Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 47-48

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*47&48*

 

 

…….daddy ya girgiza kansa cikin wani yanayi yace”bana zaton zan iya biya mata gaskiya sbd Abinda ta Aikata mun”yanxun haka takadar sakinta biyu na nan Ajiye idan tadawo gidan na bata”wannan shine hukuncin laifin data Aikata mun”sauran hukunci kuma itada Allah sbd har Abada dani da mahaifiyarku da salma bazamu tab’a yafe mata ba….. Akan me zaka saki matarka sbd mu?”to wlh kasani babu ruwana da Abinda zaije yadawo awajen danginka, sannan bazan iya rik’e mata y’ay’a ba”musammun nida ta cutarmun da tawa y’ar “cewar mommy cikin b’acin rai tana mik’ewa tsaye ta wuce ciki”hamma yusuf ya sauke Ajiyar zuciya yana fad’in hukuncin daka yanke shine daidai da ita daddy”yara kuma zaka iya basu wannan gidan naka da babu kowa ciki ta koma ita dasu su zaunah “kana cigaba da ciyar dasu,dukda nasan bazata so hakan ba daga ita har su d’in, sbd gidan ko rabin kyawun nan gidan beyi ba”sannan daddy kayi hak’uri kabiya mata kud’in nan tunda Anan tasami lalurar nan kodan sbd yaranta”sannan munaso tadawo hayyacinta taga Abinda ta Aikata baya yasaka salma taci ko gaba taci?? d’an shiru daddy yayi Alamar tunani”yayinda Amaan ta gyad’a kanta tana Ajiye plate d’in hannunta cikin gamsuwa da kalaman yayan nata”Ahankali tace”daddy babu damuwa zan bada dubu d’ari biyar saika cika sauran Amata Aikin kome tamun itada Allah “Ajiyar zuciya daddy ya sauke yana kallonsu one by one kafin yace”hak’ik’a Ina Alfahari da zuri’ar da bilkisu ta haifamun”kun sami ingantacciyar tarbiya shiyasa kuke tunani me kyau”dama Ina tunanin fidda har dubu d’ari shidda da hamsin”sbd million 3 ce nake Ajiye da ita sbd ku dake y’an mata idan natashi Auren ku”Amma ke salma Ina kika sami dubu d’ari biyar?karka damu daddy hamma shariff ne yabud’e mun Account yasakamun kud’i “nima sai yanzun nagani sbd badani yaje wajen bud’e Acc d’in ba”yayi hakane sbd yasan idan yabani hannu da hannu bazan Amsaba”to shikenan hakan ma yayi baya gajiya da hidima”daga yanzun karki koma Amsar komai nasa”yanzun inaso ku tayani bawa mahaifiyarku hak’uri game da Abubuwan da suka faru Abaya”karka damu daddy zamuyi iya bakin kok’arin mu”to shikenan Allah yayi muku Albarka”,daga haka ya mik’e tsaye yafita”Amaan kuwa bama yaya sadeeq labarin shariff ta dingayi”shidai yusuf na saurare sbd yasan shi sune basu sanshiba”sai wajen k’arfe 10 Amaan taje ta kwanta bacci batare data kira shariff ba sbd gajiya tasaka ta manta da wani ta kirashi sai tayi kwanciyarta Abinta……Afannin shariff kuwa tun bayan tafiyar Amaan ya wuce office suna wani bincike shida mus’ab”duk yadda yabasar dason ya b’oye yanada damuwa saida mus’ab ya lura”ya kuma fahimci Akan Amaan ne damuwar tasa tunda yasan yau zata koma garinsu”yaso yamasa zancen ta saidai yadda yaga yak’i walwala yanata d’aure d’auren fuska yasaka yabasar dashi kawai”sai yamma yadawo gd zuciyarsa na sanar masa kamar daya koma gidan zai ganta”saidai koda yashigo Ammi ce kawai da masu