Garin Dadi 46
{46}
*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*
~MAI DA TSOHUWA YARINYA
~FEMALE CARE
~REODEO
~VIGOR MAX
~ LONGZIT
~B CLEAR
*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*
~~~Ina shiga cikin bedroom din ko zama banyi ba naji shigowarsa shima alamar biyoni yayi, ina kokarin zama ya rikoni tare da zaunar dani cikin jikinsa,
“am very sorry my love….. Kiyi hakuri zan ci, zo muje in ci a gabanki ki gani…..”
Shiru nayi ina sauraren ban bakin da yake yimin tare da share min hawayena,
“ban san cewa ranki zai baci ba amma kiyi hakuri bazan sake ba….”
Duk da cewa a ƙoshe yake amma haka yaketa cakular abincin bayan mun koma falo ya samu nasarar shawo kaina, ɗauke abincin nayi na saka cikin fridge tunda na riga da na huce na koma normal kamar babu wani abu da ya faru,
Tun dab da lokacin kwanciyata na fara jin cikina da marata suna ciwo amma sai na daure ban fada masa ba, wanka nayi na kwanta ina jin ciwon yana ƙaruwa ahaka na samu bacci ya daukeni bayan nagama azkhar din kwanciya bacci, cikin dare ciwo ya sake tashi yace muje zuwa yayinda bacci kuma ya ƙaurace min dan azaba, zaune na tashi na zauna na zubawa sarautar Allah ido shikuma yana kwance yana ta baccinsa wanda na san bawai ya wani jima da ɗaukarsa bane, na jima zaune kafin na samu ya dan lafa min na sake komawa bacci zuwa asubah na sake tashi,
Bathroom na shiga domin kama ruwa nan naga ashe ma bleeding nake ban sani ba ga wani irin murdawa da marata keyi abin ba sauki, ganin jinin da nayine ya firgita ni shiyasa na koma na tashe shi. Sai lokacin ya san halin da nake ciki cikin firgici ya riƙeni yana cewa,
“Baby yi sauri muje hospital…. Bana son wani abu ya sameki ko cikin dake jikinki…..”
Kai na ɗaga masa ina cije lips ɗina duka biyu a haka dai ya taimaka min na cire rigar baccin jikina na saka doguwar riga da hijabi muka yi salla sannan muka tafi,
Muna zuwa likita ya shiga dubani nan ya tabbatarwa da samz cikin jikina ya lalace sai dai ni bai fada min ba dan kada hankalina ya tashi saboda ko yanzun ma cikin tashin hankali nake, faɗin irin baƙar azabar da na sha kuwa ɓata lokaci ne kuma har lokacin babu wanda ya sani daga ni sai shi sai zuwa azahar bayan cikin ya gama faduwa sannan samz ya kira yaya Abdul hakim ya sanar dashi nan shima yaje gida ya fada musu shiyasa kafin kace me asibiti ya cika da ƴan gidanmu nikam ina can ina bacci banma san wacce wainar ake toyawa ba. Zuwa la’asar na tashi daga baccin wahalar da na sha nan naga Anty, mama,Bishra, anty salaha ganin na farka duk suka yo kaina suna yimin sannu, tea anty ta hada min sannan ta zubo min abinci, da ido naketa neman samz amma da dukkan alamu baya cikin ɗakin dan da ace yana nan ai da na ganshi may be yaje gida ko kuma yana waje, nan dai duk suka shiga jajanta min ɓarin da nayi, ni dai a ɓoye na keta kuka na ban bari wani ya gani ba, zuwa magriba su Annie suka ƙaraso ita da Abba da yaya Abdul hakim wanda shine ya kawo su, basu jima da zuwa ba samz ya dawo dauke da fruits cikin leda da drinks harda balangu, kaya dai kaca kaca na ciye ciye haka ya kawo, bamu samu kebewa dashi ba saboda mutane har sai bayan ishah lokacin da duk ƴan gidanmu suka tafi sai iya Bishra kadai da aka bar min wanda zamu kwana tare
Misalin ƙarfe 9 ya shigo ya zauna kusa dani yana yimin sannu, ai kamar dama jira nake nan na fara kuka shikuma ya shiga rarrashi na yana bani baki,
“yanzu duk yadda muka ƙwallafa rai akan cikin nan ashe ba zai ma zo duniya ba….” na fada cikin kuka, hannuwana ya rike cikin nasa yana sake rarrashi na da kalamai masu dadi,
“babu komai baby haka Allah ya so kuma insha Allah zai sake bamu wani mai albarka…. Ki kwantar da hankalinki Kinji….”
