Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 10

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na goma_

 

_ADVERT_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA’ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI… AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE…_

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS… THEY ‘VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED

___________

…….Ƙarfe ɗaya da mintuna goma sha shida duk wanda ke a massalacin ya shaida ɗaurin auren Dafeeq Abubakar Ja’e da amaryarsa Kainaat Usman akan sadaki naira dubu ɗari biyar. Kasancewar massalacin a anguwar su Kainaat yake gane wanene angon nata ya haddasa ƙananun maganganu a bakunan mutane. Kainaat sananniyace a anguwar tun tana budurwa, duk da mahifinta talakane ta tashi irin yaran nan marasa jin magana da son ƙarya. Za’a iya rasa masarar tuwo a gidansu Kainaat ka ganta da dressing na kusan dubu ɗari biyu a jiki. Gashi bata da mutunci ko kaɗan, dan ko gittawa tai ka gaya mata cuta sai ta dawo ta gaya maka mutuwa. Yanda Kainaat ke fantamawa a cikin dukiya yasa tuni kowa ke mata kallon ƴar iska. Sai dai kuma a baɗini sam ba haka bane. Dan duk rashin jin Kainaat bata aikata zina, amma fa ko kai waye a wayo in har ta ƙwallafa maka sai taci kuɗinka. Zatabi tako wace irin hanya taci saboda shegen wayonta. Kainaat ƙyaƙyƙyawa ce sosai, dan ta kasance buzuwa, sai dai anan Nigeria aka haifeta, dan nan ta tashi taga kanta da iyayenta nan kuma kaɗai ta sani ko Niger da aka san asalin buzaye suke basa zuwa. Ƙawayen Kainaat duk ƴaƴan masu kuɗine, ta kuma samosu ne a yazon bin joint-joint ɗinta. Dan duk inda tasan ƴaƴan manya suke nan ne wajen zuwanta. A wannan kutse-kutsen nata ta tattara ƴaƴan manya suka zama abokanta. Sometimes ma sune ke saya mata sutura, dan in har zasu shiga shopping to itamafa dole a mata. Tayi samari kala daban-daban kama daga kan alhazawan birni har zuwa matasan masu kuɗi dama yaransu, sai dai taci kuɗinsu ta gudu. Da taimakon Nadwa ta koma makaranta, dan ta kammala secondary ɗinta tuni. Nadwa mommy’s girl ce. Dan babanta ya jima da rasuwa, kuma mai kuɗine sosai, ita kaɗai ya haifa dan haka ya barsu da tarin dukiya itada mahaifiyarta. Tunda taga Kainaat ALLAH ya ɗaura mata sonta, dan ita mutum ce mai son ƙyaƙyƙyawa. Tare suka fara karatu, daga baya Mommyn Nadwa ta turasu abroad. Da ƙyar baban Kainaat ya yarda, dan sai da Mommyn Nadwa ta lallaɓashi.
Su Kainaat na shekarar ƙarshe a school Abaan yazo yin wani course na wata shida. Tunda Kainaat ta ɗaura idonta a kansa ta haukace. Haka ta addabi Nadwa sai da ta binciko mata shi ɗin ɗan waye. Hankalin ta ya sake tashi jin bama ubansa ba, shi akaran kansa gayyane. Dan matashin mai kuɗine a harkar noman shinkafa da shigo data waje gida Nigeria, ya kuma fitar da ta Nigeria waje. Kai a taƙaice dai shine kankat a harkar shinkafa a Nigeria bama arewa kawai ba. Wannan shine irin mijin da Kainaat ta jima tana burin mallaka, matashi ga kuɗi ga ƙyawu. Uwa uba miskilanci. Dan kallon fuskar Abaan kawai ya isa tabbatar ma da mai hasashenshi shi ba kanwar lasa bane. Duk da jikin Kainaat ya ɗanyi sanyi kaɗan da jin shekarunsu ɗaya na haihuwa, amma da ga baya sai ta ware akan hakan ba komai bane. Kainaat ta fara ƙoƙarin shiga jikin Abaan sai dai ko kallo bata ishesa ba, hasalima an sanar mata shi fa mata basa gabansa sam. Mahaifiyarsa da ƙanwarsa ne kawai taurarinsa a duniya. Jin wannan batu yasa Kainaat shiga ta fita harta jawo hankalin P.A nashi kanta, da taimakonsa ta fara kusanta kanta da Abaan, sai dai nan ɗin ma babu nasara, ganin bazai kulata ba ta canja alƙibla zuwa kan ƙanwarsa da mahaifiyarsa bayan sun dawo gida Nigeria sun bar