Nasarar Rayuwata 12
*Talented writers forum*
* NASARAR RAYUWATA*
*12*
Hajjo na wani kauye mai suna gurku sunje biki tare da mmn Nana bikin wata y’ar makociyarsu hajjo tabiyo wasu yan matan unguwar tasu sun tafi saman dutse, waje ne mai kyau ga korama ga manyan duwatsu masu tudun gaske haka yaran sukahau masu waya na faman daukan hotuna ga bishiyoyi masu gwanin ban sha’awa, hajjo tahau sama can da nisa tana tafiya a hankali cikin tsautsayi ta zame ta gangara nan ta fara tsala ihu tana gangarowa har ta sauka kasa ta bugu sosai yaran suka taru a kanta , taji ciwo jini na zuba wani yaro ya dauketa cak ya tafi gidan bikin da ita ana Neman mahaifiyarta . mmn Nana ta tsorata ainun gaba d’aya ta rikice nan aka nemi keke napep mmn Nana ta shiga da ita da wasu matan unguwar tasu biyu suka kama hanyar komawa saboda babu asibiti a kauyen, a can Aso akwai wata private hospital Mizaya nan aka kaita doctor ya karbeta cikin gaggawa ya mata allura ya dora mata ruwa ta samu bacci. Aman na tsaye a kofar gidan yana kallon unguwar yana girgiza kai cikin tausayawa yanxu haka talaka ke rayuwa babu hanya babu ruwa ga datti duk inda ka duba kwatomi ne ga warin bayi ga ruwa ga kuda ya zaayi cuta bazai kamasu ba, inna ta fito ta leka yana ganinta ya ganeta saboda kamanninsu da hajjo ” ina wuni inna ” ” lafiya ya gida, kai ke Neman hajjo? ” sunkuyar da kai yayi ta kare masa kallo tace ” kai kuma a ina kasan hajjo ince dai lafiya kake nemanta ” ” inna kiyi hakuri nasan hajjo karamar yarinya ce amma ina son ki bani dama na fara Neman aurenta ” aure kuma samari , yanxu ne ta shiga 13 years kake zancen Neman aure ,kuma naga kai dan masu kudi ne ko baka furta ba ” ” inna zan jirata har xuwa lokacin da zata kara girma amma don Allah kiyi hakuri kada ki rabani da ita ” shiru inna tayi ta kasa magana mamaki ne karara a fuskarta kafin tace komai mmn salma ta sakko bisa Babur ” malama kiyi maza ki tafi mizaya hajjo tayi hatsari ta fado daga saman dutse..” ” innalillahi wainna ilaihirraji’un , saman dutse ” Aman yace ” subahanallah inane asibitin ?” ” wannan kuma waye malama, dan uwanku ne ” Aman ya mata mugun kallo yace ” wannan kuma ba huruminki bane, inna idan kinsan asibitin taho mu tafi ” inna ta shiga ta kulle kofa ta fito gaba d’aya a rikice take tasan mizaya saboda makotansu na yawan zuwa asibitin , ya bude mata baya ta shiga ya rufe ya shiga bangaren driver suka kama hanya suna tafiya tana nuna masa har suka isa asibitin.
Suna shiga ward din suka ci karo da mmn Nana tana ganin inna tace ” kiyi hakuri malama sai kika samu mummunan labari, wllhi sun fita tare dasu …” Haba malama ki nuna mana Mara lafiya ko zaki tsaya bayani ” Aman ya fada cikin takaici haka ta musu jagora xuwa dakin, suna shiga inna ta nemi waje ta xauna tare da kauda kanta gefe domin raunukan sunyi yawa lallai Allah ya kareta da yau batasan labarin da zaa kawo mata ba, hawaye ne ya fito tayi saurin gogewa batason mmn Nana ta ji haushi amma tabbas bataji dadi ba har cikin zuciyarta dama can ita ta nace kan cewa sai sun tafi da hajjo, Aman ya karasa kusa da gadon yana kallonta ya juya gun inna ” inna anya bazamu tafi cikin gari daku ba a kaita babban hospital don naga raunukan suna dayawa ” murmushin karfin hali tayi tace ” babu komai nan ma yayi Allah ya bata lafiya ” ” ameen inna amma dai da an canza wani asibitin ” ” nagode da kulawa” mmn Nana da take a rude tace ” malama da kin amince akaita na cikin garin ai sunfi kwarewa ” shiru inna tayi Aman ya kurawa hajjo ido cike da tausayawa, wayarsa ya fara ringing ko bai duba ba yasan Ammi ke kira bai d’aga ba har ya katse dama a ka’idarta bata kiran mutum sau biyu face idan kiran gaggawa ne.
