko fitarsa bata ji ba. Har lokacin gabanta bai daina faɗuwa ba jikinta kuma bai bar karkarwa ba, sai da ta kwashe tsawon awa guda sannan ta miƙa hannunta na dama ta taɓo hancinta jin iska na fita daga hancin ta tabbatar bata mutu ba a hankali ta shiga buɗe idanunta cike da tsoro tana so ta tashi Sadiya ta faɗa mata sai dai tana tsoro kuma an ce kar ta faɗawa kowa.

*IMRAN*

Tun da ya fito daga ɗakin ya dawo falo ya cire kayan ya maida wanda ya cire ya sanya su a ledarsu ya mayar ƙasan kujera ya ajiye yana so da asuba sai ya fice da su in zashi masallaci. Tun da ya kwanta yake ta dariya ƙasa-ƙasa ba abin da je bashi dariya irin yadda idanun Inna suka yi ƙulu-ƙulu ita ala dole za ta mutu, ga karkarwar da jikinta ke yi kamar mazari shi kaɗai ya isa ya sanya cikinka ya yi ciwo saboda dariya.

“Ko a ina ta taɓa jin mala’ikan mutuwa yana manta wa’adin mutum har ya zo ɗaukan ran mutum amma kuma ya fasa ya ce sai wani lokacin, har ya faɗa maka lokacin ka.

“Kai ruɗani bai yi ba wallahi” Ya faɗa yana ƙyalƙyala dariya a ɓoye.

Tun da ta buɗe idon nata ta ji wani fitsari ya cika mata mara, ga tsoro da fargaba duk sun tarar mata sai kuma karkarwar da take. Jin fitsarin na neman zubowa ta ƙoƙarta ta tashi zaune ta fara kiciniyar sakkowa daga kan gadon saboda gabaɗaya bata gama dawo wa dai dai ba. Da dibara ta sakko daga gadon amma ko ta kan ƙunshin ƙafarta bata bi ba dama tun lokacin da Imran ya ja ƙafarta ta haɗe ƙafafun waje ɗaya duk ta caɓe lallen amma ba ta shi take ba, ita dai yanzu burinta ta yi fitsarin. Haka ta tako da ƙafafunta tana jin yadda lallan ke mata santsi a ƙafarta duk ta take shi lallan da ta ci uban buri a kan sa za ta yi ƙunshin fita kunya da suna, lallan da ta taho da shi tun daga garinsu amma kuma gashi za ta ɓata shi a banza, lallan da ta yiwa mai ƙunshin nan kuri cewa ya fi wanda take ƙunsawa su Ashrof kyau amma sai gashi abu ya zo mata a hautsine, dan tun da ta ga mala’ikam mutuwa ya zo ɗaukan ranta duk da bai ɗaukan ba, sai ta ji duniyar ta fice mata a rai komai na duniyar ya ginshe ta. A haka ta taho ko fitilar ɗakin bata kunna ba saboda tana ƙiyasta, da an ɗauki ranta da gobe da safe za a sanya ta a kabari duhun kabari kuwa ya fi na duniya sai dai fatan Allah rabamu da shi.

Haka ta fito tana taka ƙafarta dakyar dan duk ta yi sanyi, ko kallon inda Imran yake kwance bata yi ba ta zo ta wuce, shi kuwa yana kallonta har wani ɗan doro ta yi. Inna kuwa ko takalmi bata tsaya sakawa ba dama ga ledar lallan a ƙafar sai kawai ta tafi bayin a haka tana gama fitsarin ta yi tsarki ta fito, ledar lallan ta fusge ta watsar ta ƙarasa ta kunna famfo ta wanke ƙafar bata damu da ganin ko ya kama ƙunshin nata ba ko kuma ganin ya caɓe ita ba wannan ne a gabanta ba ita da za ta bar duniyar ma baki ɗaya nan da sati biyu to menene na damuwa da ƙafar da ta kusa komawa cikin ƙasa.Imran yana kallonta ta dawo ta shige ɗaki abinta jim kaɗan sai ya ganta ta kunna fitilar wayarta ta fito ɗauke da bargonta tana sanɗa, haka ta zo ta cikuikuya bargon ta saka a jakarta ta ɗakko sallayarta da hijabi a kan kujera su ma ta cusa su a ciki ta ɗakko mayafinta a kan kujera ta cusa ta ɗakko takalminta a ƙofar ɗaki ta cusa ta zige jakar. Duk abin da take Imran na kallonta kuma ya fahimci mai take shirin yi.
Sai da ta gama ta janyo jakarta a hankali.

“Wallahi guduwa zan yi daga gidan nan, na fasa ZAMAN WANKAN ƙwara in koma in mutu a ɗakina, na gwammace mutuwa ta ɗauke ni a ɗakin mijina a kan ta ɗauke ni a wani waje da ban, ƙwara in koma gida in roƙi yafiyar Malam dan dama ina zargin kamar ba da zuciya ɗaya ya barni na taho ba, dan tun da na zo birnin nan abubuwa suke faruwa da ni daga wannan sai wancan” Cewar Inna a zuciyarta tana sanya hannu ta share hawaye duk Imran yana kallonta. Sai da ta kai jakar ƙofar ɗaki ta dawo ta shige bedroom yana kallonta tana haske -haske a ɗakin da alama Sadiya da su Hassan take yiwa kallon ban kwana.