Abaan acan. Yanda Kainaat ke kwantarma Hajiya Maryam kai yasa ta fara jin sonta a zuciyarta, gata kullum cikin shigar kamala. Noor ce dai ma aka ɗan sha wahala da ita, dan da ƙyar ta fara kula Kainaat saboda faɗan da Hajiya Maryam ke mata. Da taimakon Mommyn Nadwa Kainaat ta sake samun shiga jikin Hajiya Maryam, danta alaƙantata da cewar ɗiyar ƴar uwarta ce. Duk da Hajiya Maryam ba damuwarta dole sai ɗanta yay auren ƙwarya tabi ƙwarya bane sai taji ta amince Abaan ɗinta ya mallaki Kainaat matsayin mata. Dan koba komai ƙyaƙyƙyawace kuma nutsatstsiyar yarinya. (Nace Humm).
Daga ƙarshe dai anyi auren Kainaat da Abaan badan yana sonta ba sai dan biyayya ga mahaifiyarsa. Yayinda komai akayisa a hannun Mommyn Nadwa matsayin itace uwa gareta iyayenta sun rasu. Mahaifiyarta tayi kuka sosai da irin wannan aure, dan tana son ƴarta, amma gashi a dalilin auren mai kuɗi ta kashesu ta ɗauki matar data santa da girmanta. Haka dai aka sha shagalin biki iyayen Kainaat basu da wani power a ciki. Amarya ta tare, sai dai babu kulawa daga miji, hasalima randa aka kaita yabar ƙasar, hakan ya ƙonama Kainaat rai sosai, taci kuka bana wasa ba, sai dai Mommyn Nadwa nata kwantar mata da hankali ta waya. Hakama Hajiya Maryam tasa Abaan ya dawo dole bayan tafiyarsa da kwanaki uku. Anan ɗin ma Abaan bai niyyar shiga sabgarta ba, amma babu wanda yasan yanda akayi kwanakinsa biyu da dawowa yakai kansa gareta har ma ya angwance a wannan dare. Samunta da budurcinta ne abu na farko daya kankaro mata mutuncinta a wajensa, duk da kuwa asiri na cinsa, dan kai kansa da yay gareta kam tabbas magani yaci a cikin abinci. A watan da Kainaat taje bata tsallake na ciki ya bayyana, kowa murna yake tsakanin Abaan da mahaifiyarsa da Ƙanwarsa. Tattalinta sukeyi kamar ƙwai, dan ko motsi tai sai ance mike damunta. Wannan al’amari yayma Kainaat daɗi, sai ta dinga langaɓe musu kuwa fiye da jin jiki na laulayi suko suna rawar jiki. A haka ALLAH yakai ciki watan haihuwa, ta ko haifo ɗanta namiji mai kama da ubansa sak. Farin cikin wannan family bama zai misaltu ba. Amma abin baƙin ciki mahaifiyarta da ƴan uwanta da mahaifinta sai zuwa sukai dubata a matsayin wai dangin babanta ne dake Niger, Mommyn Nadwa itace komai. Ranar ma mamanta sai da tai kukan baƙin ciki, yayinda ƴan uwanta sukai alkawarin bazasu sake raɓarta ba, dan yanda ta amshesu a wulaƙance ya ƙona musu zuciya sosai. Suna baro gidanta suka tattara kayansu dama gidan da suke gidan haya ne sukai tafiyarsu Niger. Wannan shine silar rabuwarta da iyayenta da ƴan uwanta, har yanzu bata kuma nemesu ba suma basu sake memanta ba.
Ranar suna an zubar da kudi na tashin hankali, yayinda yaro yaci sunan Kakansa wato mahaifin Abaan da ALLAH yayma rasuwa tuni. A wannan ranar ne Abaan yayma Kainaat ƙyautar companyn nan, tare da maƙudan kuɗi daga mahaifiyarsa, ƙanwarsa Noor ma ba’a barta a baya ba ta siya mata danƙareriyar mota duk da kuwa Kainaat ɗin nada har guda biyu na lefe da aka saka mata da wadda Abaan ya bata matsayin tukuycin kai masa budurci. Ansha shagali an kuma samu dukiya sosai daga abokan arziƙi, dan kwarai da gaske yaro yayi goshi, Kainaat na alfahari da haihuwarsa. An fara rainon yaro matsayin ɗan gata, sai dai kuma ashe bamai zama bane, dan watansa ɗaya da kwanaki a duniya ya rasu sakamakon mura da dama aka haifesa da shi, dan Abaan nama shirin suje suga likita ne a waje ashe babu rabo.
Kuka na tashin hankali Kainaat ta dingayi, dan kuwa dai taga samu taga rashi, harta fara alfaharin dukiya ta zama tata ta gida gaba ɗaya. Abaan da Mamah suka koma lallashinta ita da Noor, dan kuka suke sosai. Ansha fama Kainaat harda kwanciya asibiti kamar ba mutuwar ƙaramin yaro ba, da ƙyar ta dawo hankalinta…..