Dr ya shigo ya dubata nan suka gaisa yace ” alluran bacci aka mata amma jikin da sauki zata warware babu matsala ” godiya inna ta masa nan ya rubuta wasu magunguna yace a siya Aman ya karba ya duba 3800 yace ” nawa total bill nata ?” ” ka sameni a office ” daga haka suka fice tare, mmn Nana tace ” wannan kuma waye ne malama ?” Umm..kedai ki bari sai mu koma gida ” tabe baki tayi tace ” naga alama yana ji da naira ” suna nan zaune Aman ya dawo ya mikawa inna receipt ta karba ta duba bill din 15k babu kudin magani a ciki ” yanxu duk wannan dawainiya haka, mun gode sosai Allah bada lada ” murmushi yayi yace ” zan tafi gida sai gobe insha Allah Dr yace gobe zai sallameta, yanxu zan duba pharmacy a waje sai a bata magungunan idan ta farka ” godiya suke masa har ya fita, inna tace ” Allah mai iko kenan , ga kaddarar da ta fado sai kuma Allah ya turo mai taimako, yanxu dubu sha takwas da dari takwas ya kashe mata Allah bada lada ” ” ameen kuwa da bamusan ya zamuyi ba ” murmushi inna tayi ” Allah baya taba rufe kofofi dole zai bar wata a bud’e , alhamdulillahi ” hira suke har ya dawo ya mika musu maganin ya musu sallama ya tafi yana mai tausaya musu da irin rayuwar da suke ciki.
_______________
Ammi ta cika tayi fam saura kiris ta fashe tana jiran dawowar Aman har aka kira magrib ta shiga sallah , bayan magrib ya shigo gidan a gajiye saboda hold up din maraba -Nyanya kai tsaye bedroom nata ya wuce ” Ammi sorry sai dazu ne nake…” ” ka adana bayanan naka bana bukatar ji , ba ka gama rainani ba, ina ka tafi da yamma bayan nasan yau baku da lectures ” ” Ammi Ni yarone duk inda zan tafi sai na fada a gida , yanxu idan nace zanyi aure zaa hanani ne ?” ” da ma auren kayi ya fiyemin wannan galantoyin da kake daga gidan rawa xuwa parks da cinemas ” ” da gaske Ammi idan nace zanyi aure zaki amince ?” ” me zai hana kuwa idan har ka samo y’ar babban gida ba yar matsiyata ba ” shiru yayi ya tashi ” kinsan dai na daina zuwa clubs da cinemas, ke dai ki cigaba da min adu’a kawai ” ya fice daga dakin ta girgiza kai ” duk yafi bani wahala cikin y’a’yan nawa ” ta juya ta cigaba da Jan carbi. A falo ya hadu da Ayman ” hey bro, bari nayi salla akwai wata magana da zamuyi da kai ” ” OK ” tsaki Aman yaja tare da cewa ” kai dai an shiga uku kamar Kaine sarkin garin naku, sai shegen girman kai ” hararinsa Ayman yayi ya shige daki yana dariya. Bayan anyi isha suka hadu a table wajen cin abinci Ammi na wajen babu yadda zasuyi magana sai bayan ta tafi ta barsu ne Aman ya koma kujerar dake kusa da ta Ayman yana magana kasa-kasa ” bro kasan me, wannan yarinyar sonta nake kuma ina son aurenta. ..” Tari Ayman yake yayi saurin ajiye cup din hannunsa ” sorry! Aman ya fada sannan ya cigaba ” kasan Ammi batason talakawa kuma yau naje gun mom nata na gabatar da kaina ” ware ido Ayman yayi ” are you serious, Ashe kana da karfin hali bansani ba , wannan small girl din me abin aure a gurin ” “man she is darm beautiful, bazaka gane bane Ni nasan kayana ” cikin zuciyar Ayman kuwa tamkar zata fito don haushin kalaman Aman yake ji, ” kana ji ina son gobe ka rakani muje dubata she met with an accident ” ” subhanallah..when.how?” ” calm down bro ya naga ka tsorata, anyway ta samu sauki tana hospital ” wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke don haka kurum yaji Abu ya tokare masa kirji, ” “Allah bata lafiya” ” ameen bro, kasan me nake tunani , I think kawai zan turata boarding school ” ” hakan nada kyau ” ” kai shawara nazo nema but baka cewa komai ” murmushi yayi ” is OK gobe zamuje insha Allah ” daga haka ya tashi ya fice yana danna waya, tsaki yayi ” banza kawai mutum ne kamar wani kurma , kai shiru shiru