Daudar Gora Book 1 Page 16
16_*
……..Cikin ƙanƙanin lokaci labarin abinda ke faruwa da Zawjata-almilki ta uku ya gama gauraye daular ruman. A take ko’ina yay tsit sai ƙus-ƙus da maganar ido kawai. Sauran Zawjata-almilki kuwa guda biyu dake gidan dama kafin kawo Iffah tuni sun sake shiga tsantsar tashin hankalin da yafi wanda suke ciki. Su dai dama rayuwa suke cikin jiran tsammanin isowar mutuwarsu. Ko lokacin da aka sanar musu sake ɗaura auren Tajwar da wata matar tsantsar tausayin kansune kawai ya baibayesu, yanzu kam jin halin da matar da aka kawo jiya take ciki ya tabbatar musu suma mutuwarsu tunkarosu take sakeyi kenan…….
Duk wata tuhumar data dace akan hadima Jaza da sauran hadimai biyu da sukaje ɗakin Iffah suma da aka gano anyi amma sunƙi faɗar gaskiyar wanda ya sakasu, sai cewa suke Diwa ce. Yayinda Diwa ke rantsuwa da ALLAH tana kuka akan ƙarya suke mata ita bata san komai ba. Iya jigatuwa sun jigatu har takai numfashi da ƙyar sukeyi saboda azabartawar da ake musu. Sanin rayuwarsu akafi buƙata a yanzu sama da mutuwarsu yasa hadiman kurkukun dake a cikin daular ruman tsagaita musu. Amintaccen hadimin Malikat Bushirat ya koma ya sanar mata halin da ake ciki. Shiru kamar bazatace komaiba. Sai kuma ta dubi Jasrah da har yanzu ke tare da ita ta ɗauke kanta.
Jasrah data fahimci mi ƴar uwar tata ke nufi takai dubanta ga hadimin. “Ghazi! A cigaba da tsaurara musu tsaro har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.
“ALLAH ya ƙara miki lafiya an gama”. Ya faɗa da tsantsar girmamawa yana mai rissinawa da gyara takobin hanunsa ya fice…….
*_ZAWJATA-ALMILKI_*
Tun Iffah na iya motsa jikinta da furta kalmar bakinta har hakan ya gagara numfashinta ya fara neman barin jikinta. Ga dai masu magani mata rufe a kanta mazan na daga waje suna haɗo duk abinda ya dace amma babu alamar wani canji sai ma ƙwaɓewa da komai ke nemanyi. Tun ana ƙirga awannin iya shawo kan matsalar har komai ya fara firgita kowa. Daular ruman tayi tsitt babu mai ƙwaƙwaran motsi a cikinta. Sautin fitar kiran salla ma dan ya zama dolene. Koda aka idar da salla ma sake komawa zaman jigum-jigum akayi domin kuwa abinda bai taɓa faruwa a tarihin masarautar bane ya faru. Tajwar Eshaan bai fito sallar zuhur ba yau. Hakama da la’asar. Magrib ma ta shiga babu wanda yaji motsinsa. Zuwa lokacin kuma akan Iffah an zubama sarautar ALLAH idone wadda ta girma ta ɗaukaka.
Dan kuwa tana a shimfiɗene jiki duk ya ɗashe tamkar wadda ta ƙone gurin yay ja kafin ya tashi. Kaɗan-kaɗan numfashinta ke fita wanda shine kawai ya tabbatar da tana a raye bata mutu ba. Masu magani kowa yayi iya iyawarsa sun koma gefe ana jiran ikon ALLAH kuma. Ana idar da sallar la’asar Malikat Bushirat ta bada izinin maida Iffah sashenta…..
Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni an maida Iffah sashenta, a kuma cikin ɗakin barcinta da babu wani mahaluki daya taɓa shiga bayan Tajwar Eshaan da Jasrah. Hakan ya bama dukkan hadiman sashen mamaki da tabbatar da lallai wannan Zawjata-almilki ɗin tana da wata daraja ta musamman ga Malikat. Dan kaf Zawjata-almilki da suka rasa rayuwukansu a gidan babu wanda ya iya ganin makamancin damuwar Malikat Bushirat irin ta yau. Ƙarin tabbaci har hawaye sai da ta share na tsagwaron tausayin Iffah. Lallai halin da Iffah ke ciki ta cancanci duk mai imani ya zubda mata hawaye, dan sauran Zawjata-almilki na baya mutuwarsu kawai akeji bayan kaisu turakarsa. Amma ita ko kaitanma ba’ayiba, a kwana ɗaya tak da tai a gidan batare da an kammala gagarumin taron bikin da aka shirya ba dominta gata a halin da gara mutuwa da shi…
Bayan idar da sallar isha’i Malikat Bushirat na hakimce a katafaren falonta na uku Malikat Ashwaq ta iso da tawagar hadimanta duba Iffah. Malikat Ashwaq itace mace ta farko ga marigayi Tajwar Haysam ibn Abdull-majeed. Hamshaƙiyar mace ce data isa take kuma amsa suna Malikat. A ƙa’idar Daular ruman matar data haifi yarima mai jiran gado a cikin matan sarkice kawai ake kira da Malikat. Mafi yawanci kuma ana samu ne daga matan farko. Sai dai ga Tajwar Haysam hakan bata faru ba. Dan matarsa ta farko Ameera Ashwaq bata taɓa haihuwa ba kamar sauran matansa, tadai taɓa ɓarin ciki na wata huɗu daga shi kuma bata ƙara ba. A zahiri mace ce isashiya mai baza mulkin da yafi na kowace mace a gidan bayan malikat Bushirat, amma kuma bata da damuwa sam. Ƙaryarka kace ga wani mugun halinta na zahiri saboda tasan kanta. Rana ɗaya aka ɗaura aurenta dana Malikat Bushirat matsayin Zawjata-almilki. Amma itace uwargida. Duk da mulkinta Malikat Bushirat ta fita, ta kuma fita zafi da nuna kishi a zahiri dan sam ita bata da haƙuri, hakan yasa ake matuƙar jin tsoronta fiye da kowace Zawjata-almilki, dan Malikat Bushirat ba kanwar lasa bace ƙwarai da gaske, sai dai mace ce mai son ƙyautatama wanda yay mata da na ƙasa da ita, hakan ya taimaka mata samun soyayyar hadiman gidan. Haihuwar Miran (Yarima) mai jiran gado Eshaan tasa dole sunan Malikat ya koma kan Malikat Bushirat. Wato Sarauniya Bushirat kenan. Amma duk da haka sai Mahaifiyar Tajwar Haysam mai suna Malikat Haseena ta bada umarnin cigaba da kiran Ashwaq da suna Malikat Ashwaq. Hakan ya ƙona ran Malikat Bushirat, sai dai babu yanda zatayi. Amma ta sake tsananta kishin da takema Malikat Ashwaq ɗin fiye da da, yayinda ita kuma Malikat Ashwaq ke nuna tamkar babu komai a zahiri, amma a baɗini hummm….
Koda ta shigo Malikat Bushirat bata nuna tasan da shigowar tata ba. Sai dai ta ɗagama hadimanta yatsu biyu da ya sakasu rige-rigen fara barin falon. Zaune Malikat Ashwaq takai bisa ɗaya daga cikin kujerun falon tanama nata hadiman nuni dasu fita suma. Da sauri suma duk suka fice aka barsu su biyu kawai. A hankali Malikat Ashwaq ta ɗan sakin murmushi daya danne zafin yarfin da Malikat Bushirat ɗin tai mata, ita ta fara gaisheta da tambayar ya mai jiki?. A daƙile Malikat Bishirat da tai kamar zata basar ta amsa mata cike da isa. Nanma Malikat Ashwaq dai murmushi kawai tayi da haɗiye ɓacin ranta. Sosai ta nuna tausayi akan Iffah ta kuma mata doguwar addu’a da bada shawarar mizai hana a kira likita ma ya duba ta ko wani abune daban da wanda ake tunani.
Karan farko Malikat Bushirat ta ɗakko manyan idanunta tai mata kallon tsakkiyar ido. Cikin yamutsa fuska taja numfashi da fesarwa, “Haihuwar magajin Daular ruman daga tsatson Malikat Bushirat rubutacciyar ƙaddara ce da duk yaƙi da gwagwarmayar masu son daƙile hakan. A baya basuci nasara ba, Taya suke tunanin samunta a yanzu kan _Saifulmulk_ ɗi na?. Kamar yanda aka haifesa daga matsayin gudan jinin Shahan-shan, Tajwar Haysam ibn Abdul-majeed. Shima haka za’a samar da Ɗa daga gudan jininsa da izinin UBANGIJI masu lissafi su fara…”
Muƙutt Malikat Ashwaq ta haɗiye yawun dake neman kufce mata, a zahiri kuwa murmushi ta saki da ɗan girgiza kanta. Batare da tace komai ba tai yunƙurin miƙewa domin barin ɗakin tana mai ƙoƙarin danne zuciyarta dake yunƙurowa. Har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya, batare data juyi ba ta saki murmushi. “Idan dai har Eshaan ya kasance gudan jinin Shahan-shan ne babu gauraye, muma irin wannan fatanne a bakunanmu garesa kasancewarmu uwaye a wajensa. Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki…..”
Har tsakkiyar kai kalaman ƙarshe na Malikat Ashwaq suka daki zuciyar Malikat Bushirat, sai dai kafin ta samu wani damar fassarasu sallamar Ameera Danish-Ara da suka kusan kiciɓus da Malikat Ashwaq ya dakatar da ita. Itace mata ta uku ga Tajwar Haysam. itama da tata tawagar hadiman. Kallon juna sukai da Malikat Ashwaq, Ameera Danish-Ara ta saki wani malalacin murmushi a kaikaice. Sai kuma ta matso cikin girmamawa ta gaishe da Malikat Ashwaq ɗin datai mata kallo guda ta ɗauke kanta. Amsa mata tai cike da ƙasaita, kafin ta matsa ta bata hanya ta shige, itama ta fice tawagarta biye da ita.