Kai na ɗaga masa ina sauraren kalaman da yake yimin na kwantar da hankali da samar da nutsuwa cikin zuciya, muna nan tare dashi har wurin 10 sai da yaga na ware na sake sosai sannan yayi mana saida safe ya tafi,
Kwana na biyu a asibitin kafin aka bamu sallama, kai tsaye gidanmu aka wuce dani dan su anty sunce sai an kula dani sosai, a ranar shikuma ya koma Abuja saboda aiki, kamar yadda yake ta cewa in kwantar da hankali na kar in saka damuwa acikin raina kwantar da hankalin nawa nayi shiyasa nayi fes dani ban wani lalace ba.
A ɓangaren mommy kuwa bayan sun gama ƙulle ƙullensu da shirye shiryensu ita da aminiyar tata daga ƙarshe taji labari mai daɗi daga bakin samz dan shine da bakinsa ya sanar mata da wai na samu miscarriage lokacin da abun ya faru kuma yakara da cemata ina asibiti ma lokacin ko sallamata ba ayi ba, ko da wasa bata nuna masa tayi farin ciki ko bakin ciki ba dama kuma ya riga da yasan duk wani lamari wanda ya shafeni to bata damu dashi ba shiyasa abin bai wani dameshi ko bashi mamaki ba amma acan ƙasan zuciyarta taji dadin labarin da yaje mata dashi dan dama bata da wani buri wanda ya wuce taga wannan cikin nawa ya lalace dan tace ba zata taba hada jini damu ba shiyasa babu ɓata lokaci ta sanarwa da aminiyar tata wadda bafa hakura suka yiba a’a sun sake ɗaura ɗamarar cigaba da yaƙar zaman lafiyarmu dashi.
Bayan tafiyar shi kullum muna tare a waya tun daga safe har zuwa lokacin kwanciya bacci shi kansa ya yaba da irin yadda yaga na saki raina kuma na kwantar da hankalina nayi Kumari ban bari na lalace ba, satinshi biyu da tafiya yazo kuma tun kafin yazo yake cewa wai a gida zai sameni?
“Gidanmu…..” na bashi amsa dan na fahimci inda zancen nasa yake son zuwa,
“Gidanmu nida ke?”
“gidan iyayena….”
Dariya yayi ya kwantar da murya yace “baby ba zamu hadu agidanmu ba inyaso after na tafi sai ki koma”
“lallai ma sannunka….. A’a gaskiya”
“to shikenan sai nazo”
“tom, me zan dafa maka?”
“ni ke kadai nake bukata, you are the real meal….”
“yen yen yen…..”
“yen yen yen yen….” shima ya fada cikin kwaikwayon muryata, dariya muka yi gaba daya kafin muka yi sallama na ajiye wayar,
Girki nayi masa da kaina farfesun kifi sai sakwara da miyar dage dage kuma da wuri yazo dan lokacin da yazo ba afi 12 ba,
Farar shadda ya saka da hula dara baƙa, nikam ban yi wata kwalliya ba dan yadda naga take takensa tun kafin yazo yasa na shiga taitayina, powder kadai na shafa sai kwalli sai ko dan lipstick da na goga ta wuri ɗaya nayi kuskure da na daddage nasha turare kamar anyi ɓarinsa bayan kuma na san yana daya daga cikin abubuwan dake jan ra’ayinsa, baƙar doguwar riga na saka na yafa dan siririn mayafinta na fita na sameshi falon saukar baƙi yana waya da daddynsu, ganin shigowa ta ya mika min hannu na maƙale kafada naƙi zuwa murmushi yayi ganin na zauna can nesa dashi,
“Ehh daddy ina Kano yanzu haka naje duba jikin Maimunatu kasan tun last tafiyan da nayi ban dawo ba sai yanzu…. Gata….”
“Gashi daddy zai yi magana dake….”
Dama na san ba zai barni nesa dashi ba kuma da biyu yacewa daddy bari ya bani wayar wato dai dole sai nazo kusa dashi, ai kuwa ina zuwa ya zaunar ni kusa dashi ya riƙeni, gaisawa muka yi da daddy ya sake duba ni dama kuma muna gaisawa a wayata lokaci zuwa lokaci, bayan munyi sallama ina kokarin tashi ya riƙeni yana kokarin saka idanuwansa cikin nawa amma naki,a gurguje yayi sallama da daddy sannan ya ɗago kaina,
“baby yakike?”