___________★

Guri ɗaya suka sake dunƙulewa sosai. Dan hatta malaman kansu a wannan gaɓar zukatansu bugawa suke da sauri-sauri. Sai dai basu yarda sun saki addu’oi ba. Masu ragguwar zuciya kam tuni fitsarin daya taru musu ya fara ɗiga, wasu ma gab suke da fashewa da kuka tsabar tashin hankali. Dan wannan al’amari ne da a film kawai suka sanshi bawai zahirin rayuwa ba.
Tsahon mintuna biyar wutar ta sake kawowa. Wani irin ihu mai jijjiga gida suka saki kusan su duka idan ka cire Baba da malaman nan sakamakon bayyanar Alimah a mummunar siffar horrors dan bata da maraba da su. Fuskarta da jikinta sunyi wani irin fari tamkar an baɗa mata hoda. Wajen idanunta yay wani zummm kamar wadda tai kukan jini, hakama bakinta duk jini ne, ga gashi a wargatse da uban tsaho har yana jan ƙasa, ta saman kanta akwai ƙahuna guda biyu. Hakama ƙafafunta kofataine, hanyenta da wani irin farcina zaƙo-zaƙo tako ina dai bata da ƙyawun gani. Dan su kansu tunda sukai mata kallo guda idanunsu suka rumtse babu wanda yay gigin sake maimaitawa.
Shuuuuu!! Ta wani irin zagayesu kamar mai tafiya a takalmin taya tana ɗaura zabgegen yatsanta a saman baki da faɗin, “Shiiiii!!!” alamar sumata shiru daga ihun da sukeyi. A tare suka shiga haɗiye ihun sai hawaye dake fita a fuskokin masu raguwar zuciyar cikinsu. Jaruman kuwa rawar jiki kawai suke yi, gashi a zagayesun da tai ɗin nan ashe ɗauresu tayi da igiyar da sudai basu gani a hannunta ba.
Kwas! Kwas!! Kwass!! Ta dingayin wani taku tamkar wadda ke jerin gasar ƙyau ta duniya. Sai kuma ta wani kwashe da dariyar data nema fasa zukatan su. Sai da tai mai isarta tana faman zagayesu kafin ta tsagaita, da wata kalar kakkausar murya ta ce, “Ku miyasa bil adama kuke da son shiga abinda babu ruwanki ne? To gashi nan shishshigin ku ya jawo muku mutuwa!!!”.
Cikin rawar baki da suɓutar baki Baba ya ce, “Baiwar ALLAH kiyiwa ALLAH ki haƙuri. Wlhy mu muzo ne domin ceton matar Jazool. Amma ki taimaka ki yafe mana”.
“Hahahaha tsoho! Idan kai wannan ya kawoka su waɗan nan miya kawosu? Sannan da kukazo ɗazun ban muku gargaɗin farko ba?!”.
“Kin mana wlhy, kin mana. Dan ALLAH kiyi haƙuri. Babu wanda zai sake maimaita kuskuren nan”.
“Wanda ma ke son maimaitawa ya maimaita. Dan ganin gawawwakin ku sai ya saka ƙafar wani bazata sake tako cikin gidan nan ba. Ɗanka kuma yanzu ya fara amsar sakamakonsa a hannunmu, dan sai ya tabbatar da bakowace mace ake taɓawa a zauna lafiya ba. Sai mun barma ire-irensa tarihin tunawa a wannan duniyar”.
A yanzu kam idan ka cire baba da malaman nan kowa kuka yake jin wai zata kashesu, sukam ganin ƙwam bai musu rana ba. Wata irin gigitacciyar tsawa ta daka musu. Sake dunƙulewa sukai waje guda suna mai sake ƙan ƙame junansu, masu fitsari na sake sakin second round. Cikin ƙarfin hali shugaban malaman ya fara karanto suratul baƙara. Da rawar jiki wanda suka iya suka fara suma. Kecewa da dariya Alimah tayi, sai kuma ta haɗe rai tare da tafa hannunta ta buɗesu. Sai ga bakunansu sun ƙage kowa ya kasa magana.
