Daudar Gora Book 1 Page 18
18_*
……….Tuni labari ya kai kunnuwan sauran matan gidan musamman Malikat Ashwaq da Ameera Danish-Ara da Ameera Haifah cewar Malikat Bushirat ta ziyarci Shahan-shan saboda rashin jin motsinsa. Hakama wasu a cikin matan manyan masu faɗa aji a gidan harma da mazan, wasu iyaye, wasu ƴaƴa, wasu jikoki. Hakan yasa aka kafa gungu-gungu na cigaba da tattaunawa tare da sukar cewar yasan tsiyar daya aikata ai shiyyasa ya ɓoye kansa. Kokuma dodon tsafin nasa ne ya bashi wannan umarnin naƙin fitowa har sai yarinyar mutane ta mutu… Wasu kuwa murmushine kawai nasu dan su kaɗai suka san kansu. Yayinda wasu ke tausayama Tajwar Eshaan ɗin da ganin abubuwa ne suka masa zafi da yawa dan suna kallon komai a matsayin makirci da mafi yawa akafi dangantashi da matan ubansa, da kuma ƴan uwan mahaifin nasa na jini masu zawarcin son hawa wannan kujera… (To koma dai miye ALLAHU shine mafi sani).
Duk inda ta gitta hadimai zubewa suke akan gwuyawunsu suna miƙa gaisuwa. Ko sau ɗaya bata ɗaga ido ta kalla kowa ba, sai hadimanta ne ke amsawa duk wanda yay gaisuwar. Tun’a harabar shiga sashen dukkanin hadimanta suka dakata. Sashen Shahan-shan shine mafi ƙyawu da ƙawatuwa na ƙyale-ƙyale a daular ruman. Gini ne da kusan zamuce an yisa da zallar gilashi. Yanada hawa huɗu dan haka sai da lifter. Zaman lissafin dukiya da daular da aka zuba a cikinsa da kuma ainahin fadar da Shahan-shan ke zaman fadanci ma ɓata lokacine. A lokuta da dama duk abinda ke faruwa a cikin masarauta Tajwar na kallo daga cikin sashensa musamman idan a hawa na ƙarshe yake, hatta da wajen masarauta yana iya hangowa. Hadiman dake tsaron sashen matsayin sojoji suka maye gurbinsu wajen take mata baya har falon farko. Anan ɗin ma hadiman zubewa suka dingayi ƙasa kawunansu a risine domin girmamawa a gareta har zuwa falon farko. Wanda suka rakota ciki suka dakata, na falon farkon dake a hawa na ɗaya suka take mata baya har zuwa falo na biyu a hawa na biyu, suma iyakarsu nan, wanda suke a falo na biyu sukai mata rakkiya har zuwa falo na uku dake a hawa na uku. Anan soja ɗaya ne, shine amintacce da yake iya haurawa har zuwa falo na huɗu hawa na huɗu a falon dake can. Anan ma akwai hadimi ƙwara ɗaya sai masu dafa masa abinci su biyu suma. Sune amintattun na ƙarshe dake iya zuwa hawa na can ƙarshe na huɗu kenan, suke iya ganin Tajwar kai tsaye kuma, suke iya sanin a wane ɗaki ya kwana, suke iya shiga ɗakin barcinsa suyi gyara ko kai abinda yake buƙata, ko isar da wani saƙo. Bayan gaisuwa a gareta Ghazi ya nema afuwa da bashi damar zuwa nema mata iso ga Tajwar. Hannu kawai ta iya ɗaga masa.
Mintuna da basu wuce huɗu da shigar tasa ba ya dawo ya zube a gabanta. “ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai amfani, shugaba ya bada damar shiga dake har ciki”. Shiru tai kamar bazata motsa ba, dan a duk sanda ta kama zasu gana anan sashensa yakan fito ne su haɗu a wannan falon ko ƙaramin falon hutawarsa dake a hawa na uku. Wannan kuwa a ƙa’ida ko matarsa bata shigarsa, dan haka jin wannan amasa yasata fahimtar akwai matsalar da gaske.
