Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 5

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 5….. Sae da Ikram ta fara siyan yakuwar da Ammi ta aiketa snn ta shiga cikin kasuwar tana rike da shi a hannu bayan ta cire ledar ta jefar, fada ta tarar wasu nayi ta shige tsakiyarsu da sauri tana kallo duk da irin tunkude tan da ake yi har aka gama fadan ganin kowa ya kama gabansa yasa tayi gaba ita ma, can bangaren groceries tayi tana kalle kalle, dai dai inda ta fara ganin matar nn ta tsaya ta juya tana kallon mutumin dake xaune wajen tace “kai, kai wnn matar nn da ta taba siyan Ayaba a nn da Apple ta kuma dawowa,” kallonta kawae ya tsaya yyi ta karaso kusa da shi tace “kai baka ji na ne,” yace “A’a ina jin ki mana yarinya, ke hka aka koya maki a gidanku” da sauri ta daga hannu sama tana xaro ido tace “kai ni Ammina shara kawae take koya min da gyaran daki kuma na fara iya wa wllh kaje ka tambayeta ma, amma ita Altine mamarta tace ma Ammina bbu abinda ta iya sae cin abinci, kaga idan Ammina ta aikeni gidansu shafa ma ina ganin tana hura itace tana daura roba a kai xata yi girki amma fa yarinyar lukuta ce kuma bana sonta don tana dukana ni kuma ban iya dukanta ba amma akwae watarana da salame tayi mata duka wae in ji sadiya, kasan sadiya kawar salame ce kuma duk a islamiyyar mu suke, malamin mu kuma yana dukan duk wanda bae iya karatu ba ni dae kuma na iya wllh,” shiru tayi tana kallon mutumin ganin ynda yake dariya ga Neighbours dinsa ma na tayasa, ta nemi benci ta xauna tana kallonsa tace “me yasa kke dariya hka, Ammina tace min mahaukaciya kadae ke dariya hka shi yasa nima na daina,” dariya yake ssae yana kallonta yace “ya sunanki yarinya,” tace “sunana Rabi’a amma Ammi da Abbana da yan unguwarmu suna kirana Ikram, baba yace kawu na lado ne yace a sa min Rabi’a wae sunan yayarsa ce da ta mutu kuma baxata sake dawowa ba, Ammi tace min wae da sunan mamarta xa a sa min amma sae kawu na lado yace baxa a sa ba, kasan kawu na ladon nn mugu ne kuma baya sonta…..” ganin ynda mutumin nn ke dariya yasa Ikram tayi shiru tana kallonsa, can ta dan tabe baki ta mike xata yi gaba ya kirata da sauri ta juya tana kallonsa yace “har xaki tafi kawata,” tace “ehh mana Ammi ce tace in siyo mata yakuwa xa muyi miya da shi yau, kila baba ya samu kudi ne ya bata, don kullum bashi da kudi yake cewa,” Mutumin yace “to dan xauna muyi hira kawata,” ta dawo ta xauna tana cewa “amma fa kafin dare yyi xan wuce don Ammi tace kar in dde kuma har ynxu bn dde ba ae, to ya sunanka yaro” yana dariya yace “sunana sani,” tace “lah sunan baban Altine ne ae, kasan me yasa na xo nn” mutumin yace “A’a,” tace “akwae wata mata da ta taba siyan Ayaba a nn gurin har na taya ta daukan kaya na kai mata bakin titi ta bani Ayaba da apple da kudi, katuwar mota ya xo ya tafi da ita, gurinta na xo ko xan ganta,” yyi shiru yana kallonta tace “ta kara xuwa nn,” yace “A’a ina xan sani kuwa yarinya, kwastamomi masu kudi da yawa gareni,” Ikram tace “to xo ka ban Ayaba don Allah,” ta fada tana nuna masa bunch din banana, ya yo waje da ido yace “ina kudin ki,” ta dan marairaice tace “ni bani da kudi Ammi da baba basa bani,” ya dan yi dariya yace “to idan na baki xaki dinga xuwa taya ni hira kawata,” da sauri ta gyada masa kai ya dauki wuka ya yankar mata Ayaba uku ya mika mata yana murmushi don yarinyar ta burgesa ta karba tana tsalle ba ko gdya tayi gaba ta bar masa yakuwar nn kan benci, sae bayan tayi nisa ya gani ya dinga dariya neighbours dinsa na taya sa, yace “lallai yarinyar nn ta tona ma uwarta asiri, kun ga fa ta bar min yakuwar,” da gudu da gudu ikram ta isa gida rike da ayabarta guda uku, wajen karfe shidda saura ita da aka aika tun biyu, rabe rabe ta shiga yi bakin xauren, Ammi har ta gaji da jira ta kada kukarta da ruwan miyan taushen, ido hudu suka yi da Ammi tana lekan tsakar gidan, Ammi ta dauke kanta bata ce komai ba, ikram na nn tsaye bakin xauren har Abbanta ya dawo ya kama hannunta suka shiga ciki yana tambayarta me tayi. Tun ranar da Mami suka hadu da Ikram bata sake samun shigowa kasuwa ba sai yau Asabar tana isa gun mai fruits dinta ya gaidata cike da ladabi ya tambayeta me xae bata yau, Mami ta xauna ta lissafo masa abinda take so snn tace “ina son nayi maka wata tambaya malam sani,” yace “tambayar me Hajiya,” Mami tace “wata yarinya ce ranar da na xo nn karshe ta taimaka min ta daukar min kayana dai dai can,” ta nuna masa gun da yatsa, snn ta ci gaba da maganarta “shine nake son tambayarka ko ka santa,” malam sani ya dan yamutse fuska alamar tunani yace “Anya kuwa Hajiya, ya yarinyar take kuma meye sunanta, ko dako take yi,” Mami tace “tace min sunan ta Ikram,” malam sani ya yo waje da ido snn ya fashe da dariya har da kyakyatawa, mami ta tsaya kallonsa da mamaki, yana rike ciki yace “daxun nn ta bar nn Hajiya, ki ce kawata kike nema,” Mami ta mike da sauri tana kallonsa tace “don Allah ka santa, wllh ita ce dalilin xuwana kasuwar nn yau,” malam sani na dariya yace kwarae kuwa ko ba Ikram Aku ba” Mami tayi murmushin jin ddi tace “to don Allah kasan gidansu,”

 

Back to top button