“am fine dear…”
“bakya missing dina? Nifa i have been missing you a lot”
“Same here….” na fada ina kissing ɗinsa a kumatunsa guda ɗaya,
“to yaushe zaki dawo? Ko zamu tafi tare?”
“a’a ba tare zamu tafi ba”
“sai yaushe?”
“nan da 2 weeks”
“Haba baby…. 2 weeks yayi yawa”
“zo Kaci abinci inyaso sai muyi maganar tafiyar daga baya”
Yana manne dani yaci abinci duk ya hanani sakat ya hanani motsawa nan da can, a takaice dai a gidan ya wuni, duk sai da muka bi sashen su mama da Annie na kai shi ya gaida su daya bayan daya, koda muka fito cemin yayi wai to in rakashi gidanmu last time yayi mantuwa dan Allah in rakashi ya ɗauko, dariya nayi na sake maƙale hannunshi dake cikin nawa,
“wai dan Allah menene matsalarka? Idan kayi hakuri ma ai na kusa dawowa”
“ba zaki raka ni ba?”
“ka bari idan ka tashi tafiya sai ka biya ka dauka daga can sai ka wuce”
“baby wayonki yayi yawa” ya fada yana lakuce min hanci, “kaima haka” dariya yayi kawai bai sake maganar ba, zuwa yamma yayi mana sallama ya tafi kuma a ranar da daddare Abba yake cewa su mama ai yadace nima in tattara in koma tunda dai lafiya nake babu wata matsala amma sai mama tace adai kara barina in warware in kara koda sati biyu ne inyaso sai in tafi,
Ai ina fada masa abinda gida suka ce ya fara murna wai da ya zaci baza a barni in dawo yanzu ba sai nayi irin wata biyun nan zuwa biyar dariya nayi nace haba sai kace ana hauka. Lokacin da na fara lissafin tafiya ziyara na kakkaiwa yan uwa da abokan arziki kafin in koma dan idan na tafi ban san lokacin dawowata ba sai Allah shiyasa wannan karon kayana na kwasa rankatakaf kaɗan na bari, naje gidan ƙawalli na wuni Irfan ɗinta har yayi wayo sosai ya girma kai kace yayi wata uku, ƙunshi nayi da kitso da duk wani gyara wanda na san ya dace inyi, washe gari na koma, lokacin da naje bai taso daga office ba amma ya kusa, duk da bana nan amma gidan babu wani datti mai yawa da alama yana kula da gidan kuma yana gyarawa.
Tun kafin ya dawo na shiga kitchen na dora mana girki inata dariyar zumundinsa ni kadai dan sai murna yake yana cewa wai shi yau ango yake, noodles na dafa mana jallop nasa kifi da vegetables dan ita kadai ce mai sauƙin dafawa,bayan na gama na sake gyara jikina na caba kwalliya nasa wani leshi fited gown ɗaya daga cikin wanda na ɗinka zuwa na Kano a sunan ƙawalli,
Ƙarfe 6 ya shigo, da gudu na ƙarasa na rungumeshi tare da daleshi, rungumeni shima yayi yana sinsinar jikina cikin farin ciki da tsantsar soyayya,
“welcome back my baby love….”
Ya yaba da kwalliyata sosai dan sai farin ciki yake yana saka min albarka, kai gaskiya munyi missing juna ba kaɗan ba, haka dai muka kwana cikin farin ciki bayan mun raba dare muna shan soyayya kamar waɗanda suka shekara basa tare, cike da farin ciki da ƙaunar juna muka yi bacci nidai saboda tsabar gajiyar da na kwasa washe gari ko tashi banyi ba ina bacci ya shirya ya tafi office bai tasheni ba, sai 10 sannan na tashi wannan dinma yunwa ce ta tadani, mamaki ne ya kama ni lokacin da na kunna wayata naga time wai har 10, kamar dama jirana yake in kunna wayar sai ga kiransa, da murnata na daga kiran ina kokarin sauka daga kan gado,
“Ina kwana….” na fada cikin shagwaba,
“morning my love…. Kin tashi”
“na tashi yanzu, shine ka tafi baka tasheni na ganka ba”
“am very sorry, bari in kiraki video call sai ki ganni”
Brush naje nayi sannan na wuce kitchen muna yin vedio call din ina kallonsa yana kallona, kwai kadai na soya sai tea da na hada nasha, sai bayan da na kammala sannan muka yi sallama saboda shima zai shiga meeting, muna yin sallama na yunkura zan tashi dan inje inyi wanka na soma jin kukan mage da na kare duk lokaci guda……..
*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*
*_Ummi Shatu_*