Miskili Ne 15-16
❤ *MISKILI NE* ❤
*15&16*
……..wani irin mugun bugawa k’irjin shariff yayi dayaji sallamar amaan”saidai miskilin ko kallon gefen datake beyi ba”yana tsugunne k’asa kan carpet “ammi na kwance kan 3 seeter kamar ba itace d’azun ba bata numfashi”amma yanzun alhamdulillah da abdallah yagano inhela d’inta kan mirror yabata”abdallah ne yayi k’arfin halin amsa sallamar amaan daketa faman raba ido tana rik’e da wayar da harta tsinke”kallon shariff tayi tana fad’in hamma gashi anata kiranka”ta fad’a tana kok’arin nufosa….ki wuce ki koma mota gani nan zuwa! shine abinda sheriff ya fad’a kamar ammasa tilas fuskarsa bbu walwala ko kad’an”amaan na juyo fuskar ta suka had’a ido da ammi dake kwance tana maida numfashi”tunda ta shigo parlourn taketa kallonta tana jin fad’uwar gaba”yayinda gefen girarta ta dama ke wani irin harbawa”duk’awa amaan tayi har k’asa tace mata ina kwana?”lafiya qlau”bakyaji ne nace kije gani nan zuwa?cewar shariff cikin tsawa”batayi mgn ba ta mik’e tsaye ta fita”abdallah yayi saurin mik’ewa tsaye zai bita….kai ina zakaje?”cewar shariff”sak’o zan amso bakin get”shiru yyi yasaci kallon ammi yaga shi take kallo tana nazarinsa”bayan fitar abdallah ahankali b yace”ammi mansoor anjima zaizo yadubaki ko akwai magungunan dazai baki….wacece wannan yarinyar shariff??”saida gabansa yafad’i dama abinda yake gudu ta tambaya kenan shiyasa yaso yazare jikinsa yabar gidan…nasan kaji mena ce maka ko?”bana son kamun k’arya shariff”kasanar mun gaskiya wacece ita datake kiranka da yayanta cikin harshen fulatanci??”ina kuma zakuje kake cewa ta jiraka?”shiru yayi kansa ak’asa ya gyara zamansa yana shafa kansa” ahankali ya shiga yiwa ammi bayanin amaan da halin data tsintsi kanta aciki”harda sunan daya saka mata da dalilin fitowarsu yanzun…. innalillahi wa inna ilaihir raju’un! kayi kuskure dabaka sanarmun ba shariff”dukda ita da watace agidan tana kulawa da ita amma akwai kuskure gayin hakan kodan sbd matsayinka”lallai yarinyar nan tana cikin babbar jarabawar duniya”shin wannan mata datayi mata haka tana tunawa da allah da mutuwa kuwa??”ko wane hali yanzun iyayen yarinyar nan suke ciki na rashinta?”allah yabaka ladar taimako”garama daka shawarci mus’ab d’in har kukaje gidan mlm”dan mutum ba’a bin yadda bane ayanzun”sannan ta hakanne zaka cire kokon ton ba wani yaturo ta tacutar dakai ba”amma yanzun dole ta dawo nan da zama! da sauri shariff da kansa ke ak’asa tunda ta fara mgn yace”nan kuma ammi?”eh mana”zan kula da ita sosai”dama ina son ganin y’a mace agaba nah”ina fatan baka matsama y’ar mutane da tsawa ko hantara??”nifa ammi bana mata komai”yafad’a yana b’ata rai “hmm! da dai bansan halinka bane shariff”amma ammi nida kin hak’ura kin barta can d’in kawai”na riga na gama mgn”sbd haka katashi ka shigo mun da ita”to amma ammi idan son ruk’on wata kikeyi baga wannan yarinyar ba dake gidan? shariff yaushe kafara mun musu?”beyi mgn ba yanata cin magani yanufi k’ofa yafita”ammi ta bishi da kallo tana d’an murmushi dan gaba d’aya tunda taga yarinyar taji tana k’aunarta…. shariff na doso parking lot ya hango amaan itada abdallah suna mgn suna dariya”har wushiryar dake a tsakkiyar hak’oranta ta bayyanah”kallo d’aya shariff ya musu ya kauda kai yana mugun