Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 59

Sponsored Links

59…..
Ganin ynda take kuka yasa Aliyu ya dago kanta a hankali yana kallon cikin idonta a sanyaye, ya rumtse idonsa don bae son jin sautin kukan nata yace “ya isa hka Ikram” kin daina kukan tayi, hkn yasa ya bude idonsa ya shiga share mata hawayen fuskarta a hankali yace “ya isa Ikram kar ki sake kuka, kinji ” kai kawae ta gyada masa tana kallonsa, ya mike yana rike da hannunta, suka fita daga falon, garden ya nufa da ita ya xauna, ita ma ta xauna gefensa, ya kamo hannunta yana kallon cikin idonta a hankali yace “Ikram” tayi shiru tana kallonsa, ya lumshe idonsa yace “promise me ko me xae faru baxa ki barni ba Ikram we wil alwayz b 2geda” shiru tayi tana kallonsa bata ce komai ba, ya ci gaba a hankali kmr me shirin mata kuka “kiyi min alkawarin baxa ki aura kowa ba sae ni Ikram” Khaleel dake xaune balconyn dakinsa yana kallonsu yyi murmushi ya kauda kansa, wae Ikram Aliyu yasa gaba yake ma wnn mgnr, Muryar Ikram yaji tana cewa “i promise yayana baxan aura kowa ba sae kai ni kai kadae nake so yayana” juyowa yyi yana kallonta da mmki, sae abun ya basa dariya, Aliyu ya rumtse idonsa ya rungumeta yace “i luv yhu more Ikram” kai kawae ta gyada masa, Khaleel ya tabe baki ya mike ya shiga dakinsa, xobe karami me kyau Aliyu ya ciro ya saka mata a hannunta tayi murmushi tace “ngd yayana” kasa ce mata kmai yyi ya tsura mata ido. Ranar wednesday Ikram na dawowa daga sch tace ma Mami ita gun Ammi xata yi Mid term Break dinta, Mami tayi shiru tana kallonta don ita kam ta rasa me ke damunta, duk ta xama wata silent kmr ba Ikram, Mami bata mata musu ba tace “to bari Khaleel ya dawo ya kai ki, but kinsan kun kusa fara junior waec Ikram ki tafi da buks dinki da xaki karanta a can” Ikram tace “to” snn ta wuce sama Mami ta bita da kallo tana mmkin sauyawanta lkci daya, ikram dae yarinyace bare tace abu tasa a rae. karfe biyar Khaleel ya shigo gidan bayan Mami ta kirasa ya kai Ikram gida, Mami ta hada mata few kayanta da text buks ta sa su a jaka snn ta mika ma Khaleel ya kai cikin mota, juyowa tayi tana kallon Ikram tace “dota ban fa ce ki ba ma Ammi lbrin abinda ya faru ba kar ki kuskura ki ce mata komai kin ji,” Ikram ta gyada mata kai snn suka fito xuwa gun mota, Mami ta buda mata front seat ta xauna, Khaleel ya shiga driver sit ya tada motar suka bar gidan Ikram na daga ma Mami hannu, har suka isa suleja be ce mata ba bata ce masa ba. Ya gama parkin karfe shidda dai dai, ta bude motar ta fita ta buda bck seat ta ciro jakar kayanta snn ta juya tana kallonsa tace “bye” ta juya tayi cikin gidansu, binta yyi da kallo har ta shiga snn ya tabe baki ya buda mota ya fito ya shiga gidan shi ma, Ammi na share tsakar gida ta mike tana kallon Ikram da mmki, Ikram tayi murmushi ta rungumeta, dae dae nn khaleel ya shigo gidan, Ikram tayi cikin dakinta da jakarta, ya xauna suka gaisa da Ammi tana tambayarsa Mami da Aliyu, mintinsa goma a gidan yace xae koma, Ammi tayi masa tayin abinci yace “Alhmdllh” tayi masa Allah ya kiyaye hade da gdya snn ya fita daga gidan. Washegari da safe Ikram na xaune tana cin koko da kosan dake gabanta ita da Amminta, Ammi tace “baki da lfya ne Ikram” Ikram ta dago kai da sauri tace “ni Ammi?? Aa ni lfyata qlau, taba jiki na ki ji” Ammi bata ce komai ba ta ci gaba da cin kosan dake gabanta a hankali, abu daya ne Ammi bata ji ddi game da Ikram ba, kuma shine rashin iya aikinta, sam bata iya komai ba, don kasa wanke kwanukan da ta bata tayi, tsakar gida ma sharan hauka tayi masa, bata dae ce mata komai ba amma ta dauki aniyar yi ma Mami mgna ta dinga barinta tana dan aikace aikacen gida tunda mace take kuma aure xata yi, da yamma Ikram na wanke wanken kwanukan da Ammi ta tara mata ta wanke tana xumbure xumbure, Ammi kuma na tankada gari, suka ji ana sallama a bakin xaure, Ammi ce ta mike ta fita dae dae lkcn da ta ci karo da yaron makwabtansu yace “mmn ikram wae ana sallama a waje” kan Mami tace komai suka shigo gidan sun kai su biyar.

Back to top button