Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 37-38

Sponsored Links

……….. Sun dade suna tattaunawa da malam akan rayuwa Kafin ya koromai zancen Karin Auren da Momy keson yi mai, Sai da yayi shiru malam yace “yanzu meye matsalar ka? Baka da muhalli ne, ko baka iya daukar nauyin mata biyu ne? Kuma meye dalilin sakin ita dayar Matar taka ba akan ka’ida ba? Yanzu dai nasan ba mata hudu ba Kanada karfin da zaka ciyar da Unguwa guda ma, sannan lafiya kana da ita, sauran ka Adalci, karike Amanar su tsakanin ka da Allah kabi umarnin mahaifiyar ka kasamu tsira kamar d’an uwan ka. Haka suka dade sai karfe kusan biyar yabar unguwar, tun fitar shi take jin ba dadi domin ta saba dashi yanzu tafara sanin dadin Aure zaman ta da khaleel, shine ya nuna mata ita mace ce mai daraja da lafiya a tareda ita, domin duk lokacin da ya kusanto jikinta bata iya misalta dadin da takeji hade da nishad’i, kewar shi ta dameta sosai har waya ta dauka sau ba adadi’ tana dubawa tareda tunanin kiran shi sai takasa, to me zatace mai inta Kira? Ganin zata damu da yawa yasa ta janyo wayarta ta fara karatun littafin ta, y’ay’an gata yasata cikin nishadi’ sosai, saida taga yamma yayi ta mike ta shiga kitchen, ta shirya mai dinner lafiyayya irin wadda tasan yakeso, Kafin tayi wanka, duk Abinda takeyi a yanzu bin zuciyar ta ne domin tana samun farin ciki ba tare da tayi tsammanin samun shi ba a cikin wannan Rayuwar Auren.
Yana tafe a hanya yana duba waya, wato ba zata iya neman shi ba koda zai shekara baya gidan? Don haka saida yayi magrib ya shigo cikin part din, lokacin tayi wanka ta saka simple gown tana zaune tana lazimin ta, ya yi sallama ciki ciki, tareda wucewa gefen gadon ya zube rigin gine, nasihar malam ta ratsa shi Amma baya jin kudurin shi zai canja sai dai ya kiyaye fadawa halaka Wanda yasan duk ta inda zai bullo ma Al’ amarin, saida ta kammala ta mike tareda juyowa tace sannu da zuwa. Bai amsa ba bai bude idanun shi ba, harta juya tafita, saida ta juya yabita da kallo tareda sauke Ajiyar zuciya, ya tashi zaune yana shakar kamshin da tabar mai,
Shigowa tayi dauke da tray, binta yayi da ido kur harta Ajiye akasan gadon kan small carpet, baice uffan ba, tace ” ga Abinci. ba tare da ta kalle shiba, “come here”. Yafada cikin bada umarni fuskar shi a hade, ta dago kai, kallon da yake aika mata kamar yana Amfani da igiya yana janyo ta ne, ba musu ta mike, remove that hijab. Ba musu ta cire tareda ninkewa ta juya ta Ajiye inda take Ajewa, duk yana binta da kallo wani irin nishadi yake jinshi a ciki a duk lokacin da suke tare, dawowa tayi zata koma kasa ya riko hannun ta tareda janyo ta ya dora kan kafar shi, ” kina wahalar da ni da yawa fa” Ya fada yana mai dora hancin shi a wuyan ta, kamshin ta mugun rikita shi yakeyi,
Nafita baki damu ba, nadawo kin nuna baki yi kewa ta ba, bayan rabin zuciya ta na nan tunfita na, Ina tunanin ki nadawo ba hug ba welcome back kiss umm why kike horani? Never mind gobe zakiga Amarya ta am getting married again. Yafada tare da dago idanun shi ya na kallon kwayar na ta idon domin yaga reaction dinta, Wanda Sai da taji zuciyar ta tayi wani irin tsalle kamar zata fito, kalmar ta caketa fiye da tunani, kallon are you serious? take mai, Wanda ya ganota domin yana karantar kowane movement dinta saboda ya gano ainihin meke ranta, ” am serious, am getting married, Salifa zan Aura gobe insha Allahu, ai badamuwa ko? Tunda kinga yanda Auren ki yazo ba shiri haka nata ma All this romance karki damu I can handle but for you. Wani irin zamewa tayi ta sauka kasa tareda fasa kuka mai karfi ba tare da ta shirya ba, jitakeyi idan batayi ba zuciyar ta zata fashe, zancen romance da wata, kwakwalwar ta bazata iya dauka ba,