had’e rai”tun kafin ya iso amaan ta fara jin daddad’an ‘k’amshin turarensa “atake gabanta yabuga”ta juya suka had’a ido “wata uwar harara ya watso mata”abdallah kuwa yana kallon sa yace”yaya wai sunanta amaan?”banza ya masa ya matso yayi lock d’in k’ofar motar “amaan na tsaye rik’e da wayoyinsa jikinta na bata laifi ta masa”atake idanuwanta suka ciko da k’wallah “abdallah kuwa tuni yabar wajen”sbd bega fuskaba wajen yayan nasa”kasancewar sa meson raha”ko ibtihal shariff ne yahanashi fira da ita”amma yanada son mutane….juyowa yayi ya kalleta da nufin yamata mgn yaga hawaye cikin idonta”doguwar tsuka yaja “dan allah hamma kayi hak’uri idan na maka laifi”nima bansan meyasa nayi laifin ba….rufemin baki marar jin mgn! nace karki biyoni sbd kinada kunnan k’ashi shine kika biyoni ko?”to yayi kyau”daga yau bazaki koma ganin baba ladi ba anan gidan zaki zauna wajen ammi “shiru dai tayi kanta ak’asa”ki wuce muje ciki….to hamma shima abdallah nan gidan yake?”yacemun wai ya sunana?”shine saina fad’a masa”wai ai na girmesa sunana anty amaan….dan allah kimun shiru da wannan shirmen”zane miki jikinki zanyi da bulala tunda bakyajin mgn”saura idan munje kiyita yawan surutu ko tambayar wani abu”kuma akwai wata yarinya tana zaune agidan bance ki kulataba koki shiga sabgartaba”dato kawai ta amsa sbd wani abun bama fahimtarsa takeyiba idan yafad’a”yana daga gaba tana biye dashi suka shigo cikin parlourn da sallama”ammin ta amsa tana murmushi tace”amaan zonan”saida ta kalli shariff “aikuwa ya banko mata harara”wanda ammi na lura dashi”tace”zonan y’ata kinjiko?”bbu musu tazo gefenta ta zauna”ita kuma ta kama hannunta tana fad’in zaki yadda ki zauna anan?”kanta ta gyad’a mata”shariff ya kallesu yace”ammi acikin d’akunan can wanne zata zauna?banaso a had’asu da yarinyar nan (ibtihal)”yafad’a fuska bbu walwala”babu ko d’aya wanda zata zauna”a d’akina zata zauna….amma kuma! sai yayi shiru kome yatuna oho”ammi ta girgiza kanta tana fad’in nasan batun alh zakayi ko?”ka manta d’akinsa daban ne?”beyi mgn ba ya mik’e tsaye yana fad’in zanje nadawo anjima zan kawo kayanta…..hamma ina zakaje?”banza yamata zai fita”shariff! ammi ta kirashi murya bbu alamar wasa “kamar yayi kuka ya juyo”ammin ta hararesa tabar parlourn “kamar yana jira yace”amaan meyasa kikeson b’ata mun rai da sakani yawan surutu?”kinsan allah zaneki zanyi”wai hamma irin yanda naga ana dukan y’an cikin firm?”shiru yayi,saita shagwab’e fuska tana fad’in to ya zancen kayan wasan?”zan kamiki anjima”nidai zan bika hamma! shiru yayi yanata kallonta dan yama rasa meye zaice mata”can ya mik’e tsaye yana fad’in tashi muje d’akin ammi ki kwanta kiyi bacci”yafad’a yana matsowa gab da ita yakama hannunta ya amshi wayoyinsa sai shagwab’a takeyi bece komai ba yana dai rik’e da hannunta ya bud’e k’ofar yana fad’in oya shiga”hamma! kallonta yayi tasaki k’aramin kuka”haka nan yaji k’irjinsa ya buga”saiya basar yace”ki shiga ciki kiyi bacci zan siyo miki ice cream shikenan?”kanta ta gyad’a masa tana shiga ciki”shi kuma ya rufe k’ofar yana juyowa yaga abdallah”kai zonan”shine abinda yafad’a yana yin gaba”abdallah yabiyosa abaya”agefen motarsa suka tsaya”fuskarsa ad’aure yace”inaso kasani amaan ba cikakkiyar lafiya ce da itaba”idan kaga tayi