Bayan buɗe mata ƙofa Ghazi yaja da baya. Cikin takunta na ƙasaita da isa ta ƙarasa shiga cikin matsakaicin falon mai fidda wani irin ƙamshi da wadataccen sanyin na’urar ac. Rashin girman falon ba komai bane, haɗuwarsa da tsaruwarsa ce mafi ɗaukar hankalin mai kallo. Dan an ƙawatashine da wasu irin tausasan tumtum na ainahin sarakan asali, dardumar falon kanta abin kallo ce, komai ya tsaru dai-dai da tsaruwar manyan mutane. A hankali takai zaune tana mai sauke ajiyar zuciya, sosai takejin matuƙar kewar gudan jinin nata, sai dai tsarin masarautar tasu ya tilasta mata haƙura akan dole tamkar kowace uwa ta Tajwar irinta da akai a cikin wannan daula….
Motsin buɗe ƙofa da ƙamshin turarensa mai rige-rigen isowa hancinta da sautin takumsa ya sata ɗago ƙyawawan idanunta ta sauke a kansa. A hankali ya cigaba da takowa cikin ƙasaita da nutsuwa har ya ƙaraso gareta. Daga tsayen da yake ya ɗan risinar da kansa alamar girmamawa. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki *_Ammie!_*”. Nutsatstsiyar muryarsa mai zurfi da rashin hayaniya ta fita a fisge, dan yanda ya motsa lips ɗinsa a hankali zama ka iya ɗauka bashi yay maganar ba. A hankali ta sauke ajiyar zuciya mai haɗe da nannauyan numfashi ta jinjina kanta da lumshe idanunta ta buɗe a kansa alamar amsawa. A nutse ya kai zaune a gefenta, yay zama irin na ƙasaita da kame kai da kuma girmamawa a gareta matsayin mahaifiya. Hanunta ta ɗaura bisa tattausar sumar dake kansa kwance, tare da ɗan ranƙwafawa ta sumbaci goshinsa da yay zafi zau alamar baida lafiya. Lumsassun idanunsa da ƙanƙancewarsu ya hanata ganin hasken cikinsu ya buɗe, ya motsa lips ɗinsa kaɗan alamar murmushi a gareta. Murmushin ta saki itama a karo na farko da gyara zamanta na ƙasaita.
“Kaima amincin ALLAH ya tabbata a gareka *Bugun zuciyar Ammie’n sa*”.
Ɗan luuu yay da idanunsa ya lumshesu tare da sake buɗewa a kanta da ɗan risinar da kai na girmamawa. Sai kuma ya kamo hanunta data janye a saman sumar kansa ya sumbata. Ajiyar zuciya ta sake saukewa mai kauri da jin ƙarin ƙaunar tilon gudan jinin nata da maƙiya suka sako a gaba. Tana matuƙar ƙishirwar rashin ganinsa a kusa da ita ko yaushe, sai dai babu yanda ta’iyane…..
“Ammie kina lafiya?”.
Ya katse mata tunanin da take neman yin nisa a ciki. Numfashi ta ɗan fisga ta fesar alamar dawowa. Sai kuma ta girgiza kanta da raunana fuskarta. “Kasancewarka lafiya itace tawa Saiful-mulk”.
A karo na biyu ya saki murmushi yana ɗan jinjina kansa shima, sai kuma ya ɗago ya ɗan kalleta ya kauda kai. “Ina lafiya Ammie”.
“Ni ba haka na gani a cikin idanunka ba *_Negar_*”.