“Sa’adiyya ki yafe min na zo gidanki na hana ki sakat da sakewa da mijinki yau zan bar muku gidan ma baki ɗaya ko ma mai zai yi Imiranan ya je ya yi in ma kin samu wani cikin kin yi ciki da goyo Allah ne ya baki, kuma shi zai taya ki riƙonsu domin Allah ba ya ɗorawa bawa abin da ba zai iya ba Allah raya miki tagwayenki da ma wanda za su zo nan gaba na san wannan ne haɗuwarmu ta ƙarshe sai kuma in kin je jana’iza ta, ba zan iya tashinki daga bacci ba ki hana ni tafiya guduwa zan yi in ya so in kwana a tashar mota da asuba in samu mota in tafi gida. Kai ma Hassan ka yafe min saboda na maidaka abin zolayata kowa ya yafe min sai wata rana” Cewar Inna a hankali yadda ba za ta tashi Sadiya ba.

Duk abin da take faɗa Imran ya kasa kunne yana jiyo wa, sai da ta gama sai gata ta fito ta zo saitin katifarsa ta tsaya.

“To Imirana abokin karawata ka yafe min na tafi na bar maka gidanka da iyalinka Allah baku zama lafiya ya kaɗe fitina, in an samu labarin mutuwata nan da sati biyu a je jana’iza a min addu’ar samun dacewa mu tamu ta ƙare za mu tafi inda Baban Halima da su uwata mai daddawa da mai barkono suka tafi” Ta faɗa muryarta na karkarwa tare da juyawa ta nufi ƙofar ɗaki inda jakarta take duk Imran na ganinta.

Jakar tata ta kinkima dakyar ta ɗora a kan ta, sosai abin ya baiwa Imran dariya haka ta fara tafiya dakyar ga sanyin jikinta ga nauyin jakarta ga hawaye yana zuba ta nufi zauren ƙofar gida.

“Ai yadda kika hana ni tafiya lokacin da na tsinci kaina cikin tashin hankali zan bi Hajiyata haka ke ma za ki dawo ki zauna” Cewar Imran ya tashi da sauri ya kunna fitilar falo da ta tsakar gida, Inna da ta kama jamlock ta cire ta fara buɗe a hankali, ta ga hasken fitilar ya mamaye tsakar gidan, da sauri ta fasa buɗe ƙofar dan kar a ganta ta dakata dan ta sa wataƙila Imran ne ya tashi fitsari ƙwara idan ya koma ya kwanta bacci ya ɗauke shi sai ta tafi. Imran fitowa ya yi ya fara sa takalmi Inna tana jinsa, ƙofar da ta cirewa jamlock ta ja ta bata gama buɗewa ba ce ta yi ƙara.

“Shikenan Imirana zai ganni” Ta faɗa a zuciyarta.

“Waye a nan? Waye a zaure?” Cewar Imran cikin maida muryarsa irin ta masu bacci ya nufi zauren.

“To Imirana an falka” Cewar Inna tana wayancewa.

“Inna lafiya ina zaki da daren nan?” Cewar Imran yana haske Inna da fitilar wayarsa da ya fito da ita, ganinta ya yi ta yi hirim da uwar jaka a ka, wata dariya ce ta kusa kufce masa amma sai ya maje.

“Kai dai bari Imirana wai da yau kwanan tashar mota zan yi saboda murna”

“Murna kuma?”

“Eh mana murnar tarɓar aminiyata Tsahare shi ne zan je in kwana a tashar in jira zuwanta gobe dan na san da wuri za ta taho, sai mu taho tare duk da ta san gidan dan kar ta yi ɓatan kai”

“Kuma da tsohon daren nan sannan kuma har da jakarki za ki je taryen nata?”

“Eh, eh, eh mana”

“A’a Inna ki dai bari sai gobe kya je” Ya faɗa yana ƙarasawa ya rufe ƙofar ya maida jamlock ɗin, yana yaƙi da bakinsa kar ya kunya ta shi ta hanyar dariya dan gabaɗaya Inna tana cikin yanayin da dole sai ka yi dariya.

“Haba Imirana ya da haka kuma, ya za ka shiga tsakani na da burina, za ka shiga tsakani na da tuba na, ya za ka shiga tsakani na da mutuwa a ɗakin mijina” Cewar Inna a zuciyarta tana jin kamar ta saki kuka ko ta samu sassauci.

“Ai fita cikin dare haɗari ne ga karnuka gashi baki san da wa za ki haɗu ba a hanya duniyar nan da ta ƙi daɗi ki je ma masu yankan kai su ɗauke ki su yi watanda da namanki” Cewar Imran yana kallon Inna da ta turɓune fuska.