wani abu daba daidai ba karkayi mamaki”sannan bana son kana kunnah kallo gabanta inba catoom bane”sai maganata dakai ta karshe kasan yadda zakayi fira da ita banda wani wasa tsakaninku”kaji ko bakajiba? da sauri abdallah yace”naji yaya zan kiyaye”shariff beyi mgn ba yakira driver yashigo mota yajashi suka fita…. amaan kuwa tana shiga cikin d’akin tasami ammi zaune kan stool tana yank’e farce”ta kalleta tana fad’in hamman naki yatafi?”eh yace nayi bacci ne”toga bed can jeki kwanta ko?”dato ta amsa ta cire takalminta ta zauna gefen bed d’in kanta ak’asa….ki kwanta mana bara na koma parlourn “daga haka ammi tabarota acikin d’akin”ita kuma ta kwanta tanata juye juye har bacci ya kwasheta”sai wajen k’arfe 1 saura mintinah goma ta farka”babu kowa a d’akin dayaji kayan alatun duniya”k’ofar dataga akwai welcome carpet ajiye da silifas asama,anan ta nufa sbd ranta yabata anan ne bayi”bayan ta gama kama ruwa ta fito daga cikin bath room d’in”hakan yayi daidai da shigowar ammi cikin d’akin “ido suka had’a”amaan tayi k’asa da kanta”kin tashi kenan?uhmm hamma be dawo ba?”be dawo ba amma nasan yakusan dawowa “shiru tayi kamar zatayi kuka ta zauna”ah ah dama na shigo naga kin tashi ne”yanzun kiyi sallah sai kizo kici abinci ko?”abdallah yadameni da kina ina?” ai bana yin sallar akace”to shikenan muje kici abinci”sai hamma yadawo”matsowa ammin tayi ta kama hannunta cikin rarrashi tace”shariff ba yanzun zai dawo ba hasalima sai k’arfe 4 yakeyin lunch….kukan shagwab’a tasaka “ammin na murmushi ta matsa jikin mirror ta d’akko wayarta ta zauna gefen bed d’in ta kamo amaan ta aza kanta saman cinyar ta sannan takira shariff”bugu ukku ya d’auka yana fatan allah yasa ba akan amaan bane takirashi”amsa sallamarsa ammi tayi tana fad’in gafa amaan nan tak’i cin abinci wai saika dawo”d’an jim yayi kafin yace “tana ina?”gata nan”amma ammi ba cikinta bane wai?”shariff wai meyasa kake haka?”to maza ka rarrasheta kaji na gaya maka”rarrashi fa kikace ammi ? ya maimaita kalmar”saidai kafin yayi mgn ammi ta kara mata wayar gefen kunnanta tana fad’in ga hammanki kuyi mgn “da sauri amaan tayi murmushi tace”hamma! uhmm menene?”bakai bane baka dawo ba”shine kuma amaan zak’i cin abinci?”to ai kaima bakaciba ko?”gabansa yafad’i ya janye wayar ya kalli wayar sannan ya maida”kina jina?”uhmm”komai ammi tasaka kiyi bana son ki mata musu maza kiyi kina jina?”to hamma zanyi”good girl! daga haka ya yanke wayar”ammi dai tayi shiru tana saurensu”daga bisani ta amshi wayar tana shafa kan amaan tace”tashi muje kinjiko?”bbu musu ta tashi tsaye suka fito daga cikin d’akin”abdallah na zaune kan kujerah yana chating “sai ibtihal na dining area tana cin abinci”tunda ta hango ammi rik’e da hannun kyakykyawar yarinyar data gani d’azun dazata fita gabanta yafad’i “fatanta allah yasa kar shariff yace yana son yarinyar…. anty amaan kin tashi?”cewar abdallah yana mata murmushi “ammi ta karb’e zancen da cewa eh abinci zataci”wai ammi niban ganeba fisabilillahi?”naga kamar kinfi jida ita akaina ko?”yafad’a yana turo baki “amaan ta kama yimasa dariya”ya d’an harareta yana fad’in yaya yakoya miki miskilancin sa ko?”ina miki mgn kikayi shiru”amaan rabu dashi wuce can ki zuba abinci”kallon dining area d’in da ammi ta nuna mata