Baice komaiba kusan minti ɗaya, hakan ya fahintar da ita bazai ce ɗin ba, tai murmushi kawai tana kaɗa kanta. Ta yarda jinin mulki gaskiya ne, dan tana ganinsa yana yawo a cikin gudan jininta. Duk ƙasaita da miskilanci irin na Tajwar Haysam da ita kanta da ake faɗi Eshaan ɗinta ya takasu ya shanye. Irin miskalayen mutanen nan ne shi masu matukar ban mamaki da wuyar sha’ani, dan kai tsaye baka isa gane ainahinsu ba balle farin cikinsu ko damuwarsu kai tsaye, a matsayinta na mahaifiya a garesa da ake ganin yafi sakewa da ita fiye da kowa sukanyi zaman awa guda bai firta jimlar magana sau goma ba, murmushi kam ita da Malikat Haseenah kawai ke gani daga garesa sai mahaifinsa kafin yabar duniya……
Lurar da yay tayi nisa a tunani ya sashi kai hannunsa cikin ƙyaƙyƙyawan bowl ɗin da aka cuɗa dabino da zuba ya ɗakko tsagin dabino ɗaya daya naɗi zuma yay luntsum, ya tare da ɗayan hanunsa ya kai bakinta. A hankali taja numfashi ta sauke alamar dawowa. Babu musu ta matso tare da buɗe bakin ya saka mata. Sai da ta cinye a nutse tana mai kallonsa da murmushi sannan itama ta ɗauka kamar yanda ya bata ta bashi har sau uku. Tasan yunwa yake ji, amma yaƙi cin komai saboda damuwa. Tun yana yaro haka yake, a duk sanda sukaje dubashi a inda ya girma ita da Tajwar Haysam ta wannan hanyar take gane yanada damuwa, ko kuma yana fushi. Dan in har yana jin yunwa yaƙi cin abinci suka matsa masa akan yaci zai ɗiba abincin ya saka a bakinsu, sukuma hakan da yayi zai nusashesu zama su bashi da kansu har sai ya ƙoshi. Tissue tasa ta goge masa bakinsa idonta dake kansa na cika da ƙwalla.
“Kanajin yuwa Negar?”.
Gajeren murmushisa ya sakar mata da kauda kansa gefe maimakon amsar data buƙaci ji daga garesa. Itama bata sake cewa komaiba, sai wayar landline dake gefensa ta ɗauka. (Inba akan Tajwar Eshaan ba waya isa ganin Malikat Bushirat a haka). Cikin ƙanƙanin lokaci aka iso da abinda ta buƙata. Shi dai kallonta yake a harɗe kamar yanda itama take zaune a harɗen. Abincine na musamman, wanda tasan shine mafi soyuwa a garesa…
“Idan kana zama da yunwa bazan yafema kaina ba”.
Idanunsa yay kamar zai rufe sai kuma ya buɗe a kanta. Ƙasaita jininsa ce, kamewa da tsumewa nagartarsa ce. Kwarjini da cikar haiba mutuncinsa ne. Miskilanci gadonsa ne. inba ita ɗin bama wake ganin murmushin kojin furucin bakinsa, dan babu abu mafi wahala da girma ga Tajwar Eshaan kamar magana. Dariya kam ko’ita a karan kanta zata iya rantsuwa bata taɓa gani ba tunda ba’a gabanta ya tashi ba, sai lokaci-lokaci suke zuwa su gansa.
Abincin ta haɗa masa a gabansa da kanta, babu musu kuwa ya amsa tausasan idanunsa na kallonta da jin ƙaunarta kamar kowane ɗa akan mahaifiyarsa. Tsahon mintuna yana tsakurar abincin cike da ƙasaita kamar wani magani, kafin ya ɗauka tissue ya goge bakinsa da janye jikinsa da ga kwanikan alamar ya ƙoshi…..
“Ya take yanzun?”.
Tambayar da take son jin tun ɗazu daga bakinsa ta fito tamkar an fisgota. Idanunta ta ɗan kafe kansa, amma sai ya kauda kai gefe kamar bashi ya buƙaci ji ba. Taja numfashi ta fesar, itama batare data sake cewa komai ba ta cigaba da nazartar sa. Kusan mintuna uku tsakani sannan ta nisa…
“Ban san mikafi buƙatar ji ba. Sauƙin ko akasin sa. Amma dai zan iya cewa muna jiran ikon UBANGIJI ne”.