Wani irin farin ciki yaji har kasan zuciyar shi, so he is right tafara jin shi a zuciya tunda har tafara bayyana kishin ta, Abun da yake kaunar gani a wurin ta, she dai yana so yaga kishinta akan shi wannan reaction din nata kawai yasa ya ji shi yana yawo a sararin samaniya saboda farin ciki, tuni zuciyar shi ta wanke fes ya sakko kasa kusa da ita zuciyar shi kamar Auduga fuskar shi kamar wata daren goma shabiyu,
Jikin ta ya shige tareda rungume ta gam a kirjin shi, yace you have the right baby cry for me, I want it, I love that, I need your jealousy, and only you have the right over Ibrahim, love me please love me. Dago fuskar ta yayi tareda dora bakinshi dai dai hawayen dake gangarowa yafara lashewa yana bata wani irin salo mai kashe jiki, tuni kukan ya dauke dif. Saida ya sude hawayen tas ya dora goshin shi saman fuskar ta, ” tell me meye matsalar? ” ba kya son inyi Auren ne? Daga kai tayi kai tsaye, ” why baby” ? ni banaso. Tafada tana tura baki, “ba akanki zata zauna ba ai”. You are going to touch her. Tafadi gaskiyar Abinda zai janyo mata ciwon zuciya, yanda yake romancing dinta ta ke jin dadi ba zata so ya yiwa wata ba. Wani irin mugun kishin shi taji tanaji fiyeda Wanda taji lokacin Auren Ahmed.

“To ai kishiyar kice Already nagani ba Fauziya bace”. Ture shi tayi ta mike kaje kayi ni ban hanaka ba ka Auro goma ma ba ruwana. Dariya yayi mai d’an sauti ta farin ciki, ya matso tareda fisgota ya rungume west dinta ya dora kanshi a kafadar ta, Hhhh admit it my diamond, kina kishina, kokarin ban bare hannun shi takeyi takasa, ” wait let have a deal with you”, Amarya ta is coming today or tomorrow, yanzu nayi Alkawarin if you give me chance, nasameki I will not touch her I promise you, yanzu Ina jiranki daga yau zuwa gobe bazan zo kusa dake ba if you are ready meet me Ina gefen mommy, and make sure you dress sexy. Ya dago tareda kashe mata ido ya bar part din, saida ya dauki duk Abinda yake so yafita ta bishi da kallo, zubewa tayi kan gadon tareda dafe kirjin ta,
Dole ta Amince wa zuciyar ta akwai soyayyar khaleel mai karfi data shigeta farat daya ba tare da ta shirya ba, son shi ya damki zuciyar ta gangar jikinta tana jin kishin shi fiyeda tunani, domin karatun da takeyi yasa ta gama gano cewa shima akwai sonta a zuciyar shi, yes bazata so ya kusanci wata ba Amma kuma tasan hukuncin ubangiji zai iya hawa kanshi, tana da ilimi tasan komai bazataso kanta dayawa ba Amma zatayi Abinda ya dace, zata bashi mamaki she is ready ta mallaki mijinta ta hanyar da takeso don haka zata dage ta cire kunya tabashi kulawar da ta dace, meye kunya a cikin Aure, bayan cikon addini ne sunnah ce ta manzon mu ( s.a.w )mai k’arfi, Ina koyarwar da yan uwa da kuma iyayen ta su kayi mata? Da kanta tabawa kanta shawara, don haka she is ready now. Aunty Raliya takira tareda tanbayar ta yanda zatayi da wasu magunguna da tabata. Dariya da farin ciki Aunty tayi tace ” Naziya mafarki na zai zamo gaskiya, domin na hango ki cikin farin ciki a gidan khaleel, na hango miki rayuwa mai cikeda nasara da kuma Albarka, kin gani ko haka Allah ya tsara, naji zancen Auren shi wurin zarah, don haka ki dage ki rike y’an cinki da martabarki, kinga kece ta biyu.. ” ai ita tafita dayar Aunty. Tafada kai tsaye. Toh Allah ya kyauta gaba nasan ayi haka, kuma ko yanzu kirike Allah ki rike Azkar ki kula da kanki gyara shine mace idan kikace bazaki gyara ba zaki zama bola a gidan mijin ki. Ta bata shawari masu Amfani da suka Kara mata kaimi da daura damara.

