Daudar Gora Book 1Hausa Novels

Daudar Gora Book 1 Page 14

Sponsored Links

14_*

 

………Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah bazata taɓa mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taɓa zama shiɗaɗɗe a zuciyarta ba. Kwana ɗaya tak ta kasance cikin ɗimuwa da tsananin kewar ahalinta. Wanda ta riga ta gama sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai bayan mutuwarta suzo jana’izarta batare da ko kan gawarta an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda ɓarawo da yaci galabar ɗaukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka biyo bayanta da shi na buɗa bakin azumin da tace batacisa ba. Kuka taci ta ƙoshi har kusan rabawar dare kafin ta miƙe zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba ɗayanta gaban UBANGIJIN talikai maji roƙon bayinsa. Duk da tsananin tsoro da take a ciki na kasancewa ita kaɗai a katafaren sashen haka ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk ƙanƙantar motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo kashetane.
Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk yanda take faman turesa da son ƙin yinsa sai da yakaita ƙasa, dole takai kwance kan lafiyayyen kafet ɗin dake gaban gadon kafin ƙiftawar ido ta fara sauke numfashi….

Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake cike da barci ta buɗe da ƙyar akan matar dake tsaye a gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai, sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita ɗin bakomai bace sai hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai babban muƙami da matsayi….
“Barka da safiya ya Zawjata-almilki”.
Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. Yunƙurawa tai ta tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaɗa da faɗin, “Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruɗewa da kiɗima a idanun matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube ƙasa da rawar harshe. “Ranki ya daɗe na roƙeki dan ALLAH wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke kika cancanta mu kira da sunan bani ƙasƙantacciyar baiwa mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama (baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a gareki”.
Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na ƙuna na raɗaɗin ƙasƙancin da su talakawan ruman ke fuskanta a ƙarƙashin waɗannan masarautu. Hadima Diwa miƙewa tai da sauri ta fita. Mintuna kaɗan sai gata ta dawo tare da wasu mata guda biyu.
“Ranki ya daɗe, waɗannan matan sune zasu shiryaki a yanzu”.
Yanzun ma iyakarta ɗago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta cigaba da yin addu’a sakamakon harbawa da ƙirjinta keyi da sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan ƴan ƙasar ta Ruman keda ya bayyana.
“ALLAH ya ƙara miƙi tsahon rai da lafiya, wannan lokacine na wanka”.
Komai Iffah batace musu ba ta miƙe, dan tanabin huɗubar Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga ƙoƙarin binta da suke.
Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faɗin, “Ranki ya daɗe ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su kuma gyara miki kai kawai su fito”.
“Karki damu zanyi da kaina”.
Ta faɗa tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu, sai dai bakinta ɗauke yake da addu’a. Wani irin harbawa zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya ƙafa cikin toilet ɗin sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi, yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu takai saman kanta tana karanto addu’a bayan ta shiga toilet da tayi sannan ta ƙarasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a yanzu fiye da ɗazun, dan yanzu an ƙawatashine da wasu irin fure da candles ta gefen jakuzzie ɗin. Sai wasu nau’inkan ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam zuciyarta taƙi aminta da hakan, atake ta dinga ɗaga tasoshin da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan halin da suke ba a yanzun suma….

Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci karo da akasin haka. Domin kuwa wayam ɗakin babu kowa, sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka ajiye ke tashi. Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba.
Knocking ƙofar da neman izinin shigowa ya sakata ɗaga idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama kanta a ƙasa, tun’a bakin ƙofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na shiryawarki da taimakon waɗan nan mata”. Ta ƙare maganar da nuna bayanta.
Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai ɗan shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi. “Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”.
Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana ƙasa sosai. “Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saɓawa kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”.
Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maƙoshi ya sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haɗiye abinda ya tokare ƙirjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar ƙyaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a gareta suka zube gwiyawunsu a ƙasa domin gaisuwa a gareta kasancewar bana ɗazun bane.
“Dan ALLAH ku miƙe”.
Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk da ƙanƙantar ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.

Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da wannan sunan. Dan ƙwalliyar tata ta dace da halittar ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da ƙyawunta. Ta cancanci a kirata Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da ƙanƙantar shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiɗe a ƙyaƙyƙyawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar ƙawata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi duk sauran Zawjata-almilki da suka shuɗe ƙyawu ba, kawai natan ya matuƙar ƙayatar dasu ne batare da sun san dalili ba. Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita ɗin bace, bawai dan ƙyale-ƙyalen gold da diamonds da aka ƙawata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko da takejin tsantsenin gani a jikinta.
Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a yanda yaso ta isar da saƙonta kamar haka….
“Ya Zawjata-almilki! Yanzu shine lokacin karin kumallonki”.
Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar numfashinta, “Bana buƙatar cin komai nikam Mama”.

 

Back to top button