Shiru babu alamar zai sake cewa komai, itama bata sake cewar ba. Kansa ya ɗan risinar gefe bayan ɗan kallon gefen idanu da yay mata. Miƙewa Malikat Bushirat tayi, ya bita da kallo harta isa bakin ƙofa sai kuma ta juyo, “Ina jin tsoron ace alaƙar da maƙiyanmu ke alaƙantawa da kai ta zam haka take Saiful-mulk”
Kansa ya ɗauke gefe, itama sai ta ɗauke nata kan daga garesa tana danne lips ɗinta da haƙori. Shiru kusan na minti ɗaya, ita bata fitaba ita bata juyo ba, shi kuma bai amsa mata ba bai kuma motsa ba, sai kawai ta buɗe ƙofar zata fice.
“A huta lafiya”.
Ya faɗa dai-dai tana ficewa. Bayan kusan minti uku da fitarta ya furzar da nannauyar iska, miƙewa yay hannayensa goye da bayansa ya fara tattaki zuwa gaban window ta saitin inda zai iya hangota. Dai-dai kuwa hadimanta dake zaman jiranta na zagayeta. Duk da nisan da sukema idanunsa bai bar wajen ba har sai da yaga ta shige sashenta da tawagar hadimanta.. Wani irin ƙasaitaccen murmushi ya saki da lumshe idanu, sai kuma ya buɗe cike da isa yana mai barin windown ya shige ƙofar daya fito ɗazun….
Lafiyayyen bedroom ne mai ɗauke da kayan more rayuwa irin nasu na manya. Ƙamshi dai kam ba’a magana dan Tajwar Eshaan ko gonar turare haka ta gansa ta bari saboda yanda yake wanka da shi a duk motsinsa, son ƙamshi da zama cikinsa tamkar al’adarsu ce data zama dole ga talaka da mai kuɗi, sai dai banbancin tsada da ƙamshi ya banbanta maka wanene tare da kai. Amma dai-dai da banɗakin jinin Ruman ko shagon sai da kaya a kasuwa ka shiga saika san kazo ƙasar ƙamshi, duniya ta sansu da wannan tun shekaru aru-aru, dan suna a sahun farko na ƙasashen dake yin turare, yana kuma ɗaya daga cikin tattalin arziƙinsu dake shigar musu da kuɗi da bayyanasu a ko’ina suka shiga a duniya. Zaune ya kai a kujerar dake ɗan gefe ta jikin window, ya kai bayansa kwance a kujerar, tare da kwantar da kansa ya kalli sama ya lumshe idanunsa. Daga ƙasa ƙafafunsa a harɗe, hannayensa duk biyu akan hanun kujerar ya ɗan fara lila kansa. Sai da ya ɗauki tsahon mintuna ashirin a haka dan zakama iya ɗauka barci yake yi kafin ya buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, zaune ya tashi da ƙyau, ya kai hannu drawer’n dake gefen kujerar ya buɗe, ƙaramar waya ƙirar nokia ya ɗakko. Danne-danne yay tare da kaiwa kunnensa yana wani yamutsa fuska. Bugu ɗaya kuwa aka ɗaga daga can, cikin bada umarni da ƙarfin ikon ya furta..
“A kawar da ukun bana buƙatarsu. Haɗuwa, da lokaci zaizo a saƙo”.
Ya janye wayar daga kunnensa da dafe kansa yana cizar lips ɗinsa a lokaci guda fuskarsa babu alamar ɗigon wasa ko sassauci a cikinta sai razani mai ban tsoro da saka firgicin ga duk wanda zai iya ganinsa a hakan………..✍
(Tofa! Tajwar…… bara dai nai shiru).
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
✨Ɗ ✨
( )