tayi ta hango ibtihal zaune tana cin abinci”abdallah zoka rakani”bbu musu yataso suka jera suka nufi dining area d’in”da kansa yaja mata kujerah ta zauna”sannan shima ya zauna yana bud’e warmers d’in abinciccika kala kala gasu nan na alfarma” da wasu ammi ne tayi,wasu kuma masu aiki ne sukayi”broth bakuwa mukayi ne? kuma bata iya yiwa mutane mgn ba?cewar ibtihal tana aikowa da amaan da harara”batare data bari kowa yagani ba”sam abdallah be luraba saidai yatab’e baki yana fad’in babu mamaki bata iya d’in ba tunda duk abinda yashafi yaya sheriff me ajine kuma baya son hayaniya”amma ke meyasa ba zaki gaishetaba ko dan ki girmamata ,amatsayin ta na bak’uwa kuma y’ar ammi??”kana nufin y’ar uwarkuce?”be bata amsaba sbd dama daga gaisuwa bbu abinda ke had’ashi da ita”kallon amaan yayi yace”anty amaan miye zakici?”nidai komai yadace zubamin”yayi murmushi yace”fevourite food d’in yaya zan zuba miki….sosai ibtihal ke kallonsu tana nazarin kalamansu”atake ranta yabata wannan yarinyar aure za’a had’ata da shariff”tunda gashi abdallah na kiranta da anty”dukda tasan inda mahaifinta yatafi(yaje yawon neman asiri) yau kwanansa guda”amma tasha alwashin kiransa ta waya tasanar masa zuwan wannan me kama da aljannun…. mik’ewa tsaye tayi tana kallon amaan dake tsakuran abincin”ga uban nama abdallah yazuba mata”amaan dai tunda ta lura da irin kallon datake mata,da kuma ta tuna hammanta yace”karta kulata saita shareta”sai surutu sama sama abdallah ke mata harta gama cin abincin”ta wuce d’akin ammi tasameta tana shirya kaya”ammi kawo na shirya miki “baba ladi idan nace takawo nayi mata aiki sai tace ban iyaba”ammin na murmushi ta mik’a mata kayan ta zauna gefen bed tanata satar kallon ta tana jera kayan”bayan ta gama tace”sannu amaan”idan shariff yadawo yakawo kayanki saikiyi wanka ko?”dato ta amsa, atare da ammin suka koma parlourn”cikin y’an awanni amaan ta sake da ammi sai shagwab’a taketa zubawa son ranta itada abdallah “tsabar bak’in ciki ibtihal kasa zama parlourn tayi…..bayan sallar la’asar ammi da abdallah da ibtihal na zaune a parlourn “kan amaan na saman cinyar ammin suna kallon arewa24″yayinda jummai me aiki keta turare parlourn “ahaka shariff yashigo cikin parlourn anutse” da ledoji ahannunsa”sai wani yaronsa dake janye da sabon trolley babba guda d’aya”zumbur amaan ta tashi zaune dataji amon jarumar muryansa me dad’i”shi kuwa yayi mamakin ganin yadda tasake da amminsa da sauri haka”kauda kansa yayi daga barin kallonta yana fad’in ammi sannu da gidata amsa cikin sakin fuska”abdallah na murmushi yamasa sannu da zuwa”yayinda ibtihal ta tsurama kyakykyawar fuskar shariff ido tana jin kamar taje ta rungumesa sbd so”amaan ta taso ta nufesa”fuskarsa bbu yabo bbu fallasa sbd yana lura da yadda ibtihal keta kallonsu”hamma nah sai yanzun ka dawo?”eh tambayau”yafad’a yana mik’a mata ledojin hannunsa”saida ta russinah kafin ta amsa tana masa murmushi cikin shagwab’a tace”to yanzun abinci zakaci ko?”hannunsa yasaka yaja karan hancinta yana fad’in wuce muje…..✍️
wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
vip grp 1000
via 2230373842 nabila aliyu uba bank
ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251
idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba