Hausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 7

Sponsored Links

Free page7
2month ya iyayi a garin Kano da kyar, Kai kace tsungulinsa, ba tare daya kammala Ayyukan gabansa ba yaji kawai so yakeyi ya tafi katsina, be san dalilin dayasa yakeso ya tafinba kawai de yaji yanaso ne ya dawo katsina. Jirgi yabi ya dawo garin katsina, daman sometimes shine kawai keson tafiya a mota in zeyi tafiye-tafiye yanada kebantaccen jirginsa,danma ynzu da rayuwa tayi tsada sace-sacen mutane yayi yawa musammanma hanyan abuja, shiyasa yake Hawa jirgin sometimes, Amma yafi kaunar tafiya a mota, sede in Nisan tafiyar yayi yawa, Kwata-kwata baya jure zaman mota sede awa biyu uku hudu biyar yake iya jurewa. Kasancewar be bar garin Kano da wuri, se after Azahar ya bar garin kanon, danma jirgine bawani jimawa ya sauka a babban Airport din dake garin katsina, already daman dreva dinsa da matakan tsaronsa suna airport din suna jiransa, Dan haka ba bata lokaci ya shiga mota aka nufo gidansa dashi,. Kallon hanya yakeyi Amma zuciyarsa na can ga tunani-tunani daban-daban, shide yasan Wani Abu na damunsa Amma ko za a kashesa besan mezece yana damunsa ba,. ”Ya Allah!” ya fadi da sassanyar muryarsa tamkar busar sarewa, yakai hannu ya dafe saitin zuciyarsa Yana mejin bugunta da sauri da sauri. ”Ya Rabbih kayimin maganin boyayyiyar damunata…” Ya fadi a zuciyarsa, yayinda wayarsa ta dauki ringing ya duba yaga Daddynsa ne, girgiza Kai kawai yayi tinda ya bar garin daddy be kirasa ba, shima kuma Aeezad din be kirasa ba, abinda yasa shi Aeezad be kirasa ba sbda sometimes koya kirasa ba dagawa yakeyi ba, musammanma in Yana tare da hajiya mommy to ko ubanwa ze kirasa ba dagawa zeyi ba,. Yana niyar daukar wayar ta katse ya kirasa back bugu biyu daddyn ya daga. Sallahma Aeezad ya masa Hadi da gaidasa cikin girmamawa. Alhaji sunusi ya amsa cike da so da kaunar d’ansa tilo namiji, kana yace “Lafiya kwana biyu shiru ubana shirun yayi yawa ko ayyukan ne?” a yadda yakewa Aeezad magana ya tabbatar masa da basa tare da rafi’ah domin da suna tare da wuya ya kirasa. “Alhamamdulillahi daddy kawai ayyukane sukamin yawa..” “tohh tohh ,,shikenan Allah yayi Albarka, Allah yasa ku gama da duniya lafiya, Ubangiji ya jikan mahaifiyarku me kaunata…” Alhaji sunusi ya karashe murya cikin rashin dadih. Cikin Wani yanayi shima Aeezad ya amsa da “Amin ya Rabbil izzatih daddy…” “Ya wajen Hafsatu da jikokina ” Girgiza Kai kawai Aeezad yayi Wani takaici ya cika masa zuciya, ace suna the same state wai shida yake wani garin shi daddy ke tambaya Ya hafsat, mutum da yaransa seya buya ze kirasu a waya ” gaskiya rashin uwa ma jarabawa ce…” Aeezad ya fadi a zuciyarsa Sam kuma se yaji Wani takaici yayima Zuciyarsa dirar mikiya, ya tabbatar da sunada mahaifiya da hakan be faru ba, tabbas inka rasa uwa ka rasa rabin dadihn duniyarka. “duk lafiya Lau suke ..” shine abinda Aeezad ya fadi a zahiri. “Masha Allahu a gaidasu Allah ya hanaku damuwa duniya da lahira ..” “ga damuwar nan kanasa mana.. ” Aeezad ya fadi a zuciya, besan mgnr ta fito fili daddy yaji ba, kawai sede yaji daddyn nacewa. “kuyi hkri wata rana se Labari, ba abinda yake dawwama…” A yadda yayi mgnr seya bawa Aeezad tausayi kawai ya furzar da iskar takaici da bakinci da tausan Mahaifin nasa gabaki daya. “Thanks daddy,Allah Kara lafiya…” shine abinda Aeezad ya fadi. Alhaji sunusi ya amsa da Amin daga haka sukayi sallahm. Aeezad ya ajiye wayar gefensa kawai Yana me tunano abubuwa da dama, shi da kansa yasan matsalolinsa sunada yawa,ga rashin uwa, ga mahaifinma da kadan yaso yafi kwara babu, ga na’eema itama matarsa da tini tazama kwara babu, Tako ina deshi babu dadih, mommynsa ce kawai inya tunata yakejin sanyi a ransa, a nan yake samun saukin wasu lamuran, da besan ina ze tsaya a damuwa ba. Da tunani tunani a ransa Aka isa gidansa dashi, wanda tin daga bakin get har zuwa cikin gidan abun kallo ne , duk iya gayunka in kazo gidan Aeezad dole ka zama Dan kauye, shi karshe ne a gayu da tsari. Tin kafin dreva ya karasa packing dinsa a packing space din gidan Aeezad ya kula da motar Na’eema wadda tafi Hawa a farfajiyar gidan, da wata motar ma da besan ta wacece ba,kirar Jeep, hakan yabawa Aeezad tabbacin na’eema tadawo gidan, haka kawai ya tsinci kansa da rashin farin ciki akasin da, da ace Dane da tini yanata murna a part dinta ze yada zango,ko wanka baze ba ze hauta daci, se ya sauke nauyin mararsa kana ze samu nutsuwar ko abinci yasamu yaci. Akasin yau, yanajin sha’awarh bawai beji ba,Amma sam be tunkari part dinta ha, ya tinkari nasa part din,. Direct a bedroom dinsa ya yada zango ba bata lokaci ya fad’a bathroom yayi wanka ya fito daure da Alwala ya shirya cikin kananun kaya na hutu, ba karamin amsar launin fatarsa kayan sukayi ba, dai-dai ana Kiran la’asar already daman ya dauro alwala lallausar takalminsa ya saka ya fito farfajiyar gidan ya nufa masallacin dake cikin gidan. Bayan sun idar da sallar ya fito daga masallaci hannunsa rike da counter Yana lazimi. Dai-dai Na’eema da khady sun fito ,na’eema zata rakata motar khadyn wadda zata tafi gidanta, domin ta d’an jima a gidan tin kafin Azahar tazo. Sukayi kicibus da Aeezad, kallo daya ya musu ya dauke idanuwansa A kansu yayi kamar ma be gansu ba, na’eema ta tabe baki ganin kallon dibar iskar dayayi musu daman shi haka yake Amma a daki ya dage yayita cin gindi, ya iya zunguri Kam kuma ya iya yarfi. khady ta kuresa da Ido a zuciya se wow wow kawai takeyi knr motar Ambulance! bata taba ganinsa da kananun kaya ba se yau, Ashe kyansa ya wuce tunanin khadyn bata sani ba se yau. “Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci kyakyawan namiji me Asali(wato tsawo)…” Khady ta fadi a ranta seda ta sauke ajiyar zuciya, ko a Ido tasan guy dinnan zeyi dadih na matsifa, itafa wlhi da ace ze aureta tini zata kashe aurenta ta auresa koda ace beda ko sisi balle uwa uba ya tara qualities na fitar hankali, ga kudi ga kyau ga cikar haiba, ga asali (wato tsawo). “Ina wuni ranka ya dade…” khady ta gaidasa cikin girmamawa dai-dai sun karaso daf-daf da junansu. “Lafiya Lau,,, ya iyali?” Aeezad ya amsa a takaice Hadi da Tambayarta ya iyali sbda ya ganeta, yasanta a matsayin Aminiyar matarsa tin kafin ya Auri na’eemar. “Lafiya Lau Alhamamdulillahi….” Khady ta amsa, yayinda Wani irin sanyi da dadih me ni’ima ya ratsa khadyn tana bala’in San muryarsa tana narkar da ita over,, khady tayi murmushinn boye tabi bayansa da Ido yayinda tuni ya isa part dinsa, yanada sassarfa yanada sauri sosai kuma a hnkli yake tafiya. “Daman Yana Nan ne?”” Khady tayi tambayar taba dawo da akalarta ga na’eema wadda suke tafiya zuwa motar khady ita Kuma na’eema na danna wayarta a duniya na’eema bata rabin second bata danna waya ba, kullum wayarta na hannu tana chart a groups da friends dinta ko kuma tana kan tiktok tana kallo, ko toilet zata shiga da waya a hannunta. “Aah bayananfa inaga yanzu yadawo gaskiya,,,” cewar na’eema datayi mgnr irin ko a jikinta dinnan, itade tasan tana kaunar Aeezad Amma sam wahalace ita bataso, shi kuma Aeezad nada sa Aiki, uwa uba kuma shegen San sex din tsiya, wanda dayayi dayasa mata ciwon jiki. “Amma shine baki gaidasa ba ko ki nuna murnarki a fili na dawowarsa…” khady ta fadi fuska dauke da mamakin hali irin na na’eema. Tabe baki na’eema tayi dai-dai suka iso bakin motar khady. “Murnar me zanyi danya dawo ? Daukarsa zan in goyasa a bayana in maidasa jariri…” cewar na’eema dake mgnr tana tabe baki. Khady tace “No but at least ai yakamata de ko gaidasa ne Kiyi…ke koni da raini yashiga tsakanina da mijina sbda rashin iya tabuka komi inya dawo daga tafiya ina tarairayarsa, sannan ina gaidasa cikin girmamawa,…” Cikin kosawa da mgnr na’eema ta amshe da “uhmmm kede khady da Allah kyale mutuminnan..ni wallahi zuwanki ma ya temakeni,nasan danya ganki ne ai da direct part dina zezo ya tasani da gafza,,jarababbe kawai!” khady tace “Allah kyauta…” Tana me duba time, saboda mijinta na gari kuma baya barin fita shegen kullen tsiya ne dashi, in zata fita seya bata awannin da yakeso tayi, inko ta wuce awannin Nan se yayi fada sosai, in bayanan Sam baya barinta fita ,gashi ya cika gidan taf da matakan tsaro, in zasuje kasashen waje sede duk inda tasa kafa yana Nan ko kuma sakataransa na Nan kusa da ita , Sam bata sakewa, da ace ita kazar sake ce da Allah kadai yasan me zatayi. “ni zan wuce , nasan Alhajin Allah nacan yana duba time tin dazu,…” Khady ta fadi tana bude gidan baya tashiga domin daman dreva ne ya kawota.. “Alhajin Allah manya,, duk tsoronsa fa karkije a sosa miki inda shi be sosa miki ..” cewar na’eema, khady ta kyalkyake da dariya Hadi da nunawa na’eema dreva din khadyn dake gaban motar Alamar tayi shiru karya jisu. “Afff….” Na’eema tace Hadi da rufe baki, khady takai mata dukan wasa sukayi Yar dariya, kana sukayi sallama dreva yaja khady suka fice a gidan, Na’eema ta juya zata koma part dinta, taga Aeezad ya fito daga part dinsa hannunsa rike da car key, ta kallesa taga shi ko kallonta ma beyi ba tamkar be ganta ba, ya nufa motarsa yashiga yaja da kansa ya fice a gidan. Na’eema ta daskare a tsaye ba karamin mamaki Aeezad ya bata ba yau, ganin yadda bebi ta kanta ba, mamaki ya tsaya mata a wuya wai yau Aeezad ne ze dawo ya iya fita ba tare Daya Addabeta da laguda ba. “Tafi nono fari ” na’eema ta fadi Hadi da daga kafad’arta ta nufa part dinta.