Aiki yasamu a gidan”da dare ma da Ammi ta kamasa coffee jinsa yayi wani iri daya kurb’a”sai yaji wanda Amaan ke had’a masa yafi dad’i”coffee d’in dabai koma shaba kenan yakoma parlourn sa yakirata yaji muryar ta” sbd driver yasanar masa sun sauka”to bayan sun gama waya yayita jiran yaga kiranta Amma shiru”shi kuma zafin kansa ya hanashi ya kirata”saiya basar yayi kwanciyarsa “saidai gaba d’aya tunaninta da kewarta sun hana zuciyarsa sukuni”da farko mamakin kansa yakeyi daga k’arshe yabar abun Amatsayin shak’uwa kawai”da k’yar yayi bacci….. washe gari da Asuba daya dawo daga masjeed ya shiga ya gaida Ammi sai yaji kamar zai ganta”harma kunnuwansa najiyo masa sautin irin yadda take shagwab’a”yabi saman bed d’in Ammi da kallo bbu ko k’iftawa”tayi d’an murmushi sbd tana Ankare dashi duk sbd Amaan yaketa kalle kalle…kunyi waya da Amaan ne?”muryarta ta katse masa tunani”Eh tun jiya dai”yaufa?”ah ah”ka tasheta sallah mana”ko Ajikinsa yace”tana fashin sallah ne Ai”kasa cewa komai Ammi tayi tana mamakin taya yasan Amaan batada tsarki??….yana fita ya zaro wayarsa sbd zuciyarsa ta kasa jurewa”dealing d’in number Amaan yayi”bugu ukku Amaan ta d’auka cikin muryar bacci tana hamma”saida shariff ya rintse idonsa yana hawa stars d’in murya can k’asa yace”bakima tashi ba ko?”da sauri ta bud’e Ido sbd jin muryarsa dama bata duba ko waye ba ta d’auka ne dai kawai”hamma Ina kwana?”lafiya qlau”kinyi sallah ne?”da sauri tace Eh”jinin har ya d’auke?zaro Ido tayi tana sakin kukan shagwab’a”yayi murmushi yana fad’in sai bayan 4 days zaki fara sallah yarinya”shine zakimun k’arya ko?”kuma Allah kika kashemun waya zan miki hukunci….kasa mgn tayi sbd dama niyar kashe wayar takeyi yadakatar da ita” yanzun kin koma mak’aryaciya ko?”ni wlh ah ah”tafad’a cikin shagwab’a”ya zauna kan kujerah yace”fad’amun kinyi kewata?”uhmm uhmm! Hmm Amaan kenan”kindai koma mak’aryaciya d’in da gaske ko?”to wai ni k’aryar mena maka hamma?kince bakiyi kewa taba bayan naji Ajikina kina kewata”uhmm hakane gaskiya”meyasa bakayi fushi ba daban kiraka ba?”na miki uzurin ko kinyi bacci sbd gajiyar hanya”kuma sannan kin hanani saurin fushi”daga shi sai me?”sai Abinda nakeyi yanzun wato surutu”tayi dariya kafin tace”wlh har mamakinka nakeyi hamma”kaga gashi na koya maka surutu ko?”Eh mana “Ina yaya mus’ab?yana gidansa”kai kuma kana gidan Ammi ko?to Ina kikeso naje bayan nan?wai hamma shekaranka nawa?”ta canza topic d’in”40yrs”tad’an zaro Ido Alamar mamaki”sai kuma tace”nidai 20 yrs gareni”kaga da 20 yrs ka girmeni”uhmm Amaan baki gajiya da shirme ko?niwai shirmen menayi to?”ta fad’a Ashagwab’e”yayi shiru”hamma! Uhmm” yanzun kaje ka koma bacci ko?”sbd kin gaji da mgn dani?ah ah wlh”bath room zan shiga nayi wanka sai naje nataya mommy Aiki”to shikenan kin kyauta”yaya Ammi nah take?”lafiya qlau itama tayi kewarki”Anjima zan kirata Ai”okay yafad’a yana yanke wayar……cikin kewar shariff data Ammi Amaan ta yini Agidan su”wani lokacin tayi tagumi tana tunani har sai mommy tace”lafiya?”sai tace mata babu komai”Adaren