A ranar bata kuma ganin shiba har Washe gari, ko wayar shi bai kirata ba, tasan he is serious kuma zata nuna mai ita din mace ce mai dauke da nata irin Salon, Kwana tayi a internet tana koyan salo Kala Kala Wanda tayi Amfani da nata, da safe tana tashi ta tura mai text, “good morning husband, how was your night? Ta tura hade da Alamar hasken rana da kuma hoton teddy bear mai dauke da hoton zuciya.
A zaune ya Kwana a part din mommy yana aiki a computer tareda yin booking flight to bangkok shirin shi yakeyi sosai domin yanada tafiya agaban shi da ya kirkiro wadda zata zama da manufa biyu, yanayi Amma rabin zuciyar shi na wurin ta, yana a takure ne sosai Amma dole ya daure yayi wannan aikin in yana tare da ita ba uwar da zai tsinana sai lalubeta karshen ta yayi aika aika batareda ya shirya ba, don haka har Asuba idon shi biyu haka yake famar aikin shi, saida yayi sallah yaci gaba,
Sakon ta da yashigo ne yasa ya dauki wayar tashi duk da baisa rai daga ita bane, ware idanun shi yayi, yayi saurin budewa. Farin ciki ko ihu zaiyi saboda murna, sakon nata means a lot to him, ya karanta yafi sau Ashirin harda ture laptop dinshi yayi gefe ya kwanta yana runtse idanun shi, tareda dora wayar a kirjin shi. Saida ya dauki lokaci kafin ya daga ya fara mata reply, ” Hmmm morning wife, are you missing your husband touch?
Tana zaune tana jiran sakon shi ta kagu, taji shigowar text harda tashi zaune tayi ta bude, ba amsar da take so taji ba kenan taso taji yace mata yakasa bacci like her amma let go, ta mayar, ” I can’t help it”.
Wani irin buga kafa yayi, duk kalmar da tafito tanada muhimmanci a zuciyar shi,
“Me too I couldn’t sleep all night long.
Mayar mai tayi, ” then come back.
“Really? “Yes. Saurin kiran ta yayi, tayi dariya tareda picking, Ajiyar zuciya ya sauke yace ” are you serious baby?
” uhm. ” you know what am going to do if I come. “Is your right”. Tafada kai tsaye. “Really baby”? Yafada with so much excitement, Zaki sani in karya duk wani plan dina baby, ko yanzu tun text dinki na farko look at me, bafa ganin ki nayi ba am hard like rock, you are the only woman who can move the man in me, duk lokacin da na kusanto ki zanji inada cikakkiyar lafiya, do you feel the same baby? ” um um please stop it ina jin kunya zankashe. Tafada tana rufe fuskar ta kamar yana ganin ta, shy baby look ba kunya a rayuwar Aure kinga am frank so nake ki zama kamar ni idan bukata na kikeyi koda Ina office just give me a call and tell me, husband please come back it scratching me. Wani irin dariya yabata harta kyalkyace tareda rufe baki, he is funny wallahi, wani irin farin ciki ne ke bin zuciyar shi jin dariyar ta akaron farko, Alhamdulillah Yafada, “my diamond” tayi shiru domin sunan yana yimata dadi is she really a diamond? , yace ” stay happy always, yaja numfashi yana mika, ” please come to mommy side kinji am so so so honey bazan iya fitowa a hakaba ta cika wandon you can come.
“Da safen nan Mommy na nan inajin tsoro.” dodo ce ita kizo please kiga Abinda kikayi coursing Yafada yana mika tareda dafe jikinshi gam yana runtse idanun shi saboda zafi domin na yau daban ne.
Kashe wayar tayi ta nata saka da warwara, saida ta dauki lokaci ta mike, tafada wanka ta mulke in and out na jikinta da kamshi, ta samu wata Oman gowan mai shegen kyau da tsada kamar weeding gowan ta zura light brown taji adon dutsina kamar wata princess, Naziya akwai sirrin kyau da iya ado kuma duk shigar da tayi saita fito tayi kyau.