5:pm tini ta gama girkin dare , daman girkin kadai takeyi a gidan shine aikinta, akwai ma’aikata kusan goma a gidan masu share-share da wanke wanke, kasancewar gidan nada tsananin girma kuma ga yawan part’s,kullum se an gyara kowani part sbda baban Noor na yawan yin baki abokan Aikinsa. Zaune take a tamfatsetsen falon kasa, ita da yaran sunata bata labarai iri-iri wasu ta gane wasu kuma Sam bata ganewa,mahaifiyar yaran tana sama domin yau weekend ne ranar hutunta kenan, bata cika sakkowa kasa ba in ana weekend tafi zama a sama, Baban Noor kuma yana part dinsa. Kaman daga sama taji an turo kofar falon baki dauke da sallahma Kasa-kasa a natse, tin kafin yayi sallama tasan shine ya shigo sbda taji kamshin turarensa tin before ya bude kofar shigowa falon. zubo masa dara-daran idanuwanta masu kyau na fitar hankali Tayi se wani lumshewa idanuwan nata keyi cikin salon fisgar wanda ake kallo, ita haka idanuwanta suke, kullum cikin yauki suke. Maida kofar yayi ya kulle ya jingina bayansa da kofar shigowa falon, yana mejin zuciyarsa na Wani irin harbawa cikin hanzari, sbda zuro masa idon da tayi,, shima zuro mata dara-daran idanuwansa yayi narkakku sede basu Kai nata narkewa ba, sanye take da rigar zaman gida faraa sol me rodi-rodin d’awisu a gaban rigar cikin adon red-red, yayin datasa hula red a Kanta. Tamkar An kara masa matsifar dake damunsa haka yaji Nan da Nan yayi losing controlling, idanuwanta suka masa kisan gillah, kwata-kwata abinda yakeji bazeyu ya iya jurewa ba. “Wayyo Allah nah! Zuciyata namin zugi Me kunah!” Ya fadi Yana me dafe saitin zuciyarsa wadda ke barazanar fashewa daga ciki, Kawai seyaji wasu hawaye masu Azabar zafi tamkar ruwan Daya kusa tafasa suka wanke masa kyawawan kumatunansa, shi irin Mutanen Nan ne marasa juriya a kan abinda yakeji mara dadih a zuciyarsa, Jarumi neshi me firgita maza, Amma a Wani fannin shi rago ne!.

 

 

Paid book ne naira dubu Daya, 0542793718 Saadatu Abdullahi gt bank 08101626484.

🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
*NAMIJIN ZUMA*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥
(Love And Romantic Story)

https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Free page group

SAADATU BINTU ABDULLAHI (Writer of kyautar Allah)

Back to top button