ranar ta turama daddy 500k yacika kud’in daza’ayiwa Anty zabba’u Aiki”da dare bayan sallar isha’i Amaan na zaune a parlourn su tana kallon Arewa24 tana tsammanin kiran shariff”sai mommy na zaune kan carpet itada daddy yana cin Abinci “Ahaka hjy hauwa mahaifiyar Nasir tashigo da sallama fuskarta da Alamar rashin mutunci”saida Amaan taji gabanta yafad’i data ganta”ta kalleta tace Ina wuni?”lafiya qlau ta Amsa tana tsareta da Ido”mommy kuwa tunda ta Amsa sallamarta ta hade rai bata tankata ba”daddy ne kawai ya gaisheta…..naji duk Abubuwan da suka faru shine sbd rashin tsoron Allah za’a yiwa zabba’u sharrin ita tayiwa salma Asiri tunda…..kinga Hjy ya Isa haka dan Allah! koma miye itada Allah, dama Ai goyon bayanta kike”Abinda nasani duk Abinda mutum ya shuka shine zai girbe”zabba’u idan tasami lafiya zan rabu da ita shine hukuncin dana yanke ko yayiwa kowa dad’i ko kar yayiwa kowa dad’i “nasan kinsan tabbas ta Aikata son zuciya ya hanaki Amincewa harkiga laifinta”oh haka zakace?”beyi mgn ba mommy da Amaan suka mik’e tsaye suka fita daga cikin parlourn “daddy yaci gaba cewa”zancen Nasir kuma dama na riga na gaya miki babu shi babu salma”zan baki naira dubu d’ari yanzun ki mayar masa”da dangin mahaifinsa suka kawo kud’in gaisuwa “tunda Abin yazama da zargi Aciki Allah ya had’a kowa da rabonsa…..ba shakka! dole kace haka mana tunda kasan ko baka maido ba muzamu turo A Amsa”idan salma itace kad’ai ce mace Aduniya ka hana nasir yanemi wata….kinga Hjy wlh Ina rage miki ne sbd gudun zumuncinmu ya lalace….yo harna nawa kuma ya lalace d’in?”ta katsesa cikin fad’a tana mik’ewa tsaye “daddy yaja tsaki shima ya mik’e tsaye shine yafara fita sannan ita”mommy da Amaan na zaune bakin k’ofar parlourn suna jin komai”wani irin mugun tsanar matar Amaan taji Azuciyarta”daddy yafito daga cikin parlourn sa rik’e da kud’i ya wurgo mata yana fad’in ko bayan raina duk wanda ya had’a zuri’ata da taki ban yafe masa ba”Allah ya sawak’a na koma barin wani Acikin yarana yaso yaranka”idan kabayar da dubi d’ari sauran irin wahalar da Nasir d’in yamata fa?”koka d’auka banida labarin yana kashe mata kud’i?”to bari kaji gata nan ka tambayeta kuyi lissafi zaizo da kansa ya Amshi kudinsa daya kashe dan bazasu tashi a banza ba”kuka Amaan ta fashe dashi tana fad’in bana k’aunar sa na tsanesa yazo yafad’amun wace uwar yamun ko nayi kama da wacce ke cikin fatara balle harna rok’esa??tashi ki wuce ciki karki koma mgn”cewar mommy fuska Ad’aure “Hjy hauwa taja tsaki tana fad’in mu zuba nida ku”daga haka tayi waje”daddy ransa Ab’ace yanufi sashensa”yayinda mommy tabi bayan Amaan daketa kuka”tana lissafin iya saninta koda Nasir yakashe mata wani abu be wuce 500k”sbd batama Amsar kome dazai bata takeyiba”tasan yasiya mata waya ,yana turo mata kati da data”sai kayan kwalliya haka,koga sallah yamata siyayya shima zata iya k’irga Adadin yaushe da yaushe yamata siyayyar “tana ganin kiran shariff Amma ta kasa d’auka sbd damuwa”tunda shariff yake be tab’a kiran wani mahaluk’i sama da sau biyu ba Amma saida yakirata sau biyar bata d’auka ba”harma yafara tunanin ko babu lafiya”saiga text message nata ya shigo cikin wayarsa kamar haka…..*kayi hak’uri hamma inada uzuri shiyasa banyi picking call d’in kaba* sosai yaji haushi tare da shan Alwashin bazai koma kiranta ba”Aganinsa koma meye yaka mata ta d’auka tasanar masa damuwarta ko uzurinta”washe garin ranar tun bayan sallar Asuba yana masjeed yana Azkhar yaga kiranta yamata banza”shi kira biyar yamata ita kuwa kira 12 ta masa”Amma d’an zafin kan yak’i d’auka”shiga wanda ke fushi da ita…..wasa wasa Ayinin ranar daga ita har shi cikin damuwa sukayisa”ko A office cikin bad mood shariff yaje”Akuma ranar ya rufe mutum 3 babu wani k’wak’wk’waran laifi”yakuma kori mutum biyu dake Aiki Agidan man fetur nasa sbd sun kirashi ta waya kawai”ko lunch Aranar beyi ba”sai gab da sallar magrib yashigo yanata d’acin rai”idanuwansa sunyi jajir”Abdallah na ganinsa yace yaya tun d’azun kai nake jir…..doguwar tsuka shariff yaja kamar zai huda harshensa ya haura upstairs “Ammi tabishi da kallo tana girgiza kai Afili tace Allah ya kyauta”daga yanzun idan yana a haka kudena tankashi daga kai har sadeeq… sharif be fitoba sai Anata kiraye kirayen sallar magrib “sannan yafito yatafi masjeed,be dawo ba kuma sai bayan sallar isha’i”coffee yaje ya had’a da kansa yasha”yana jin yunwa Amma beda nutsuwar cin Abinci”rabonsa da Abinci tun jiya”koda safe tea kawai yasha yafita”Awannan daren daga shi har Amaan cikin damuwa suka yisa”saidai bacci b’arawo daya sacesu “washe gari haka shariff yayi zuru zuru dashi”da sabon miskilancin sa ya motsa”su sadeeq da Abdallah har gaishesa sukayi da Asuba yamusu banza”ya nufi parlourn sa yayi zaune jugum tunanin daya zamar masa jiki ya kutso kai”wato tunanin Amaan….motsin0 turo k’ofar parlourn yasaka ya kalli k’ofar da jajayen idanuwansa”saida gabansa yafad’i dayaga Ammi ce”da k’yar ya Amsa sallamar ta”zuwa nayi na gaisheka tunda kafi k’arfin zuwa ka gaisheni…shiru yayi na second biyar kamar Ammasa tilas yace”saida na shiga kina kitchen”kaina ne ke ciwo shine na zauna Anan “meyasa baka Amsa gaisuwar su sadeeq ba?”b’ata fuska yayi yak’i mgn”ta girgiza kanta kafin tace “wace damuce ke damunka har haka?babu komai fa Ammi”shikenan Allah ya kyauta”daga haka ta fita….*bayan kwana hud’u* kimanin sati guda kenan da komawar Amaan garinsu”Anyiwa Anty zabba’u Aiki cikin nassara”tana Asibiti daddy be tab’a zuwa dubiyaba,yayinda danginta keta k’ananun maganganu waiya watsar da ita kamar ba Aurenta yakeyi ba”sun kuma fantsama neman mata maganin gargajiya sbd yadda takoma kamar k’aramar yarinya….Amaan kuwa tunda ta kira sharif sau 12 beyi picking ba ta tabbatar da fushi yakeyi da ita”tayi k’ok’arin ganin ta sharesa da kauda tunaninsa Aranta Amma abun yaci tura”Ada tanama Alak’arta dashi d’aukar k’aramin abu sai yanzun da bata kusa dashi ta tabbatar da idan babu shariff da wuya ta rayu cikin farin ciki”gaba d’aya tayi shiru shiru da ita”bata son cin Abinci sai yawan tunani”duk mommy na lura da ita ta zuba mata Ido kawai…..Ayau