baiyi ba ” ya dauki wayarsa yana chat . d next day suka shirya tare da fauzan da driver mota d’aya suka shiga suka tafi, inna na waje saboda an shiga mata allura ta bar d’akin tana xaune Aman ya shigo harabar asibitin Ayman na baya sai fauzan dake ‘dauke da ledoji gaisheta sukayi suka tambayeta mai jiki tace ” ana mata allura but nasan angama , dama Dr yace anjima zai bamu sallama ” ” Allah kara lafiya ” ” ameen mun gode da dawainiya ” ” babu komai inna ” daga haka suka wuce ciki a bakin kofa suka hadu da nurse tana fita sai kallonsu take suka wuce babu Wanda yace mata uffan. Hajjo na kwance gashin kanta ya baje bisa filo kanta babu hula ga bakin gashin nata sai daukar ido yake , she was surprised da ganin Aman, tunda suka shigo Ayman ke kallonta ya kasa cire ido a kanta yaune ya samu damar kare mata kallo tana da innocent beauty Wanda sai ka maida hankali zaka gane hakan ” ina wuni ” ta fada cikin siriryar voice nata ” ina ka tafi sati biyu ina zuba ido bana ganinka ,nayi fushi da kai ” ” afuwan besty na nayi tafiyane kiyi hakuri ” ” um um ” ” please my little girl ” , fauzan dai ya ajiye Leda ya fita waje ya tsaya bakin kofa Aman ya nemi waje kusa da ita ya xauna Ayman yace ” amma dai kasan hakan bai dace ba , n beside her mom is here she might not like it , don’t disqualify yourself please ” hajjo bata fahimci sauran zancen ba amma ita kanta taji dadin tashin da yayi saboda idan inna ta shigo ta samesu hakan batasan matakin da zata dauka kanta ba, “waya nuna ma unguwarmu kuma who told u bani da lafiya ” ” zuciyata ce ta rayamin baki da lafiya, gane inda kike kuma tambaya nayi ” murmushi take sannan ta maida kallonta gun Ayman suka hada ido tayi saurin cire nata tana murmushi yana da matukar kyau na daukar hankali gashi da natsuwa da sanin ya kamata ” besty ba hirane yau ko kina jin kunyan wannan he is my cousin bro ” murmushi tayi tace ” yana da kyau har yafi ka ” hararinta Aman yayi ” wannan bak’in ne zakice ya fini kyau for wia, abeg makeuna lookam wella ” ” he fine pas u na ” ” iyye my besty ta fara koyon pidgin ” murmushi Ayman yayi yana jin wani irin yanayi a cikin zuciyarsa. ” ka gaya masa ya zauna yana tsaye ” ” ke baki da baki ne” turo baki tayi tace ” naga baya son magana ne na gaishesa bai amsa ba ” murmushi ne ya kubcewa Ayman baisan lokacin da yace mata ” am sorry na amsa miki baki ji bane maybe, ya jikin ” zare ido Aman yayi ” I cant bliv dis, sarkin yan girman kai ne ke furta sorry, wow …” juya ido Ayman yayi ya kauda kai gefe , inna ce tayi sallama ta shigo ” Sannunku fa, mun gode da dawainiya Allah bada lada, ga takardar sallama yanxu aka bani ” ” OK inna Ku shirya idan muka ajiyeku gida sai mu wuce ” ” ah ah wllhi mun gode zamu shiga keke,” “haba inna ga mota ” ” kuyi hakuri nagode ” nan ta fara harhada kayansu duk nacin Aman taki amincewa dasu saukesu gida dole ya hakura ya barsu, hajjo ta tashi ta saka hijabi Aman na tsokanarta yace ” nidai zaki rakani wannan dutsen ina son ganinta ” ” idan ka shirya zuwa bismillah ” suna tafiya suna hira fauzan ya rike wasu kayan inna na rike da wasu tayi gaba ta barsu har ta tare keke , hajjo ta shiga suna d’agawa juna hannu har suka tafi yana murmushi yace ” idan na shirya har gida zan samu inna muyi magana ta ajiyemin hajjo amana har xuwa lokacin girmanta , I really like the girl ” ” Allah yasa da gaske kake babu yaudara ko wata manufar ” ” am serious man, Ni kaina bansan zan kamu da sonta haka ba” ” Allah ne ya kama ka ” tsaki ya ja ya bude mota ya xauna, Ayman ya zagaya ya shiga fauzan ya shiga gidan gaba suka tafi.
*Nasarar rayuwata is not for free Ku biya 300 tuntubi 07030077024 for payment details thank you*