Kitchen dinta ta shiga ta samu madara mai dumi tasha domin batajin yunwa,
Batasan me yasa zuciyar ta ke ingizata zuwa gareshi ba, don’t blame her, domin khaleel ba irin mazan da zuciya ke iya jawa aji bace duk ego din Naziya ya hambarar cikin sauki, Wanda shi a gefen shi yasan ba zata zoba don haka juyi yayita yi kafin ya zabura ya iya watsa ruwa ya dawo dai dai, mommy ce cike da farin ciki ta turo kofar dakin nashi lokacin ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda green tana maiko sumar shi yake tajewa, fuskar ta a Washe tace d’an Albarka bazaka fadamin a nan ka Kwana ba? Aida tuntuni an kawo maka breakfast, yanzu zoka ci kaji. Tafada tana ajiyewa a kan gadon, ” good morning mommy. Yafada yana zama gefen ta, ya riko hannun ta, he love her but he hate her ways of thinking, takasa gano illar Auren da zatayi mai, saida yaci yagama tanata tsaro mai zancen Auren tareda cewa “nasan zaka dawo hanya ai don kaima kasan baka kyautawa rayuwar kaba khaleel duk fadin kano an san da arzikin ubanku tun yana raye bare yanzu da kuka Kara bunkasa kuka ginu ace baka Auren Y’ar da duk kano zata dauka asan yes kayi aure nima infita anuna ni ace ga surukar wane kuma uwar wane y’ay’an ka su fita a nuna su ace jikokin wani ne a garin kano ai shine farin ciki. Saida ta gama yasa tissue ya goge bakin shi ya juya dakyau ya kalleta ya riko hannun ta, ” Mommy na meye laifin Naziya? Tana da mugun haline? Gidan su ba tarbiya ne? “Talauci ne banaso kasani bankaunar hada iri da talaka shiyasa nafada maka karka sake ka hadomin jini da talauci. ” Hmmm mommy meye ribar Auren fauziya danayi? Meyasa kike so ki hadani da salifa? Mommy I don’t want to argue with you, banaso kice na bijire miki amma ni har a abroad nasha ganin ta tana yawon banzan ta,…. “Dakata, sunada kudi Ina kakeso ka gansu a Zaure da Almajirai ko suna kulle a gida bayan sunada Abinda zasu huta? ” mommy understand yarinyar nan gwara fauziya da ita you… “Quit Ibrahim Aure dai yau sai andaura kuma yau zata tare yau nake so ka shiga dakinta domin jikoki nake so daga tsatso mai daraja ba gidan malamai ba.
Mikewa yayi OK sai tazo tayi gadi tareda zaman jiran agama budar kai, ai al Ada ce mai muhimmanci dataja har yayana yabar duniya baisan dadin Aure ba. Ya dauki key ya fita abin shi, yabarta sake da baki, khaleel baya wani ganin girmanta take gani baisan mutuncin taba kamar Ahmed, “Allah ya jikanka yaron Albarka”. Tafada tana share hawayen kewar Ahmed tafita da kayan Abincin da yaci.

Yana fitowa tana fitowa cikin adon ta mai daukar hankali, tayi matukar tafiya da hankalin shi, saidai ganin mai gadi da masu aiki dake kai kawo yasa yaji wani irin mugun kishin ta tuni ya hade rai yayi saurin cewa ” go back, cikin kausa shashshiyar murya, mai cikeda umarni da tsantsar kishi, yayi saurin rufa mata baya, domin bata tsaya wata wata ba ta juyan saboda yanda fuskar shi ta juye kamar bashi bane dazu yake kwantar da murya a waya, a tsaye ya ganta ya doge daga nesa, ban lamunci ganin adon ki awaje da rana ba bayan kinsan akwai gardawan banza a ko Ina, wallahi zakija musu asara idan kika kuma fita batareda hijabi ba, ke ki nemo nikab kirika sawa if necessary sai kinfita da rana. Ya juya ranshi a bace, by the way, Ina ma zataje? Ya manta y’an da sukayi da ita a waya saboda kishi,
Yana tuki yana dukan sitiyarin motar shi, saida ya koma gefe ya faka motar ma ya kife kanshi, bai taba tunanin yanada zafin kishiba sai akanta, zuciyar shi har wani tsalle takeyi, kuma gashi dole ya fito da ita ayi mata passport, domin shi kadai yasan shirin shi, dukan iska yayi, Allah yagani bazai kawowa wani katon banza Matar shi ta tsaya yana kallon ta cikin camera ba zai iya shake shi, wayar shi ya ciro tareda kiran manager dinsu yace yaza’ayi asamu mace photographer tazo tayiwa madam a gida? Yace za’asamo mai yau, yayi Ajiyar zuciya tareda kiran ta, kamar jira takeyi dama tunfitar shi take dariya kishin shi ma dariya yabata domin tana tunanin bayau suka saba ganin taba a gidan, wani irin farin ciki takeji a zuciyar ta now she relax domin inda kishi da so, don haka tanaji a jikinta yana sonta domin Abinda yakeyi da ita yafi karfin wasiyyar d’an uwan shi, tanata tunanin moment dinsu dashi taji karar wayar da yabata, mikewa tayi da sauri ta dauka don shikadai ke kiranta da ita, picking tayi tareda yin shiru, saida yaja numfashi yace “am sorry for shouting at you diamond, kin tashi kishin da bansan ma dashi ba do you know, you look very pretty and beautiful? “Sorry ai kai kace inzo insame ka. Tafada cikin Y’ar shagwabar da batasan daga Ina tafito ba, “Hmmm really babe wurina zakizo Yafada jikin shi na rawa saboda farin ciki, yes dole inbi umarnin ka domin Aljannah ta na karkashin kafarka Ina gudun tsinuwar ubangiji.
Ajiyar zuciya yayi tareda hamdala, ba Abinda yafi ka Auri macen da ta ginu akan addini a rayuwa. ” am coming back home soon my diamond don’t change that dress please zanzo inkalla in more, and am Ina mana wani shiri ne zan d’an dade kadan kidafa min lunch ki jirani a gefen Mommy, bye. Ya katse wayar yana tayar da motar cikin sauri, domin tun baije inda yayi niyya ba jiyake kamar ya koma saboda ya shiga jikinta yayi yanda yake so, yanzu ne zai samu damar da yake mafarki akanta domin tagama sakin jiki dashi sosai, “babe am coming for you get ready. Yafada yana jin yanda jikin shi ya mugun motsawa saboda ya kwadai tu, “control madam you get in don’t worry yourself. Yafada yana murmushi mai cikeda farin cikin da baya iya boyuwa, ko office da yaje kowa mamakin sakewar shi da farin cikin shi yakeyi domin tun rasuwar d’an uwan shi basu kuma ganin fara’ar shiba, fara’ar shi sai yana tareda Naziya, ita din wata bangoce mai yaye mai dukkan damuwa batareda tasan da haka ba, da bata a rayuwar shi ya rasa Ahmed saiya susuce, Ahmed yayan shi ne ubane kuma bango mai muhimmanci, Wanda bai tashi rushewa ba saida ya gina mai Wanda zai jingina yaji sanyi, itace Naziya, haske ce wadda mommy ta kasa hangowa farin cikin yaranta biyu Wanda take wa kallon banza ita ba Y’ar kowa ba, Addu’a yakeyi just once mommy ta gano Naziya itace surukar kwarai,
Bayan sun gama wayar bata bata lokaci ba ta shiga cikin kitchen tareda zuba tagumi tana tunanin me zata dafamai da zata burge shi yau? Dariya tayi domin tasan me ta shirya a ranta, I will change you I will make you test our food our tradition today d’an China. Tafada tana dariya, don haka ta fara kokarin dora mai tuwon danyar shinkafa da kuma miyar taushe, lafiyayya, domin anzuba mata komai a gefen ta, tundaga kalolin namomi har zuwa kan kayan miya da duk wani Abun amfanin kitchen kamar part din Momy, don haka ta dage ta zage ta yimai lafiyayyan girki da yaji namomi ta kuma hadamai zobo domin ta lura yaji dadin shi ranar nan, cikin hour daya ta kammala ta zuba a new warmers masu kyau, sai tunanin yanda zatayi takai cikin gidan kamar yanda yace, zata jira shi first a nan har yazo ko zai Amince ya shigo cikin part din ta yazo yaci, tana gudun haduwar ta da Momy, batason cin mutuncin ta zagin da take mata yana mata ciwo a kullum don batada y’an da zatayi ne bata koyi yiwa babba rashin kunya ba kuma uwar miji dole ta kawar da idanun ta ta to she kunnen ta domin khaleel yana kokarin taka mata birki ba kamar Ahmed ba,

 

Momy nacan tayi busy sai taya kawayen ta takeyi ana tsara gefen salifa, jinta takeyi a cikin farin ciki yau, duk yanda zatayi ta raba khaleel da Naziya sai tayi, haka malanin su yabata tabbacin khaleel bazai taba kusantar Naziya ba muddin tabashi Abinda yabata ta zuba mai a Abinci, kuma tayi nasarar bashi yaci, don haka batada fargaba yanzu target dinta shine yanda zatasa ya kula salifa, saida suka gama tsara gefen y’an da sukeso kafin su koma gefen ta su baje suna tattaunawa itada su Zarah, “Aunty yanzu hankalinki ya kwanta ko? ” eh zarah ai ni nasan banda kanwa kamarki, jini nane banaso ya hadu dana talaka kuma Alhamdulillahi wannan malamin yamun komai. “Toh Aunty idan kika hana khaleel kusantar Naziya kinada tabbacin zai kula salifa? “Kibarni dashi aiba shi ya haifi kanshi ba, ni zansa yaje gareta. ” Aunty khaleel ba Ahmed bane kinsani. ” eh kinsan ya akayi ya A mince da zancen Auren salifar? Toh kiyimin shiru zakiga mai zai faru. Rungume ta tayi tana dariya ” yayi Auntyn mu na Y’ar da dake.

Yana hanyar shi ta komawa gida malam ya kirashi a waya, Wanda shine karon farko da yataba daga waya ya kirashi, yayi mamaki sosai saida ya faka ya kirashi back, suka gaisa cikin mutunci yace ” kazo gidana yanzu idan baka komai, muna tareda kawun ka yanzu haka. dafe goshi yayi ya manta ma da zancen Aure yasan kan maganar ne suke neman shi, don haka baida zabi haka ya burkita ya nufi hanyar gidan malam din,

A zaune suke cikeda Almajiran malam manya, ya parker daga nesa ya karasa Wanda kamshi da haibar shi kawai zaifada maka shi din wani ne, kawun shi na gefe suna magana, ya tsuguna ya gaida su kafin ya zauna a tabarma, kanshi akasa, “Alhamdulillahi Ibrahim yanzu muka dawo daga daura Auren ka, Wanda nayi kokarin kiranka tun lokacin Alhaji Muhammadu yace inbarka kanada uzuri, Toh yanzu dai nauyi ya hau wuyan ka, mata biyu, sai kayi kokarin kwatanta Adalci, Allah ya tayaka riko. Wani irin bugawa kirjin shi yayi tunda Malam yafara magana, Allah yagani ya tsani salifar nan fiyeda ma fauziya, Adalci Hmm. Yafada a ranshi, yanaji har sukayi suka gama doguwar nasihar su, kawun shi ya mike yace shi yatafi gida sai sunyi waya, Malam ya kalleshi yace ” Ibrahim me yasa ku matasa yanzu kuke sakaci akan Addu’a, bakwa neman tsarin ubangiji tareda kariya a tareda ku, bayan kunsan akwai makiya da mahassada atareda ku a kowane lokaci zasu iya kawo maku hari, karkayi wani tunani ba Abinda ya sameka kawai ka rike Azkar ka kuma dage da sallar dare, Allah ya Kara tsare ku yakuma bada zaman lafiya. “Amen yace kamar dole sukayi sallama
Yana wucewa malam ya Kira Amintattun Almajiran shi yace suzo zasuyimai sauka yanzu, ya tashi ya shiga cikin gidan yasa Inna ta girka musu Abinci mai yawa, harda kaji yasa aka Kama yace ayi miya,
Inna tasan Indai malam yayi irin hakan to karya sihiri zaiyi Wanda tasaba, kuma ba ruwanta da bincike aikinta kawai takeyi don haka ta dage ta tado Shukrah suka fara aikin su………. 🖊

Back to top button