Saɓanin Malikat Ashwaq ita ta samu tarba daga malikat Bushirat. Dan duk da take mata itama ga Tajwar kuma Malikat Bushirat kishiya a gareta hakan bai hanata risinawa ta gaidata ba da matuƙar girmamawa tana mai tambayar jikin Iffah. Malikat Bushirat dake kishingiɗe har yanzu a yanda Malikat Ashwaq ta barta ta amsa mata da sassauci mai haɗe da jimami. Cike da makirci Ameera Danish-Ara ke nuna tsantsar tausayin Iffah tana mai yin ALLAH wadai ga duk mai hannu akan waɗan nan al’amura.
Malikat Bushirat taɗan jinjina kai irin na ƙasaitattun mata da yamutsa fuska kaɗan, a saman lips ta furta, “Nagode”.
A kaikaice Amera Danish-Ara ta ɗan saƙi murmushi tare da harararta ta ƙasan ido. A zahiri kuwa zamanta ta gyara tare da risinar da kanta. “Wannan abunda ya shafemune ai gaba ɗaya ranki ya daɗe. Domin Zaki ɗammu ne, fatammu dai ALLAH ya warware waɗannan al’amura cikin sauƙi”.
Har cikin zuciya Malikat Bushirat taji daɗin kalaman Amera Danish-Ara, dan haka a lips ta amsa da “amin” tana mai sauke ajiyar zuciya, dan bata cika samun damuwa da ita a gidanba tunma sunada ƙuruciya. Amera Danish-Ara mace ce mai tsananin kissa da ba lallai a lokaci guda ka iya gano wacece ita ba. Duk da kasancewar ita Zawjata-almilki ce a daular ruman zakasha mamakin irin girman da take bama Malikat Ashwaq da Malikat Bushirat a gidan a zahiri tunda ta shigo. Kai hatta da Amera Haifah dake amarya kuma ƙarama a cikinsu ita bata taɓa bari saɓani ya shiga tsakaninsu ba a zahiri. Wannan halin nata yasa sanda surukarsu Malikat Haseena ke da lafiyar ƙafa take sonta da janta a jiki fiye da su Malikat Bushirat. Wani lokacin har kwatance take musu da halin Amera Danish-Ara ɗin wai suyi koyi ta fisu dattako. A yanzu haka da take zaune babu lafiyar ƙafa Ameera Danish-Ara ɗin tafi kowa sintirin zuwa dubata da mata hidima a zahirance, duk da itama Malikat Bushirat na kamantawa sai dai babu ruwanta da sai wani ya gani yace tayi.
Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna, Amera Danish-Ara na son taga Iffah babu fuska ga Malikat Bushirat, dole ta miƙe cikin ƴan kame-kame tana tambayar ko Amera Haifah tazo kuwa?.
Kallon ƙasan ido Malikat Bushirat tai mata tana ƙara tsuke fuska, dan ita duk yanda take da zafi babu wanda zaice ga ranar data zauna maganar wani a cikinsu koda da su Jasrah ne kuwa. A ganinta idan tai hakan sunma isa kenan a wajenta. Murmushin yaƙe Amera Danish-Ara tayi cike da basarwa. Sai dai ƙasƙantaccen kallon da Malikat Bushirat tai mata ya matuƙar sokar mata zuciya. Taɗan risina da faɗin, “Na barki lafiya ranki ya daɗe”.
Kai kawai Malikat Bushirat ta jinjina mata batare data ko ɗago ba. Amera Danish-Ara ta cije baki da ficewa hadimanta dake jiranta daga falo na biyu suka take mata baya.
Sam Amera Danish-Ara bata gaban Malikat Bushirat, kalaman Malikat Ashwaq ne keta faman mata kaikawo a zuciya musamman na ƙarshe. (Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki) waɗan kalamai bakwai a cikin tarin kalaman Malikat Ashwaq sunfi komi tsayawa Malikat Bushirat a zuciya. Dan kuwa tana fassarasu ne da wani abu daban ne. Haka manyan mutanen masarautar suka cigaba da shigowa duba Iffah daga sassa daban-daban na gidan. wasu iyaye ne, wasu yayu, wasu ƴaƴa harma da kakanni maza da mata duk da basu samun damar shiga ciki iyakarsu wajen Malikat Bushirat. Bata damu kanta ba sai da dare yaja. Koda hadimanta suka dawo sallamarsu tai dan tafi buƙatar kaɗaici a yanzu saboda son ƙara tunani akan kalaman Malikat Ashwaq da suka gagara haɗiyuwa a gareta. Da kuma nazartar kowa daya shigo sashen nata domin duba Iffah. Tun tana a zaune har takai ta miƙe tsaye hannayenta goye da bayanta tana faman kaikawo tamkar mai safa da marwa……….✍
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
✨Ɗ ✨
( )