“To, to, to, to” Cewar Inna a fili da ke ta furta to, har babu adadi dan ji take kawai Imran ya gama da ita.
“Ko ban samu masu yin watanda da namana ba ai sha huɗun rana i ta yau na daɗe a ƙiyama, un ma gudun mutuwa ake” Ta faɗa a zuciyarta.

“Yawwa ko ke fa, kawo jakar taki” Cewar Imran yana miƙa hannu ya saukewa Inna jakar daga kanta. Haka ta barshi ya sauke jakar ba dan ta so ba haka ya juyo cikin gidan da jakar a hannunsa tana jin kamar ta juya ta buɗe ƙofar ta gudu ta bar masa jakar.

“Shiga gaba mana Inna ai kamar ba girmamawa in barki a baya” Cewar Imran yana matsawa gefe Inna ta wuce gaba ba dan ranta ya so ba, sai dan babu yadda za ta yi kuma ma bata son yin hayaniya dan tana ganin kwananta ya kusa ƙarewa bata da lokacin ɓatawa.

Haka ta shige falon jiki sanyi ƙalau. Imran kuwa sai da ya tsaya ya ɗan matse dariyarsa sannan ya shigo ɗauke da jakar Inna ya ajiyeta a inda take ajiyewa. Kallonta ya yi ya ga ta zauna a ƙasa ta rafka uban tagumi.

“To Inna ya ga kujera kuma za ki zauna a ƙasa?”

“Yo ai da na ga ƙarshen alewa ƙasa”

“Kamar ya Inna?”

“Yo duk mai rai mamaci ne kuma dai da ƙasa aka halicce mu kuma cikinta za mu koma sannan daga cikinta za a ƙara fito damu” Cewar Inna tana tuna nan da kwana goma sha huɗu tana cikin ƙasa hakan ya sanya ta share hawayenta tana jin bata da wani abu da ya wuce ta cigaba da kusanta kan ta ga Allah har ranar da mutuwarta za ta riske ta.

” To Inna ai kowa ya san da hakan amma ai manzo S.A.W ya ce, ka zauna a cikin duniya kamar matafiyi, sai hakan hakan ba yana nufin ka bar komai na jin daɗin duniyar ba” Ya faɗa yana kallonta sai ya ji duk tausayinta ya kama shi.

“To haka ne Allah dai ya sa mutuwa ta zame mana hutu, Allah sa mala’ika mutuwa ya zare ranmu a hankali, Allah raba mu da duhun kabari, azabar kabari nauyin ƙasa ya bamu ikon amsa tambayoyin kabari ya sanya aljanna maɗaukakiya ta zame mana makoma kuma madawwama” Cewar Inna cikin sanyin murya.

“Amin dan alfarmar annabi da alqur:ani” Cewar Imran yana neman wuri ya zauna a kan katifarsa.

“Amma Inna ki tashi ki koma ki kwanta mana tun da yanzu fa dare ne”

“Ina ni ina runtsawa Imirana ai sai dai ko na tashi na rinƙa nafilfili har asuba ta yi sallar asuba sai na zauna lazimi har garin Allah ya waye”

“To ikon Allah abu mai kyau gaskiya hakan ma ya yi Inna Allah dai ya ja da kwana ya sa ki yi tsawon rai dan ki yi ibada mai yawa”

“Kayya Imirana ni da wa’adina ya kusa cika ina zancen dogon kwana sai dai a ce Allah sa mu cika da kalmar shahada”

“Wa’adinki ya kusa Inna ta yaya aka yi kika sani kuma?”

“Uhmm da wasa nake kasan ɗan adam ana so ko yaushe ya kasance cikin shirin tafiya, in ya wayi gari ya sanya a ransa ba zai kai yammaci ba in ya kai yammaci ya sa a ransa ba zai wayi gari ba haka ne kawai ya sa na faɗi hakan” Cewar Inna cikin wayincewa dan ta ga ta kusa yin ɓaran ɓarama sai kuma ta tuna mala’ikan ya gargaɗeta.

“Eh kuma fa haka ne”

“Bata sake tanka masa ba ta fita ta ɗauro alwala dan bata so ma zuciyarta ta cigaba da kissima mata dalilin sakkowar Imran har yana biya ta suna magana yana kuma nuna mata kulawa da tausayawa, ga sakin fuska, dan ita yanzu ta kanta take bata ma so ta fara tunanin wani abu ita da za ta bar duniyar ma dan me za ta damu kanta. Haka ta zo ta wuce ta ɗauki sallayarta da hijab a jakar ta nufi ɗaki.

“A sanya mu a addu’a Inna ” Cewar Imran yana dariyar zuci.

“To Imirana” Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.

“Yo ni ina ma na ga lokacin yiwa kowa addu’a yau ai yau kawai nafsi – nafsi, ta kai-ta kai, kaina kawai zan yi ta roƙawa gafara da neman dacewa a lahira”

09030283375
*MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

 

Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

Back to top button