da yamma tana zaune a parlourn sai tsokanarta sadeeq keyi tasharesa can tasaki kuka tabar masa parlourn “tana shiga bed d’in mommy tasameta tana waya”saman bed ta zauna taci gaba da kukanta”bayan ta idar da wayar ta kalleta fuska Ad’aure tace”k’aramar yarinya ce dazaki tasani gaba kinamun kuka salma?”dan Allah mommy ki kira Ammi tabawa hamma shariff hak’uri yazo ya maidani wajensa….. bak’i bud’e take kallonta kafin tace”na yarda bakida hankali salma” muharramin kine shi dazaki ce ki koma wajensa?”wace irin shashasha ceke?to wlh karki bari yusuf ko khalifa sujiki”idan yadamu dake zaizo nan yaganki ai”zaki tashi kibani waje ko kuwa?”jikin Amaan Asanyaye ta mik’e tsaye ta fita……
Afannin shariff kuwa yafima Amaan damuwa”yayi wuri wuri dashi”uwar k’asumba tacika masa fuska yak’i gyarawa”ga rama yayi”se yawan zama yayi tunani shine Aikinsa “ba k’aramin kewar Amaan da muryarta yayiba”tunda ta kirashi bata koma gigin koma kiransa ba”duk sadda zai shigo gidan koya shiga d’akin Ammi sai yaga kamar zai ganta”Ayanzun ya Amince Abubuwan dayakeji game da Amaan tabbas SONE! tunda gashi sati guda kacal sbd rashinta yadda yakoma”Ada ya d’auka shak’uwace Ashe sone”kasancewar yau week end tunda yadawo masjeed be fitaba”ganin har 11 am ta wuce be fitaba yasaka Ammi kiransa ta waya yafito yayi break fast”Amamakinta taga yafito da jallabiya Ajikinsa Alamar duk zamansa side d’insa beyi wankaba”directly cikin parlourn yanufa”ta kallesa gabanta na fad’uwa Aranta tace” karfa yaron nan yakashe kansa sbd Amaan…..pls Ammi dan Allah Adawomun da Amaan gidan nan! yakatse mata tunani cikin tattausan muryansa daya marairaice”meke damunka shariff? kamarya Amaido maka Amaan? Aurenta kakeyine ko kuwa muharraminta ne kai??”to bari kaji duk Ina lura dama dakai duk Akanta tabi ka k’untata rayuwarka”raguwa zakayi idan kacemun kana sontane?”garama kayi gaggawar sanar mata kar wani yarigaka sbd Anfasa Aurenta da wannan Nasir d’in “idan kuwa kayi sake ka rasata wlh bazan lamunci zamanka a haka ba”shekarunka 40 kenan cif babu Aure”to kasani duk wacce na gadama saidai kaji na had’aka Aure da ita tunda bazaka fito da wacce kakeso ba”Amaan kuma kar Allah yasa ka furta kana son nata kayita zama da Abun Aranka”tana fad’in hakan ta mik’e tsaye tabar masa parlourn”cikin wani yanayi ya mik’e tsaye ya wuce up stars”cikin mintinah 45 yagama shirinsa na d’aukar hankalin duk wanda yayi tozali dashi”yanata zuba k’amshi ramar da yayi ta masa kyau sosai”babban yaronsa yakira akan A masa booking jirgin dazai tashi k’arfe 2 pm”sakkowa k’asan yayi ya had’a tea me kauri yasha”sannan yaje ya had’a kayansa kala biyu yafito yasami Ammi akitchen yasanar mata tafiyar gaggawa tasamesa zuwa Abuja zaiyi kwana 1″fatan Alkhairi ta masa, saidai ranta yabata wajen Amaan zashi babu wata zancen zuwa Abuja”yana fitowa yasanarwa body quards nasa su d’auki hanyar Adamawa tun yanzun shi ta jirgi zaizo”bayan ya sallamesu ya shiga mota ya nufi gidan mus’ab dake tudun wada……✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button