Banana Island 30
Washekari saida taci barcinta ta more sannan ta fito da er rigar swimmingɗinta zata je pool ɗin gidan . Tana sakkowa daga falon taji ƙarar laptop ana bubbugata da ƙarfi ana aiki akanta da sauri da sauri .
Shiga falon tayi ta gansa a zaune ,Yina kan laptop ɗin
“Good morning Mr mie” dakatawa da danna laptop ɗin yayi ,gamida stretching Hannunsa akan laptop ɗin alamar miƙā. Haka ya kafeta da ido fuskarsa a murtuke kamar wanda aka aikowa sakon mutuwa
Zuwa tayi ta tsaya a gabansa “My sugar plum yakake?…” banza yayi da ita
“Baza kayi mun magana ba,nayi maka laifi ne?”
Sunkuyar da kansa yayi ya cigaba da danna laptop ɗinsa . Da sauri ta dawo gabansa sosai ta saƙa jikinta ta raba tsakaninsa da allon fuskar laptop ɗin ,ya zama baya kallon laptop ɗin sai ita
“Meye amfani na a gidan nan in baza kayi mun magana ba ? Must be talking”
“Matsa ki bani waje” yayi magana Yina hura hanci kamar wani boss ,Wanda yasa gabanta fadi rasss bata taɓa ganinsa a wannan yanayin ba hakan ya tuno mata da first visit dinta wajensa
Jan leɓen bakinta tayi a hankali tayi da haƙori tana tsotsan leɓen cikin jan hankali ta kafesa da lumsassun idonta ,a sanyaye takai hannu zata taɓa fuskarsa da sigar rarrashi .
Da ƙarfi ya riƙe tsintsiyar hannunta
Buɗe baki tayi zatayi magana kawai yayi sauri ya miƙe zai bar wajen ,da sauri ta biyo bayansa ta fara magana cikin sigar kuka .
“Me nayi maka kuma?”
“A sharudda na ban yarda ki taɓeni ba”
“Me yasa zaka ringa horani da hakan?…ni ba matarka bace? Plz mu zama normal couple Mana da Allah ,Muslunci da musulmai zasuyi Alfahari damu ba irin wannan bahagon zaman ba , I’m getting to reach here wlh” tayi magana tana nuna maƙoshinta da hannu .
“And…?”
Narai narai da ido tayi saboda batasan me kuma zata sake ce masa ba ,kasai sai taje da gudu ta fada ƙirjinsa tana ƙoƙarin hugging ɗinsa Saidai da ƙarfin tsiya ya ɓanɓareta a jikinsa
“meyasa bazaka bari in rungumeka ba”
“Kin mun laifi”
“me nayi mka ,shikenan hanyar da ake hora mace? Baka tunanin nima kana mun laifi? Kanason nima in ringa horaka da Sex pattern dinka ne?…shikenan Adnan ka mun hukuncin da ya dace nima in Ina cikin fushi zan maka kwatankwacin abinda kau mun….oya beat me!!!”
Jikinsa rawa ya kamayi da sauri ya kamo kafaɗarta yana girgizata amma gabaɗaya ta haukace masa sai masifa take tana sambatu
“Me yasa zaki bugeni? Kin taba ganin inda mata ta daki mijinta …? Kin maidani lusarin namiji ne?”
A zuciye cikin hawaye tace “Meyasa zakayi ta dukana ,ka maisheni mace mara galihu ne ? A musulunci babu inda aka yarda miji ya daki mace ,bare kawai for your own raw sex…”
“Shikenan kin dakeni kinsa su preety sunzo sun ganni fuska a kumbure,tambayoyi suka shiga mun a ruɗe yau ,wai nayi dambe da kura ne bla…bla ”
Lumshe ido tayi cikin tashin hankali “Kagani ko? Kai Kanada wanda suka damu dakai rana daya tak ,an suffantani da kura nikuma dukan da kake mun inda wani nawa ya gani me za’a suffanta ka dashi dodo…? Yes Dodo na!..amma bani da gatane ,da mahaifina Yina da rai wallahi da baza ayi mun haka ba ,da ban aure ka b bare ka wulakantani” wani kakkauran kukane ya nemi sufce mata da sauri ta juya zata wuce . Tausayinta ne ya kamasa da sauri ya rungumota ta baya ,kiciniyar ƙwace kanta takeyi “Kawai ka ƙyaleni”
“Kinsan ya rayuwar aure yake a musulunci right?” Shiru tayi masa bata bashi amsa ba
“Babe illiteracy shi yake damuna banyi ilimin addini ba komai ya shato kaina shi nakeyi ,yanzu muje ki natsu ki koya muna yanda zamu gina zaman auren mu yanda musulunci yace ,bansan raɗaɗin da kike sha ba saida kika zane Ni kika tafi kika Barni with my agony”
Juyawa tayi ta tallafo fuskarsa “Ni ba Malama bane ,lokaci yayi da zaka ware lokaci cikin precious time Dinka ka nema addininka…kuɗin da ka tara ya ishi ba kai ba zuri’anka karni goma masu zuwa baza suyi talauci ba ,amma shifa ya tanajin lahiranka kayi guzuri mai yawa? I’m sorry to say ba naga ana sallah alwala da sauransu a gidanmu nima Inyi shi ke kai mutum aljanna ba ,ka nemi ilmin lahiranka ,kayi aikin Allah a yanda Kur’ani da littafan addini sukace ,ka koyi mu’amala da mutane shi zai baka damar aiki mai kyau ….”
Rungumeta yayi dakyau a jikinsa ya ɗan kissing goshinta
“my wife material”
“Mijina Aljannah ta”
***
Lili soyayya mai tsafta ne ya ƙullu tsakaninta da Faisal ,ya tubure bazai koma ƙasarsu ba sa manya sun shiga magana don dama dalilin hijiransa saboda rashin macen aurene to Allh ya bashi ,sai ya koma ma iyayensa da kyakyawar Albishir .
Lili duk kwane kwanenta dole ta hakura ,tunda maganar gasky itama Faisal yayi mata ,bai bar Nigeria ba saida yayi magana da iyayenta bayan sati guda ya dawo da iyayenta aka tsaida ranar Biki .
Great late comer kenan ,yazo a baya yayi wufff da ita …sorry mr. Mubarak
***
Page Y
Half way…
To be continued️ _*BANANA ISLAND*_
_(Billionaire’s paradise)_
Book 3
Page *Y²*
Na…
Oum Aphnan ✍