“Hahaha!! Ni zakuma karatu. Ni nan kuke tunanin ƙonawa? To kafin ku ƙonani ni bari na shafe babinku.” ta wani irin sake tafa hannaye sai ga wasu mugayen halittu na fitowa ta cikin bangwayen gidan a kowace kusurwa. Gaba ɗayansu sun gama rikicewa. Hatta da su baba a wannan gaɓar kam babu sauran jarumta a tattare dasu. Kowa zufa yake kashirɓan jiki na rawa Kaff-kaff kamar waɗanda aka kaɗama gangi. Yanda suke sake curewa waje guda sai sun matuƙar baka tausayi. Masu ƙarancin ƙarfin zuciya tuni sun fara sumewa dan ganin halittun nan kawai ba ƙaramin tashin hankali bane mai rikita tunani. Balle kaga kai suke dimfarowa tamkar mayuntan zakuna suna wani irin nishi da fesar da wuta a bakunansu. Suna gab da isowa garesu ta sake tafa hannayenta suka ɓace. Dariya ta shiga ƙyalƙyalawa tana kallonsu. Kafin ta wani irin fesa musu ruwa da hannunta data ware a kansu kamar mai musu daƙuwa. Sharaf suka jiƙe, waɗanda suka suma duk suka farfaɗo. Kuka ƴan maza suka shiga fashewa da shi suna roƙonta tayi haƙuri sun tuba ta yafe musu. Tamkar bata jisu ba ma ta koma jikin bango ta maƙale.
Shugaban malaman nan ne cikin galabaita da sauke numfashi ɗai-ɗai ya ce, “Baiwar ALLAH kiyi haƙuri. Ki sani akwai hisabi tsakanin aljan da bil adam. Yanda makomarmu take a tsakanin aljanna da wuta haka kuma makomarku kenan. Mu bamu zo nan domin cutar dake ba. Dan ALLAH kema kada ki cuta mana. Bamu san komai tsakaninki da Jazool ba. Amma zamu roƙeki shima ki yafe masa, ki kuma fita a jikin matarsa dan ALLAH ki barsu suyi zaman aure kamar kowa…..”
“Har abada hakan bazata faruba! Nace maka har abada! Har abada JJ bazaiyi aure ya zauna da wata mace ba. Kuma bazan taɓa iya yafe masa ba!!” sai ta fashe da wani irin mahaukacin kuka daya sake firgitasu da gigita su. Sosai tai kukan kafin ta ɗago kanta dake lulluɓe cikin dogon gashinta tana kallonsu. Ƙasa duk sukai da kawunansu. Muryarta na rawa da karkarwa ta ce, “Zan baku dama ta ƙarshe saboda wasu dalilai. A cikinku akwai bayin ALLAH, akwai masu ƙananan yara, akwai masu taimakon marayu, akwai masu ƙoƙarin bautama UBANGIJI, akwai masu ƙyautatama iyaye, akwai masu yawaita karanta Alkur’ani. Duk da dai akwai tamtirai irin JJ kuma sun san kansu. To sunci alfarmarku, zan barku ku tafi, amma ku sani, duk wanda ya sake gigin shiga gonata saina sabauta masa rayuwa. Alimah kuma kuje JJ ya fara sanar muku *_WACECE ANOOSH_*, ni da kaina zanzo gareku da Alimah. Kuma ku sanar masa ko ƙoƙarin yin ƙarya yay akan Anoosh ina gefensa zaisha mamakina, dan duk inda yake ina a tare da shi kamar yanda zuciyarsa da jininin jikinsa ke tare da gangar jikinsa. Na barku lafiya”. Ta wani irin harba hannunta kamar mai san ture abu. Sai gasu a tsakar anguwa an watsosu kamar kayan wanki.
Wayyo ALLAH zo kaga yanda ƴan maza ke rige-rigen tashi suna cika wandunansu da iska. Sai dai kaji garamm an buga ƙofar gida an shige. Wasu ma ba gidajensu suke ƙoƙarin shiga ba. Sai mai gidan ya farga ya jawosu waje shi ya shige yana faɗin, “Tafi gidanka”. Su baba da su Malam daba anguwar sukeba kam sun ma manta da motocinsu kowa ƙafarsa ce motarsa har zuwa titi. Babu mai sauraren ɗan uwansa kowa ƙoƙarin tare abin hawa yake. Burinsu kawai su gansu a nasu gidajen suma……✍️

_To Bara nayi takaina Nima dai, malam na neman ƙafar zuwa gida, ni kuma Bilyn ku fa_.

Mura ta rikeni kwana biyu.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button